Showing 48001 words to 51000 words out of 84782 words

Chapter 17 - FARAR WUTA 1 Complete Hausa novel

01 Apr 2025

10771

da Hafsa dasu Mimi da Fatima da wasu daga cikin ?a?an Baban kurna, su takwas, sun riko wasu sauran tarkacenta da tsintsiyoyin nan... Ranta ya karasa yin fari ?al ta hau rungume su daya bayan daya tana murna, rungume sun da bata san tayi ba sai da taji Fatima na cewa.
"A ina kika koyo wannan sabuwar gaisuwar kuma?"
Ita kaWai ta cije lebbenta tana murmushi.
**
A cikin Wakin Hajiya Kilishi, ta kalli kawarta Salamatu tana girgiza kai.
"Banbanci na dake kenan, bana faWuwa na hakura, a sannu nake bin abu ina gutsira har in kai ga ci, kuma nasha gaya miki hakurin da kika kasa a tare da Shamsu (mijinta) kenan. Shi yasa har rayuwa ta kawo ki wannan gaSar."
Hajiya Salamatun ta girgiza kanta itama.
"GaSar da nake cin duniya ta da tsinke ba, kar ki kawo wannan zancen kuma bayan mun gama na Saratu, mu tattauna abinda ya kawo ni, Ya zaki yi da al'amarin ?ar tasa?"
Hajiya kilishi ta kalle ta sosai tace.
"Na gaya miki ai, saboda ban samu nasara akanta a asibitin nan ba hakan baya nufin na hakura, ai na rantse sai naga bayanta don ko wajen uw*rta ba zan bari ta koma ba tunda har zata fara zame min ?alubale tun daga yanzu. Babu wanda ya isa ya shiga zuciyar Ma'aruf da tasirin da yafi nawa Salamatu kema kin sani.
Saboda haka matsalolin nawa zan hade guri guda, bayan tsinannun asibitin nan da suka hana ni kwana a wajenta sun sallame ta, wani Creche wai ya kaita a hanyar Bompai saboda kin san muna cikin sha'anin bikin nan. Saboda haka a yanzu da komai ya lafa zan saka ne ya dawo da yarinyar wajen ita Aminar, ta yadda zan aiwatar da manufata hankali a kwance.
Kin san dai dalilin da yasa na shiga na fita ya auri yarinyar nan, saboda daga ita har iyayenta zan iya juya su sannan an tabbatar min tana da sanyi halin da al'ummar gidan nan kaf zasu karbe ta cikin ?ankanin lokaci, na gaya miki tana da irin fuskata Salamatu, fuskar da zata daWe tana yin abun da ba mai iya Wora zarginsa akanta."
Hajiya Salamatu ta kalle ta tsawon wasu sakanni tana nazarin maganganunta kafin ta girgiza kanta tace.
"Kin san nice mai gano miki da matsalar dake ba kya taba hangenta Kilishi, jiya da suka kawo yarinyar nan banga fuskarta ba, amma daga yanayin jikinta kawai na san ?arama ce, kuma idan har halinta ne zai sa jama'ar gidan nan su sota, ba kya tunanin zuciyar yaron ma zata iya ta karkata kanta?"
Hajiya Kilishi ta gyaWa kai tana murmushi.
"DaWina dake ragon azanci Salamatu, ai dama haka nake so, in ba haka ba don me nake ta koWa ta da ?anuwanta a wajensa, so nake ta siye min zuciyar kowa har shi Win kamar yadda nima nayi, ta yadda a nutse zan sa ta dinga kai min sa?ona kowacce kusurwa babu mai zarginta."
Hajiya Salamatu ta sake girgiza kanta.
"Baki gane ba Kilishi, abinda nake nufi shine idan har ta siye zuciyar Ma'aruf da darajar da zata fi taki nauyi fa? Idan har yayi nisa a duniyarta ta yadda ba zai iya jiyo ko da muryarki ba fa?"
Wannan karon dariyar da Kilishi tayi sai da ta ratsa kowanne bango a dakin ta kuma fita ta windon Wakin da yake a rufe, tabi iska zuwa nisan da ?arfin amonta zai iya kaiwa, hatta jikinta sai da ya girgiza saboda nauyin dariyar, kafin ta kalle ta sosai tace.
"Ita kanta yarinyar ai na shirya mata Salamatu, sau nawa zan gaya miki ne Ma'aruf nawa ne ni kadai?!"
***
Tafiyar ta fara! Insha Allah.
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
BABI NA GOMA.
Ina mai baku hakuri, an samu jinkirin wannan babin ne saboda rasuwa da aka yi min ba a gari ba don haka har tafiya sai da ta kama ni zuwa can... Ina rokon ku taya ni addu'ar Allah ya jikanta ya gafarta mata.
Sannan duk a cikin kwanakin nan mun rasa Abdallah ma, Wan gidan Sanah S. Matazu editar Fikra, ina rokon Allah ubangiji ya bata hakurin rashinbsa yasa mataryin can ne, sannan ina yiwa duk wanda ya rasa wani nasa ma addu'a, mutuwa na taSa mu a bangarorin da bamu san muna dasu ba, Allah yaji ?an wadanda muka rasa mu kuma ya kyautata namu zuwan.
Ameen ya Allah.
~~~~~~~
We should talk.?
? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? - Unknown
**
"Maamah don me yasa zai kira shi? Nace ya kira shi ne? Me yasa zai yi deciding abinda bai shafe shi ba kai tsaye?"
Muryar Ru?ayya ta fito da ?arfi a lokacin da take kallon ?aninta Ahmad dake tsaye a gaban gadon da take kwance. A cikin asibitin da aka kwantar da ita ne, tun bayan lokacin data faWi take asibitin ba'a sallame ta ba sakamakon hawan da jininta ke tayi babu sauka, don hatta fuskarta da kafafunta dukkansu a kumbure suke suntum.
"To hell with you and him! Shi waye da baza'a kira shi a gaya masa yayi ba daidai ba? Me yasa akan Ma'aruf ?wa?walwar ki ba zata taba hankali bane Rukayya? Meye a duniyar nan ki gani a jikinsa da sauran maza badu dashi? I swear to God idan kika kara daga min murya a yanzu zan sake kiranshi na zage shi a gaban idanunki."
"Maamah kina jinsa ko? Kina jin abinda yake faWa?!"
Ta faWa tana juyawa wajen mahaifiyarsu Hajiya Nafisa dake zaune daga gefe tana haWa mata tea, idan da sabo ta saba da wannan fada a tsakaninsu, don ko Ashraf da yake sakon Rukayyan basa faWa tare kamar yadda suke yi da Ahmad Win, shi mutum ne kaifi Waya mai tsatsatsauran ra'ayi, Rukayya kuma ba'a taka ta tayi shiru, don haka inuwarsu bata taSa zama Waya.
A yanzu ma dalilin Waga jijiyoyin wuyan nasu, Ahmad Win ne ya zo ne yana shaida musu cewa shi ya sake kiran Ma'aruf akan zancen Hamida, tunda sunyi magana da Ashraf yace zai tuntube su kuma bai sake cewa dasu komai ba, don haka shi ya kira shi da Sacin ran hakan wanda a ?arshe wayar tasu bata ?are da daWi ba, don Ma'aruf Win har gargadi ya masa da cewar labarin zai canja idan har ya sake kiransa.
Ita kanta bata ga aibu a abinda Ahmad Win yayi ba, don Allah ya sani idan da Ru?ayya zata bata dama a lokaci guda ne zasu juya dukkan tanadin da suke mata akan Ma'aruf ita da kawarta zuwa sharri, zata fi jin karfin gwiwar cutar dashi akan abinda suke yi a yanzu, don haka ta cigaba da haWa mata shayin kawai tana jinsu, tana ji kamar Ahmad na furta rabin kalaman dake cikin ranta ne da ba zata iya faWawa Rukayyan ita da kanta ba.
Kuma sai da taji kalaman nasa na shirin yin tsauri da yawa sannan ta kalle shi tace.
"Ahmad, fita daga wajen nan."
System Winsa da ya ajiye akan Fridge din Wakin bayan shigowarsa ya Wauka cike da fushi sannan ya nuna Rukayyan da Wan yatsa tace,
"Daga yau kar ki sake kirana a matsayin danuwanki duk sanda wani abu ya haWa da mutumin nan, idan ba haka ba daga ke har shi I'm gonna rip your as* off! (Zaku gane kuranku!)"
Da haka ya fice tana bugo ?afar Wakin asibitin, Rukkaya ta koma da baya ta rufe fuskarta da duka tafukan hannayenta biyu lokacin da Hajiya Nafisan ke mi?o mata kofin shayin.
"Kin san halinsa ai sarai, amma kika biye masa kuke Waga murya a cikin asibiti, na sha gaya miki da kin ga ransa ya Saci kawai ki rabu dashi, wannan shine girman."
Ta girgiza kanta a hankali sannan ta buWe fuskar tana karbar kofin.
"Maamah ba zan iya shiru akan abinda yake fada ba, kina ji?fa yace har gargadi Ma'aruf yayi masa, to waye ya san iyakar abinda ya gaya masa ma? me yasa zai sake Sata min al'amura ya sake Sallo wani abu kuma?"
Ta ?arasa tana karSar shayin, kuma garWin abubuwan da aka cika masa da kuma Wuminsa ya sauka har cikin ?irjinta, ya sanya ta lumshe idanuwanta a hankali kafin ta buWe su sosai akan kofin, da Waya hannun nata shiga murza bakinsa a hankali ba tare da ta kalli Mahaifiyar tata ba tace.
"Maamah kince kawai aura masa yarinyar akayi ko?"
Taji sanda Hajiya Nafisan tayi ajiyar zuciya kafin tace.
"Tabbatar min akayi cewa a cikin sati uku akayi komai, ance bai taba ganinta ba ma har aka daura auren, sannan yarinyar bata da wani daraja, mahaifinta ance irin sana'ar ?ananun aikin katakon nan yake yi, don haka na tabbatar miki akwai wata manufa ta daban dangane da auren nan da bamu sani ba, amma ba wai aure yayi irin wanda kika sani ba."
Wannan karon Ru?ayya rufe idanuwanta tayi duka, tana jin yadda wani tiririn zafi na daban da yafi karfin shayin dake hannunta yana cigaba da zurara a cikin ?irjinta yana kona duk inda ya bi.
"Nima na sani ba auren gaske bane Mami, don wallahi na san babu ta yadda za'ayi yarinyar nan ta shigo cikin tsarinsa, a yanayin arzikinsa dana gidansu ko haukacewa yayi akwai ?anmatan sa suka fita daraja da yawa da zasu so shi a haka."
Shi yasa bana son inyi wasa da kowacce irin dama Mami, a yanzu ban damu da duk hanyar da zamu bi mu lalata komai ba, don ban damu da manufar kowa ba, burina kawai kada yarinyar nan ta daWe a rayuwar Ma'aruf, don ta haka ne kawai zan iya cimma burina Maamah, idan akwai ta, na sani ba zan taSa iya samun abinda nake so ba."
Kafin Hajiya Nafisan dake kallonta tace wani abu, ?arar ringtone Win wayarta ya cika Wakin, don haka ta dauko wayar tata dake gefen bedside drawer ta miko mata, Ru?ayya ta karba tana kallon sunan da ya fito akan screen Win, Jawad... Taji ranta ya ?ara dugunzuma ya Saci a take, bata san wane irin mutum ne shi marar zuciya haka ba? Me yasa zai cigaba da damunta alhali da kowanne yare da zai iya fahimta ta gaya masa cewa ya rabu da ita? Sai kawai ta danne buttton Win wayar gabaWaya ta kashe ta sannan ta ajiye ta a gefe.
Takaicin dake cike fal da tausayin ?ar tata ya nuna akan fuskar Hajiya Nafisa kafin ta girgiza kanta a hankali.
"Na gaya miki ki kwantar da hankalinki ki samu sau?i mu koma ki gida, don Hajiya Saude?ta gaya min sai da haWin kanki tukunna sannan komai zai daidaita, nayi miki al?awarin Ma'aruf da ?afarsa zai tako har inda kike ya neme ki."
Wani abu kamar murnushi ya fito kan lebben Ru?ayyan yayin da ta sake jingina kanta baya da jikin gadon kafin a hankali kuma ta Wago da kofin shayin nan ta kai bakinta.
Daga can jihar Abuja, a cikin gidan rawar da Jawad yake a can sama, inda yaken wani lungu yana zaune akan luntsememiyar kujerar wajen shi kadai, a gabansa wani haddadden kwandon shisha ne da yake zu?a yana hurawa lokaci zuwa lokaci, a Waya hannun nasa kuma wayarsa ce da hasken screen Winta ke haska fuskarsa yayin da yake danna number guda cikin contact list Winsa ana kuma maimaita masa abu guda daga daya bangaren wayar.
"The number you're trying to call is currently switched off, Please try again later." (Lambar da ake kira a kashe take, a sake gwadawa bayan wani lokaci.)
Hannunsa ya sake danna number yayin da aka sake maimaita masa maganar.
"Jawad?? For real? Kai kadai anan sama? Na zata wasa su Sa'id suke da suka ce kana nan ai."
Wani abokinsa da suke kira da Haro ya ?araso daidai wajen yana zama daga gefen kujerar, bai ce dashi komai ba don haka ya sake kallonsa yace.
"Naji rumours din, it was bad man, amma bai kamata hakan ya dame ka ba, kar ka jawowa kanka depression."
Sai a yanzu Jawad ya juyo ya kalle shi, ya san abinda yake magana, jita-jitar dake yawo cewa za'a cire mahaifinsa daga kujerar Minister, har a tunaninsa abinda zai dame shi kenan? To me zai same su idan an cire shin tunda ko a yanzu sun tara dukiyar da ya san har su mutu ba zata kare ba, ya zuki hayakin ya fesar sannan yace.
"Kar Allah yasa a fasa cire shin, al'amarin wannan tsohon ya isa ya dame ni ne Haro? abinda yake gabana daban."
Kan shishar Haro ya karSa yana dariya sannan yace.
"Pray tell."
Sai kawai ya jefo masa wayar hannunsa shima sannan ya jingina da kujerar. Haro ya cafe wayar sannan ya kalli screen Winta, kuma sunan da ya karanta na farko akan call log din ya sashi jan tsakin da bai shirya ba.
"Ban san ranar da asirin da yarinyar nan ta naka zai karye ba Jawad, har sau nawa zan gaya maka ka rabu da wannan tsilar abar, ub*n me zata tsinana maka da baka samu ba a duniyar nan? You're young, kana da kudi, kana da status mai kyau, kana kan lokacinka Man, sannan babu yarinyar da zaka kalla duk kasar nan ka kasa samunta.?Me yasa ba zaka yi hankali ka fahimci cewa wannan yarinyar sharri ce ma a rayuwarka ba?"
Jawad ya lumshe idanunsa ya bude yana saurarensa ta cikin sautin kidan dake tashi daga can kasa kuma sai da ya kai har karshe sannan ya girgiza kansa, idanunsa na kallon fitilar dake samansu mai kala-kala a cikin duhun wajen yace.
"Ba zaka gane ba Haro, ba zaka gane abinda nake ji bane, na rantse da Allah idan Ru?ayya bata aure ni ba, ba zata sake auren kowa ba a duniyar nan!"
***
"What do you find? Me ka samo?"
Faruk ya tambaya ri?e da Tab Win hannunsa yana kallon Ma'aruf dake kokarin fitar da lissafin da suka kwashe fiye da awa guda suna yi akan kamfanin wasu abokan kasuwancinsu da suka gano cewar suna da nasu kamashon cikin wannan mummunar asarar da har yanzu suke bincike akanta.
Suna zaune ne daga cikin office din Ma'aruf Win, bayan kusan jiran awa uku da Faruk din yayi yana jiran dawowar Ma'aruf da ya bar office din tun kusan sha Waya na safe.
Kuma sai da ya dawo sannan ya buWe email dinsa ya karanta bayanan da Martha sakatariyar tasa ta turo masa sannan suka fara haWa komai suna tarawa da ?aiyadewa.
"So shi wannan Mr. Ishmael Grahm Win shine ya karbi aikin accountant Winsu a farkon shekarar nan kenan kuma sunansu Waya da wanda ya tafi har surnane Win."
Ma'aruf Win ya faWa, idanunsa manne da tab Win gabansa yayin da muryar tasa ta fito kamar ta ?wace ne daga cikin tunaninsa.
"What a ina ka ga hakan? Dama sun canja accountant ne? When?"
Faruk yayi tambayoyin yana komawa cikin kan tasa wayar.
"A cikin wanda ka min sending zaka duba, anyi naming dinsa 13th March na wannan shekarar."
Kuma sai da Faruk din ya kusan zuwa can ?asa wajen nemowa kafin ya isa inda yake gaya masan, idanunsa suka ?an?ance yayin da yake karanta bayanin dake wurin.
"Bala'i! B ya akayi hankalinka yaje wajen nan, I was goung through it fa tun safe amma wallahi ban gani ba."
"Shi yasa na gaya maka na kusa korarka daga aikin nan, ban san me yake Sata maka tunaninka ba kwana biyu."
Dariya Faruk Win yayi yana cigaba da karantawa kafin yace.
"Aikin Shahida ne wallahi, tunda ta yaye Aarif nake ji kamar watannin farkon auren mu muka koma."
A lokaci guda Ma'aruf ya tsaya da karanta abinda yake yi ya juyo ya kalle shi, sai kuma ya girgiza kansa sannan yace.
"Baka da hankali Faruk, na daWe ina gaya maka."
Faruk Win ya sake yin dariya yana daukar tambulan Win lemon da Martha ta kawo musu kafin yace.
"Inji wanda yake amsa sunan sabon ango, you didn't even tell me ya yarinyar take."
Yaya yarinyar take. Maganar ta sake tuno masa da fuskarta a yau da safe kafin ya fito, sati guda kenan da yin auren, kuma a cikin sati gudan nan baya jin magana ta haWa su wadda tafi kirgen cikin yatsu, wani lokacin dai su kan haWu da asuba idan jamlock Win kofar falo ya rufe bayan ya fita masallaci, zata zo ta buWe masa idan yayi knocking sanye da dogoon hijabinta har kasa, ranar farko bata ce dashi komai ba, amma a rana ta biyu ne ta fara gaishe shi. Sannan kuma sau da yawa idan ya koma da daddare zai ganta, har ya fahimci wani lokaci ma tana fitowar ne kawai don ta gaishe shi.
Bayan hakan maganganun da suka haWa su baya jin sun wuce biyar, ya san ranar juma'a da zai fita masallaci ya tambaye ta dardumar sallah ta dauko wata sabuwa kuwa fil mai laushi ta kawo masa, sai kuma ita da ta tambaye shi Panadol ya fita da kansa ya siyo mata, amma bayan hakan baya tunanin wata maganar ta kara hada su don baya son ya takura ta ko kadan, so yake hankalinta ya kwanta ta fahimci cewa da gaske ba abinda zai mata, don a o farkon nan ya lura cewa da gaske a tsorace take dashi.
Ya rasa irin tasiri kalamansa suka yi a zuciyarta, ya kasa gane ma me yasa ta yarda da auren idan har tana tsoronsa haka, wata?ila laifin tun na wannan ranar ne, da ta fito ya ganta, da tun a lokacin zai san tayi ?an?anta yayi mata wannan barazanar, don haka yake son da kanta ta karkade duk wani tunani da take yi game dashi da kuma damuwar kalaman nan.
A shekaranjiya da yaji tana waya da wata tana yi mata bayanin cewa har yanzu bata fara girki ba, a cikin muryar tata yaji da wani abu kamar damuwa, wani abu da ya tsaya masa a rai yasa yasa ba shiri a lokacin da ya shiga cikin gida yaji Mami na yiwa Malam Sani lissafin cefenan wata, ya bishi a baya ya ?ara masa wasu kuWin yace duk abinda ya siya na cikin gidan ya sake siyan rabin sa ya kai mata.?
Komai na wannan auren daban yake da lokacinsa da Rukayya ya sani, babu abu ko guda daya da zai danganta shi da farkon wancan Win, kamar komai Win yana zuwa ne a kishiyar Wayan, sai dai abu daya kawai zai iya dorarawa shine a yanzu yana jinsa mutum mai ?anci tunda babu ruwanta dashi sabanin a wancan da kwanakin farko suka sa shi yaji kamar an tsare shi a wani waje ne da lissafin abubuwan da ya kamata yayi.
"Kaji ai matsalata da kai kenan, da an taSo wani zancen ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login