Showing 39001 words to 42000 words out of 84782 words

Chapter 14 - FARAR WUTA 1 Complete Hausa novel

01 Apr 2025

10755

tsakar gida kira, a cikin Wakin nasu ?anmata me fal da suka haWa da kusan duka ?awayen su na islamiyya da kuma na makarantar boko wanda duk a ?o?arin Fatima ne ta tattaro su, sannan ga su Ummi ma da tasu tawagar ?awayen, don haka Wakin ya cika taf sai faman hayaniya suke wadda ke sajewa cikin tarin ta gidan gaba Waya.
Don ko'ina a cike yake taf da mutane sai faman rabon abinci kawai ake, babu wanda yayi tunanin za'ayi wannan taron, Amma bata taba lissafa cewa yawan waWannan mutanen zasu taru ba, amma ance wai biki dama ba'a masa gayya da kansa yake fallasa kansa, musamman ga su Win da kusan duk wanda suka mu'amalanta yana jin daWin zama dasu.
A lokacin Maryam ta shigo Wakin ri?e da wani faranti da aka cika da ?ullin zobo. Ummi da tasha kwalliya cikin ankon atamfar nan tace.
"Yawwa Mary, matso ta nan, tun dazu dama Aunty Safiyya ke cewa mu jira a kawo."
"TaS! Wallahi na wannan ?awaye na ne suna can a dakin Aminu, plate nazo nema idan kun gama zan zuba gurasa."
"Au ba zaki bamu ba?"
"Waashi can fa ana ta Wiba a Wakin Amma, kuje ku Webo naku kafin ya ?are don wallahi har yaje rabi."
Ummi ta mi?e da sauri tace.
"Mu nawa ne a dakin?"
"Ai kawai je ki Webo ashirin, in ma da saura ma kara." Cewar wata a cikin ?awayen Aminan suna ?yal?yalewa da dariya gabaWayansu.
Ummi ta fita daidai lokacin da Fatima ta shigo rike da plate guda biyu na banWashen gurasar, Maryam kuma ta juya ganin ba zata samu abinda tazo nema ba.
"Wallahi kowa ya Wauke hannunsa kafin in ajiye." Cewar Fatiman ganin yadda kowannensu yayi shiri da hannunsa.
"Dalla malama ki ajiye kawai meye haka wai?" Cewar Shukra.
"Wallahi sai kowa ya Wauke hannunsa, salon ina ajiyewa in rasa."
Ta faWa tana dariya, yayin da hayaniyarsu ta ?aru kowa na fadin ta ajiye, ai kuwa tana dire farantin kafin ta mika nata hannun ta nemi gurasar ta rasa, sun wawushe ta tsaf suna ?yal?yala dariya, kuma yanayin fuskar Fatiman yasa Amina dake daga gefensu yin dariyar itama, lebbenta yayi talewar da har ha?oranta suka fito, don abu ne da ba yau suka saba ba, tun a makaranta sun saba irin wannan abin da an kawo abinci kawai wanda ya samu ya samu.
Kuma dariyar taji tana tafiya har ciki ?irjinta, tana taSo wani abu da ya kamata dama ace yana nan, wannan farin cikin da mace ke ji a lokacin aurenta.
A cikin hayaniyar da Wakin ya ?ara ruWewa dashi Aunty Ma'u tazo ta kira ta, tana fita taga Aminu ne yazo da mai hoto, aka shiga Waukar hoton kowa da ?ungiyarsa, Aminu na tsaye shine mai bada umarnin dake sa kowa yin dariya, don haka kusan duk a hotunan an Wauka ne Amina na dariya, tayi kyau a cikin kayan da suka zauna a jikinta sosai ga kuma skirt Win kayan daya buWe ta ?asa, ita kanta ta yarda cewa telan nasu Ummi ya iya Winki ba'a banza suke ta yabonsa ba, kuma a kowanne hoto ita idonka zai fara gani saboda shigar kayan nata farare tas da kuma ba?in gashinta daya fito ya haWu da ba?in ?unshin hannaye ta yana ?ara haska farin.
Hatta Amma tayi kyau cikin shigar wani lace da ya dace da maman Amarya, itama tana ta dariyar da har ta mantar da ita haushin da zuciyarta ke ciki game da kayan jere da suka kai aka ?i karba.
Ranar da su Tanti suka tafi za'a fara jeren nan, ranar zuciyarta ta sake yin ba?i game da al'amarin auren, don a waya Hajiya Kilishi ta kira tana gaya mata cewar ai su basu ce su kawo kaya ba, wai mahaifin yaron daya bada kudi ayi gyaran gida ya bayar har dana komai don haka su sun riga sun gama jeran su amarya kawai suke jira.
Sai da ?yar bayan Tanti ta dage cewar baza su kawo ?arsu haka ba sai da abinda zata kalla itama ta san cewar iyayenta ne suka yi mata kamar kowacce ?a, sannan Hajiya Kilishin tasa aka fitar da kayan gado guda daga wani Waki suka jera nasu, kayan Kitchen kuwa suka zube mata gabaWaya don shi dama abubuwan da aka ajiye basu da yawa, sai a sannan ne zuciyar Amman ta Wanyi sanyi, amma har a wayewar garin yau bata dawo dai-dai ba sai a yanzu da Aminu ya saka ta yin dariyar dole.
Kuma duk yadda bikin ya kai ga zuwa a gaSar da kowa ke ganin ba'a shirya ba, yayi mutu?ar yin daWin da wata?ila ko da sun shekara ne suna tanadi haka komai zai kasance, banbancin kawai na farin cikin da za'a samu a zuciyoyinsu ne.
Wajen yamma, Adam ya kawowa Amina sa?on wata sallaya mai kyau da kuma al?ur'ani daga Abdallah, a hannayenta Amina ta rungume ledar ba tare da tace komai ba, idanunsa kawai take hangowa a ranar da ta gaya masa aure zata yi, yana kallonta da yanayin da bata iya fassara shi ba.
"Dama na gaya miki, ba wani son ki yake yi har cikin zuciyarsa ba."
Haka Fatima tace lokacin da ta gaya mata yadda suka yi, amma sai ta girgiza kanta ta bata amsa.
"Cewa yayi dama ya sani ba lallai ya iya aurena bane Fati, yace ya san ba lallai ni ko iyayena mu iya jurewa tazarar dake tsakani na dashi ba."
Da yamma Fatima dasu Ummi suka sa ta canja zuwa wani material kalar ruwan madara, a lokacin kuma kusan duka ?awayen nasu na nesa sun tafi sai mutum uku kawai da kuma wasu daga cikin ?awayen su Ummi, kalar kayan ta ?ara fito da hasken fararen idanunta, suka saje sosai cikin wani Wauri mai kyau da Momi ta sake yi mata.
"Kece amarya ta farko a wannan lokacin da naga anyi bikinta bata yi make-up ba Amina, Allah ya shirya miki halinki."
Cewar Momin sanda take Waura mata Wankwalin, sai kawai tayi wani murmushi tana kallon ?unshin hannunta yayin da wata ?awarsu ta ke cewa.
"Amma kuma tayi kyan da wasu amaren ma da yawa basu yi ba, kin san natural look ?arshe ne."
Da haka sai hirar Wakin ta koma kan kwalliya, kowa na faWin ko a kwalliya simple make-up tafi kyau, wasu kuma na lissafo masu kwalliyar da ko heavy make-up Win suka yi tana yin kyau. Ta sani itama da aurenta bai zo a karkace ba zata yi kwalliyar, amma babu kalar tanadin data shiryawa wannan, ?unshin ma don su Momi sun takura ne kuma ta san shine abinda kowa zai fara lura dashi akanta.
"Dama da kika haWa kayanki baki Webi waWancan litattafan ba?"
Fatima ta tambaya daga gefenta sanda idonta ya kai kan wani kwali a can saman durowarsu na litattafan makarantar ta, litattafan da ta san ba zata taba rabo dasu ba, don kullum cikin bitarsu take yi.
"Maryam ce ma ta haWa kayan ai, ni ban san me da me ta haWaba, kawai dai tace min ta hada su ne tare da sauran kayan akwatunan."
"Allah yasa dai bata haWa miki da kayan sawa da yawa ba, don yawa zasu yi miki idan aka hada da sababbin, gwara ita a ta Wan ?ara akan nata. Ina ledar su sallayar da aka kawo, bari na haWa na kaisu kusa da akwatunan, kar a manta."
Fatiman ta faWa tana ?okarin mi?ewa, sai dai kafin ta kai ga mi?ewar Amina ta jawo hannunta da sauri, ta juyo ta kalle ta, idanunta sun kaWa daga farinsu ta girgiza mata kai.
"Ki zauna kawai Fatee, ki bari ko anjima sai ki Wauko su."
Muryarta da kaWan tafi kuka, kukan dake kwance a ?irjinta tun bayan Waurin auren da su Kawu Mallam suka kirata soro bayan dawowarsu, Kawu mallam Win ya dan?a mata sadakinta dubu Wari a hannunta, da kuma bayan tafiyarsu da ?anuwansu na Niger suka ?araso suna faWin angon bai je ba... Kalaman da suka sata tambayar me yasa take yaudarar kanta ne? da kansa yazo har nan ya gargaWe ta tun kafin komai yayi nisa don haka don ya fara nuna mata bala'in da ta kawo kanta cikinsa hakan ba komai bane.
Har bayan sallar magariba gidan nasu a cike yake, koina yayi kaca-kaca da ruwa da kuma abincin da aka zuzzubar, sannan ga tarin wanke-wanke fal a gefe, don haka ana idar da sallar magaribar ?anuwansu na Niger suka fara aiki kotaina, Allah ya taimaka da wutar Nepa don haka akwai haske koina.
A lokacin ne kuma motocin Waukar amarya suka hallara!
***
A cikin motar dake tafiya kan titin Lamido cresent, Wan karamin mayafin da Ru?ayya ta yafa akan doguwar rigarta ya zame ya sauka kan kafaWunta, gashin kanta ba?i sidik da ya haWu dana ?arin data nannaWe cikin bun ya fito ta cikin hasken street lights da kuma na fitilar motar ?an sandan dake jiniya a bayansu, amma bata damu ba, hannayenta na rawa ne yayin da take kokarin sake kiran layin mahaifiyarta daya katse saboda rashin service yanzu da suke magana.
Ta samu kiran ya shiga a lokacin da muryar Ashraf dake tu?a motar da kuma ta abokinsa Bilal da suke kira da B-man ta shiga kunnenta. Ashraf Win ne ke tambayar abokin nasa idan har lambar wayar da suke jira an turo masa, amma a gajarce kawai ya bashi amsa yana girgiza kai.
"Ina jin ki Ru?ayya kuna ina?" Muryar mahaifiyar tata ta shiga kunnenta daga cikin wayar.
Sai a lokacin ta jawo mayafin ta sake rufe kanta sannan tace.
"Maamah muna hanya, mun Wauko Bilal Win yanzu zamu tafi can sabon garin, su Ibrahim ma sun je sun taho da police Win suna bin mu a baya,? muna jira ne yanzu a turo masa da number wanda ya sani a gidan don a tabbatar idan tana nan."
Daga cikin wayar Hajiya Nafisa tace.
"Ko bata nan ku ?arasa ku sami iyayenta ko kuma duk wani wanda zai iya baku bayani akanta, duk abinda ake ciki da kun isa you let me know, yanzu zan kira Daddy in gaya masa."
Ta gyaWa kanta kafin kiran ya katse, idanunta na tafiya kan abokin Ashraf Win dake danna wayarsa hankali a kwance, tsawon kwanaki kenan suna nemansa amma ba'a same shi ko a waya ba sai a yau da da wanin abokin Ashraf Win ya kira cewar gashi nan ya dawo daga Ondo, don haka ba shiri suka taho har wajen da aka kwatanta musu yana nan, kuma cikin sa'a suka same shi. Amma don rashin mutunci irin nasa bai fito ya same su ba sai da suka yi kusan awa guda suna jiransa, har su Ibrahim da Ahmad da suka je suka taho da police Win da aka kai report wajensu, sannan ne ya fito da uzurin cewar wasu abubuwan yake kammalawa da baza su iya jira ba.
Kuma duk da irin tashin hankalin da yaji suna ciki da kuma ma babban labari na Satan Wan mutum guda, bai nuna ko a jikinsa ba bayan Allah ya sawwake guda din da ya furta. Ta sani cewa shi kansa Ashraf Win yaji haushi amma bai nuna bane saboda abu suke nema daga wajensa dole sune a ?asa, amma duk da haka ta fahimci cewa akwai wani abu ne da ya faru da babu wannan kalmar ta abota a yanzu tsakaninsu.
Sai dai ba wannan ne a gabanta ba yanzu, a cikin kwanakin da suka gabata, zuciyarta ta mutu ta mi?e fiye da ?irgan mai ?irga, ?arya ne ta iya kwatanta tashin hankalin da take ciki, tashi hankalin da sai da ya shafi kowa a gidan nasu gabaWaya, ya zamana ba abinda ake yi banda fafutukar neman Mary ko ta wacce hanya amma basu same tan ba, hatta mahaifinta dake can ?asar Romania yana aikinsa kullum? sai yayi waya tsakaninsa dasu da kuma ?ansanda akan abinda ake ciki.
Idanunta kaWai idan ka kalla sune shaidar rashin baccin da kuma na abincin da take ciki. Ta rantse a ranta fiye da sau shurin masaki cewar Mary zata gwammace bata zo duniya ba idan har suka kama ta, tunaninta baya iya lissafa abinda ya kamata tasa ayi mata.
Sun isa cikin unguwar ta sabon gari a lokacin da duhu ya riga yayi sosai, a lokacin kuma gabanta ya shiga faWuwa cike da tsananin tsoro ganin irin cakuWaWWun layikan da suke wucewa da kuma mutanen cikinsu, zata yi rantsuwa ba adadi cewa Mary ba zata taSa rabarsu ba inda ta san daga waje irin wannan take fitowa, amma a haka ta zauna tana kula da ?arta tsawon watanni bakwai.
Kwatancen Bilal ya kai su har wai takurarren gidan da mutane ke ta fitowa daga ciki kamar gidan tururuwa, bata san lokacin da ta dun?ule ?arshen mayafinta akan bakinta ba yayin da kwall??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a ta shiga fitowa daga idanunta da suka riga suka kaWa, zuciyarta bata iya kwatanta mata cewa Hamida tana wannan wurin ko kaWan.
Ibrahim da Ahmad da suka fito daga motarsu bayan sun tsaya suka bada shawarar cewa ta tsaya su suka shiga ciki, amma jikinta na rawa ta girgiza musu kai, ruhinta zai bisu ciki ne ko da ta tsaya Win.
Ashraf da Ahmad ne suka fara shigewa gaba sai Bilal da kuma Ahmad, ita tana daga bayansu sai kuma ?ansanda biyar dake rufa musu baya, warin iskar gidan ta fara sha?a kafin ta fahimci girman da yake dashi daga ciki,? ga tarin ?ofofi birjik daga kowanne gefe inda hayaniya ke fitowa kamar zata fasa kunne.
Kuma ganin ?an sandan yasa hayaniyar gidan ta ?aru har da masu ihu suna shigewa Wakunansu, a tsakar gidan su Ashraf da kuma ?ansandan suka shiga tambayar cewa Mary suke nema, kuma wasu ?attin inyamurai da su kaWai suka tsaya suka shaida musu cewar Maryn dake gidan sun fi mutum ashirin.
Koina a jikin Rukayya kawai rawa yake yayin da take kallon ?ofofin Wakunan da dukkan fatanta na duniya, da ?yar da kwatance aka samu wani a cikinsu ya gane wadda suke nema, kuma kai tsaye suka shaida musu cewa kwana biyu da suka wuce Maryn tare da iyayenta suka kwashe kayansu tsaf! suka tafi garin su.
Sai da ?yar ?an sandan nan suka samu mutanen nan suka fito musu da wani tsoho da akace Wanuwansu ne. Kuma shima ganin ?an sandan ya ruWa shi, ya dinga rantsuwa bai san komai ba sai da yaga da gaske ana shirin tafiya dashi sannan yayi bayani cewar ya san yarinyar da ake neman, kuma har da ita a dalilin barin su Mary garin bayan ciwon mahaifiyarsu.
Ru?ayya gabansa taje ta tsugunna a lokacin yayin da yake bayani da gurSataciyar hausarsa.
"Wani mutum ne anan yazo ya dauki yarinyar ya tafi dashi, kuma Mary yace ya bawa yarinya maganin bacci mutumin zai kamata, kuma the madam she's serving zai ce ta Satar da yarinya, ita bata san yadda zata yi ba, don haka sun kwashe kaya nasu sun tafi."
"Shi mutumin da yazo ya tafi da yarinyar waye shi?" Wani daga cikin Wansandan ya tambaya tsaye akansa.
"Mary yace shine oga na inda babanshi Mr. Okafor yake aiki."
"Ka san wajen aikin nasa?"
Ya Wago cike da tsoro yana kallon Wan sandan.
"Ka san wajen da baban nata yake aiki?"
Wannan karon Ru?ayya ce ta tambaya, muryarta na rawa da dukkan fatan na cewar amsar da zai bayar ta kasance abinda take son ji, kuma cikin abinda zata iya kira da sa'a, sai ya daga kansa yace.
"Eh ya sani, wajen inda ana..."
Bai karasa ba Wan sandan ya bashi umarnin tashi su tafi, jikinsa na rawa ya mi?e tsaye ya shige gaba, aka sanya shi a motar ?an sandan bayan sun fita, suka fara yin gaba sannan su kuma suka shiga nasu motocin suka bi su.
Wannan karon Ibrahim ya shigo motarsu ya zauna a wajen Bilal da shi ya koma motar Ahmad, tana ji kowannensu na waya, Ashraf da matarsa yana gaya mata inda suke, Ibrahim Win kuma da Daddy yana yi masa bayanin abinda ya faru.
Fuskarta ta juya waje idanunta na bin fitulun kan titi ke haskawa akan gilashin da kuma fuskarta, hawaye take sharewa da gefen mayafinta yayin da hannyenta ke rawa kamar zuciyarta, bata iya hango yadda zata kasance idan har bata sami Hamida a wajen nan ba.
Sun iso daidai gaban wani dogon gini mai Wauke da gilasaivda kuma fitulu kamar rana, akwai manya-manyan rubutu a sama wanda bata iya karantawa ba saboda halin da take ciki da kuma ?wallar da ta taru a idanunta. Ashraf da ya tsayar da motar ya juyo ya kalle ta, kuma ganin yadda take share hawaye yasa ya girgiza kansa yace.
"Stay inside, bari muje mu gani."
Da haka ya buWe ?ofar motar ya fita, Ibrahim na bin bayansa.
Sai kawai ta kifa kanta akan cinyoyinta ta shiga rera kukan da take kasancewa a cikinsa duk dare, gani take idan har ta rasa Hamida rayuwarta ta gama rushewa gaba Waya, ba lallai ne ta samu fatan da dashi take ganin zai sake gina rayuwarta ba.
Don samun Ma'aruf shine ?arshen fatanta? yanzu a duniya, bata hango komai a gabanta sama dashi, wani gefe na zuciyarta na jin cewa zata iya hakura da Hamidar ma idan har rayuwa zata iya dawo mata da Ma'aruf ta wata hanyar, amma ta san daga shi har iyayenta babu mai sake kallonta idan babu yarinyar, don haka ba zata taSa rasa ta ba.
Wayarta tayi ?ara a lokacin daga gefenta, ta kalli screen Win tana karanta sunan Jawad da ya fito tar! akai, tun da ta barshi a hotel Win nan bata ?ara bi ta kansa ba, ya kira wayarta sau da yawa bata Waga ba, a jiya da yamma har gidansu yazo amma ta aika masa da sa?on ba zata iya fitowa ba, tana kallonsa ta tagar Wakinta ya juya da motarsa ya fita.
"Babe I'm really sorry, ki manta maganar da na gaya miki dan Allah, just talk to me!"
Sak?on message Winsa bayan katsewar kiran ya nuna akan wayar, sai kawai ta Wauke kanta tana kallon waje, bata lissafa Jawad a cikin matsalolinta na rayuwa ko kaWan.
Ta kalli wajen daidai lokacin da idonta ya kai kan su Ashraf da ?an sandan nan, magana suke da wasu mutane a ?ofar wajen basu shiga ciki ba, kuma ta cikin hasken fitulun wajen taga Ibrahim ya dafo kansa ta baya tare da ri?e ?ugunsa alamun wani abu ake gaya musu da ya sa shi mamaki don ta hango mutanen na magana.
Ta hango Ashraf daga gefen tsohon da ya rako su yana sauraren mutumin kafin ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login