Showing 24001 words to 27000 words out of 84782 words

Chapter 9 - FARAR WUTA 1 Complete Hausa novel

01 Apr 2025

10747

Munaya tsaye tana waya, duk ta rikice kamar yadda take kullum sai faman gyara glasses Winta take alamun bayani ake mata ta cikin wayar, don haka bata ma ganshi ba har ya buWe motarsa ya jata?ya bar cikin gidan, kuma zai iya rantsewa zuciyarsa na lissafa kowanne wucewar lokaci kafin ya isa gida.
A ?ofar gidan ya ajiye motar don ?wa?walwar sa ta gaya masa cewa ba zai iya jira har maigadi ya buWe masa gate Win ba.
Ya shiga har ciki zuwa Wakinsa, ya buWe ?ofar da? ko waye ya shigo Wakin zai ce wardrobe ce. A ciki komai yana nan kamar yadda yake hango shi kafin tafiyarsa.
Tebura ne da duruwoyi masu cike da files Win takardu da kuma hotuna, ga tarin printers da photocopier a gefe, sannan bayan kayan rubutu akwai allo har kala uku Waya na rubutu biyun kuma ya manne su da takardu da kuma hotuna. ?aki ne da ko makaho ya shafa zai danganta shi da kalmar binceke balle kuma ga mai ganin da kallo Waya da zai yi masa zai bashi amsar da ba sai ya tambaya ba.
A jikin allon nan bayanai ne da kuma hotunan mutanen da Jamal yayi mu'amala dasu tun daga lokacin da ya dawo daga karatu har zuwa ranar mutuwarsa, kuma a jikin kowacce takarda da hoto Ma'aruf ya zana tambarin ? da jar marker alamun abinda yake nema bai Sulle ga wannan? hanyar ba, kusan hakan ne ma a jikin kowacce takarda dake barbaje a Wakin har kuwa da waWanda aka yayyaga.
A wata durowa daga can ?arshen Wakin ya shiga fito da duk takardun cikinta har hannunsa ya kai kan wani file daga can ?asa.
A cikin file Win tarin takardun Jamal ne wanda suka haWa da duk certificate dinsa na gama makaranta da kuma takardun Waukarsa aiki a matsayin sabon ma'aikaci a kamfanin Baffa, takardun Waukar aikin ya shiga buWawa Waya bayan Waya idanunsa na nazarin komai sai dai har yaje ?arshensu bai ga komai Win da yake nema ba, ya zauna daga tsugunnen da yake, ya sake bin komai dalla-dalla, amma har a lokacin babu komai Win.
Hannayensa duka biyu ya cusa cikin gashinsa yana fitar da iska ta hancinsa... Tunani da yawa ke tsere a cikin kansa, yana ji yadda yanayinsa ke ?o?arin canjawa, ciwo na harbawa a cikin kansa yana gaya masa cewa zai koma halin da baidade da fitowa ba.
A lokacin ne kuma idanunsa suka hango masa wata ?ar mitsitsiyar takarda da alamun ta faWo daga cikin file Win ne ba tare da ya kula ba, ya mi?a hannu da sauri ya Wauko ta...
Rubutun Jamal ne, hanwriting Win sa...
Mamaki ya kama shi tun kafin yafahimci me aka rubuta, don yasha buWe file Win nan ya zazzage shi amma bai taba ganin takardar ba. Kuma mamakinsa bai karu ba sai da hankalinsa ya gane masa me Jamal Win ya rubuta a jiki.
Amina Sulaiman.
Gadon ?aya.
***
Me kuke tunani ya haWa marigayi Jamal da Amina?
Me Hajiya Kilishi ke yi da magungunan Ma'aruf?
Me yasa Ma'aruf baya son hayaniyar yara?
Me Ma'aruf yake son cimma ne game da bincikensa?
Waye ya saka kansa a takalmin Amina?=??
#Aysha Shafi'ee.
#FikraWriters
#FararWuta.


BABI NA SHIDA.
~~~~~~
Wani mai adaidaita sahu ya shigo layin har zuwa ?ofar wani gida mai baranda, kuma da tsayuwarsa Aminu ya fito daga ciki yana dariya alamun sun daWe suna hira da saurayin dake jan adaidaita sahun wanda shima ya fito bayan ya kashe mashin Win, kuma a tare suka kamo wani buhun shinkafa ?ato guda suka shiga kiciniyar shiga dashi cikin gidan, inda tin daga soro ?ar hayaniyar mutanen ciki zata shaida maka cewar an samu baki fiye da mutanen gidan.
A tsakar gidan Amma ce tare da ?anuwanta su uku da suke uwa Waya uba Waya suke ta kiciniyar hada wasu kayayyaki a cikin kwalaye.
Yayarta mai suna Zahra'u da suke kira da Tanti wadda ke zaune a goron dutse ta kalli Amman da ta fito daga kitchen ri?e da ?aton tire Win data yanko kankana tace.
"Ni kuwa Halima wai yarinyar nan kaya kala nawa ta Winka a cikin lefen?"
Amma ta ajiye farantin hannunta a tsakiyarsu kafin tace.
"Ina ga kusan rabi ne, ai tun zuwan su Momi ?ar gidan Kawu Mallam wancan satin suka Wiba suka kai mata wajen mai Winkinsu, har da na fitar bikin."
Tanti ta gyada kanta tana faWin.
"Ko da naji, don na lura ita bata da wannan niyyar, a baki kawai Amina ta karSi zancen auren nan amma banda a al'amuranta wallahi."
"Kinga ko jiya..." ?aya ?anwar Amman mai suna Ma'u ta shigo zancen.
"... Abinda nake gaya mata kenan, nace tunda dai har ta amsa, ya kamata ta saki ranta tayi komai kamar kowacce amarya a haka ne zancen zai cigaba da rufuwa, komai ya tafi daidai."
?ayar da take ?ar autarsu Safiya tace.
"Ai ce miki zata yi hankalinta a kwance yake, ba irin faWan da banyi mata ba wancan satin amma?? ?iri-?iri ce min tayi ita ba abinda ke damunta."
"Allah ya kyauta, yaya kuka sake yi da ita Hajiya Kilishin? Yaushe za'a fara kai kayan ne? Ya kamata ma aje a ga wajen."
Aunty Zahra'u ta tambaya tana rufe ?aton kwalin da ta gama tara ?an ?ananun kayan kitchen a ciki.
Kuma tambayar ta dawowa da Amma tarin abubuwan da suka faru a cikin wucewar sati uku, yadda ka ranar da taje gidan Tantin a goron dutse, ta hau ta da fada bayan ta shaida mata komai, tace Uba yana da ikon zaSawa ?arsa mijin aure don haka ita bata ga aibu a cikin zancen ba, tunda a yadda ta san Baba ta ba zai aurawa ?arsa mara hankali ba kamar yadda Amman ta kira lamarin.
Don haka babu yadda ta iya dole ta ja bakinta tayi shiru, kuma kamar wasa al'amarin auren ya cigaba gudana bi da bi, a yanzu saura sati guda bikin, an karSi kuWin aure hade da lefen da bai wani girgiza su ba kamar yadda take zato a gidan Kawu mallam, sannan har sau biyu Hajiya Kilishi ta kira ta a waya tana shaida mata yadda wasu daga cikin al'amarin bikin zasu kasance a wajensu da kuma cewar gidan da za'a kai Aminan a cikin gidan da suke ne.
Sannan a jiya ta aiko da Wan aike ya kawo tulin wasu katinan Wan aure da ba su ko san yadda zasu yi dasu ba, don haka a dole ta karSi al'amarin itama suka fara shiri sosai, Baba yana ta fafutukar kayan katako da ?an kudin hannunsa da kuma wanda yayyensa suka haWa masa, yayin da ita da ?anuwanta mata ke iya nasu ?o?arin na kayan kitchen da kuma sauran na amfanin gida, wanda su Aunty Safiyan ke ta sintirin zuwa kasuwa tun wancan satin.
Sai da al'amarin ya kai duk da irin halin da zuciyoyinsu ke ciki, shirye-shirye a yanzu sun kama kamar dama sunyi tanadin lokacin. Don haka kafin ta bawa Tantin amsa su Aminu suka yi sallama a lokacin suna shigowa da buhun shinkafar nan.
"Yawwa master, nagode sosai..."
Cewar Aminun bayan sun jingine buhun shi da wani saurayi daya kamo masa, saurayin yayi waje yana fadin babu komai yayin d shi kuma ya juyo ya kalli su Amma dake kallonsa suna jiran ba'asin abinda zai ce.
"Haba Amma ke ma fa kin san bana sata, Baba ne ya kira ni yanzu naje na karSo a wajensa."
Ya faWa cikin raha yana kallon Amman. Aunty Ma'u tace.
"Na ga ranar da zaka yi al'amarin ka kai tsaye Aminu, in ma satar kake ai kowa ya san ba zaka kawo gida ba."
"Ameen wallahi..." Cewar Aunty Safiya.
"Amma da ?yar ne canjawar Aminu, ai hali ZANEN DUTSE ne."
Ya ?araso ciki da dariyarsa yana shirin buWe babin shafin tsokanar Aunty Safiyan da yafi rainawa, amma tun kafin ya zauna Amma ta katse shi.
"Zaka koma ne?" Ta tambaya.
"Eh yace in Webi kati in kai masa."
Kai tsaye ya bada amsar da a lokaci guda ta shiga kunnen Amina wadda ta fito daga Wakinsu a lokacin ri?e da tsintsiyar laushin da abin kwashe sharar data Webi abinci fal a ciki kasancewar Aunty Safiya da Aunty Ma'un duk sun zo da ?ananun ?a?ansu, suna ta dabdala a Wakin.
Riga ce ?ar kanti a jikinta kalar ruwan toka da wani tsohon zanin atamfa da babu mitar da Amma bata yi ba amma ta kasa rabuwa dashi saboda daWin Waurawarsa, sai ta bayar da sabuwar atamfa ma amma shi yana nan, Gashinta mai laushi yana ta fitowa ta saman Wankwalinta dake zamewa.
Tayi wajen sharar ta zubar lokacin da su Amma suka cigaba da zancensu, Aminu kuma ya dage wai sai sun yi cinikin sabuwar motar Aunty Safiyan da mijinta ya siya mata kwanakin baya kasancewar sa mai hali.
Sai ta juya ta koma Wakin a lokacin da wata ?ar Aunty Ma'u mai suna Yusra ke janyo kaya daga cikin drawer ta.
"Me kike nema anan Yusrah?"
Yarinyar ta juyo ta kalle ta.
"Hijabi Aunty Amina, Sallah zanyi."
"To ya zaki yi da hijabina, duka sun fiki tsawo... Kije Wakin Amma ki Wauko na Hafsa, me yasa ma baki bi su Hafsa aiken ba?"
Ta faWa sanin cewar?Hafsan da ?ar gidan Tanti da kuma Waya yayar Yusran basu daWe da fita siyan kayan miya ba. Adam ma tunda ya samu sa'ansa Wan gidan Tanti mai suna Mubarak suka fita filin ball shikenan sai an gansu kuma.
Ta tsugunna tana ?o?arin kwashe kayanta bayan fitar Yusran, yayin da hayaniyar ?an ?ananan yaran da suka Wane katifar Hafsa suna doki ke shiga kunnenta, tunda satin nan ya kama komai ?ara gaya mata yake yi cewar sauran wasu ?aiyadaddun kwanaki rayuwarta ta fara daga gaSar da zata ?are.
Musamman wannan haWuwar ta ?anuwan Amman a gidansu, wani abu ne daban da basu saba ba don Tanti itace babba a cikin su Amman, don haka mafi yawanci a gidanta ake yawan haWuwa, ko da Sallah kowa can yake tafiya su haWu har su, shi yasa ganin yadda gidan nasu ya zama wajen haWuwa yanzu yana ?ara tabbatar mata cewa da gaske komai ke shirin faruwa, gashi Baba ma har ya fara aiko da tanadin abincin biki duk da Amma ta daWe da?kafa layin cewa ba wani taro za'ayi mai yawa ba, ko ?anuwansu a can Niger tace duk a waya za'a shaida musu kawai, sai dai idan maza zasu zo Waurin aure don ya zama shaida a wajensu.
Wani abu ya wuce ta ma?ogwaronta lokacin da idonta ya kai kan tulin katinan Waurin auren nan, sunayen mutane takwas ne a jiki banda sauran bayanai, amma idan ta kalle shi ba abinda idonta ke gani sai nata sunan dake ?asan rubutun Ma'aruf Mansur Bakori, sunan da ko sau nawa zata maimaita shi sai ta ji bugawar zuciyarta a cikin allon ?irjinta.
Ta rufe idanunta ta buWe tana jin yadda har yanzu zuciyarta ta kasa yarda cewa tana shirin buWe shafin kaddarata ne da hannayenta. Ba lallai ne ya kashe ta kamar yadda ya rubuto a takardar nan ba ta sani, ya rubuta ne kawai don ya tsoratar da ita, amma hakan ba zai hana ta WanWani gwargwadon azabar da ya tsara mata ba, tunda ta tankwabe gargaWin da yayi mata.
Ta tuno shekaranjiya lokacin da Tanti ke tambayar Amma 'yaron kuwa yazo?' sai da ta ?ware da yawunta tsabar yadda tsoron hakan ya shige ta, ita har yanzu bata hango cewar in dai wannan Ma'aruf Win da ta sani ne zata ganshi a kusa da ita ma balle ?addara ta haWa su. Gani take yi kamar za'ayi auren ne kawai a kaita wajen Hajiya Kilishin da sunanta ne kaWai ke yawo a gidansu game da auren. Shi yasa bata fatan kowa ma ya ambace shi, tafi son ayi dukkan abinda za'ayi a kaita Win kawai, acan zata tsara matakan da watakila zasu iya siyar mata lokaci kafin dukkan abinda zai faru ya faru har Amma tazo tace.
'Dama na gaya miki Amina'
Fatima ma tace.
'Me yasa kika yi tunanin zaki iya Amina?'
Maryam zata dinga da binta da kallo kawai, Aminu kuma zai iya cewa.
'Ko ba komai kin ?o?orta Amina.'
Baba ne kadai zai saka mata albarka ta sani, yayi mata addu'o'in da wata?ila zasu iya gyara rayuwarta a gaba, don ya san tayi komai ne don shi, don tallafar mutuncinsa.
Ta kai ?arshen tunaninta lokacin da sallamar su Ummi da Momi ta cika tsakar gidansu, taji su suna gaisawa dasu Amma har da muryoyin wasu daban don haka ta rufe wardrobe Win ta juyo tana korar yaran zuwa waje.? A lokacin Ummi ta Wage labulen Wakin ta shigo.
"To amaryar ?ulle, kina nan mu munje mun samawa kanmu mafita.."
Suka shigo suna ajiye ledojin hannayensu yayin da Momy ke cewa.
"Amina ruwa dan Allah, wallahi mun Webo rana."
Da murmushi ta fita zuwa kitchen ta Wauko jug Winsu na roba haWe da kofinansa ta Webo musu ruwa sannan ta dawo.
"Wai daga ina kuke?" Muryarta a hankali ta tambaya tana ajiye musu ruwan.
Ummi ta mi?o mata ledar kusa da ita tace.
"BuWa ki ga."
Ta karSa kuwa ta shiga zaro wasu atamfofi masu kyau kalar ruwan hoda, (pink). Wani abu ya zarce ta ma?ogwaronta, tun lokacin da aka kawo kayan lefen nan su Ummi? suka san zancen auren, tunda suma sun san Hajiya Kilishin a matsayin ?ar uwarsu kawai dai tafi shiri da Baba ne duk a cikin si Kawu Mallam Win, don haka sai rawar ?afarsu ta ?aru kamar me sanin cewar bikin irin wanda suke so ne.
"Kowacce dubu Waya kenan da Wari biyar, jikinsu mai kyau ne baza ki taSa cewa roba bace."
"Wai na meye?"
Momi tace.
"Har tambaya kike? To anko ne muka fito dashi tunda ke baki da niyya, kin san mu ?an ayi sha'ani ne babu ta yadda za'ayi muyi biki lami ko amaryar bata so."
Amina bata ce komai ba, Momi ta sake cewa.
"Ina Fatima? Ga guda Waya nan ta Maryam mun siyo sai ta nunawa ?awayenku ita, wanda yake da hali yayi tunda dai saura ?an kwanaki, waWannan kuma ?awayen mu ne su ma gashi sun siyo tasu."
Sai a lokacin ta Wago ta kalli ?awayen nasu da murmushi a fuskarta tace.
"Allah ya saka da alkhairi, nagode." Ummi ta kalle ta tace.
"Su da kuWinsu kike musu godiya? Zo muje ni kiga wani abu."
Da haka ta ja ta suka fita daga Wakin, a tsakar gida su Amma duk sun shige can Wakinta suna cigaba da haWa kayan dake ciki, sai Aminu kawai dake ta Waga yaran nan sama suna dariya.
A ?ofar Wakin Baffa suka tsaya Ummin tace.
"Amina duk shiru-shirunki na san ba haka halaiyarki take ba, akwai wani abu game da auren nan da kike Soye mana, kin sani ni da Momi ?anuwanki ne kuma sa'aninki da zamu iya jin irin ciwonki, idan akwai matsala ki gaya mana, wallahi in zamu iya zamu taimake ki."
Amina ta haWiye wani abu, duk kauWin su Ummi ta sani cewa suna da zuciya mai kyau a can ?asa, kuma ta sani cewa suna sonta fiye da yawanci daga cikin ?an uwansu don haka zasu iya taimaka matan da komai, sai dai bata yi tunanin cewa Ummin zata iya ganin damuwarta sama da Wokin bikin da suke yi ba. Amma duk da haka ta san babu amfani sanin nasu kamar yadda Baba ya shar'anta tun farko, musamman su biyun nan da ta san idan suka ji kamar ta saka lasifika ne a tsakar gidan Kawu mallam ta faWawa kowa. Don haka sai kawai ta girgiza kanta.
"Wallahi ba wani abu bane Ummi, kin san ban taSa kawowa kaina aure a yanzu ba ne kawai, kuma sai komai yazo a lokaci guda shi yasa kawai nake jin wani iri."
Kamar Ummin bata yarda ba, amma bayan ta kalle ta na wasu sakanni sai ta gyaWa kanta tace.
"To ai shikenan, idan wannan ne da an kai ki sati Waya na san zai tafi, don duk da haWa ku akayi ke bata wasa bace Amina, kuma duk yadda yake jin kansa na san zaki iya dashi....Wai yaushe zamu ganshi ne ma? Ya bamu kuWin walima..."
Wai me yasa kowa yake son ganin sa? Me yasa kowa yake son jawo shi da baki? Basu san a lisafin tashin hankalinta wannan shi ne a sama ba? Jin bata ce komai ba yasa ta sake cewa.
"Ko da yake da alama kema ba wani ganinsa kike ba, masu kudin nan sai a hankali, amma dai na san zaku haWu kafin wani satin sai ki karSo a madadinmu, idan ba haka ba kuma ni zan karSi lambar wayarsa na tambaya da kaina."
Jin haka yasa tayi saurin girgiza kanta tace.
"Kar ki damu baza'a kai hakan ba ma."
Ina zata kai kanta idan har Ummi ta kira shi da wannan zancen? Ai ko a mummunan mafarki ta san wannan rashin sa'a ce babba a rayuwarta. Ummin ta kalle ta sosai.
"Amina auren masu kuWin nan fa dama ce da kuma rabo, ki saki jikinki ki ci kuWin gayen nan son ranki, don baki san irinsa ba, ba lallai ne in kin shiga ma ya buWa miki ba."
A yanzu ta dawo Ummin data santa, ?anwar ?anmatan Kawu mallam me cike da buri, don haka sai kawai ta faWaWa murmushin ta tana fadin.
"Toh shikenan."
Da haka suka koma wajen su Momi, inda suka dasa hira su da ?awayensu, hirar da taso tafiya da yawan tunanin zuciyarta, don hira suke har da dariyar da har ?asa suke kaiwa wajen ?ya?yata ta, daga baya ta zubo musu abinci a ?aton faranti suka zagaye shi su bakwai suka cinye tas, a lokacin su Tanti duk sun tafi kuma har Amma ta yaba da atamfar da suka siyo bayan an nuna mata.
Maryam ma ta dawo ita da ?awayenta da suka tafi gidan wata mata tambayar Beads Win da zasu yi amfani dasu a bikin, kuma ganin atamfar murnarta ta ?aru don tace tayi kalar beads Win da ta bayar ayi mata na atamfar da Baba yayi musu na fitar bikin. Kallonta kawai Amina take don ta lura ita mantawa ma take da zancen cewar ba auren da suke so za'ayi ba, don gabadaya ma ta manta da zancen saukarsu da suke ta shiri, yanzu bikin ne a gabanta don ko jiya tana jinta tana takurawa Aminu cewa ya ?ara mata kuWi zata siyo kayan da zata yiwa ?awayenta 'takeaway'.
"Tun safe Fatee, tun Wazu nake ta kallon hanya, baku dawo da wuri bane?"
Ta faWa lokacin da Fatima ta shigo gidan da daddare, don tun safe tace mata zasu je bikin ?aruwarsu.
Sai dai maimakon Fatiman tayi dariya kamar yadda ta zata sai kawai tace.
"Go slow

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login