Showing 39001 words to 42000 words out of 63435 words
birni ka nemo 'yarka....ni 'yar ALMAJIRA HALIMA ce, bani da wani uba bayanta... Mugu azzalumi..!"
Ji kake "taasss...!" Aliyu ya wanke ta da wani gigitaccen mari sai da ta ga walkiya.... sannan yace
"Mind your tongue, ko in tsinke miki shi yanzun nan!".
Ta fita aguje tana kuka ta yi dakinta ta banko kofa, har da murza 'key', ta kuma barshi jikin kofar.
Mama ta bi bayanta tana bugu tana cewa, "Nice Muhaseen, bude min kofa".
Cikin rishin kuka ta ce, "Wallahi Mama ko zan shekara ba zan bude ba sai wannan mutumin ya bar gidan nan, mugu ne azzalumi ne, shi ya makanta min uwa, ya yi sanadiyar rabuwarmu, ya wulakantata karshen wulakanci, ko me zai gaya muku karya yake ba sona yake yi ba, ya sheganta ni".
Ta ci gaba da kuka kashirban. Mama ta jinjina kai ta rasa abin cewa, ta koma wajen su suka ci gaba da al'ajabin wannan ikon Allah.
Dr. Omar kuka yake sosai. Shi kuwa Daddy cewa yake,
"Hikimar Ubangiji yawa gare ta, ashe ni 'yata ce nake rike da ita ban sani ba. Wallahi duk shekarun nan goma da muka yi tare da Muhaseen, duk sanda na kalleta a fizge sai in ga kamar na san fuskarta, amma Allah bai taba sawa na yi tunanin da kai take kama ba. Sai in ce a raina kama ce kawai".
Aliyu ya ce, "Ni kam na sha zargin hakan, don lokacin da na kade ta da mota na tambaye ta inda ta fito, cewa ta yi ita jikar San-Turaki ce, to San-Turaki na da yawa, gashi ta ce ita ta manta sunan garin da Ummanta ta ba ta labari.
Na yi na yi ta tuna ta ce ta manta, sai kawai na kyale ta. Amma abin kullum na yi min yawo a ka".
Mama ta ce, "Yanzu dai a kyale ta zuwa gobe idan ta huce a hankali sai a lallaba ta a rarrasheta. Ban taba sanin Muhaseen tana da zuciya haka ba.
Lallai kam anyi kuruciya a lokacin, an bata musu ita da mahaifiyarta, wadda muma bamu san inda take ba, tun muna cigiya har mun gaji mun barwa Allah ikonsa.
Ban da abin Muhaseen ai farin ciki ya kamata ta yi gata ga mahaifinta Allah ya hada su, ita ma mahaifiyar da sannu Allah zai bayyana ta.
'Yar halak kenan, mai yin fushi da fushin mahaifiyarta".
Dr. Omar ya mike,
"Ai zama bai ganni ba, bari in wuce Dukku in sanar da Turaki da sauran 'yan'uwa".
Ai kuwa washegari sai ga dangin Muhaseen mota-mota daga masarautar garin Dukku, manya da kanana, yara da 'yanmata.
Har zuwa lokacin Muhaseen na daki ba ta fito ba, amma ta bude kofar da ta tabbatar Dr. Omar ya tafi, don duk hirarrakinsu daga falo tana jinsu.
Aliyu ya shigo falon yana daura 'links' din hannun rigarshi, ya tadda falon Mama cike taf da jama'ar Dukku mazansu da matansu, amma Muhaseen din ta ki fitowa don tana tsaye ta taga tana kallon hamshakan matan dake fitowa daga manyan Jeep-Jeep har da tsofaffi, ita abin ma tsoro ya bata, wai yau ita ce da wannan taron dangin amma suka barta cikin watagigin rayuwa. Sai da ta gama gwagwarmayar rayuwar ta sannan za su bayyana, to su yi mata me?
Ta yi tsaki ta saki labule ta yi kwanciyar ta tana jinsu suna ta rangadawa Mama godiya da fatan alheri. Suka kara da cewa basu da abin da za su biya su sai addu'a, Allah ya duba gabansu da bayansu, ya yi musu sakayya da mafificiyar Aljannah.
Kai tsaye ya wuce 'dining' din Mama, ya hado 'tea' mai kauri, ya zubo samosa biyar a kan karamin farantin tangaran, ya yi sallama a dakin ta amsa tana daga kwance.
Ya isa gabanta ya yi wani dan durkuso abin dariya, ya ce,
"Takawar ki lafiya, 'yar mutanen Dukku!"
Sannan ya karasa gare ta, ya tsuguna a kan gwiwoyinsa, ya daura mata 'plate' din a kan cinyarta, ya nufi bakinta da shayin.
Ita abin ma dariya ya bata, amma da yake she is not in the mood...., sai ta zumbura masa baki ta ce,
"Ni ba 'yar Dukku ba ce, 'yar karkashin gada ce, ba abin da ya hada ni dasu, in kuma suka nemi shiga harkata to wallahi zan gudu, kuma ba za ku kara ganina ba".
Ranshi ya baci sosai, ya ce,
"Koh?
To ga fili ga mai doki, ki gudu.... Dr. Omar ba zai kasa rayuwa ba, in sha Allahu!!!".
Jikinta ya yi la'asar, sakamakon yadda ya yi maganar cikin sanyi? Me yasa suke son Dr. Omar haka? Don dai basu san shi din wani irin azzalumi bane, don ba ta taba basu labarin da Ummanta ta bata ba.
Ya sake mika mata kofin shayin da ke hannunsa, fuskarshi babu walwala,
"Karbi ki sha!!".
Ba musu ta karba, ta soma sha a hankali, duk da zafin sa. Amma ta kasa cin 'snack' din, hawaye fal idonta.
Ya zauna kusa da ita har kafadunsu na gugar na juna ya ce,
"Muhaseeeeen.....!"'
Ta dago a hankali ta dube shi ba tare da ta amsa ba. Wasu irin kibbau ta ji suna keta zuciyarta daga kyawawan idanunsa. Gaba daya sun rikide, sun juye kamar ba Yayan ba.
Ji ta yi tsigar jikinta na tashi, sannan bugun kirjinta ya tsananta. A take ta ji wani zazzabi-zazzabi na neman kama ta.
Ta yi kokari sosai kafin ta iya dauke idonta, don gaba daya ta galabaice da sabbin abubuwan da ke zarya a zuciyarta da gangar jikinta, akan Yayan nata.
Tunda take ba ta taba jin wadannan abubuwan da ta ke ji yanzu game da Yaya Aliyu ba, wasu sabbin feelings ne wadanda a shekarunta na yanzu, (18), za ta iya fassara su da KAUNA wadda jigonta shine SOYAYYAH!!!
In haka ne kuwa zuciyar ba ta yi mata adalci ba, da ta kai kanta inda Allah bai kaita ba. Ta soma jan hirji cikin zuciyarta, tana addu'ar Allah ya cire mata wannan sabon al'amari da ta tsinci kanta a ciki, rana daya, lokaci daya, cikin dakikan da basu wuce goma ba.
Ba tare da ya lura da halin da take ciki ba ya soma magana.
"Muhaseen, dukkaninmu ajizai ne, babu wanda baya kuskure, mahaifinki ya yi kuskure ya kuma gane kuskurensa, ba tun yau ba, ba tun jiya ba. Tun ma kafin ya ganki.
Don Daddy ya yi min bayanin komai. In kika ki yafe masa kin yi butulci da rahamomin da Allah yayi miki. Sannan su danginsa idan shi ya yi miki laifi, su mene ne laifin su don sun zo gare ki da so da kauna?
Idan har kina so in ci gaba da shiri dake, to ki yi hakuri ki yafewa mahaifinki. Ubangiji ma muna neman afuwarsa ya yafe mana balle ke baiwarsa? Yin afuwa ga wanda ya saba maka daya ne daga cikin dabi'un Ma'aiki (SAW.)
Ki mike yanzun nan ki shirya cikin kyakkyawar kama ki je ga iyayenki.....idan fa har na isa in fada miki ki ji kenan. Na barki lafiya!". Ya mike ya fita.
Ita wace ce Yaya Aliyu zai nemi alfarma ta kasa yi mishi ko wacce iri ce kuwa a wannan duniyar? Ta mike a hanzarce ta fada bayan gida (toilet) tana wanka, tana kukan tuna Ummanta, tana magana ita kadai,
"Ka fi karfin komi a wurina Yaya Aliyu!".
Ta fito ko mai bata shafa ba. Tana daura atamfar super a jikinta tana hawaye. Mama ta shigo ta sameta a haka.
Ta karbi zanin ta daura mata, ta taimaka mata ta sa riga ta dauki turare a kan madubin kwalliyarta ta fesa mata. Ta daura mata kallabi, ta jawo hannunta ba tare da ta tsaya yi mata wani 'make up' ba suka fito.
Har rige-rige ake wajen rungumar Muhaseen tsakanin Yayar Dr. Omar wato Yaya Haula, da kanwarsa Aunty Badi'a.
Dukkansu farare sol dasu kamar Dr. Omar, kuma ita da Aunty Badi'a kamar an tsaga kara.
Mahaifiyar Dr. Omar Iya Ramatu ta rasu tuni, amma mahaifinshi San-Turakin Dukku yana raye, sai dai tsufa ya cimmasa sosai. Sauran matansa ne guda hudu, Hajiya Dijah, Hajiya Antu, Hajiya Saude da amaryarsa Inna Bintu. 'Yammatan 'ya'yansu ne da jikokinsu suna da yawa sosai.
Aunty Badi'a wadda da alama duk ta fi su wayayyen kai, da yake aure take a Abuja, tana auren Ministan shige da fice na kasa, ita ta dinga yi mata bayanin kowa, sunansa, da alakar dake tsakanin su. Ta roketa ta bisu su tafi Dukku kakanta San-Turaki ya matsu ya ganta gashi ba shi da lafiya.
Ta ce, "Amma za a dawo dani wurin Mama ko? Kuma ba za ki kaini gidan Baba Umaru ba?"
Kowa ya sa mata dariya. Mama ta ce,
"Da nan da can duk daya ne Muhaseen, inda kike so kika zaba a nan za ki zauna. Ba wanda zai rabamu sai Allah da ya hadamu".
Ta ce, "To bari Yaya Aliyu ya zo in tambaye shi, in ya yarda sai muje, in bai yarda ba shi kenan..."
"....Balle ma ba zan hana ba, nine babban dan rakiya. Maza dauko mayafinki, ga kafata ga taki, haka zamu je mu dawo..."
[9/4, 12:57 PM] Asmau: AMANA TA-3
Mama ta yi dan jim, tana nazarinta, idanunta sun sauya launi, jikinta ya yi sanyi, ya kuma saki sharaf!.
Ta ce,
"Baki da lafiya ne?"
Girgiza mata kai ta yi wato "A'ah".
Ta ce, "To wuce mu ci abinci, har karfe hudu baki sa komi a cikin ki ba tun safe".
Ya fito daga dakin yana waya ya fita da sauri ya wuce su, Mama ta bishi da kallo, sannan ta dawo da kallon ta ga Muhaseen da ta yi tsuru-tsuru ya-bera a gaban kyanwa.
Ta ce,
"Ce min za ki yi maigida ne ya zo, ba ki yi ta zaro min idanuwa ba".
Ta ji kunya sosai, ta wuce 'dining' ba ta yiwa Mama magana ba sai kunya da ta kara kama ta.
Mama ce ta yi serving dinta ta tura mata plate cike da farfesun zabuwa ya sha hade-haden kayan manya.
Ta ce, "Shanye shi tas, yanzu ki bani farantin".
Ta zumbura baki a ranta tana cewa, "Ita ma Mama kamar Aunty Badi'a, sai suyi ta turawa mutum magungunan da bai san na mene ne ba, kuma ba za a yi masa bayani ba".
Haka nan dai ta sa 'fork' (cokali mai yatsu) da cokali tana yaga tana ci a hankali.
Mama ta ce, "Har romon za ki hada ki shanye tas".
Ta yi dariya ta ce, "Toh".
Sai da suka gama sannan ya shigo, shima ya ja kujera a 'dining' din ya zauna ya ce, "Mama ni ina nawa?"
Ta ce, "Bamu dafa da kai ba, ka bari Hanifah ta dawo sai ta dafa maka".
Muhaseen ta dago a sanyaye ta ce,
"Kuma Mama sai ya yi ta zama da yunwa har sai ta dawo?"
Mama ta yi murmushin jin dadi ta ce, "Gaskiya kam, mai mata biyu ba zai yi maraici ba!".
Ta hau zuba mishi abincin tana cewa, "Wasa Mama take yi maka Yaya Aliyu, amma da kai aka dafa". Dadi ya kashe shi, kansa ya kumbura, Muhaseen ta birgeshi, yana ta murmusawa 'softly'
Mama ta ce, "Ko? Maza gama ci muje in raka ki dakin ki ki yi ta dafa masa mai miji".
Ta zaro ido ta ce, "Don Allah Mama ki yi hakuri ni a nan zan zauna'.
Ta ce, "A'a, Muhaseen ba za a yi haka ba. Ni sai in zama uwar banza idan na kyale ki, ki yi hakuri wannan shine auren, dake wuyan 'ya'ya mata baki dayansu.
Ko bakya ganin muma a dakunan mazajenmu muke zaune? Kuma ba gashi gida daya muke ba? Ko da safe kike son tahowa ki taho, ni ba zan hanaki ba, amma kwana kam, baki kara yin sa a sassan nan.
Bari Hanifa tadawo sai in raka ku baki daya".
Shi dai yana jinsu, yana cin abincinshi bai tofa musu ba, ji yake kamar ya goya Mama don fisabilillahi yana son daukar matarsa, wadda ta sauya duniyar zuciyarshi baki daya.
Ta sauya tunaninshi a kan diya mace, ta mallaki dukkan soyayyar da Allah Ya halitta a zuciyarshi wadda shi kansa bai san adadinta ba. Kuruciyarta na birge shi. Ita kanta gaba dayanta birge shi take (ko cikin fushi take).
Karfe shida daidai Hanifah ta shigo gidan, kai tsaye sassan su ta nufa, don har lokacin ita fushi take da Mama.
Mama ta kira wayarta ta ji ta a kashe. Ya fita don samun jam'in sallar magariba, can ya hadu da Daddy sai da aka yi sallar isha suka shigo tare.
Mama da Muhaseen duk suna daki suna sallah, ya wuce sassanshi. Nan ya cimma Hanifah a falo daga ita sai gajeriyar rigar barci tana kwance cikin 3-seater tana shan 'cream-soda' (SANS) da 'remote' a hannunta tana canza 'channels'.
A ciki ta amsa sallamarshi, kai tsaye dakinshi ya wuce ya yi wanka ya canza zuwa wasu fararen kayan barci masu kauri don ana tsaka da sanyi.
Ya fito dakinsa uffan shima bai ce mata ba, idan miskilanci ne gidan shi ta tarar. Da ta kasa jurewa sai ta mike ta yi dakinta tana kuka sosai.
Zuciyar Aliyu mai laushi ce, musamman akan mace, a take ya ji tausayinta ya kama shi, musamman da ya tuna cewa yadda fa yake son Muhaseen, haka Hanifah ke son shi.
Shin ya ya zai ji idan shine, ranar da Muhaseen ta yi mishi kishiya? Ai a hakan ma ta yi kokari, don in shine da Muhaseen din da kishiyar zai hada ya kone, in yaso shima a kashe shi.
Da wannan tunanin ya sauka daga kan keken motsa jikin duk ya yi gumi, duk da sanyin da ake tsulawa.
Ya murda dakinta ya shiga, tana kife da kanta a kan filo tana rusar kuka. Sai ya dago ta a hankali ya rungume ta, ya ce.
"Me ya yi zafi Hanifahh?"
Ta kara kwanciya sosai a jikinshi tana jan shesshekar kuka, ta ce,
"Ai shi kenan tunda ka auri wadda kake so ni sai ka banzatar dani? Yaushe rabonka da shigowa dakina? Balle bincikar halin da nake ciki, ko in mutu ko in yi rai ba abin da ya dame ka bane.
Wannan tun kafin Muhaseen ta shigo kenan, ranar da ta zo ni kuma sai yadda Allah Yayi da ni".
Ya rasa ma me zai ce mata don ya amsa a zuciyarshi cewa ya yi laifi. Sai dai nata laifin ya fi yawa, zuwa yanzu ba zai iya cewa baya son ta ba.
Ko babu komi 'yar'uwarshi ce ta jini, shi dai kawai halayenta ne baya so, ga dukkan alamu ita kuma ba za ta daina ba, musamman aikinta da gadarar ta.
Ya zaunar da ita bakin gadonta, ya zauna kusa da ita ya dauki tishu a kan 'side drower' dinta ya mika mata.
"Ungo share hawayen, ki nutsu, sai mu yi maganar".
Ta yi yadda ya ce din. Ya bata mintoci kafin ya yi magana, ya dube ta a hankali ya ce.
"Idan kina yi min gadara, ba zan iya yi miki adalcin da kike so ba".
Ta dube shi da fuskar neman karin bayani.
Ya ce cikin daga gira,
"Yeah, aikin ki ya fini muhimmanci a gare ki, kina da lokacinsa baki da lokacina. Ni da kwata-kwata ma ba mazauni ba".
Ta ce, "Ba haka bane?"
Ya kalle ta a kaikaice,
"To yaya ne?"
Ta yi shiru ta rasa abin cewa, don dai kam ba zai samu yadda yake so ba, wato raba ta da aikinta, ta dogara da namiji wanda ba shi da tabbas. Ta manta haka Allah Yace diya macen ta yi.
Sai da ya kara shakar iska sannan ya ce, "Sai abu na biyu, meye dalilin da don na auri Muhaseen za ki daga hankalin ki? Kamar wata annoba na kawo miki?
Idan kana son mutum ko kare yake so taya shi son shi kake, balle mutum bil'adama. Yarinyar nan a gabanki ta tashi, kin san dukkan halayenta, da me za ta cutar dake?"
Nan ma shiru ta yi, don ita kanta ba za ta ce ga halin Muhaseen guda daya mara kyau ba.
Ganin ta fara amsa laifinta a fuska, ya juyar da kai wani sashen daban, ya ce (ba tare da ya dubi inda take ba).
"Abu na uku shine, kin kulla gaba da iyayen mu, wadanda basu da hannun komi cikin kaunata da Muhaseen balle auren ta.
Yaushe rabon ki da shiga sassan Mama ki gaishe ta? Kwanan Innani uku cikin gidan nan baki je inda take ba.
Ba fa gaya min ake yi ba ina hankalce ne, kina tunanin wannan shirmen naki shi zai sa, ko shi zai hana?
Ga ki babba, ga ilimin ki, amma kina yin abubuwa wadanda mutum mai hankali ba zai yarda dasu ba.
Tunda kin dage kina son aikinki ni ba zan hanaki ba. Tunda na dinke tawa matsalar. Amma don Allah Hanifah ki gyara halayenki, sai nima in gyara miki nawa.
Muhaseen AMANATA ce na baki, kamar yadda Allah Ya bani AMANAR TA. Ki zauna da ita lafiya, ki kama girmanki, sai itama ta ci gaba da ganin mutuncin ki. Don wallahi ni kam (Aliyu) ba zan iya rayuwa ba tare da ita ba!
Koda ace ba'a ga iyayenta ba, ni niyyar AURENTA ta ne a zuciyata, tun daga ranar da na fara ganinta cikin tsumma.........
Kina tunanin wannan soyayyar ta wasa ce? Soyayyar shekara goma! Excuse me Hanifahh (ki gafarce ni) ina son ta 'very-very much to the extent .........." Ya girgiza kai, "I can't say! (bazan iya cewa ba)".
Ya juyo ya dube ta, hawaye ke ta gudu a kan fuskarta, ya dora kanta a cinyoyinshi yana share mata da tafukansa.
"Ban fada don ranki ya baci ba, gaskiyar zuciyata nake gaya miki. Don ban iya munafunci ba. Ki taya ni mu so ta, sai kema in so ki, ki tsaneta, nima in tsane ki.
Daurewa za ki yi, na san is not easy ka hada tarayya da wani a kan abin da kake so. Amma idan ka dauki hakan da sauki, sai ka ga ya zo maka da sauki.
Ina so (idan fa har na isa da ke kenan) in Allah ya kaimu gobe ki je ki baiwa Mama hakuri, da kin san yadda take son ki, da baki yi mata haka ba".
A sanyaye ta ce, "Allah Ya kaimu".
Yace "Innani fa?"
"Itama zan kirata...."
Aka shiga danna kararrawa, ya sunkuya ya sumbaci goshinta, sannan ya mike ya fita. Ta bi bayanshi da kallo har ya fita, wata sabuwar soyayyar shi na kara ratsa ilahirin zuciya da gangar jikinta, ta lumshe idonta a hankali ta ce,
"What a brave man!"
Mama ce da Daddy suka shigo, tana rike da hannun Muhaseen wadda ke lullube linkif cikin katon mayafin karan miski kalar (cotton lace) navy blue dake jikinta.
Ya basu hanya suka wuce cikin