Showing 63001 words to 63435 words out of 63435 words

Chapter 22 - Amanata HAUSA NOVE

ASMAU   

11 Nov 2024

19034

ta. Don Asabe ce mata take "Mungo Park ma mun ga karshen sa balle ku asararru, nasara asarar duniya, tun da aka haifesu nake goyasu kafafun su basu lankwashe ba sai yanzu da kike tare da su? Da wani wuyanki kamar marikin lema, "
Ba kuma ruwanta da cewa Synthian din ta ji abinda take cewa ko bata ji ba? Asabe kenan.
Ranar litinin Muhaseen ta fara daukar lacca a jami'ar Abuja don 'Baze' basa bangaren da Dr. bello ke so, tana karantar medicine, za ta yi specializing a kan Idanu, kamar yadda Dr. Bello ya zabar mata. Ko don gorin ilimi da aka yiwa Ummanta, ya ce ba za ta yi karamin karatu ba. Balle wani aikin sadarwa.
Insha Allahu idan ana kure ilimi sai Muhaseen ta kure shi, ko da zai rasa duk abin da ya mallaka a duniya. Balle kuma mijinta wanda ya lullube ta da duk wata alfarma da dan Adam ke nema a wannan duniyar don kyautata rayuwar shi.
Muhimmi shine soyayyar da yake yi mata, da kwarin gwiwar da yake ba ta akan dukkan al'amuranta.
Sai dai kuma ba a dade da fara karatun ba laulayin ciki ya ce salamu alaikum. Oga Aliyu bai yi da wasa ba, burin shi duk shekara a haife mishi da, don haka Oga babu sassauci.
Haka Muhaseen ta daure ta cije take jifan tsuntsu biyu, da dutse daya. Wato haihuwa, kula da maigida da sauke dukkan hakkokinsa dake wuyanta da kuma karatun, tunda ba ta nemi komi ta rasa a rayuwar ta ba.
Shekara na zagayowa ta sake dire musu 'yan biyu, maza zar. An bar musu sunan su wato Hassan da Hussaini.
Dr. Umar ya kwashe Arfat da Taufeek tunda aka yayesu. Muhaseen ta tattara kayan Leena da komai nata ta dankawa Hanifah. Wadda a lokacin ita ma yaron ciki ne da ita. Sai dai ba mai laulayi irin na Muhaseen ba. Babu wanda bai yi murna ba, kuma Aliyu ya bude mata office nata na kanta a matsayin lauya mai zaman kanta a nan Abuja.
Haihuwa akufi-akufi ga Muhaseen don shekarar su Hassan biyu ta haife Gambo mai sunan Ummanta, wato Halimatus-Sa'adiyyah.
Hanifa yaro namiji ta haifa mai kama da Arfat da Taufeek. Suka hada kai suka rungume mijinsu suna tarbiyyantar da 'ya'yansu. Ga albarkar da iyayensu ke sa musu kullum.
Umarah ba ta wuce su duk azumi, daga farkonsa har karshen sa, haka aikin Hajji duk shekara. Ko zuwa hutu Abha da Jeddah. Suma basa shekara basu zo ba. Rayuwarsu, (in ji MUHASEEN) sai "ALHAMDULILLAHI!"

Masha Allah Lakuwwata Illa Billah!.
Anan na kawo karshen littafin Amanata. -ina godiya ga duk makaranta litttafan Takori, Allah Ya sada mu da alherinsa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login