Showing 6001 words to 9000 words out of 63435 words
goma.
Tunda ai ke kika daure masa gindi ya tafi (Custom) din, maimakon (Air Force ) da na ce ya je. A kaina aka soma shigo da Tobbacco Nigeria?
Ko su mutanen da suke shanta, basu san illarta ba suke sha?
Da sana'ata ya tashi ya ganni, ban ga dan abu kazan da ya isa ya hanani ba.....(ya lailayo ashar ya kunduma)".
Ita dai Haj. Maimuna sum-sum ta lallaba ta fice, domin idan Alhaji Suraj ya soma irin wannan bala'in nasa, ba ta tanka masa, don sai ya huce a kanta ko ya ce tasa danta a gaba su bar masa gida, tunda dan ya nuna aikinsa ya fishi muhimmanci a gare shi, bayan da kwabon Tobbaccon aka yi karatun da ake tinkaho dashi, amma ake kuma son a kawo masa rainin wayo.
Yana jira ya ga uban dan da zai iya hana shi shigo da Tobbacco Nigeria. Balle dan sa na cikinsa.
Ko kallon inda abincin da ta jera masa yake bai yi ba, ya suri hularshi ya fita. Direbansa Danlami ya taho da gudu ya zube a gabansa yana fadin.
"Ranka ya dade fita zamu yi ne?"
Ya ce a fusace, "In ba fitar zan yi ba me zai fito dani a daren nan?"
Ya mike a sukwane ya jawo mota gabansa, da alama yau Oga na cikin bala'in nasa da kowa ke gudu a cikinsu. Ya fito ya bude masa. Bai tsaya tambayar sa inda za su je ba don ya san hali, ya sukwani motar aguje. Buzu maigadi ya wangale musu girgijejiyar get din suka fita.
Sai da suka hau titi sosai sannan ya ce da Danlami, "Dau hanyar damanka, Airport zamu, Lagos zan wuce".
****
Yana zaune a kayataccen ofishinsa, sanye cikin 'uniform' dinsa na ma'aikatan Custom din Najeriya. Da farin gilashin PRADA a idanunsa. Zarkadeden saurayi Bafulatanin Kumo, ta jihar Gombe.
Bai yiwuwa ka kintata shekarunsa a lokaci daya, saboda ya yi kuruciya ainun da matsayin Controller na Custom din Nigeria gaba daya.
A jikin aljihun gaban 'uniform' din sa, cikakken sunan sa ne wato ALIYU SURAJ KUMO. A kan kafadarshi ta dama 'rank' din sa ne na (controller). Fari sol, ma'abocin gargasa ta gashi a ido, sumar kai da gefen fuskarsa. Haka kuma suka bi duk wata gaba suka kwanta linkif a fatar jikinsa.
Yana da wasu irin idanuwa tamkar an diga musu silber. Dan shekaru talatin da daya, wanda ya dama ya kutsa cikin ilimummukan zamani daban-daban.
Da farko dai 'Engineer' ne, wanda ya karanci (Electrical Engineering). Tun daga Digiri har Masta, daga nan ne ya yo 'course' din aikin yaki da fasa kwauri a Jami'ar 'Lancaster' da taimakon mahaifin shi Alhaji Surajo, kuma yana dawowa ya soma aiki da hukumar Custom ta kasa baki daya.
Yau shekara guda kenan da ya hau kujerar (Controller), ba don shekarun shi sun kai ba, sai don kwarewa, rashin wasa, jajircewa da sadaukar da kai ga aikinsa wanda (Controller) na baya Alh. Tajuddeen Olayemi ya fuskanta. A shekarar da ya yi ritaya ya dora shi a kan kujerarsa, ya kuma ci gaba da koyar da shi dabarun sanin makamar aiki, kuma dama shine ubangidansa a Custom.
Matsala ta farko da Controller Aliyu Suraj ya fara cin karo da ita da hawa kujerarsa shine; bribery and corruption, (matsalar karbar cin hanci da rashawa), daga kananan ma'aikata har manyan su.
Wannan ce matsalar da ya fara kokawa da ita daga hawa kujerarsa. Ya tsaya tsayin daka kan aiki da gaskiya da amana, babu sani babu sabo babu sanayya. Ya kau da cin hanci da rashawa, yana aikinshi da zuciya daya babu sani babu sabo. Ciki kuwa har da kalubalantar mahaifinsa a kan sana'arsa ta shigo da Tobbacco, wanda hatsari ne ga lafiyar al'umma.
Yana so Daddy ya fahimce shi ya sauya sana'a, amma Daddyn ya ki tsayawa ya fahimci abin da Aliyun ke son fahimtar da shi, a ganinsa kawai Aliyu ya raina shi ne saboda ya yi ilimin zamani mai zurfi.
In ban da haka ba da kudin Tobbacon aka yi dawainiyar karatun nashi ba? A ganin Daddyn, babu wanda ya isa ya sa shi sauya sana'ar da ya riga ya saba da ita, har ta zamo hanyar cin abincinsa.
Taba ba giya ba ce, ba 'cocaine' ba, ba kayan maye ba, ba sholisho ba. Sai dai abu ce wadda ke da hatsari ga lafiyar al'umma. Duk da dai hukuma ba ta hana shigo da Tobbacon.
Aliyu, a nashi tsarin, ya hana. Don abu ce da ke wanzar da cututtukan huhu, take kuma kashe matasa da kuruciyar su.
A jikinta baro-baro ma'aikatar lafiya ta kasa (Federal Ministry of Health) ta rubuta cewa; 'smokers are liable to die young.....' Amma ya rasa me al'umma ke ji a cikinta, suna wasa da rayuwarsu suna sane? Da gangan? Shin menene a cikin Taba ne da ya wuce hayaki da daci?
Ya maida kai ga tarin ayyuka cikin 'file-file' din dake gabansa. Aka bankado kofar ofishin aka shigo babu ko sallama.
Ya cira kai a hankali ya dubi mai shigowa, Daddy ne.
Ya nuna shi da dan alinsa ya ce,
"Wallahi-wallahi Aliyu ka fita daga idona, ka sakar min kaya, ni sa'anka ne ko abokin wasanka?"
Ya mike yana cewa,
"To Daddy yi hakuri ka zauna tukunna".
Ya jawo masa kujerar da ke fuskantarsa ya ce,
"Zauna Daddy".
"Ba zan zauna ba".
Ya yi murmushi ya nufi dan karamin firjin da ke gefe ya dauko gongonin Coca-Cola, ya dauko kofin gilashi garai-garai da shi ya bincire hancin, ya juye lemon ciki.
Ya isa ga Daddy ya durkusa a kan gwiwoyinsa, ya mika mishi yana kallon shi yana murmushi.
"Amshi Daddy!". Ya fada, cikin sautinsa mai sanyi.
Sai da ya yi kwafa sannan ya amsa, ya zauna ya ce,
"Lumbu-lumbu wutar kaikayi, ai ka iya munafuncin da dole mutum ya karbi lallashinka".
Ya sha lemon, Aliyu yana durkushe gabanshi, ya kwantar da kai a cinyoyin Daddyn ya ce.
"Ka yi hakuri Daddy, zan biyaka kudin kayanka, amma ba zan bada kayan ba!".
Alhaji Suraj, ya aje kofin bisa tebur ya dube shi sosai ya ce.
"Wai meye illa a sana'ar Tobbacco ne da ka bi ka sawa kahon zuka?".
A raunane ya ce,
"Daddy it is harmful ga lafiyar matasan mu. Wadanda sune iyayen gobe, kuma shuwagabannin gobe. Kai kanka in ka yi tunani ai ba sha kake ba, sabida ka san tana cutarwa, amma kana sayarwa.
Abinda kasan bazaka ci ba, ai bai kamata ka bari wani yaci ta hanyarka ba. Bayan kana sane da cewa illa ce ga lafiyar al'umma".
Ya yi shiru, yana kallon dan nasa. Wai ka haifi da a cikin ka ya fika hankali. Ya gaza cewa komi, sabida yadda Aliyu ke magana cikin sanyi da girmamawa, tare da lallashi mai sanyawa dole ka yarda da shi.
Ya mike, Aliyu ma ya mike, ya kama hannun Daddyn har gaban motarsa kirar 'Opel-Astra' baka wuluk, sai sheki take, ya bude mishi ya shiga shima ya zaga ya shiga mazaunin direba, ya ja motar suka fita daga harabar ma'aikatar suka harba kan titi.
Gidanshi dake Victoria Island ya nufa kai tsaye, suna tafe yana jan Daddyn da hira mai ban dariya, tun yana kumbure-kumburen, har ya ware suka rika hira da dariya.
Suna isa ya tarar kukunsa Jim ya kammala hada abinci bisa 'dining'. Sai da suka fara yin sallah tukunna suka ci abincin, Daddy ya huta.
Aliyu bai gushe ba yana lallashin Daddyn a kan ya canza sana'a, shi kuma ya kafe kan cewa sana'ar da ta amshe shi kenan, kowa yana da hanyar abincinsa, to shi tasa kenan.
In kuma shi din yana da wata sana'ar da yake ganin za ta karbe shi to ya samo. A take Aliyu ya ce.
"Daddy mu gwada sana'ar fata man da kasar Italy? Ana samu sosai".
Ya ce, "To zai yi tunani".
A haka suka rabu ya kai Daddy Airport din Murtala Mohammed ya bi jirgi ya koma gida.
Aliyu ya girgiza kai yana murmushi, ya koma office yana mai godiya ga Allah da Ya daura shi yau a kan mahaifinsa Alhaji Surajo Tobbaco.
Ya dade yana kyamar sana'ar Daddyn, sai yau Allah Ya sa ya samu kan birkitaccen Daddyn nasa.
Ya soma addu'a cikin zuciyarshi kan Allah Ya sa sana'ar da Daddyn zai canza ta zamo mafi alkhairi a gare shi, kuma mai albarka.
****
Saukar Aliyu kenan daga Lagos ranar Juma'a da yamma, ya bude waya yana kiran Mamanshi ya ce,
"Ina Airport Mama a turo Danlami ya zo
filin jirgi ya dauke ni".
Mama ta ce, "Ya tafi Kumo dauko Gwaggon Kumo ba ta jin dadi, gani nan da kaina ka jira ni".
Ya ce, "A'ah Mama ki zauna kawai zan yo shatar taxi, bana so kina 'dribing' dinnan, ina Hanifah?"
Ta ce, "Hanifah ma ta je bikin kawarta a Mubi, ni kadai ce a gidan".
"To yi zaman ki Mamana, ba zan iya jira ba gani nan".
Ya rufe wayar ya sanya a aljihun coat dinshi, yana rataye da karamar bakar jaka mai dauke da 'Ipad' da sauran muhimman abebaden shi.
Ya fito daga filin jirgin ya tadda taxi-taxi masu jiran mai daukan su shata, ya samu daya ya hawo ya ce "Shango Estate".
Sanda suka iso, Mama na harabar gidan, kamar ta rungume dan tilon dan da Allah Ya bata. To saidai fillancin, ya hana.
Hannun su cikin na juna suka isa cikin gidan, fuskar Hajiya Maimuna fal far'a kamar wanda ya shekara bai zo ba.
Rabon su da juna yau watanni uku kenan, shima ya yi kewar Mamansa. Yadda ba'a zato. Abinci kala-kala Maman ta shirya mishi har kala biyar, duka babu wanda ba fabourite dinshi ba;
Ga dai Sinasir da miyar ganye, ga Kisra da miyar bindin saniya, ga beef sausage, da stuffed atomy. Duka babu wanda ba zabinsa ba, ya fita masallacin dake makale da gidan ya yi sallah, can suka hade da Daddy suka taho gida tare.
Mama ta yi serving dan lelenta tana ta zuba mishi hira, sannan ta yi serbing Daddy. Shi dai yana kallon ta yana dariya a cikinsa, kaunar Hajiya Maimuna da danta Aliyu Haydar sai Allah, sam ta manta da Daddy balle ita kanta. Sai shi Daddy ne ya cika filet ya tura mata, ya ce,
"To kowa ya kula da nashi". Aka sa dariya gabadaya.
Bayan sun kammala Asabe mai aikin Maman ta fidda komai ta gyara 'dining'. Daddy da Aliyu na bisa 'cushion' suna tattauna lamarin da ya shafe su.
Daddy ya ce,
"Har gobe ina alfahari da haihuwar ka Haydar, kai din nan kwaya daya ka fi min gayyar 'ya'ya goma. Shi yasa aka ce da daya kwakkwara, ya fi taron dubu yuyuyu.
Duk shawarar da ka bani in nabi ina ganin fa'idarta. Yaro da tunanin manya.....ina alfahari da kai da haihuwarka ALIYU-HAYDAR. Allah ya yi maka albarka.
Sai dai kuma alfaharin nawa ba zai cika ba, sai na ganka da iyalinka, kamar kowanne managarcin mutum, kullum addu'ata kenan Aliyu-Haydar, Allah Ya nuna min'ya'yanka kamin ya dauki raina".
Aliyu wanda kansa ke sunkuye bai dago ba, sai dai kuma da zai dago din, da Daddyn ya ga yadda fuskarshi ta sauya zuwa wani kwantaccen bacin rai.
Shi fa sam, babu aure cikin lissafinsa, domin a ganinsa duk 'yammatan zamani halinsu daya (yaudara, kwadayi da rashin sanin darajar da Allah ya yi musu ta 'ya'ya mata uwayen al'ummah, tareda rashin sanin darajar soyayyah ta hakika) irin tsohuwar masoyiyar shi (Shareekah).
Don haka har Daddy ya gama maganganun shi bai ce komi ba. An sosa wa Mama inda ke mata kaikayi.
Ta muskuta ta ce,
"Ga 'yar'uwarshi ma Hanifah ta ki kowa sai shi, ta dauki soyayyar duniya ta dora a kansa. Amma ya yi shakulatin bangaro da ita.
Meye laifin Hanifah saboda Allah Daddy? Yarinya mai kyau, ilimi da asali. Sannan gata 'yar'uwarshi wadda ta san ciwon sa.
Ni kam in har kana son albarkata da farin cikina to ka aje waccen kabilar daga ranka ka auri 'yar'uwarka mai so da kaunar ka saboda Allah".
Kanshi dai na kasa bai dago ba, sannan bai ce komi ba har suka yi shiru. Ya mike yana cewa,
"Zan je in huta Mama, ruwa zan watsa in kwanta zuwa maghriba. Amma idan har Gwaggo ta iso, to a taso ni". Ya sa kai ya fita.
Uwar da Uban suka bishi da kallo. Kafin da su saki ajiyar zuciya a tare. Sun rasa mece ce matsalar dan nasu ta kin aure.
Mama ta kasa shiru ta ce, "Nifa ina tsoron anya haka Bayerabiyar nan ta barshi? Tunda suka rabu ya daina zancen aure, ya kuma tsani ayi masa.
Gashi ni Allah bai bani yawan 'ya'ya ba, burina kadai in ga 'ya'yanshi na yawo cikin gidan nan".
Daddy ya yi murmushi ya ce,
"Ki bishi a hankali, komai lokaci ne. Idan lokacin aurensa ya yi ko yana so ko ba ya so dole zai yi. Ki daina turasasa shi a kan zancen Hanifah, ko don ki saya mata mutunci a idanunsa.
Gobe in Allah Ya kaimu zan ga liman Halilu a fara yi mishi addu'a. Insha Allahu kwanan nan Aliyu zai yi aure, ina ji a jikina".
Mama ta ce, "Toh, Allah Ya yarda".
Suna haka suka jiyo tsayuwar mota, Danlami da Gwaggo sun iso kenan. Daddy ya mike ya fita ya shigo da mahaifiyarsa, Mama kuma ta nufi dakin da take sauka ta duba an gyare ko'ina.
Ga katifar gado an sauke mata ita kasa. Kasancewar bata yarda ta hau gado. Anyi shimfida ta alfarma. Dan firjin dake gefe cike yake da ruwan FARO da fresh milk din Oldenburger, da madarar Hollandia, an saki labulen, an kashe fanka da A.C, duk don Gwaggo ba ta son ko daya daga cikin su.
Ta kunna 'burner' ta zuba turaren wutar bakhour, ta jawo kofar ta fito tana lale da Gwaggo.
Gwaggo Hassana ta zauna cikin luntsuma-luntsuman kujerun falon suka gaisa, gaisuwa ta mutuntawa da ganin girman juna da sirakuta. Sannan suka shiga labarin 'yan'uwa da abokan arziki dake Kumo. Sannan ta tambayi Maman Hanifah Innani, da dan lelen ta, jika kwaya daya ya tsoka daya a miya, Aliyu-Haydar.
Nan Mama take gaya mata yadda su kai da shi yanzun nan, kan cewa zai je ya kwanta ya huta, idan ta iso a taso shi.
Gwaggo ta yi dariya ta ce, "Haydara Zakin Manzo kenan. Kyale shi dai ya yi barcin shi ai ina cikin gidan duk sanda ya tashi ya ganni".
Mama ta ce, "Gwaggo hawan jinin ne dai har yanzu?"
Ta ce, "Uhm! Bari ke dai Maimuna, jikin girma sai a hankali. Ga hawan jini, ga ciwon kafa da baya, sannan ga tarin fika, duk ni kadai".
Ta yi tarin kuful-kuful, ta ci gaba da cewa, "To ya za a yi? Girman kenan!".
Mama ta ce, "Allah Ya kara sauki Gwaggo, bari ya fito sai ku tafi asibitin".
Ta ce, "Ni kam ba inda zan iya zuwa a yau dai, sai ko gobe in Allah Ya kaimu, kafin nan na huta daga jijjigar motar nan da ta kara min ciwon jiki".
Cike da tausayawa Hajiya Maimuna ta ce, "To Allah ya kaimu goben. Da yau da goben duk daya ne. Ta so muje ki kintsa, ki sha 'panadol', zaki ji saukin ciwon jikin".
Ta kama hannunta ta mike suka nufi dakin saukar tata. Mama ta koma ta kawo mata abinci, ta fiddo ruwa da madara. Ta zauna tana zuba mata abincin suna hira.
Da ta kammala ta sha ruwa da madarar, ta kishingida ta ciro goro cikin ledar kayanta tana ci.
Mama ta hada kayan ta fita dasu da kanta ta kuma fara aikin tuwon acca miyar kubewa danya, wanda Gwaggon ta ce shi take so ta ci da dare.
Karfe biyar dai-dai Aliyu ya tashi daga daddadan barcin da ya sure shi. Ya kai idon shi ga agogon bango, da sauri ya tashi yana "Subhanallah! Lokacin maghriba, ya fita, ban yi sallah ba".
[9/4, 12:57 PM] Asmau: Ko da yake ga dukkan alamu, almajira ce, ko daga annakiyar daudar ta, da ratattakakkun kayan jikinta, da himilin gashin kanta da aka yiwa wata irin tufka kamar ciyawa.
Doctor Misau ya dubi Aliyu ya ce,
"Kai Yayanta ne?"
Kawai sai ya samu kansa da cewa "Eh, mota ce ta bige ta".
Ya girgiza kai ya ce, "Ta samu karaya har biyu a kowacce kafa, sannan ta ji mummunan rauni a kanta, wanda muke addu'a Allah ya sa kwakwalwarta ba ta tabu ba, ta tashi cikin hayyacinta.
An dora dukkan kafafun anyi mata dinki a kan. Sai mu ci gaba da addu'a Allah Ya takaita ya kuma tashi kafadunta".
Ya ce, "Ameen".
Doctor ya ce, "Sai ka je ka biya 'bill' din ka".
Ya mike ya fita. Ya shiga dakin da aka kai yarinyar ya ce,
"Gwaggo taso in kai ki gida in yaso sai Asaben Mama ta zo ta zauna da ita kamin a sami iyayenta, zan je in biya 'bill' in zo mu tafi".
Ta ce, "To, Allah ya kiyaye gaba".
Ya ce, "Ameen".
Da suka shiga gida Mama na kicin tana kiciniyar hada abincin dare. Jin shigowar su ta fito falon ta ce, "Lafiya kuwa? Ina kuka makale ina ta kiran layinka a kashe?"
Gwaggo ta zauna tana cewa,
"Tsautsayi kawai Maimuna, yarinya muka bige duk ta karairaye, kai ya fashe, kuma ba a san daga ina take ba balle iyayenta".
Mama ta ce, "Subhanallahi! Garin ya ya?"
Gwaggo ta ce, "Garin gangancin sa mana? Kin ga irin gudun da yake yi kamar ya tashi sama, ina ta fada amma ko ya kalle ni. Kai wannan halin miskilancin na Haydara bai yi ba wallahi".
Shi dai bai tanka ba, ya nufi 'side' din sa ya sakar ma kanshi 'shower', ya yi alwala ya rama sallolin da bai yi ba, ya canza zuwa caftan na wata jikakkiyar shadda rini, mai ratsin baki da toka-toka (grey).
Ya taje sumarsa wadda ke kwance linkib tana sheki saboda samun kulawa. Yana taje sumar, hoton yarinyar da ya buge dazun nan na gilma mishi, hankalinshi a tashe yake kwarai, don dai bai nuna bane kada Gwaggo ta samu gangara ta ci gaba da yi mishi bala'i, shi yasa kawai ya yi shiru, amma ko kiyashi ba ya fatan ya kade balle dan mutum bani Adam.
Cikin gidan ya shigo lokacin Gwaggo na dakinta tana sallar isha. Ya tadda Mama da Asabe a kicin, ya gayawa Mama zai koma asibitin ta ba shi Asabe ta dinga kwana da yarinyar kamin ta ji sauki ta fadi inda iyayenta suke a kaita.
Tuni Mama ta hada abinci cikin dan karamin kwando har da fulas din ruwan zafi da kayan shayi, da duk abin da maras lafiya zai bukata ta fannin abinci mai ruwa-ruwa da maida kuzari, ga su 'lucozade' da