Showing 21001 words to 24000 words out of 63435 words
ta ki yin magana. Mama ta dau waya ta kira shi, ta yi ta 'ringing' ya ki ya dauka don ya san kwanan zancen, ya tattara kayan shi Danlami da ya dawo daga kai Muhasin makaranta ya kai shi Airport ya yi tafiyar sa.
Sai da ya sauka a Lagos sannan ya fiddo waya ya yiwa Mama (text) ya sanar da ita wani aikin gaggawa ya same shi a Warri (Porthearcourt) zai tafi gobe, yanzu yana Lagos, yana neman albarkarta. Yana tura mata ya kashe wayarsa bai kara kunnata ba.
Mama ta dube ta sosai ta ce,
"Ki gaya min gaskiya Hanifah in har kina so mu shirya, duk yadda aka yi kece baki da gaskiya, don ni dai bai taba tafiya ba tare da ya yi min sallama ba.
Yanzu ma na san don kar in yi muku sulhu ne ya yi hakan".
Hanifah cikin kuka ta ce, "Wallahi Mama ban san me na yi masa ba, kawai don ya ji muna waya da Halisa wai........."
Ta ki karasawa. Mama dake sauraron ta ta ce, "Wai me?"
"Wai ni munafuka ce ina ha'intarsa".
"Maza kuke kulawa ke da Halisan?"
Ta zaro ido, "A'a, Mama ita ba ta ma san komai ba, kawai magani nake sha......."
"Maganin me?"
"Contraceptive pills.......'
Ji kike tass.......tasss! Mama ta dauke ta da wasu gigitattun mari guda biyu a jere a dukkan kuncinta.
"Butulcin da za ki yi min kenan Hanifahh? Haihuwar da Allah ya karanta min, ina nema ruwa a jallo ban samu ba. Duk burina na samun 'ya'ya na dora shi a kanku.
Muka yi ruwa muka yi tsaki muka baki abin da kike so ba tare da nashi son zuciyar ba, muna murna ya yi mana biyayya ya zauna dake lafiya bamu taba jin kanku ba, amma da abin da za ki saka mana kenan?
To nima babu ruwana da ke, kije ki ji da bokon ki. Amma fa kada ki ga laifina ranar da ya kawo mai sonsa ya ce zai kara aure, don zan bi bayansa ne kawai".
Hankalin Hanifa in ya yi dubu to ya tashi, ta tsorata sosai ta razana. Ita ba ta dauki abin da zafi yadda suka dauke shi ba. Hasalima sun yi mata mummunar fahimta. Ya za'a yi ta ce ba ta son hada zuri'a da su?
Ita dai tana ganin kawai lokaci bai yi bane, ko 'Law School' ba ta fara ba. Ga kuma hujjojinta na sakwarkwacewar jiki, amma ba yadda su suka fassara ba.
Amma da ta yi tunanin karancin haihuwar da Allah ya jarrabesu da ita sai ta yi musu uzuri, ta dinga baiwa Mama hakuri kamar ranta zai fita, tare da alkawarin duk ranar da suka kamata da wani laifi makamancin wannan to ta yarda duk hukuncin da ya kama suyi mata.
Mama na son Hanifah sosai, dole ta hakura suka koma tunanin yadda za suyi su shawo kanshi, don shi bai iya fushi ba. Da wuya ya yi fushin, amma da wuya idan ya yi ya sauka da wuri.
Gashi ya ce baya Lagos balle su bishi. Waya kuma tun suna kira har sun gaji. Don kullum abu daya shegiyar kwamfutar nan take gaya musu, wato 'a rufe take'.
Dole suka hakura suka sawa sarautar Allah ido, Mama ta san duk ranar da ya huce zai zo ne, ko don Muhaseen.
A nan sassan Mama ta zauna ta ki komawa gidanta a dakin Mama. Sai dai sam Mama ba ta jin dadin mu'amalar da Hanifa ke yi da Muhasin, ta tsani yarinyar kamar mutuwarta, abu kadan za ta yi ta gwale ta, ko ta daka mata tsawa mai gigita yaro.
Ta mai da ita kamar 'yar aikinta, in har tana gidan duk hidimarta ta dora mata, har da wankin inner wears dinta ita take yi mata amma ba ta godewa, balle kuma idan Mama ba ta gida, ta dinga surfa mata zagi kenan wai tsintacciyar mage mai neman fin 'yan gida.
Ita kuma Muhasin din mugun tsoronta take ji, ko muryarta ta ji firgita take balle idan ta kwala mata kira "Ke!"
Don ko sunanta ba ta kira, don haushin sunan take ji saboda dadinsa.
Haka nan suka zauna har tsayin watanni uku. Ranar wata asabar Mama da Hanifah basa nan sun je Darazo duba Innani mahaifiyar Hanifa anyi mata operation an ciro mata 'ya'ya biyu duk babu rai.
Ita Muhasin tana gida saboda tana da lesson karfe hudu da Malam Usaini, kuma suma din ba kwana za suyi ba, don haka ita da Asabe ne kawai a gidan.
Ita tana toilet tana wankin kayan barci da 'panties' da 'bra' din Hanifah, ita kuma Asabe tana kicin tana girka musu abin da za su ci.
Tana sanye da doguwar rigar Larabawa ta sha aiki irin wadanda yake kawo mata duk sanda ya je Umrah. Kalarta 'coffee' ne, kanta rufe da kallabin rigar wanda ya bayyana jelunan kitsonta yiri-yiri da Asabe ta yi mata sun kai guda dari biyu. Ga 'yan nonuwa sun fara fitowa har ana ganin tudunsu ta cikin rigar.
Asabe ta shigo tana kiranta ta ce, "Bako kika yi yanzun nan".
Cikin mamaki ta ce, "Ni din kuwa?"
Ta rufe mata ido ta ce, "Kawo goron albishir".
"Me kike so in baki a matsayin goron idan har albishir din naki mai dadi ne?"
Ta ce, "To muje, kuma kada ki bude idon sai na ce ki bude".
Ta ce, "To".
Suka taho main palour, ai tun kan ta bude idon ta shaki American-Crew wanda ya cakude da Onde - Bertige. Wannan wani kamshi ne da ba ta taba jinshi jikin wani dan Adam ba, face mutum daya.
Asabe ta bude mata idon. Ta tafi da gudu za ta rungume shi, ko me ta tuna? Sai ta tsaya kawai gabansa ta sarke hannuwanta a baya tana dariya da fararen hakoranta kamar kankara.
Yana mike cikin three seater sanye cikin wani lallausan yadi ruwan toka yana latse-latse cikin wayarshi sabuwar 'Thuraya'. Ya daga fararen idanunshi masu sheki ya dube ta kamar ya rungume ta, sakamakon dadewar da ya yi bai ganta ba.
Maimakon hakan sai ya janye kafafunshi ta zauna gefensa.
"Yayana mai yasa ka tafi ka barmu har wata uku? Kullum sai na tambayi Mama yaushe za ka zo?"
"To me Maman take ce miki?"
"Cewa take yi sai ka gama fushi za ka zo".
Ya yi murmushi mai sauti,
"Waye ya ce da ita fushi nake?
Ni kuwa me zai sani fushi a duniya bayan albarkar da ta ke sa mini kullum?
Na yi tafiya ne kawai a kan aikin mu".
"Ina ka je?"
"Na je Warri".
"Ina ne haka?"
"Niger Deltan".
"Musulmi ne?"
"A'a, Inyamurai ne".
Ta jinjina, "Allah yasa ba za ka koma ba".
Murmushi ya sake yi, "Zan koma. Da nake cewa ma in zan koma zamu tafi tare?"
Da sauri ta ce, "A'a, wallahi ba za ni ba".
"Saboda me?"
"Saboda ni kyankyamin Inyamurai nake, a ajinmu ma akwai wata Inyamura Chinyere ban cin abinci da ita sai da Amina".
"To mu bar wannan chapter, ya ya karatu? Ya makaranta? Me yasa baki bisu Darazon ba?"
"Makaranta anyi hutu, in an koma zamu fara 'common entrance'. Abin da yasa kuma ban bisu ba Mama ce ta ce in zauna kada Malam Usaini ya zo bana nan, yau zan bashi haddar Suratul Tagabun".
Shi kansa bai san irin kallon da yake mata ba, ji yake kamar ya janyo hannunta ya dora ta a kan santar kirjinsa. Ta ji irin bugun da zuciyarsa take yi a kowacce dakika da kuma duk lokacin da suke tare.
Dauriyar da ya saba yi yau ma ita ya yi. Ya ce, "Gara da kika tuna min zancen common entrance, don na fara neman form din Federal School. Don makarantar kwana zan kai ki ta 'yanmata don ki koyi gwagwarmayar rayuwa, ko ba kya so?'
"Boarding Yayana?" Ta tambaya cikin dariya. "Wallahi ina so ka kaini in dinga wanki da guga da kaina, don ka ga Mama ba ta barina in yi, sai ta ce wai jika-jika zan yi, sai dai ta bawa Danfulani (mai wankinsu), ni kuma na fi so in dinga yi da kaina. Don Allah ba da koyo a kan iya ba?"
Ya yi nisa a cikin kallon ta, yana hasashe masu yawa. Tana kama da wata fuska da ya sani, musamman dogon hancinta, da idanuwanta kanana masu maiko. Da dan karamin bakinta tamkar cokali ba ya shige duka ba.
Ba wannan ne kadai abin da ke daukar hankali a halittar Muhasin ba, sai gashin idonta mai tsayi da gashin girarta mai taushi baki, kuma siriri, gefen kunnuwanta kuwa duk saje ne mai fallasa cewa akwai fin haka cikin sumar kanta.
Tana ta zuba, ta ga bai kula ta ba, kallon ta kawai yake yi, ba ta san ko jinta baya yi ba. Sai kuma ta ji duk kunya ta kama ta da surutun da take ta yi.
Ba wai halinta ne surutu ba, hasalima in ba shi ba babu wanda take iya bude baki ta yi doguwar magana da shi. Ta saba da shi sosai, saboda yadda shima yake sakin jiki ya ji damuwar ta da shirmen ta, ya biye mata su yi ta yi.
Amma ko Mama basu fiya doguwar hira ba, amma idan shi ne ji take kamar da aminiyarta take magana.
Ta kai tafukanta ta rufe fuskarta cikin dariya da jin nauyi, sannan ne ya san cewa
"He is lost..." (Ya tafi cikin tunani).
Ya yi saurin dauke idanunshi a kanta, ya ce, "Samo min samosa da Maltina in ci".
Ta mike ta nufi kicin da gudunta har tana tuntube, ta zubo samosa da cake da dambun nama wanda Mama ba ta rabo da yin su saboda cimar Daddy ne, ta dauko gongonin Maltina da lemun 'Shany' shima na gongoni, ta shiryo a karamin 'tray' ta kawo masa, ta ja 'center-table' dan karami ta dora 'tray' din a kai ta tura gabansa.
Yana ci suna hirar karatun ta, har aka kira sallar azahar ya fita masallacin Daddy dake like da gidansu.
A lokacin ne shi kuma Daddyn ya dawo, bai wani zauna ba shima ya yi alwala ya fita masallaci.
Tare suka shigo shi da Daddy bayan an idar da sallah. Shima Daddyn ba mazaunin gida bane, tun sanda ya soma harkar cinikayyar fata da kasar Italiya kullum yana hanyar Italy da Thailand, suna shigo da takalman fata da jakunkuna nan fata kirar 'Gucci' da 'Burberry' suna rabawa manyan 'Malls' na cikin garin Gombe da wajenta, kuma suna samu sosai, budi da nasara ta ko'ina, wane cinikin Tobbacco. Don shi Daddy yanzu har baya son sunan Tobbacco da ya bishi, don ba yadda zai yi ne.
Kamin su shigo tuni Asabe ta shirya tebur, shi da Daddy suka nufi 'dining'. Suna cin abincin Daddy ya kira Mama, ta hada shi da Innani suka gaisa ya yi mata ta'aziyya da sannu, shima Aliyun haka.
Ta ce, "Gasu nan yanzu za su taho zuwa karfe biyar za su iso.
Suna zaune a nan falo suna ta hira shi da Daddy, hirar yaushe gamo, ta Uba da dan da yake matukar so.
Wajejen la'asar suna shirin mikewa don tafiya masallaci. Muhasin ta fito daga dakinta cikin hijabinta har kasa, tana rungume da 'pieces' na Alkur'ani.
Ta zube a kasa ta gaida Daddy, don ita har ta mance rabon da ta ganshi a gidan. Ya ce, "Malama Muhasin hadda za a yi ne?"
Ta ce, "Eh Daddy".
"In ce ko kin yi sallar la'asar kuma kin ci abinci?"
Na yi sallah amma ina azumi ne".
"To in an sha ruwa ayi mana addu'a, a yiwa Umma Allah ya bayyana mana ita".
A sanyaye ta ce, "Insha Allahu Daddy".
"To maza wuce ki tafi kada yai ta jiranki".
Ta wuce ta tafi da saurinta. Aliyun na jinsu bai sanya musu baki ba, illa jin dadin hakan da yake yi a zuciyarsa da alfahari da iyayen da Allah ya ba shi, wadanda duk abin da ya kawo ya ce yana so, sai su nuna sun fishi so. In har abun ba mai illa bane.
Biyar daidai Danlami ya yi 'horn' maigadi ya bude get su Mama suka shigo. Muhasin da malaminta Malam Usaini suna nan zaune a harabar gidan cikin rumfar adana motoci yana biya mata sura ta gaba don ta kawo haddar ta jiya.
Dukkansu suka yiwa Mama sannu da zuwa, ta amsa cikin far'a. Hanifah kam ko kallo basu ishe ta ba, ta yi wucewar ta cikin gida tana kyabe baki, a ranta tana cewa, "Kai! Wannan yarinyar jaraba ce wallahi, ta zame min karfen kafa. Insha Allahu sai ta bar gidan nan, don ban ga zaman me take yi ba, ga shegen kyau da kilbasa kamar rainon karuwai".
Wani bangare na zuciyarta ya ce, "To wa ya sani ma ko uwar tata karuwar ce ta yi shegenta ta yar ta gudu? Aliyu ya kwaso musu?". Ta yi tsaki ta riga Mama shigewa gida.
Nan ta yi turus, ganin wanda ke kwance cikin kujerun falon yana waya. Wani sanyi ya ziyarci zuciyarta.
Ta karasa da gudu ta rungume shi, shaf ta manta da wai sun samu sabani. Ta azabtu kwarai da wannan horon, na rashin gani ko ji daga gare shi har tsayin kwana casa'in. Sai kuma ta soma kuka, tana ba shi hakuri.
Mama ta shigo ta same su a haka, sai ta yi saurin dauke kanta ta shige ciki. Ya ce, "Ke baki da kunya ko? To daga ni".
Ba ta daga shi ba sai kara shigewa jikinsa da ta yi, ya kuwa daddage ya ture ta ya mike duk ta yi squeezing kayansa (yamutsa shi).
Ya yi kwafa ya ce, "Shashashar banza!" Ya bi bayan Mama.
Maman tana kishingide tana hutawa a gadonta don a gajiye take da zaman mota, ya zauna a stool din madubinta suka gaisa.
Ta ce, "Ka kyauta kenan abin da ka yi?"
Ya ce, "Me na yi Mama?"
Ta ce, "Ban sani ba, tambayi kanka".
Ya ce, "Wai don na rufe waya Mama? Ni fa ba don ke fa na rufe ba wannan shashashar ce bana so ta dame ni".
Ta dunkule hannu ta ce, "Ungo naka?" Ta yi mishi dakuwa. Ta ce, "Ban haifi shashasha ba, kuma insha Allahu ba zan haifa ba.
A shekarunta da iliminta ta wuce a kira ta shashasha. A to, ka sani tunda wuri. Don ba a shashashan Alkali".
Ya yi dariya ya ce, "Wato Mama saboda 'yarki tana Alkaliya ba za ta yi kuskure a nuna mata laifinta ba? Who the hell she thinks she is?"
"She is Uwaka-Ubanka!" Inji Mama. Shin ko ka san hukuncin mijin da ya kauracewa matarsa tsayin watanni uku ba tare da dalili ba? An gaya maka aure abin wasa ne?"
Ya ce, "To ai ni Mama da dalilina da hujjata. Ina so ta fahimci muhimmancin laifin da ta yi min ne. Har yanzu kuma ban hakura ba, don haka za ta ci gaba da hutawarta a nan dakin ki, har sai ranar da ta canza kudirinta daga munafuntata. Wai a ce ana sonka amma......."
"Duk na ji, ban kuma tambayi ba'asi ba. Ta gaya min komai, na yi mata fada har dukan ta na yi.
Saboda haka ka yi hakuri ta gane kuskuren ta, ta kuma rantse ba za ta kuma ba". Tasa murya ta ce,
"Hanifah".
Ta shigo tana rabewa a bayan kofa kamar bera ya ji kukan mage. Duk sai ta bawa Mama dariya, shi kuwa ya kara daure fuska.
"Zo ki ba shi hakuri".
Ta zube a gabanshi idanunta cike taf da kwallar SO ta ce,
"Don Allah Yaya Aliyu ka yi hakuri....."
Ji ya yi kamar ya rungume ta, to amma a gaban Mama ne. Yau ne ya taba ganin weakness dinta (kasawarta).
Duk gayun ta sauke shi ta yi tubus. (Ina ruwan zuciya da abin da take so).
Mikewa ya yi ba tare da ya ce komai ba, amma fuskarsa ta nuna sassauci. Mama ta ce, "Hada kayanki ku tafi, Allah ya yi muku albarka, ya baku 'ya'ya masu biyayya a gare ku kamar yadda kuka yi mana.
Ku dinga hakuri da juna, in ba haka ba ba za a ci ribar zaman tare ba. Shi auren gaba dayan shi hakuri ne jigon shi da yin afuwa ga juna, in ba haka ba ba zai je ko'ina ba. Kun fahimce ni?"
Ta ce, "Eh".
Ya fice. Ita kuma ta soma hada shirginta.
Tana shiga dakinta wanka ta yi, ta zuba bakaken nighties na wasu riga da wando masu taushi. Aka bi ko'ina da sassanyan turaren cool water aka nufi turakar maigida.
Zaune yake a kan kujera da dan karamin teburin gilashi a gabansa yana shan coffee, pajamas ne farare a Jikinsa.
Ta kwanto ta bayanshi ta sa bakinta a nashi tana kissing. Kofin hannunshi ya subuce ya fadi ya zube a cinyoyinsa, ya kuwa mike a fusace kamar zai dake ta.
Ta yi maza ta rungume shi ta hanna shi masifar ta hanyar zuba mishi hot kisses a wuyansa da bakinsa.
Wata uku ba kwana uku ba, ga cikakken namijin da baya zina, baya neman mata. Tuni ta samo kanshi, fada ya koma mai ban mamaki. Ya rungume matarshi suka shiga barje kuruciyarsu. Shi dai a kan kansa bai san inda lagonsa yake ba, amma makirar lauyar nan ta sani, shi yasa take saurin rinjayarsa.
Ranar lahadi zai koma Lagos, Mama ta ce ita ba ta yarda ba, yasa matarshi a gaba su tafi tare hankalinta ya fi kwanciya. Duk wani gyaran gida da har yau ya ki karewa ayi shi tana cikin gidan.
Murna a wajen Hanifa kamar ta goya Mama. Ta ce, "Kinga kuma Mama a can zan fara 'Law School' dina".
Daddy ma ya ce tare za su tafi, dole ya sayi tikiti tare da ita. Mama ta hada mata kayan girki sosai suka tafi.
****
[9/4, 12:57 PM] Asmau: Cikin 'yan rakiyar kai Muhaseen makaranta ranar litinin har da Hanifah, don ta ce ba za ta zauna ita kadai a gida ba.
Aliyu ke jan motar da kansa, Hanifa na gaba, Mama, Muhaseen da Asabe suna baya. Hira suke yi sosai har suka iso Bajoga.
Sai dai Aliyu baya sanya musu baki a hirar su, shi kadai ya san abin da ke damun zuciyarsa, ko Mama ta sako shi a hirar bai fiya tankawa ba.
Ita kuwa Muhaseen doki take ta yi sai far'a take za ta shiga cikin yara sa'o'inta ta yi rayuwa, sabanin ita kadai a gida, sai Mama da Asabe.
Suna isowa kai tsaye ofishin principal suka nufa, duk wasu cike-ciken takardu na daukar dalibi Yaya Aliyu ya yi, ya biya kudin makaranta da dukkan 'charges' din, aka karbi Muhaseen a matsayin daya daga cikin daliban FGGC Bajoga.
Sai da Yaya Aliyu ya juya zai tafi ne idon Muhaseen ya raina fata, ta saki hannun metron din da aka hada ta da ita ta tafi da