Showing 63001 words to 66000 words out of 84782 words

Chapter 22 - FARAR WUTA 1 Complete Hausa novel

01 Apr 2025

10770

?arar wukar da Munaya ke amfani da ita daga can kitchen Win, da kuma nuryar Samirah da ta fita waje tana waya.
Ta sake haWiye wani yawun a makogwaronta.
"Ba komai na wanke ne kawai."
Sai ya kawo daya hannunsa yasa su duka biyu ya rike natan, sannan ya buWa ciwon sosai don yaga zurfinsa, zafin ya tafi har cikin kanta ta runtse idanunta da sauri tana cije lebbenta, sai yayi saurin sakin wajen sannan ya rufe yatsan nata da duka hannayensa biyu kafin yace.
"I'm sorry na duba ne na ga yadda yayi and it was deep." (kuma yayi zurfi.)
Ta buWe idanunta a hankali sannan ta Waga kai ba tare da tace komai ba, kuma bai saki hannunta nata ba sai ya cigaba da rike shi yana kallonta, hakan yasa ta Wago da idonta kalle shi da Wan ?aramin mamaki.
"Aikin me kuke yi haka?"
Ya tambaya tun kafin tayi wani tunanin, sai ta girgiza kanta.
"Abinci ne kawai."
"Kala-kala haka?"
Muryarsa ta sake fitowa da wani abu da ya shiga bin kowacce jijiya ta jikinta yana kassara ?arfinta, taji kamar wani yana zazzaga mata wani magani mai karfi ne da aka ha?i?ance zaiyi tasiri akanta, kuma a yadda tata muryar ta fito tana rawa, kamar dama anyi mata baki ne cewar hakan ne zai faru.
"Kace abokin ka zai zo."
"Ishaq?" Ya tambaya kai tsaye sai kuma ya sake cewa.
"Ya salam duka saboda shi kuke yin wannan aikin?"
Shi ko kadan unaninsa bai kawo masa cewa don Ishaq Win zai zo ya kamata ayi wani abu ba, duk da a baya ma idan zaiyi ba?i Ru?ayya kan shirya musu wani abun amma a yanzu ya riga ya manta da hakan kwata-kwata, saboda haka a lokaci guda zuciyarsa taji dadin hakan, sai kawsi ya gyada kansa yana kallonta sannan yace.
"Thank you."
Ta Waga kanta da sauri itama tana fatan hakan ne karshen zancen nasa, don bata san me zata zama ba idan har ya cigaba da magana rike da hannunta a hakan. Kuma kamar yaji fatanta, sai ya zare hannunsa nasa a hankali, taji Wuminsu yana barin fatarta.
"Zan nemo abu in rufe miki ciwon anjima insha Allah."
Da haka ya juya ya fita rike da robar ruwan a hannunsa.
A lokaci guda Amina taji kamar numfashinta yayi wata tafiya mai nisa ne sai a yanzu take iya zu?o shi, ssi kawai ta juya itama ta Wauko wata robar ruwan ta balle hancinta ta shiga sha yayin da bayanta ya jingina da drawers din store Win.
Sai da ta kusa shanyewa sannan ta tsaya, tasa bayan hannunta tana goge wanda ya zuba a gefen bakinta. Bata san me yake shirin fara damunta ba amma koma meye, so take ta tunawa kanta cewa duk abinda ke faruwa wannan gaske ne ba labari ba da komai zai tafi daidai, abubuwa ba zasu tafi kamar a mafarki tare da mutumin da daga shi har ita basu san juna ba sai bayan aurensu kuma har yanzu bsta san manufarsa akanta ba.
Ma'aruf ba zai taSa sauko da kansa haka akan ita Win da ba kowa ba, don ta sani cewa bayan matar daya aura Allah kadai ya san matan daya sani a a rayuwarsa ko ma wanda yake tare dasu a yanzu, to don me yasa hankalinsa zai tsaya akan ita din da ba kowa ba, ita Win da sa baiyane yake cewar ba sa'ar rayuwarsa bace.
Ta girgiza kanta tana kokarin rufe robar ruwan, wannan lokacin kamar zubar ruwa ne kawai kafin zuwan tsawa, kamar iska ce mai daWi kafin guguwa, sannan kamar kaWawar ruwan teku ne a hankali kafin ambaliyar sa, akwai wani abu dake jiran ta bayan wannan, kawai dai dan adam baya taba sanin lokacin da ?addara ko kuma wata masifar rayuwar ke zuwar masa ne.
Muryar Amma ta cikin mafarkin nan ta gifta a cikin kanta lokacin da take cewa
"Me yasa kika yarda ba zaki iya ba Amina..."
A hankali tayi ajiyar zuciya tana fatan Allah yasa koma meye ke shirin faruwa ta iya tunkararsa da ?afafunta a tsaye, daidai lokacin da a zahiri ta jiyo muryar Samirah ta shigo tana kiranta.
"A ina kika ajiye sugar?"
Sai kawai tayi sauri ta ?arasa goge bakinta sannan ta ajiye robar ruwan ta fita.
****
Karfe Bakwai daidai Ishaq ya iso, kuma Amina bata san me ya faru ba, don minti biyar bayan zuwansa sai ga sallamar Waya abokin Ma'aruf da shima ta riga ta haddace shi a waya mai suna Faruk.
Su uku kaWai suka cika falon da surutu kamar su biyar, kuma duk yadda take ganin Ma'aruf na da magana sai a lokacin taji nasa mai sauki ne, don kafin taji muryarsa taji tasu da yawa musamman Faruk Win, don shi yafi Ishaq yi mata magana sosai ma, har matarsa da ?a?ansa yayi alkawarin kawo mata tunda yace yanzun a sama kawai Ma'aruf ya kira shi yace masa yazo.
Kuma har lokacin da suka zo Win su Munaya basu tafi ba, Samirah dai taso tafiya amma sai Munayan tayi ta ro?onta akan su ?ara tsayawa tukunna, wani abu da ya ?ara bawa Amina mamaki don ita kanta ta san babu wani dalili Munayan ba zata yi ta cewa su tsaya ba. Ilai kuwa a lokacin da suka je kai musu abincin nan, a lokacin ta samu amsarta, saboda idon Ishaq na kan Munaya tunda suka shiga har ta juya Kitchen don ta Wauko wani abun, kuma zata rantse ma taga sanda suka yiwa junansu murmushi lokacin da take zuba masa lemo, Allah ya sani yau ta fara ganin Ishaq Win amma sai taji zuciyarta na jiyewa Munaya daWi idan har hasashenta akansu gaskiya ne, don duk inda nutsatsen namiji yake za'a saka Adam a wannan layin, kuma itama Munaya babu ruwanta da wani hargitsi sam.
Sun ji daWin tarbar da suka samu kwarai, don ba'a kalamansu kaWai ta fahimci hakan ba, har a fuskar Ma'aruf da kuma yanayin kallon da yake mata tun lokacin da taje ta sako wani dogon hijabi bayan shigowar su, wani abu da ita kanta taji ta kyauta da tayi hakan.
Bayan sallar isha'i ne sannan suka yi musu sallama suka fita, kuma sun daWe a waje suna magana don har bayan tafiyar Faruk Win shi da Ishaq suna nan, har su Munaya suka tafi ta ?arasa wanke iya kwanukan da aka Sata kasancewar basu tara wanke-wanken ko Waya ba dama a Wazu.
Kuma tana sallah lokacin da ta jiyo ?arar fitar motar Ishaq Win, sai dai har ta idar ta gama addu'o'in ta da komai bata ji lokacin da Ma'aruf ya shigo ba ko kuma don haka ta ?udirta a ranta cewa cikin gida ya shiga. Da wannan tunanin ta ninke sallayar tare da hijabin ta ajiye su a gefe, ta Wauko wayarta don kiran su Amma, sai dai daga layin nata har na Aminu bai shiga ba, kuma bata son kiran Baba a wannan daren, don haka ta bari zuwa gobe, ta nufi wardrobe Winta don ta Wauko kayan bacci, wata sabuwar doguwar riga ta dauko sannan ta dawo gaban gadon don ta canja.
?ankwalinta ta fara cirewa ta ajiye shi a kan gadon sannan ta shiga kokawa da zip Win rigarta, amma ga mamakinta saiya ri?e Sam yaki ko motsi, gashi ciwon hannunta ba zai bari ta rike shi da kyau ba, na dama kuma yaki ?arasawa can saman, dama tunda tazo saka kayan ta kula yana da matsala amma bata yi tunanin ta kai haka ba.
Har sai da hannunta ya ?age ta tsaya ta tattaro dukkan ?arfinta sannan ta cigaba da jansa, kafin a lokaci guda kamshin turaren Ma'aruf ya shiga hancinta.
***
A waje bayan Faruk ya tafi, sun dade a tsaye shi da Ishaq suna hirar tarin wasu abubuwan da suka shafe su wanda yawanci duk akan matsalolin dake baibaye da rayuwar Ma'aruf ne, sai kuma zancen Abdurrahim, ?anin Ma'aruf Win dake can New York wata makaranta ta Bebaye irinsa, (Rochester Institute of Technology.) Don Baffa ya gaya musu cewa saura watanni biyu kawai ya kammala ya dawo gida.
Bayan wannan sun tattauna zancen Hamida ma inda Ishaq yayi-yayi da Ma'aruf akan ya Wauko yarinyar daga inda ya kaita ya dawo ta ita cikinsu, amma ya Sata bakinsa a banza don ya riga ya rantse cewar Ru?ayya ba zata taSa sanin inda Hamida take ba sai ya kammala da al'amarinta gaba Waya, ko shekaranjiya da Mami taso yi masa zancen itama kai tsaye ya dakatar da ita ta hanyar gaya mata cewa lokacin da zai Wauko ta bai yi ba, don haka itama taja bakinta tayi shiru, don dukkaninsu sun sani cewar idan har ya furta abu, Baffa ne kawai zai iya sauke shi daga kansa, amma ko da suka yi magana da Baffan shima cewa yayi...
"Wannan zancen naku ne kai da mahaifiyar yarinyar Muhammad, duk abinda kuka yanke idan har ba kuskure bane mu namu addu'a ne tunda kune kuke da iko akanta fiye damu. Kuma kowannen ku yana da ikon da zai ri?e ta, duk da dai a matsayinta na mace an fi so ta zauna a gaban mahaifiyarta, amma idan har za'a samu matsala wajen tarbiyarta ko lafiyarta kamar yadda aka fara yanzu, to zamanta a wajen naka zai fi."
Wannan zancen na Baffa shi ya bashi ?warin gwiwar cigaba da shirin da yake da niyya wanda yake jiran lokacin kawai. Daga ?arshe kuma suka ?are da zancen ginin su wanda Ishaq Win ya gaya masa cewar ya samo wasu sababbin masu ginin da zasu fara aikin tunda Ma'aruf ya sallami waWancan.
Kuma baiyi mamaki ba da Ishaq Win baiyi masa zancen Amina ba, don ya riga ya fahimci cewa ba sai yayi Win bane, akwai wasu abubuwa da ba lallai sai sun furta su a tsakaninsu ba, wasu abubuwa ne da ?arara kowannensu ke ganewa idan Wayan yana ciki, don haka a yanzu ma Ishaq ya riga ya sani cewar ya riga ya yanke koma wane irin hukunci ne game da zamansu ba sai sun Sata lokaci wajen biya shi ba.
Da haka suka yi sallama, sabon maigadin da ya samo ya sake budewa Ishaq gate Win gidan, shi kuma ya koma ciki.
***
Yayi sakanni biyu tsaye daga bakin kofar yana kallon yadda take kokawa da zip Win rigarta kafin ta ankara dashi, watakila jikinta ne kawai ya bata cewar yana daga bakin kofar, don a lokaci guda ta juyo da sauri tana kallonsa, fararen idanunta suka zare akansa yayin da a lokaci guda ta saki hannayenta duka biyun suka sauka a gefenta.
"I'm sorry banyi sallama ba ko?"
Sai ta girgiza kanta.
"Babu komai ban ji lokacin da ka shigo bane."
Ya cije lebbensa tsaye a jingine kofar kafin yace.
"I'm sorry bana so in Wauki lokaci ne kiyi bacci."
Idanunsa na kallon fuskarta da yaga kamar tana ?o?arin kore wani abu wani abu mai kama da mamaki kafin ta tambaya.
"Wani abu kake so?"
Lokaci ne ya tsaya cak a cikin kansa da wannan tambayar yayin da fatar bakinsa ta bude kamar zai ce wani abu yana kallonta, tsakaninta da Allah ta fadi hakan ba tare da ta san tarin ma'anonin da za'a iya fitarwa daga kalaman nata ba, ganin tana cigaba da kallonsa yasa ya sake cije leSSensa na ?asa sannan ya girgiza mata kai.
"I want to treat your hand." (Hannunki zan duba.)
Ya faWa yana kallon yadda fuskarta ke nuna tarin yanayi kala-kala, ?afafunsa suka tako cikin Wakin a hankali zuwa inda take tsaye, kuma kamar a wani shiri sai iska ta buso daga windon da yake fuskantar su daidai lokacin da ya tsaya a gabanta, kuma bai Sata lokaci ba yasa hannunsa Waya ya Wauko nata mai ciwon nan.
GabaWaya tsawonta iya kafadarsa ne, gashin kanta da babu dankwali ya taso sama yana shaida laushinsa, da zai iya a wannan lokacin zai zare ribbon din data Waure shi ne don ya sauko kafadunta yaga iya tsawonsa, amma sai ya daurewa wannan tunanin ta hanyar kallon yatsun hannunta da yake ri?e dasu.
Ya san cewa shi mutum ne da yake ?arbar respe??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ct daga Wimbin mutane, kuma a iya kokarinsa yana kokarin ganin ya kyautatawa duk wanda ya shigo hanyarsa, da kuma kaffa-kaffa musamman a yanzu don ganin bai yi wani abu da zai iya cutar dasu ba, amma Allah ya sani bai taSa haWuwa da wanda a lokaci guda yaji zuciyarsa na tsoron ciwonsa akanta ba irin yarinyar nan, yarinyar da a baya bai damu da yadda zaiyi kokarin samun bayanin da yake so daga gare ta ba,
Wani bandeji ne mai haWe da audugarsa a jiki, don haka magani kawai ya Wiga a jiki daga cikin wata ?ar kwalba sannan ya rufe ciwon nata dashi, ai kuwa ta runtse idanunta a lokaci guda tana jin zafin na tafiya har tafin ?afarta.
"Zuwa safe zaki iya cirewa sai a saka wani, insha Allah a kwana biyu zai warke."
Ya faWa yana sakin hannun nata, kuma duk da zafin da take ji haka ta shiga daga kanta da sauri alamun ta fahimta.
Ya rufe maganin sannan ya wuce ta zuwa wajen da mudubin Wakin yake, ya ajiye roll Win plaster da kuma kwalbar maganin akai sannan ya juyo ya dawo inda take tsaye tana cigaba da danne ciwon.
Kuma bata yi wani tunani ba lokacin da ya tsaya a bayanta, dab da ita sosai, don haka da sauri ta juyo gabadaya ta kalle shi amma sai ya saka hannayensa duka biyu akan kafaWunta ya juyar da ita.
"Zan taimaka miki da zip Win ne..."
Ya faWa muryarsa na fitowa dab da kunnenta sosai, kuma kafin tayi ?okarin kamo tunaninta muryar tasa ta cigaba da cewa.
"Akwai abubuwa da yawa game dani a zuciyarki na sani, amma ina so a saman komai kisa a ranki cewar ba zan taba cutar dake ko in takurawa rayuwarki ba insha Allah."
Ya furta hakan yayin da hannunsa ya kai kan zip Win, sauran yatsunsa na Waya hannun suna taba fatar bayanta, sai kawai ta rufe idanun gabadaya tana ?o?arin saita numfashinta, kuma da ja Waya kawai hannunsa yayi ya sauke zip Win sai dai bai kai shi har ?asa ba, daga daidai tsakiya ya barshi, taji sanda yatsunsa suka dauke daga saman fatar ta, da kuma sanda yake matsawa, sai ta buWe idonta lokacin da ya zagayo daidai saitin ta.
"Nagode." Ba zata ba taSa iya tantance yanayin yadda muryar tata ta fito ba, ya gyaWa kansa.
"You are welcome, sai da safe."
Da haka ya juya ya nufi kofar Wakin yana rufo mata ita.
Sakan Waya, biyu, uku, suka wuce Amina tana ?o?arin saita numfashinta kafin a hankali ta Wauko rigar baccin nan ta karasa abinda zata yi, wanda har ta gama komai ta kashe fitilar Wakin kalamansa na yawo a cikin kanta.
...ba zan taba cutar dake ko in takurawa rayuwarki ba insha Allah.
Sai kawai ta rufe idanunta sannan ta dunkule jikinta akan gadon, kuma bata bawa zuciyarta wani damar tunani ba don bata san buhu nawa zata kwance na tambayoyin da bata da amsar su a zahiri dama cikin kanta ba.
Ya rabbi lakaal hamdu kam yanbaghi li jalaali wajhika wa adheemu sulWaanik.
Bakinta ya furta addu'ar hankali yayin da take jin ma'anar ta na tafiya har ?asan zuciyarta.
***
Washegari...
?arfe goma na safiyar Litinin, a irin wannan lokacin Amina ta saba da wani irin shiru don ko'ina tsit yake, duk wani mai fitar safe ya daWe da yin gaba, ?an makaranta da masu aiki da mafi yawanci sun fi yawa a kowanne gida.
Tana daga kitchen a lokacin tana ?o?arin fara aikinta ta tsinkayi ?arar ?wan?wasa kofar, mamaki ya Wan kamata don ta san babu wanda zata yi tunanin zuwansa a wannan lokacin, ta gyara zaman Wankwalinta yadda ta yafa shi sannan ta fito daga kitchen Win ta iso ?ofar falon kuma ba tare da tunanin komai ba ta buWe ta,a lokaci guda siffar Hajiya Kilishi dake tsaye ta shiga idonta tun kafin sakon saninta ya ?arasa ?wa?walwar ta.
Tana sanye da wata haWaddiyar lafaya ruwan makuba (maroon) da ta nannaWe ta tsaf a jikinta, fuskarta kamar kullum Wauke da wannan murmushin nata, murmushin dake haska annurin fuskarta a kodayaushe yana ?awata kammaninta.
Babu dalili Amina taji gabanta ya faWi amma tayi saurin kore hakan wajen yin nata murmushin itama.
"Sannu da zuwa Mami, barka da zuwa."
"Barkanmu dai Amarya. Yau dai na ajiye kyuiyata a gefe nazo ganin Wakin amarya."
Wani murmushin mai haWe da kunya Amina ta sake yi kafin tayi baya don bata hanya tana kara fadin 'Barka da zuwa', kuma kai tsaye kuwa ta shigo haWe da sallama yayin da ?amshin daddaWan turarenta ke rufo mata baya.
"Wa'alaikum salam."
Ta amsa sallamar tana rufe ?ofar har a lokacin da murmushi a fuskarta, murmushin da a lokaci guda ya Wauke sakamakon juyowar da Hajiya Kilishi tayi tun kafin ta kai tsakiyar falon tace.
"Idan akwai mu?ulli rufe ?ofar dashi Amina, akwai maganar da zamu yi ne."
Zuciyarta ce ta fara bugawa a kirjinta kafin ta juyo ta kalle ta, amma ganin murmushin dake kan fuskarta har yanzu, yasa itama ta dawo da wani dan guntu kan leSSenta sannan tace.
"Toh Mami."
Da haka ta rufe kofar tana ?o?arin gayawa zuciyarta cewa gabanta ba faWuwa yake ba sannan ta juyo ta ?araso ciki.
A lokacin ta zauna daga tsakiyar kujera mai cin mutum uku a falon don haka ita tameni waje daga Waya karshen ?aton carpet Win ta zauna tana fuskantar ta.
"Barka da Asuba Mami, fatan kun tashi lafiya?"
Ba kallonta take ba amma daga yanayin yadda muryarta ta fito wajen amsawa ta fahimci har yanzu murmushin take yi.
"Mun tashi lafiya, Ya bakunta kuma? Ko da yake ai naga su Samirah sun saka kin saba tuni."
Bata ce komai ba illa wasa da karshen skirt dinta da take yi tana cigaba da murmushin da zata kira na dole, don bata san me yasa zuciyarta ta kasa zama waje Waya ba.
Hajiya Kilishi ta kalli ?aton screen din Tvn dake tsakiyar falon dama sauran kayan kallon da aka jera akan hadadden stand Win Tvn da dubu tamanin da biyar ta bayar aka siyo shi sannan tace.
"Gidan shiru ke kaWai baki ko kunna Tv ba?"
Da wani murmushin a fuskarta tace.
"Ai ba'a hada Tvn ba har yanzu Mami."
Muryarta ta fito ?ar ?arama a cikin shirun dakin, kamar tana son ta shaidawa Hajiya Kilishin ?an?anta da kuma rauninta.
"Baku gaya min ba ai, gashi jiya kuwa yaro mai gyaran satelite ya shigo har cikin gida, da ya karaso ya hada muku, amma a bar ki a gida haka shiru, shi ya fice ya tafi hadaniyar gabansa ba zai tuna da wani sha'anin Tv ba.
Sai ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login