Showing 15001 words to 18000 words out of 63435 words

Chapter 6 - Amanata HAUSA NOVE

ASMAU   

11 Nov 2024

19038

afka musu, suna neman tasu lafiyar.
Ta zubawa yarinyar ido, duk kafafunta anyi dori, ga plasta a kanta. Ta ce,
"Na shiga uku ni Hassana, yau ina za mu nemo iyayenta?"
[9/4, 12:57 PM] Asmau: Tana fita Asabe na sawo kai niki-niki da ledoji. Ya biyo bayanta rike da wasu ledojin bai ga Hanifah ba.
Ya ce, "Ina mai jinyar taki?"I'm
Ta ce, "Ta fita".
Sai gata ta shigo. Ya balla mata harara ya ce,
"Abin da nasa ki kenan?"
Ta ce, "Ba fa wani waje na je ba, nan din ne ba serbice and I wanna mek a call, shine na dan fita".
Bai kara bi ta kanta ba ya mai da duban shi ga Asabe.
"Ga ruwan dumi a filas ki zuba Dettol kadan da wannan 'bath-gel' din ki goge mata jiki sosai da wannan karamin tawul din, ki dauki daya cikin kayan nan ki sa mata. Amma ki yi da kula, kada ki fama ta".
Cike da ladabi ta ce, "To".
Ya juya ya fita Hanifah ta bishi, don dama dai duk ta gundura da zaman.
Da suka iso gida suka tarar da Gwaggo sun dawo. Gwaggo ta ce, "Ya ya mai jikin?"
Ya ce, "Ta ji sauki sosai".
A nan Gwaggo ke bawa Daddy bayanin abin da ya faru.
Ya ce, "Allah ya kiyaye gaba. Ba tun yau ba nake hana ka gudu da mota amma ba ka ji".
Shi dai ya mike zai gudu don barci yake ji sosai, gashi gobe zai yi sammako ya koma Lagos.
Gwaggo ta ce, "Ina za ka ne? Ka zauna magana zamu yi".
Ta dubi Hanifah ta ce,
"To bamu waje, kin zauna kina rabawa mutane ido, ko a gabanki kike so ayi zancen auren naki?"
Da sauri ta tashi ta yi dakinta tana murmushi. Ya koma ya zauna yana sauraron su.
Daddy ya ce, "Mun je Dukku yau, ganin kan hanya ne kawai muka shiga Darazo. Alhamdulillahi tafiya ta yi kyau, don Alh. Abdullahi (mahaifin Hanifa) ya karbi lamarin sosai.
A take muka gabatar da komai har sadaki, muka yanke lokacin aure farkon watan April mai kamawa, zamu je can a dauro aure. Yaya? Ya yi maka?"
"April Daddy? Ai ni zuwa lokacin ban shirya ba. A bani nan da watanni shida, don kuwa ko gidana ban yi tsarin shi da mace ba, yana bukatar gyare-gyare".
Daddy ya ce,
"Wannan ba matsala ba ce, ai itama karatu take ba binka za tayi ba, za ku zauna a nan a 'side' dinka zuwa sanda za ka gama gyaran gidan a nutse, kafin sannan ita ma ta hattama karatun ta, tunda saura shekara daya ya rage mata.
Maganar lefe kuwa wannan an dauke maka nauyinsa, za su je Italy ita da Mamanku ta zabi duk abin da take so sati mai zuwa. Sai me ya rage na shirin?"
Aliyu ya mutu a zaune, ya rasa abin cewa. Sai ya dukar da kai ya ce, "Shi kenan Daddy, hakan ya yi, Allah Ya kara girma".
Gwaggo da Daddy suka ji dadi har cikin ransu, suka fara sanya mishi albaka.
** **







A daki ya samu Mama yake sanar da ita gobe zai koma office, don Allah ta kular mishi da AMANAR SA, wato MUHASEEN. Sati mai zuwa zai dawo insha Allah.
Mamaki ya kama Mama, mutumin da sai ya kwashi watanni uku basu ga keyarsa ba, yau shine mai cewa zai dawo sati mai zuwa saboda 'yar almajira?
Ba ta dai furta ba ta ce,
"Har da ni da Daddy zamu hadu mu yi jinyar AMANAR KA. Kada ka damu, ka dauka cewa ni na haifi Muhasin kawai".
Ya yi godiya ya juya ya fita.

Washegari sammako su kai shi da Danlami, yana kwance a bayan motar shi da yake amfani da ita a Gombe kirar (Peageout 406) za su wuce filin jirgi.
Sai dai baya jin zai iya tafiyar nan bai ga ya Muhasin ta kwana ba. Bai yi mata sallama ba. Ya yiwa Danlami magana ya karya kan motar suka nufi SUNNAH HOSPITAL.
Ya tura kofar a hankali tare da sallama. Asabe na bisa sallaya tana jan carbi tana gyangyadi, ya yin da maras lafiyar ke sharara barci sadidan.
Ya gai da Asabe kafin ita ta gaishe shi, ya ce, "Yar taki ba ta tashi ba ko? Na zo yi mata sallama ne, zan koma bakin aiki. Sai karshen sati zan zo insha Allah".
Asabe ta ce, "Allah Ya kiyaye hanya. Ai jiya mun sha hira, da na goge mata jikin, na sauya mata riga, sai ta ji dadin jikinta, aka shiga bani labarin Gizo da Koki da Bala da Babiya sun tafi Bunjuku".
Ya yi dariya, ya karasa gabanta. Fuskarta sumul, jikinta fes, cikin tsadaddiyar doguwar riga 'yar Dubai da ake ya yi.
Numfashinsa ya ji ya tsaya a wuya, kamar ba zai wuce ba. Akwai wani sirrin kyau a tattare da ita, haiba da kamala, da bai taba ganin shi a wata diya mace ba.

Fara ce sol mai kananun ido da wadatar dogon karan hanci. Bakinta kamar an sa reza an yanka mata shi. Muhimmin abu cikin kyawun nata shine, gargasa a ido, da girar ido.
A koda yaushe idanunta a lumshe suke, cikin kwantaccen gashin ido, mai santsi da tsayi, kamar ta shafa 'mascara' komai nata 'natural (na halitta), babu kari da na Bature ko daya, amma sai a zabe ta da gudu a bar Baturiya.
Da kyar ya iya dauke ido a kanta lokacin da Sister Habiba ta shigo za ta ba ta maganin karfe bakwai.
Ta gaishe su ta ce, "Manya ba a tashi bane?"
Asabe ta ce, "Ba a tashi ba, don jiya bamu kwanta da wuri ba ana ta yi min tatsuniya".
Ta yi dariya ta ce, "To nima kam ba zan tashe ta ba kada in sata ciwon kai, idan ta tashi ki yi min magana'.
Ta ce, "To".
Ta fita tana satar kallon Aliyu. Shi bai ma jinsu don a lokacin waya yake da Alh. Tajuddeen. Da ya kammala ya wa Asabe sallama, ya kuma bar mata sallahun abin da za ta fadawa Muhasin in ta tashi, ya fita suka tafi.
Sanda suka isa Airport jirgin da zai hau na Mangal har ya kusa cika. Yana shiga ana rufewa, jirgi ya soma tafiya cikin kwaltarshi, kafin ya tashi gaba daya suka lula birnin Ikko ikon Allah.

****
Washegari Mama da kanta ta yi shiri, bayan sun gama kalaci, da abinci kala-kala irin masu sanya kashi saurin hadewa, wato romon hanta, faten wake da ganye, da kuma gasasshen kifi.
Danlami ya ja ta zuwa asibitin, ya nuna mata dakin. Ya biyo bayanta da kayan da ta taho dasu. Misalin karfe goma na safe.
Asabe ta karbi Danlami tana wa Maman sannu da zuwa. Suka gaisa tana tambayar ta ya ya mai jikin?
Ta ce, "Jiki alhamdulillahi yana yin kyau. Ai babban likitan ya san aikinsa wato Dr. Misau. Ya ce nan da sati biyu za a kwance kafafun ta fara tafiya da sanda kafin ta karasa warkewa".
Mama ta isa gaban gadon tana kallon kyakkyawar yarinyar da ke yi mata yanayi da wani da ta sani, amma ta rasa ko wane ne.
Ta kama hannunta ta ce,
"Sannu kin ji?"
Ta yi murmushi, "Ina kwana?"
"Lafiya lau Muhasin".
Asabe take gaya mata sakon Aliyu cewa ya koma aiki sai sati mai zuwa. Har ranta ba ta ji dadi ba, domin cikin dan lokaci har ta shaku da shi saboda kirkinsa da kulawar shi ga al'amarinta. Amma ba ta ce komai ba.
Tana ta kallon Mama saboda tsabar kamannin su da ta gani, ko ba a gaya mata ba ta tabbatar wannan Yayar Aliyu ce, domin a yadda take cike da kuruciya da wadatar lafiya ba za ka zaci a haife ta haife shi ba.
Mama ta zuba mata faten waken ta ba ta da 'tea' mai kauri ta mika mata ta soma ci. Doctors suka shigo round suka duba 'file' dinta tare da yi mata tambayoyin yadda take jin kafafun nata.
Bayan sun fita Mama take yi mata 'yan tambayoyi a kan Ummanta tana ba ta amsa iya dan abin da ta sani.
Ta ce ita dai ta manta sunan garin da Umman ta gaya mata, kuma ba a can suke zaune ba a Billiri ta girma, kuma ba ta da kowa a can yanzu, don Baddo marikiyarsu ta dade da rasuwa.
Mama ta gamsu, 'ya ce kawai Allah Ya ba ta. Ba za su kaita hannun hukuma ba, a kaita gidan marayu a sheganta ta in ta girma.
Addu'a sosai Mama ta yi Allah ya bayyana mata Ummanta cikin gaggawa. Su kuma Allah ya dubi zuciyarsu ya basu ikon rike ta da AMANA.
Haka Mama da Asabe suka ci gaba da jinyarta cike da kulawa. Ko uwar da ta haife ta karshen abinda zata yi mata kenan.
Idan daya ba ta nan daya tana nan. Daddy ma ya zo har sau biyu. Hanifa ta koma makaranta yin jarrabawar karshen zango, wanda daga shi za ta shiga shekarar karshe.

Juma'a da daddare Aliyu ya iso, Danlami ya je ya tarbo shi. Shi da Mama sun dade suna hira a ranar tare da Gwaggo wadda za ta koma Kumo a washe gari ta yo shirin biki ta dawo.
Shi yadda suke dokin auren ma dariya suke ba shi, sai ka ce wata macen arziki suka ba shi ba wannan da ya sha yiwa tsarkin kashi ba. Da me za ta birge shi? Duk kuruciyarta ya santa, a kan idonsa aka haife ta suka tashi gida daya, to dokin na mene ne?
Washegari Danlami ya mai da Gwaggo Kumo da magungunanta da likita ya rubuta. Shi kuma ko kalaci bai nema ba ya karbi karin kumallon su a kwando ya wuce asibitin.
Sister Habiba ce ke koya mata tafiya da sanduna biyu a harabar karamin asibitin. Ta hango shi yana tahowa ta bare baki tana dariya. Ya karaso shima dariyar yake mata.
Ya ce, "Lallai kanwata, lafiya ta samu, kafafu sun yi kyau, Alhamdulillahi".
Ya juya ga Sister Habiba ya ce, "Muna godiya fa".
Ta yi fari da ido ta ce,
"Ba komi, aikinmu ne ai".
Ta karbi kayan dake hannun shi ta ce, "Mu koma ciki".
Su uku suka yi kalaci har da shi, nan ya yi zaman sa suna ta hira tana ba shi labarai irin wadanda Ummanta take ba ta yana shan dariya.
Sai da aka yi kiran sallar azahar ya tafi don bada farali. Bai kuma dawowa ba gida ya wuce ta can.
Tunda ya zo Mama ta huta zuwa asibiti, sai shi yake zuwa. Ranar lahadi ya yi shiri zai koma ya bar komi a hannun Mama, ya ce shi da zuwa sai wata mai zuwa tunda Muhasin ta ji sauki.
Bayan sati biyu aka sallame su don komai ya hade, duk da haka da sanduna take tafiya. Suka koma gida, dakin Hanifah Mama ta kaita.
Asabe ta ci gaba da kula da ita ita da Mama. Kafin sati ya zagayo ta yi shar kamar diyar Lebanese.
To ga cima mai kyau, ga suttura, ga rabar A.C, ga ruwan wanka na famfo garai-garai ba na tuka-tuka ba. Ga sabulai masu tsada.
Ai kuwa ta rikide ta yi kyau, daudaddiyar fata ta murje, jiki ya yi sumul-sumul, sai ka rantse ba Muhasin din karkashin gada ba ce. Ta fi kama da 'yar Mama ta cikinta, domin ita ma sol take.
Biki na matsowa, 'yan'uwa da iyaye na ta shirye-shirye, ango da amarya rana daya suka iso abin kamar hadin baki, but is just a coincedence (arashi ne kawai aka samu).
Ita ta gama jarrabawa ana saura kwana biyar daurin aure, ya yin da shi kuma hutu ya dauka na musamman na sati biyu, wato bayan biki da sati daya.
Washegari Mama da Hanifa suka tashi zuwa kasar Italy, kwanan su uku kacal suka dawo da sayayya rankatakaf.
Washegari kuma Gwaggon Kumo da sauran jama'arta suka iso daga Kumo. Gida ya soma cika tun ana gobe kamun amarya. Ita ma amarya 'yan'uwanta na Darazo da kawayenta na ATBU sai isowa suke. Ga dangin Mama ko in ce dangin amarya duk sun iso.
Nan da nan gida ya yi albarka, biki ya kacame. Sai dai kuma daga amaryar har angon babu mai neman wani.
Ita tsoron shi ma take ji, shi kuwa ta jinyar Muhasin yake 'yar kanwar shi da ta yi mishi kane-kane a zuciya.
Washegari aka yi kamu mai kayatarwa, a nan harabar gidan. Washegari juma'a kuma aka wuce Picnik din da abokan ango suka shirya a Yankari Game Reserbe.
Mama kuma ta shirya Mother's da daddare bayan an dawo daga Yankari, komai ya yi yadda aka so, ya kuma bar tarihi.

Wayewar garin asabar aka daura auren Engr. Aliyu Suraj Kumo da Barrister Hanifah Abdullahi Darazo.
Daurin auren da ya kunshi manya-manyan ma'aikatan 'custom' na Najeriya. Hatta Tajuddeen Olayemi (tsohon controller kuma ubangidan shi) ya samu halarta.
Aka zarce da yinin biki a ranar. Hatta Muhasin Mama ta yi mata kwalliya da wani bakin tattausan 'cotton lace' mai yarfin 'dark pink flowers'. Kin san irin wannan 'colour' a jikin farar mace kuwa? Ta wanke mata kai sosai da kumfar (head and shoulder), ta yi steaming din shi. Ta tufke mata shi a baya.
Muddin ka san Muhasin a tasha, ka kuma ganta a yanzu, ba za ka gane ta ba. Kin san dai bakin kaya da ratsin 'dark pink' a jikin farar mace.
Tana zaune cikin kujerar falo tana ta kallon gilmawar 'yan gayu (kawayen amarya), duk sun bi sun kikkifa wata hula a kai (goggoro), sannan duk kayan jikinsu iri daya. Sannan sun saka wani cokalelen takalmi kamar zai karye don sirinta da tsayi.
Abinki da gidan biki, babu wanda ya kula da ita balle a tambayi Mama inda ta samo 'ya. Sai dai ita Maman duk da hidimar dake kanta ba ta manta da ita ba, shiga dari fita dari idan za ta yi ta hango ta sai ta ce,
"Ya ya ne Muhasin? Kina son wani abu?" Sai ta yi murmushi ta ce,
"A'ah, Mama ki yi hidimarki".

Ango ne ya ratso jama'a ya shigo gidan wurin Mama, sai sheki yake da walainiya cikin farar shadda Edcellencior ruwan madara, dinkin 'yar ciki da babbar riga.
A kuryar dakinta ya same ta tare da kawayenta, ya ce, "Mama kin manta dani yau ko kalaci baki bani ba".
Ta ce, "Wannan dutyn ai ya tashi daga kaina daga yau, ka nemi matarka ta baka".
Ya ce, "Ni naki nake so Mama, ki hada min zan raka Oga Airport zai koma yanzu zan dawo, ki hada min komai a kai min daki".
Ta ce, "Zan gayawa Hanifar ta kai maka".
Ya fice yana kunkuni...., "Kai wallahi Mama so take yarinyar nan ta raina ni".
Zai wuce a falon zuwa waje ba tare da ya lura ba da mutanen dake zaune ba, ya ji 'yar muryarta tana cewa
"Yaya na.....!"
Da sauri ya juyo, saboda yadda muryar ke dukan zuciyarshi a duk inda ya ji ta. Muhasin ce zaune cikin 'yammata, ta yi kyan ta yi kyan har ta gaji.
Duka rantsatstsun 'yanmatan dake wajen ta haske su, tamkar tauraruwa (zarah) a cikin taurari.
Ya iso har inda take yana murmushi ya ba ta hannu, amma sai ba ta mika mishi nata ba ta sunke shi a bayanta tana 'yar dariya.
Ta ce, "Ba kyau shan hannu da maza".
Ya kama baki ya ce, "Kai Muhasin, nine mazan?"
Ta ce, "Eh mana, maza ne kai babba ma kuwa".
Ya yi dariya ya ce, "To yanzu ina sauri sai na dawo zamu sha hira".
Ta ce, "To, sai ka dawo".
"Me zan siyo miki?"
Ta ce, "Wainar fulawa da awara".
Ya ce, "Toh? Ai ban san inda ake sayar dasu ba, amma zan gayawa Asabe ta yi miki ki ci ki koshi, kin ji?"
Cike da murna ta ce, "To, na gode sai ka dawo".
Har ya raka Controller Tajuddeen ya dawo bai manta da zancen ba. Ya yiwa Mama waya ya ce a kawo mishi abincin ya dawo. Kuma Asabe ta yiwa Muhasin wainar fulawa da awara.
Mama ta yi dariya ta ce, "Muhasin kanwar ango mai uwa a gindin murhu. Sai dai ta yi mata wainar don muna da fulawa, amma bamu da 'soya beans' (waken suya).
Ga Hanifah nan zuwa za ta kawo maka abincin".
Ya mike santala-santalan kafafunshi a kan 'rest sofa', subul dasu kamar baya taka kasa, da 'yar ciki da wando a jikinsa ya balle botiren na wuya da 'links' din hannun shi, babbar rigar shi na aje gefe yana lallatsa wayarshi.
A sanyaye amaryar ta yi sallama, ba tare da ya dube ta ba ya amsa. Ta shigo ta aje kwandon da ta riko a kan 'dining' ta jera komai, sannan ta dube shi ta tausasa murya,
"Ga abincin, ni zan koma ciki".
Ko kallon ta bai yi ba, ya ce,
"A gaishe su, na gode".
Ta ji haushi, amma fushin fari ai ba nata bane. Tunda ita take so kuma ta ci ribar samun abin da take son, sai ta lallaba, tunda ta amincewa ranta tana son kayanta a hakan.
"Wata rana sai labari, zai wuce idan kuka soma samun 'ya'ya, ya zama kamar ba a yi ba". Haka Mama ke yawan gaya mata.
Asabe ta soyo wainar fulawa ta kawo mata, tana dangwala ya ji tana ci, dadi ya ishe ta.
Washegari lahadi Mama ta shirya walima a gidan gonar Daddy dake bayan gidan ta mata zalla. Inda Malama Fatima Ja'afar Mai-Yadi (Yakanah) ta yi lacca a kan HAKKOKIN MIJI A KAN MATARSA, DA HAKKOKIN MATA A KAN MIJINTA.
Ta zaburar da matan aure a kan garabasar dake cikin biyayyar aure, da kuma tabewar dake cikin wulakanta shi. Ta sanya zuciyar mata ta yi tubus, kuma da yawa sun dauki sabuwar damara ta inganta rayuwar aurensu.
Daga nan aka kai amarya dakinta, 'side' din ango 'flat' ne hawa daya, mai manyan dakunan barci uku falo biyu babba da karami. Cikin kowanne daki akwai toilet makale, sai tafkeken 'dining area' da aka zubawa wani ubansu 'dining table' na 'crystal' zallah. Kicin na makale cikin babban falo shake da duk wani nau'in na'urar sarrafa abinci da abin sha.
An jera kowanne cikin tsari. Cikin dakunan barcin gadaje ne maka-maka wanda kowanne ke amsa naira miliyan daya da dubu dari biyar, sai dai ba iri daya bane kowanne da irin dizayin dinsa da irin kalarsa, tafiyayyu daga (Lombard) din Italiya.
Su kansu labulayen da aka zuba musu ruwan madara kallo daya ya ishe ka kamanta darajar su, don babu irin su sam a kasar Hausa.
Amaryar ce ta zabo abinta, baki daya gidan kai ka ce cikin wani 'flat' kake a kasar Turai ba a Najeriya ba, Najeriyar ma a Arewa.
Komai dai ya yi yadda ake so, gidan 'yan gata, 'ya'yan so a wurin Hajiya Maimuna da Alh. Surajo Tobbacco.
'Yan rakiyar amarya duk suka tafi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login