Showing 60001 words to 63000 words out of 63435 words
Watanni uku kamar yau ne, za ka zo ka dauke su in Allah Ya yarda".
Ya langabar da kai kamar karamin yaro, ko da yake duk girman mutum a gaban mahaifiyarshi yaro ne.
Ya ce, "Mama sai in zauna ni kadai kwal kamar maye? Ita waccan kun ce na barta tai aikinta, na barta. Wadda nake da 'hope' a kanta kun hanani.....ba abin da zai samu jikokinki Mama.
Zan yo hayar 'proffessional Nanny' daga (Stratford) har itama Muhaseen ta koma makaranta, don admission da na nema mata a jami'ar 'Baze' ya kusa fitowa".
Mama ta ce, "Kai! Kada fa ka dame ni da tsari, na ce ba za su tafi ba".
Ya mike a kumbure ya ce, "Na tafi Mama, na barki lafiya".
Ta ce, "Umma ta gaida Aissha".
Duk Muhaseen tana jiyo su daga daki, tana dariya, sai kuma tausayin Baban Arfat din ya kama ta. Duk jikinta amsawa yakeyi da son sa da kaunar sa. Bata ga dalilin da Mama zata dinga kyarar sa ba akan jikokinta, ta ma lura Mama ta fi son jarirannan akan Aliyun, sai kuma tayi la'akari da Karin maganan nan da hausawa suka ce "abin cikin kwai ya fi kwan dadi".
Washegari da safe ya zo musu sallama zai wuce Abuja. Kallon Muhaseen yake da idanunshi da suka kankance suka yi ja. Zaka iya karantar tashin hankalinsa da damuwarsa karara. Yana zaune a gefen katifarta da Leena a hannunshi.
Ya sumbaci bakin ta ya ajiye ta, ya dauko Taufeek yana shafa gashin kanshi. Muhaseen ta kwantar da kanta a bayan shi ta ce.
"Ka yi hakuri Baban Arfat, kamar yau ne wata ukun za ta cika, don Allah mu yiwa Mama biyayya, da alheri take son mu ba wani abu ba, ka duba ka gani tun haihuwar nan bata kara zama ko na rabin awa ta huta ba, sai hidimarmu, ko bacci bata yi sabida farkawar yarannan cikin dare suyi ta ihu in rasa yadda zan yi dasu ita kadai ke iya lallashinsu, ko Daddy bata da lokacinsa wallahi".
Ya ce, "Ai na hakura Muhaseen, ina tunanin yadda zan jure rayuwar ne ba tare da ku ba". Murmushi tayi, tasa yatsan ta cikin 'cleft' dinsa (lotsawar tsakiyar gemu), ai kuwa ta kara kunno shi, ya janyota jikin shi dake masifar rawa yana cewa "matso nan don Allah in ji dumin jikinki, in sumbace ki kadan ko na samu sa'idah".
****
Bayan tafiyarshi Mama ta shigo dakin ta sauke Arfat dake bayanta a gadonsa, ta ja lallausan shawul ta lullube shi. Ta dauki takwararta tana canza mata diaper, ta dubi Muhaseen ta yi dariya ganin yadda take daddauke mata kai.
Ta ce, "Wai ke yanzu saboda Allah in aka ce ki bishi sai ki bishi? Duk wahalar da kika sha kin manta har kina marmarin yin wata kwana biyu ko?. Ga 'ya'ya bul-bul cikin koshin lafiya amma kina so ku lalata su?".
Ta yi shiru bata yi magana ba. Mama ta ce, "To ki bishi mana, amma wadannan bayin Allah babu inda za su je, ki bar mini su".
Ta ce, "Kai don Allah Mama, ni na yi magana ne?'
Ta ce, "Uh-uh! Na ga dai kina harara ta ne a fakaice. Gata nake miki, ya dandana rashinki na lokaci mai tsawo zai fi marmarin ki".
Ta yi dariya ta ce, "yayi marmari na sai ka ce wata abinci Mama?"
Ta ce, "Abinci ce mana, abincin Aliyuuu".
Ta rufe fuska tana dariya, kunya kamar tace da kasar ta tsage ta shige, itama Maman ta fada ne daman don tasa ta dariya.
Tunda ya tafi bai kara waiwayo su ba, ayyukan dake gabanshi kawai ya sa a gaba. Dr. Saudah ta yi mishi waya bayan sun gaisa ta ce, "In da hali me zai hana ya yiwa Hanifah shirin tafiya Belarus (Russia), akwai wata shahararriyar likitar mata malamarsu a Kuala Lampur, ta duba ta sosai. Irin wadannan matsalolin kanana ne a wurin ta. Ita za ta raka ta har Russia. Ya ce ba matsala zai mata biza kuma zai dauki nauyin komai.
Cikin sati biyu biza ta kammala, sai dai jirgin Saudiyyah Hanifah ta hau, suka hadu da Dr. Saudah. Kwanan su uku a Jiddah suna karasa shirye-shiryen tafiyar, a rana ta hudu suka daga kasar Russia.
****
A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah, yau su Muhaseen sun cika wata hudu, 'yan uku sun fara koyon zama, sunyi bulbul dasu tubarkallah.
Don haka Mama ta shirya musu tafiya yawon zaga dangi. A lokacin Hanifah ta dawo daga Belarus, tana kan treatment din Dr. Janny.
Har da Mama da Asabe aka yi shirin tafiyar. Tripple sun sha ado, kamar ka sace ka gudu. Kumo aka fara zuwa.
Gwaggo ta rasa ina-taka-saka-ina-taka aje da 'yan tattaba kunnen ta, gidajen dangi daya bayan daya tasa aka raka su. A ranar suka juyo da abin alheri fal bayan motar su, hatta Danlami ya samu kaji biyar, zabbi biyar da kwarya cike da kwan zabo.
Washegari dangin Mama dake nan cikin Gombe aka zage, daga nan suka wuce Dukku. Abin tausayi Turaki yana kwance babu lafiya duk 'ya'ya da jikoki sun zo.
Dr. Umar ma da mai dakinsa suna can. Duk da haka dangi sunyi murna da ganinsu, har Aunty Badi'a tana nan.
Turaki yana daga kwance amma bai kasa gane Muhaseen ba, aka jera masa tripple a gabansa, idon shi a rufe yake shafa kansu yana murmushi yana yi musu addu'a.
A nan suka kwana bayan sun je gidan Mal. Tanko sun ga yara. Cikin dare jikin Turaki ya rikice kuma ya ki yarda a kai shi asibiti, sai likita aka kirawo yake ba shi taimako a dakin sa.
Da aka yi sallar asuba Dr. Umar da Hajiya Dijah suka shigo don su ga ya ya jikinsa, sai suka tarar ya rasu.
Wannan 'family' sun ga tashin hankali irin wanda basu taba gani ba. Muhaseen kuka take sosai saboda tana kaunar dattijon ba kadan ba. Ga sabo da shakuwa, ga kaunar da yake mata ita da Ummanta. Dr. Omar kuwa hawan jinin shi ne ya tashi sai da likita ya ba shi taimako.
Wayewar garin dubban al'ummar garin Dukku da wajenta suka halarci jana'izar mutumin kirki mai kaunar talakawa San-Turaki Abdullahi. Muhaseen ta gode Allah da tana nan Turaki ya rasu ba labari aka ba ta ba, kuma ya ga 'ya'yanta. Sannan ta yi mishi addu'a tun kan a saka shi a kabarinsa. Wannan gagarumin rashi shi ya tunkudo Baban Arfat gida a ranar sadakar uku. Aka ci gaba da karbar gaisuwa da shi.
Tunda ya zo bai ga Muhaseen ba saboda yadda gidan ya cika, gashi yana jin kunya ya aika wani, kuma ta rufe wayarta, yana so ya yi mata ta'aziyya don ya san yadda take son Turaki.
Sai Aunty Badi'a ya kira ya ce don Allah ta turo mishi Muhaseen soro na uku. Ta ce za ta zo yanzu. Ta kuma sa aka bude mishi wani karamin falon Turaki, da kyar ta ga Muhaseen a dakin Hajiya Antu tana tare da Mama da Dr. Salwa.
Ta kamo hannunta ba tare da ta ce da ita komai ba har zuwa karamin falon sannan ta sake ta ta juya.
Sanye yake da shaddar 'getzner' baka wuluk, sai sheki take dinkin Mohammed. Kin san bakar kala a jikin farin mutum mai gogaggen jiki, kanshi babu hula, sumar shi ta kara kwanciya sosai a wuyanshi ta fulanin usli kai ka ce bako ne daga 'Frankfurt'. Agogon 'Swatch-blustery' sai sheki yake cikin tattausar fatar hannun shi.
Tana isowa bude hannuwa ya yi ya rungume ta, yana yi mata ta'aziyya. Sai a lokacin ne da ta ji ta jikin Baban Arfat ta samu hawayenta da suka kasa zuba suka balle a kan kuncinta.
Ta kara rungume shi itama ta ce, "Na yi rashin mai kaunata Yaya Aliyu!".
Ya ce, "Bai yi gaggawa ba Muhaseen, dukkanninmu na haka ne. Gashi ya mutu kowa na fadin alherinshi, dubban jama'ar da suka halarci jana'izar sa kadai abin farin ciki ne a gare mu, ya samu kyakkyawar shaidah!".
Kinsan ance duk mutumin da akallah ya samu mutum arba'in a jana'idarsa ana yi mishi kyakkyawan zaton rahmar Ubangiji. To Turaki ya samu sama da dari, don haka muyiwa Allah godiya abisa rahmominsa a garemu".
Ya zaunar da ita bisa tuntu, shi kuma yana kan carpet. Ya kama hannayenta biyu ya dago habarta yana dauke hawayenta da halshen sa.
Ya soma sumbatar ta a take ya gigita ta ya mantar da ita bacin ranta. Sannan ya sake ta ya ce ta je ta debo su Taufeek ta kawo mishi.
Ta ce, "Ba zan iya ba kunya nake ji suna dakin Hajiya Dijah, ni ba a dakin ma nake ba".
Ya ce, "To meye labari? Mama har yanzu tana nan tana ta wanke ku ko? Ni ba ta tausayina, ba ruwanta da halin da nake ciki balle me nake ci?".
Ta yi murmushi ta ce, "Allah sarki Mama, wallahi kullum tana zancen ka".
Ya ce, "To me take cewa?"
Ta ce, "Haka kawai sai ta ce, Allah sarki Baban Arfat, yana fushi dani ko waya ba yai mini. Ko in suka rikice mata da kuka sai ta ce, "ku yi shiru in dai don ubanku ne ban raba ku ba, so nake ku yi kwari kada ya lalata ku".
Ya yi dariya sosai ya ce, "Mamana kenan, ya ya za ai in lalata su?"
Muhasin da ba'a rufa asiri da ita ta ce, "Oho! To nima dai ban sani ba, don ban tambaye ta ba. Amma ta ce in na bika wani cikin zan samu da wurwuri su kuma wadannan su lalace".
"Mama kenan, wato har 'ya'yan sun ishe ta ita mai cewa so take in cika mata gida da 'ya'ya?".
Ta ce, "A to, nima dai ba zan sake yarda da wannan abin ba, don baka san ya ake haihuwar ba ne...". Ta sake kwanciya sosai a jikinsa tana cigaba da cewa "babu maraba da ciwon mutuwa" Ya yi dariya sosai irin wadda ya dade bai yi ba, ya ce, "Ni da nake addu'ar 'nedt year' mu haife 'yan hudu?"
Ta yi mishi wata irin hararar kauna kamar ta hadiye shi, ta ce, "A'a, mantawa ka yi 'yan shidda, tunda nice akuya sarkin haihuwa".
Ya rungumo ta yana 'kissing' ya ce, "Ba tare muke nakudar ba? Ko ba ina tayaki ba? Insha Allahu har 'yan goma sai mun haife".
Badi'a ta yi sallama tana dauke da Arfat, 'yarta Husna da kanwarta Jamila suna dauke da Taufeek da Leena.
Mikewa ya yi yana godiya ya karbi Arfat da hannu daya, Taufeek da hannu daya, ya ce, "Shi yasa nake son ki Auntyna".
Murmushi ta yi ta ce, "Koh?' yace "wallahi.."
Su Husna suka gaishe shi, Jamila ta dorawa Muhaseen Leena a cinyarta suka juya suka fita.
Sai ya jere su a kan lallausar 'carpet' din yana yi musu cakulkuli suna ta bangala dariya. Ya koma sunsunarsu da sumbatar su, yana ta mamakin girman su. Don kauna kamar ya hadiye su. Ya ce,
"To yanzu yaushe za ku koma gida?"
Ta ce, "Mama ta ce sai anyi addu'ar bakwai".
Ya ce, "To Allah ya kaimu, ni zan koma, zan dawo upper week ki taya ni rokon Mama ta bani ku. I promised to take care of you, as I'll take care of my nakedness...... karshenta dai kenan ko? Ki nunawa Mama muna bukatar juna don Allah ki daina fulako. Don ita ba ta san shi ba".
Ta yi dariya ta ce, "Wallahi babu ruwana, duk abin da Mama ta ce shi zan yi".
Ya tsare ta da kaifafan idanunshi sosai, "Umarnin Mama ya fi nawa?"
Ta ce, "Don Allah ka bari, ni ba nufina kenan ba. Amma ka san ba za ta ce in yi abu in ce a'a ga yanda zan yi ba".
Ya kwantar da kai a kafadunta yana sunsunar ni'imtaccen kamshin ta ya ce, "You are right Muhaseen, balle ma insha Allah ba za ta hana ba".
Ta ce, "Ina Aunty Hanifah? Ba za ta zo ba?"
Ya ce, "Watakila ba ta sani ba, ko kin mata waya?"
Ta ce, "Ni tunda muka zo na ga Turaki ba lafiya ban kara tuna inda na jefa wayar ba".
Da kyar suka yi sallama ya debi biyu ta dauki daya ya rakata har soron karshe, sai ga wata dattijuwa za ta shiga, ya bata yaran ta dauke su suka shiga ciki shi kuma ya juya.
Washegari Muhaseen ba ta zata ba ba ta tsammana ba, ta fito daga wanka sai ganin Ummanta ta yi zaune tare da Mama ita da Dr. Saudah.
Ba don gidan makoki bane da ihu za ta saka, sai ta karaso a hankali ta rungume Ummanta.
Ta ce, "Ummana na kusa lekawa lahira amma baki zo kin ganni ba".
Ta ce, "To ai gashi na zo yanzu, kin dawo daga lahirar lafiya?".
Ta shagwargwabe fuska ta ce, "Wallahi ba wajenmu kika zo ba, gaisuwa kika zo".
Ta koma ga Dr. Saudah itama ta rungume ta tana ta yi musu shagwaba suna biye mata.
Ranar da aka yi sadakar bakwai suka nufo Gombe, su Umma Maiduguri suka wuce, daga can za su tashi har uwargidanta. Ta wuce tare da su Ta-Birni da Maigari da Hajiya Tafisu, duk tare za su tashi aikin Hajji.
Lokacin da Aliyu ya dawo a sati na sama Mama ta gama duk gyaran da ta ke so ta yiwa Muhaseen. Don haka ta yi musu izinin tafiya washegari tare da Asabe.
Ta yi musu shirin tafiya sosai, wannan karon a mota suka tafi. Aliyu na tuki tana gefensa rungume da Arfat, Asabe na baya rike dasu Leena. Dole ya kashe A.C saboda yaran sun soma atishawa.
Tafiya sannu-sannu mai dadi, da sanya nishadi, suna tafe suna hirarsu ta masoyan da ke tsananin kaunar junansu.
Sun tsaya a Kaduna a 'masjidul musafir' sunyi sallar azahar da la'asar kasaru, sannan suka dibi hanya basu tsaya ba sai a Minna. Suka shiga wani gidan abinci suka ci abinci sannan suka mika har Allah ya kawo su Birnin Tarayya lafiya.
****
Rayuwar Muhaseen a Abuja da 'ya'yanta da maigidanta Controller Aliyu Suraj Kumo, rayuwa ce da aka gina ginshikinta da soyayya ta gaskiya da AMANA, irin wadda tayi karanci a wannan zamanin. Rayuwa ce abar kwatance, kuma abar sha'awa ga duk wanda ya san me rayuwa ke nufi.
Rayuwa ce wadda ke cike da kauna da soyayya, yarda da girmama juna. Babu abin da suka sanya a gaba daga aikin shi sai kula da 'ya'yansu da taimakon jarumar dattijuwa Asabe.
Da dai Hanifa ta ga abin ba dama, domin Baban Arfat ya manta da ita, ba ta gabanshi kwata-kwata. Sai ta sallama aikinta na Gombe akan kashin kanta, don sai ya yi watanni uku bai neme ta ba, 'ya'yanshi da matarshi sune kawai a gabansa.
Tana kuka ta gayawa Mama, ita ma za ta koma Abuja. Ta ce, "Aikin fa?"
Ta ce, "Na hakura Mama, ban da kudi, me nake samu? Ba soyayyar miji, babu 'ya'ya! Babu bautar aure domin tanadin gobe kiyama!".
Mama ta sa habar zaninta ta share hawaye saboda tausayin Hanifah, ta ce, "Ta je ta debo kayanta ta rufo gidan ta kawo mata mukullin".
Ta yi yadda mama ta ce. Mama da kanta ta sa ta a mota Danlami ya ja su zuwa Abuja.
Yana tsakiyar babban falon shi daga shi sai singileti da 'short nicker' yana yiwa su Arfat sukutun doki suna ta kyalkyala dariya, Leena na cinyar Mamanta tana jera mata 'ribbons' a gashinta wanda ya yi tsaho sosai, ga sulbi da santsi sai sheki yake saboda samun kulawa.
Kararrawar kofar shigowa ta yi kara har sau biyu, Muhaseen ta aje Leena a cikinsu ta nufi kofar ta ce, "Waye?"
Mama ta ce, "Baki ne".
Da sauri ta bude tana dariya ta rungume Mama, ta sake ta ta rungume Hanifa sannan ta yi musu jagora zuwa ciki.
Baya falon ya shiga dakinsa domin ya sauya kaya. Su Arfat duk sun makalkale Mama, Leena kuwa tana kwance jikin Hanifa. Yarinyar na sonta sosai, ita ma tana son ta kamar ita ta tsuguna ta haife ta.
Ya fito cikin jallabiya ruwan toka ya zauna a kujerar dake fuskantar Mama suka gaisa, aka tambayi lafiyar juna data iyali.
Ya ce, "Mama zuwa haka babu sako babu waya? Allah dai yasa lafiya".
Ta ce, "Lafiya kalau, Hanifa na rako".
Ya daga oily eyes dinshi a slow ya dubi Hanifan, ya ce, "Wani abu?"
Ba ta yi magana ba, sai ma ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsun Leena. Mama ta gyara zama ta ce.
"Ta dawo nan ne don na ga alamar ba za ka iya rike mata biyu ba a gari daban-daban, shine ta dawo nan, a gyara mata dakinta".
Ya ce, "To dama Mama wa ya ce kada ta zauna? Ita ce ta nuna ba ta son zaman. To amma aikin nata fa?"
Ta ce, "Ka yi mata 'transfer' in zai yiwu ta dawo nan, in ba zai yiwu ba ka nema mata wani".
Ya ce, "Shi kenan ba matsala, Muhaseen za ta fara zuwa makaranta sati mai zuwa, sannan Nanny dana hayo daga (Stratford) za ta iso gobe, duk hidimar yaran tana wuyanta.
Asabe sai ta kula da gida da kitchen a ci gaba da yi mana addu'a".
Mama ta ji dadi sosai, ta ce, "Addu'a kam kullum yi muku muke, Allah Ya raya muku zuri'arku, Ya baku hakuri da juna, Ya kuma yi muku albarka".
Duka suka amsa da "Ameen".
Tarbar girma Muhaseen ta yiwa Mama da Hanifah, girki na musamman ita da Asabe duk da ba ta san me ya kawo su ba.
Sai bayan Mama ta ci abinci. Ta huta a dakin Muhaseen take yi mata bayanin dawowar Hanifa wajen su.
Ta ce, "Kai Mama na ji dadi, kuma hakan ya fi. Wallahi kullum da tunanin da nake kwana nake tashi kenan, mu zauna waje guda don Baban Arfat baya son jaura, kuma idan ya fita tun safe sai dare, wani zubin ma a office suke kwana ga yawan tafiye-tafiye".
Da kanta ta je ta gyara dakin Hanifa fes ta shigar da kayanta, don tunda suka shiga daki ita da mijinta ba ta kara jin duriyarsu ba.
Asabe ke ta hidima da yara, ita kuma tana tare da Mama suna tattauna matsalolin su da na 'yan'uwa.
Washegari Mama da Danlami suka juya. Kuma a ranar ne Nanny Synthia ta iso Nigeria, babba ce sosai don za ta yi shekaru arba'in da biyar.
Aka sauke ta a dakin yaran wanda ke cike taf, da duk abin da zai sa yaro farin ciki. Tun daga kan motoci da jirage masu aiki da batir, liluna, teddy da ire-iren su.
Synthia ta soma kula dasu, Asabe ma in ta gama ayyukanta, goya su take, tun Synthia na bala'i har ta gaji ta kyale