Showing 9001 words to 12000 words out of 63435 words

Chapter 4 - Amanata HAUSA NOVE

ASMAU   

11 Nov 2024

19040

sauransus. Asabe ta dauka suka tafi.
Har zuwa lokacin da suka shiga dakin yarinyar bata farka ba. Ya danna kararrawa Nurse ta shigo ta canza mata 'drip', za ta fita ya ce,
"Har yanzu ba ta farka ba?"
Ta ce, "Nan da karfe goma na dare insha Allahu za ta farka".
Asabe ta shimfida dardumar da ta taho da ita a kasa ta zauna. Shi kuma ya karasa jikin gadon, ya zubawa yarinyar ido. Bery cute da ita, fara tas mai yalwar gashin ido, giran ido da sumar kai.
Hatta a hannayenta gashi ne kwance lambam kamar ta hada jinsi da Lebanese. Sai dai kuma dukun-dukun take, kamar an tsamo ta daga kwatami. Wata daudaddiyar atamfa ce a jikinta duk ta kekkece, riga da zani da kallabi, suma din wari-da-wari.
Ya ja kujera ya zauna, ya dauki magazine ta asibitin a nan kan 'side drower' yana dubawa. A lokacin Dr. Misau ya shigo suka yi hannu, ya ce, "Sun yi hoton kwakwalwarta dazu komai normal, insha Allahu lafiya za ta farka nan da awa daya, idan allurar barcin da a kai mata ta sake ta.
Karfe goman kuwa ta bude ido. Ta dade tana nazarin inda take. Ta ji ta kasa motsa komai na jikinta, radadi da zugi da kafafunta ke yi suka shige ta.
Ta soma kuka tana kiran "UMMA! Wayyo Umma-wayyo Umma........."
Kuka sosai, da ta lura duk mutanen da ke dakin babu Ummanta, kuma bata san su ba.
Asabe ta taso ta iso gareta ta ce,
"Ki yi hakuri ki yi shiru, kinga baki da lafiya.
Ina Umman take aje a kirawo ta?"
Ya aje 'magazine' din yana kallon ta. Asabe nata lallashin ta amma ta ki yin shiru, musamman da ta tuna ta baro Umma a gefen titi ta tsallaka don ta karbo sadaka wajen wata mai fanke, daga nan ne kuma ta ji anyi sama da ita an watsar, daga nan ne kuma ba ta kara sanin abin da ke faruwa ba, sai yanzu da ta farka ba ta ga Ummanta ba.
Ai kuwa ta zabura za ta mike, ta kwalla kara saboda azabar da ta ziyarce ta har cikin kwakwalwarta. Ta koma ta kwanta tana kuka da nishin azaba sabin gwanin ban tausayi.
"Hada shayi ki ba ta". Ya ce da Asabe. Karo na farko kenan da yayi Magana tun farkawarta.
Cikin sauri ta hada shayi mai kauri wanda ya ji madara da bombita. Ta sa mata kofin a baki bayan ta tallabo ta, ta jingina mata filo.
Ta kuwa kama sha sosai yana warware dunkulallen hanjinta da ya dunkule waje daya saboda yunwa. Kan Asabe ta farga sai kofin a hannunta.
Ya ce, "Zuba mata abinci mai ruwa-ruwa".
Ta zuba faten dankalin turawa wanda ya ji hanta da ganyen alayyahu da tumatur, ta zauna a bakin gadon tana ba ta da cokali tana shan faten hannu baka hannu kwarya kamar kunnen ta ya tsinke.
In ba ta yi kuskure ba tunda uwarta ta kawo ta duniya ba ta taba cin abinci mai dadin wanda ta ke ci yau ba. Nan da nan ta cinye.
Ya ce, "Kara mata!".
Asabe ta kara ta ba ta tana ci da kanta. Ta balle hancin lemon 'Mountain Dew' ta ba ta, suma nan da nan ta share su. Ta koma ta jingina da filo tana ajiyar zuciya, nutsuwa ta zo mata. Ta ci gaba da kukan neman Umma.

A nutse Aliyu ya taso ya tsaya a gabanta. Ya fiddo hankicinshi mai kamshi da tsafta fari sol da shi daga aljihunsa ya mika mata.
"Ungo share hawayenki".
Ta daga kai tana kallon ma'abocin wannan lallausar murya, lallausar kamshi, da bayyanannen kwarjini, sai ta ji ta kasa yin musu, ta karba tana share hawayen da sauri da sauri.
"Ya ya sunanki?" Ya tambaye ta.
" Habibah, amma (MUHASIN) Ummana take ce mini". Ta ba shi amsa.
"A wace unguwa kuke?"
"Can karkashin gada".
"Wace gada?"
"Ta cikin tashar Dukku".
Ya boye mamakinsa ya ce, "Idan aka je gobe za a samu Umman a can?"
"Ban sani ba".
"To ki yi hakuri, ki daina tada hankalinki. Gobe in Allah Ya kaimu zan je na taho miki da Ummanki, in har tana can. Ki daina kuka, tsautsayi ne, nine na buge ki ba da sani na ba. Yanzu ma dan dare ya yi ne da na je karkashin gadar. Ki yafe ni kin ji Muhaseen? Insha Allahu zamu kula da lafiyarki har sai kin warke, kwanta ki huta".
Ta koma ta kwanta, ta lumshe idanunta. Shi kuma ya yiwa Asabe sallama ya tafi.
Washegari Aliyu ya koma dai-dai inda ya kade Muhasin, ya yi 'parking' ya fito daga mota. Ya doshi wasu matasa dake sayar da rake a gefen titin ya yi musu sallama suka yi hannu.
Ya dubi mai raken ya ce,
"Don Allah dan'uwa tambaya nake".
Ya ce, "Allah Yasa na sani dan'uwa".
"Tashar Dukku nake nema?"
"Ai ko ka baro ta can baya". Ya kwatanta mishi.
Aliyu ya yi godiya ya koma motar shi ya ja.
Lokacin da ya isa cikin tashar, kowa na harkar gabansa babu wanda ke kula da wani.
"Alhaji ina za ka? Hajiya ina za ki?'
Abin da yake ta ji kawai kenan, shi kuma bai ga wata gada ba balle karkashin ta.
Ya matsa ga wani shagon aski a nan cikin tashar, mutane hudu a ciki ana yiwa na biyar din aski.
Ya yi sallama suka amsa duk suka yi hannu, ya ce, "Don Allah tambaya nake?"
Mai shagon ya ce, "Yi tambayar ka".
Ya zura hannayenshi cikin aljihu ya ce, "Shin akwai wata gada ne cikin tashar nan da mutane ke zama karkashin ta?"
Mai shagon ya ce, "Eh, akwai gada a can gaba da almajirai suke zama, musamman in ana ruwa".
Ya ce, "Don Allah a nuna mini, don wata yarinya na buge jiya ta ce mahaifiyarta a can take, shine nake so in je in dauke ta in hada su da 'yar ta".
"Kwarai, akwai wata almajira makauniya da suke tare da 'yar ta, wasu farare tas dasu, suna yawan zama a wajen. Don ana cewa ma a nan suke kwana, duk zafi, duk sanyi".
Hankalin Aliyu ya kwanta, ya ce,
"Don Allah a raka ni".
Dayan ya ce, "Haladu raka shi don Allah".
Haladun ya mike ya wuce gaba suka tafi. Tunda suka doso wajen gaban Aliyu ke faduwa, don da alama babu kowa a wajen sai kullin kayansu cikin buhu.
Dan rakiyar ya ce, "Nan ne wurin tambayi mai sai da abincin can ko ta ganta, don idan ba 'yar, ba ta fita bara ita kadai".
Aliyu ya karasa gurin mai dan wake ya yi mata sallama, ya kuma tambaye ta almajira babar Muhasin.
Ta tabbatar mishi tun jiya ba ta gansu ba, don wani almajiri ma yake gaya mata an kade 'yar, uwar kuma wani mai katuwar mota ya sace ta, don yana ganinta ya danna ta a mota ya tafi da ita.
Hankalin Aliyu ya kai kololuwar tashi, ya yi mata godiya, kafafunsa a salube ya koma karkashin gadar ya dauki kullin kayan nasu, ya yiwa Haladu ihsani ya nufi motarsa.
Ko da ya iso asibitin jikinsa a sanyaye yake, yana cewa cikin ransa shi ya shiga uku, yarinya ta rasa uwarta a dalilinsa, ta rasa kafafunta dalilinsa, yanzu ya ya za su yi da ita? Ina za su kaita?

Ya tura kofar ya shiga cikin sallama. Asabe ta amsa, ya shiga. Muhasin din na barci, amma jin muryar wanda ya ce zai je ya kawo mata Umma ai tuni ta watstsake, ta kafa mishi kananan idanunta.
Ya ja kujerar robar da ya zauna jiya ya zauna, yana kokarin zakulo murmushin dole a kan siraran lebbansa.
Ga mamakinshi sai ji ya yi ta ce da shi, "Ina wuni?"
Ya amsa "Lafiya lau kanwata, ya ya jikin? Ina ke miki ciwo yanzu?"
Ta runtse ido, "Duka jikina yana ciwo".
"Ki yi hakuri kin ji, za ki ji sauki bery soon insha Allahu".
Ta rufe ido hawaye suka ziraro. Kafin ta amayo da abin da ke cin ta a zuci,
"Baka ga Umman ba ko?"
Ya girgiza kai cikin tausayi,
"Sun ce wai wani mai mota ya tafi da ita. Yanzu haka garinku zai kaita, ina ne garin ku?"
Ta rushe da kuka tun karfinta, "Wayyo Umma! Wayyo Allah Ummana!! Shi kenan an sace ki, ba zan kara ganin ki ba".
Duk dauriya irin ta Aliyu sai zuciyarshi ta tsinke, kwalla ta cika kyawawan idanunsa. Ya yi kokarin mai da su.
"Take it easy kanwata....., zamu ga Umma in Allah Ya yarda. Nima ina da Ummata mai kirki kamar Ummanki, za ta rike ki Muhasin kamar Umman ki, har zuwa sanda Allah zai sada mu da Umma.
In kuma kin san garinku ki gaya min yanzu in je in binciko".
"Ni ta gaya min sunan garin amma na manta. Ta ce ita har abada ba za ta koma garin ba saboda abin da Babana ya yi mata. Ta ce sunan sa Umaru, ta ce ni jikar San-Turaki ce. In suka ganni za su kwace mata ni".
Ta ci gaba da kuka.
Daga Aliyu har Asabe sauraron ta suke, muryarta mai kumaji (husky), lafuzanta masu taushi. Ga irin abubuwan da take fadi cikin kuka, za ka fahimci ba karamar kauna take yiwa mahaifiyarta ba.
Asabe ta rungumo kafadunta tana lallashin ta, shi kam ido ya zuba mata. Can ya ce,
"Ba za ki iya tuna sunan garin ba? Ki yi kokari ki dan tuna".
"Ni fa na manta, amma idan na tuna zan fada maka".
"To shi kenan, fatana yanzu shine Allah ya baki lafiya, zan kai ki wajen Mamana ki zauna har zuwa sanda za mu ga Umma, zan ba da cigiyarta cikin radio da talabijin, za a ganta in Allah ya so, kwantar da hankalinki Muhasin, kuka kara ciwon zuci yake, sannan baya baka abin da Allah bai baka ba. Sai dai ki yi ta addu'a Allah ya bayyana mana ita da sauri".
Ta ce, "To".
Ya duba agogon hannunshi 'swatch', "Bari in je in kawo muku abinci. Zan iya tafiya ba matsala MUHASEEN?" Ya fada da wata irin tattausar murya, mai kwantar da hankalin karamin yaro.
Daga mishi kai ta yi alamar ya tafin. Ya juya ya fita. Da ya kai bakin kofa sai ya kara juyowa, suka kuwa hada ido, don ita ma bayan shi ta bi da kallo.
Ta yi murmushi ta ce, "Sai ka dawo". Ya fita ya ja musu kofar.
Yana zuwa gida ya tarar da Hanifah ta dawo, tana mike cikin 'sofa' da 'Ipod' a kan cinyarta.
Budurwa baka, 'yar gaye, mai masifaffen gayu irin wanda ya zarta hankali. Dalibar 'Law' a jami'ar Tafawa Balewa dake Bauchi, tana kokarin hada LLB dinta shekara mai zuwa.
A fuska kam ba ta da makusa sai a 'structure' ta yi siranta da yawa, sai dai akwai tsayi irin wanda MANYAN MAZA ke rububi a wannan zamanin.
Ya yi sallama, ita kadai ce a falon. Ta dago cikin slow tana kallon sa da fararen kwayar idanunta, kirjinta ya shiga harbawa da sauri da sauri, kamar yadda ya saba duk sanda ta yi tozali da Yayan nata.
Namijin da yasa ta raina sauran maza, da duk abin da suke takama da shi. Namiji daya da zuciyarta ke so. Shi kadai ne a duniya take jin za ta iya aura, ta kuma iya yin rayuwar aure dashi, don in har yana raye, to ba za ta iya auren kowa ba.
Kallon maza take with contempt (a raine) a duk lokacin da ta daga ido ta dube su; a ganinta babu kamar shi, ta fannin komai; shine kadai cikakken mutum a idanunta da duniyar zuciyarta.
Amma abin takaicin bai taba yi mata wani kallo bayan na kanwar shi ba. Ita kadai take sha'aninta.
Ciwon kana so ba a son ka, matukar ciwo ne da shi, amma a yau ji take ta fi kowa farin ciki da sa'a a duniya, tun sanda Mama ta shaida mata cewa ita din dai zai aura ba wata ba. Addu'arta ta shekara da shekaru, ba ta tashi a banza ba.

Ta amsa sallamar tashi muryarta tana rawa, bai tsaya ba kai tsaye ya wuce 'bed room' din Mama, don bai ganta a falon ba.
Tana daura kallabi a madubin dogon yaro, ya yi sallama tana kallon shi ta cikin madubin ba tare da ta juya ba ta ce.
"Ina ka shiga ne? Ga abincin su Asabe tun safe na rasa mai kai musu".
Ya ce, "Bari ke dai Mama, ina tashar mota tun dazun".
"Tashar mota? Me ka je yi tashar?"
Ya zauna a kujera cike da gajiya ya soma warware mata yadda abin yake. Mama ta nutsu tana ji, ba ta katse shi ba.
"Babarta makauniya ce, almajirai ne masu kwana a tasha. Babu wanda ya san daga garin da suka bullo. Yanzu kuma uwar ta bata, bai san ya zai yi da yarinyar ba, don ba zai iya barinta ta fada mugun hannu ba.
Ya kare da cewa, "Mama sai kinga yarinyar wallahi za ki ji ta shiga ranki. Naibe and Innocent....."
Ta yi murmushi, "Tunda ka yaba nima ina sonta, in ta warke ka kawo min ita tunda dama duk gidan za ku bari, ni kadai za ku bari, sai in samu bokiyar debe kewa".
"Da gaske kike Mama za ki rike min Muhasin har in nemo mata babarta?"
Ta baro jikin madubin ta zauna kusa da shi.
"Na taba yi maka wasa ne? Ina nufin abin da na ce, zan rike ta har gaba da abada idan akwai. Da na kowa ne, sannan tsautsayi yana kan kowa.
Ka daina dorawa kanka damuwar cewa kai ne ka yi sanadin rabuwarta da babarta, haka Allah ya rubuta mata. Babu kuma wanda ya isa ya kankare mata kaddarar rayuwarta".
Ya ce, "Thank you my dear Mum, na san za ki yi min fin haka. Kullum na kalli uwar wani sai in ce tawa ta fi ta kowa....."
Ya bawa Mama dariya sosai ganin ya kama hannayenta ya rungume.
Ta ce, "Baka ga Hanifah bane?"
Nan da nan ya yi fuska, "Na ganta". Ya mike, "Bari in kai musu abincin in dawo".
"Ka tafi tare da Hanifah ta zauna da mara lafiya din zuwa dare, ka taho min da Asabe, akwai ayyukan da za ta min in yaso da daddare sai ta koma ku dawo da Hanifah".
Bai ce komi ba ya fita. Tana nan a inda ya barta, ta nutsa cikin yanar gizo.
Ya ce, "Ki dauko abinci a kicin ki biyo ni".
Da hanzarinta ta mike ta yafa mayafin doguwar rigar dake jikinta, ta yi yadda ya ce din, ta bi bayansa.
A darare ta bude kofar motar gidan gaba ta zauna. Ta aza kwandon kayan abincin a baya. Zai ja motar ya tuna bai gaida Gwaggo ba yau, kuma sam bai ganta ba.
Ya juya ga Hanifa ya ce, "Ina Gwaggo?"
Tana kallon gefen titi ta ce, "Sun fita da Daddy tun safe wai za su Dukku gidan abokin Daddy Dr. Omar, matarshi ta rasu".
Cikin ranshi ya ce, "Allah ya ji kan rai". Ya ja motar suka tafi.
Sanda suka murda kofar suka shiga, Asabe na sallah, maras lafiyar na jingine da filo tana shan 'tea' a dan kankanin kofi.
Ta yi kuka har ta gode Allah. Idanunta sunyi luhu-luhu sunyi jajir. Ita dai Hanifa tana kallon ikon Allah, tana kuma cewa cikin ranta "wace ce wannan almajirar kuma ni 'ya su?"
Da sauri ya karasa ya zauna a kujerar da yake zama, ya ce cikin damuwa,
"Kuka Muhaseen, why? Ban ce ki daina kukan nan haka ba?"
Ta ja shessheka, ta ce cikin rishin kuka, "Mafarki na yi wai sun yanka Umma......"
Ya girgiza kai,
"Mafarki ne kawai, don kin sa hakan a ranki. A duk lokacin da kika tuna Umma addu'a za ki yi Allah ya bayyanata da gaggawa.
Ina ji a jikina ita ma tana kyakkyawan hannu. Tashi ki ci abinci".
Hanifa dai na tsaye jikin gado, hannaye rungume a kirji. Uffan bata cewa mara lafiyar ba.
Asabe ta shafa addu'a ta tsuguna tana gaishe shi, bai amsa ba ya ce,
"Maza zuba mata abincin".
Ta jawo kwando tana budawa. Yau da kanshi yake ba ta abincin a baki tana karba tana ci, ya cika mata kofi da kunun gyada ya bata ta soma sha.
Ya mikawa Asabe filet din ya ce ta kintsa su tafi Mama na kiran ta, ga Hanifa nan za ta zauna.
Ya dube ta ta gefen ido, kamar an barota daga cikin kwai saboda kyau da gayu, amma ba ta ko dada shi da kasa ba.
Ya ce, "Yarinya ce na bige da mota ba a ga Mamanta ba, ki kula da ita mu zamu tafi, sai bayan isha zamu dawo".
Ta turo baki gaba ko uffan ba ta ce ba. Suna fita ta ja tsaki tana kunkuni,
"ni na zaci ma 'shopping' zamu shine za a kawo ni jinyar almajira. Mts!"
Ta kara jan tsakin. "Dubi yadda ya ware wannan kulalliyar fuskar tasa yana tarairayarta, ni ko murmushinsa ban taba gani ba. Na ga wadda za tai jinyar".
Ta juya tai ficewar ta ta zauna a 'reception' tana faman kiraye-kirayen wayar kawayenta.
Ba ta koma dakin ba sai da aka yi sallar magariba. Muhasin na so a cire mata 'pampers' din da Asabe ta sa mata, ta cika taf kuma ta dameta.
Hanifa ta shigo ta ja kujera gefe tai zaman ta tana faman 'chatting' da waya. An ce wai 'wargi ma wuri shi ka samu....', tana so ta gaya mata ta cire mata amma babu fuska, tilas ta yi shiru.
Allah ne ya kawo Nurse Habiba mai kula da ita. Ta cire mata 'drip' ta ce ta huta zuwa anjima sai a mayar.
Ta ce, "Cire min kunzugun nan, na yi bayan gida".
Ai da jin haka Hanifah ta gudu. Sister Habiba tasa 'tissue' da ruwa da sabulu da 'dettol' ta wanke mata, ta fita da 'pampers' din waje. Ta dawo ta sa mata wata ta ba ta magani da ruwa a cup ta sha ta fita.
[9/4, 12:57 PM] Asmau: Ya fada 'toilet' ya sakarwa kanshi 'shower'. Daman kuma Aliyun ba daga nan ba. Dan gaye ne danye sharaf (fresh) na karshe, wanda ya san sirrin kula da jiki da daukan diresin. Ma'abocin parmanent (tabbataccen) kamshin turaren American-Crew.
Ya zuba wata sassalkar shadda 'filted' fara tas mai santsi kamar boyel, ya taje kwantaccen gashin kansa. Bayan ya yi sallah ya sunkuya yana daura bakin sandal a kafarsa na fatar damisa.
Wayar shi na ta ruri amma bai kula ba, sai da ya gama abinda yake. Ya dauki wayar ya duba ya ga missed call din na Hanifah ne, ya yi tsaki ya jefa wayar aljihu yana kunkuni......
"Yarinyar nan na nema ta uzzura min don ta ga Mama na bayanta. To ana so dole ne?" Ya ja wani matsiyacin tsaki, ya fito ya nufi cikin gida.
Ba kowa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login