Showing 33001 words to 36000 words out of 63435 words

Chapter 12 - Amanata HAUSA NOVE

ASMAU   

11 Nov 2024

19046

shi ya shigar da shi aikin kwastam. Don haka ta san shi farin sani a matsayin aminin Daddy tun suna kanana.
Karfe shida na yamma, ango sha kamshi, ya danno hancin motarsa gate din gidansu, ita ma tana sako hancin tata motar (Honda).
Maigadi ya wangale gate suka shiga a tare, kafin ta gama 'parking' ta kwaso komatsanta a kujerar baya shi har ya shige ciki.
Ita da Mama suka shiga gidan, shi Daddy masallaci ya wuce. Ta yiwa Mama sannu da zuwa ta nufi sashinta.
Mama kamar ta kirata tai mata bayani sai kuma ta ce a ranta,
"Oh-oh! Ku karata can ke da mijinki, kada ki sa min hawan jini da haukan ki". Ta nufi saman Daddy.

Yana kwance a makeken gadonsa bayan ya idar da sallar magariba, don yau ko masallaci bai iya ya je ba.
Yana waya da Aunty Badi'a yana so ta hada shi da Muhaseen amma kememe ta ki yarda ta karbi wayar.
Aunty Badi'a tayi-tayi amma ta ki, don ita yanzu Yayan ya zame mata dodo, kunyarshi da al'ajabin yadda aurensu ya kasance duk sun cika ranta.
Da gaske an mata fin karfi, ko tana son Aliyu a karkashin ranta, ba ta taba kwatantawa zuciyarta ta zama kishiyar Aunty Hanifa ba. Ina ita ina kishi da Hanifah, gaskiya an sata a uku. Da anyi shawara da ita, da cewa za ta yi a'ah.
Suka gama wayarsu da Badi'a ta aje wayar a gefe, ta harare ta tana cewa.
"Ke wallahi in za ki ware ki ware, wannan kunyar ko shirme zan ce babu inda za ta kai ki. Gidan kishiya za ki, kyankyasassar 'yar boko, maza irin su Aliyu sai da tarairaya, in ba haka ba wallahi za ki zama 'yar kallo kina ji kina gani".
Ta zumbura baki ta ce,
"Saboda Allah Aunty Badi'a haka ake aure babu shiri babu soyayya? Ni fa Yaya Aliyu Yayana na dauke shi na jini, ya ya zan yi da shi a matsayin miji? Gaskiya ni dai a'ah".
Ta shagwargwabe fuska. Badi'a ta yi dariya ta mike tana cewa,
"Kya gaya masa can in kun hadu a 'football-field', ni meye nawa a ciki? Ban da gulma sanda aka tambaye ki me yasa baki ce a'a din ba sai yanzu?"
Za ta yi magana Badi'a ta dakatar da ita, "Tashi ki je ki kwanta, kin san jirgin 5:00 am zamu bi gobe zuwa Dubai, kada ki kasa tashi a kan lokaci".

Hanifah ta tsaya a kanshi kawai tana kallon shi, ga alama yau cikin farin ciki da nishadi yake, irin wanda ba ta taba ganin shi a ciki ba.
Ya aje wayar ya juyo ya dube ta yana murmushi ya ce,
"Ran uwargida ya dade an dawo?"
Ya mika hannu ya janyo ta, ta fizge tana cewa, "Kai da wa kake waya kake wannan nishadin?"
Kai tsaye ya ce, "Da amaryata!"
Ta dauka zolayarta yake don haka ta ce, "Uhm....su amarya manya".
Sannan ta fada jikinsa tana cewa,
"Don Allah yi min tausa, wallahi wata shari'a muka yi yau mai sarkakiya na gaji sosai".
Ya kuwa hau yi mata tausar yana cewa, "Oh! Sorry.... my dear darling...."
Kanta ya fasu, ta yi murmushi ta manta da zancen tausa ta rungumo abinta.
Washegari da safe tana shiri za ta fita, yana zaune gefen gado yana kallon ta. Yadda take wa aikin rawar jiki shi ba ta yi mai rawar jikin, sunan wai ana sonsa.
Ya rasa abin da take samu a kan aikin nan wanda ya sa ta kallafa rai a kanshi. Shi dai ya san yana iya kokarinsa wajen sauke hakkokinta da suka rataya a wuyansa, ci da sha da suttura da bukatar auratayya.
Hatta kudin fetir din da za ta zuba a mota yana ba ta duk wata. Ya rasa me take yi da kudin da take samowa. Ita ba ma'abociyar kyauta ba balle a ce alheri take yi dasu.
Ya girgiza kai, yanzu kam bai da damuwa, ya rage nata, ta dinga kwana ma a wajen aikin ba abinda ya dame shi bane.
Ya yi gyaran murya ta juyo daga 'dressing mirrow' ta dube shi.
"Ya aka yi?"
"Zo nan ki zauna sako zan baki".
Ta ce, "Ka ga fa ina nema in makara, ba za ka bari sai na dawo ba?"
Ya ce, "Nima ina da abin yi, ba zan bari ba".
Ba da son ranta ba ta zauna kusa da shi ta ba shi hankalinta don ta ga ba alamun wasa a tare da shi.
Chekue ya dauko ya yi rubutu na kudi masu yawa ya dora mata a kan cinyoyinta.
"Kudi ne na kayan fadar kishiya ki sayi abin da ya yi miki. Abin ne ya zo ba cikin shiri ba, don haka ban yi muku wani shirye-shirye ba don ko lefe ban hada ba, balle in yi tunanin inda za ta zauna, don haka ki kwashe kayan ki daga dakin dake kallon naki nan za ta zauna kafin in karasa ginin da nake yi a Federal Lowcost ku koma can baki daya.....'
Ai bai karasa ba ta zuba wani uban ihu ta yi kanshi da shaka.......
"Gara in kashe ka kowa ya rasa, da dai in ganka da wata a matsayin matarka.....!"
Kyaleta ya yi, ta dinga zuba masa shaka, cizo da yakushi, da duka. Amma da ya ga abin ba dama, tana neman ji masa ciwo sai ya yi kwallo da ita.
Ta fado a kan bakinta ya kuwa fashe ya yi suntum, ya shige toilet ya barta a nan tana ta kuka.
Da ta ga kukan ba zai mata ba sai ta wancakalar da rigar lauyoyi da hularsu, tana kuka ta yi sassan Mama.
Mama na kicin tana hadawa Daddy abin karin kumallo, ta jiyo ihun Hanifah ta doso kicin din.
Ta ce a ranta,
"To fa! Balli ya tashi kenan".
Ta daure fuska sosai tun kan ta shigo, tana shigowa kuwa ta daka mata tsawa mai gigitarwa ta ce,
"Bana son hauka, koma me ya sameki ki ce 'Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un' amma ba wannan kafircin ba.
Kafiri shine ke yin ihu idan masifa ta same shi amma ba dan musulmi ba".
Ta fada jikin Mama tana rage sautin kukanta...
"Wai aure ya yi Mama....ni ban sani ba. Mama da sanin ki aka yi hakan ko zolayata yake yi?"
Mama ta ce, "To dagani in gama aikina sai in zauna mu yi maganar".
Ta daga ta, ta rurrufe komai ta kashe gass ta ce, "Muje".
Suka koma falon Maman. Ta zauna a kujerar dake fuskantarta ta ce,
"Me ya yi zafi Hanifah har da fasa baki haka?"
Ta share hawaye ba ta ce komi ba. Mama ta ce, "Ki kwantar da hankalinki, ba wata kishiyar zafi ba ce, cewa nake nan gabana ya gaya miki sharadinsa, ko ki aje aiki ki zauna a gidanki, ko ya kara aure?
Don haka ban ga dalilin da za ki tashi hankalinki ba tunda kin kwana da sanin hakan. Muhaseen ce fa! Me za ta yi miki? Ko me za ta gutsire a jikin mijin?"
Ihun ta sake kurmawa wanda ya tsorata Mama. Sai ta tsaya tana kallon ikon Allah. Cikin kuka ta ce.
"Dama tuntuni na gane, Mama bakya sona da danki, kin fi son wannan tsintacciyar magen a kaina.
Na san kuma da yawunki aka yi min haka! Kin munafunceni Mama. Gara in zauna da mata dubu da in zauna da wannan yarinyar, kuma daga yau na hakura da auren Dan......."
Ji kake dau! Mama ta zabga mata mari, "Ni kike zagi Hanifah? Nice munafuka? To ki yi duk abin da ranki ya raya miki.
Tunda ke baki da hankali, duk shekarunki da kwalin ilmin ki na banza ne, fitar min daga daki tun ban lakada ki ba".
Ta juya ta fita daga dakin har tana hadawa da gudu-gudu tabar sassan.
Tana shiga dakinta jaka ta dauko ta soma hada kayanta. Ta samu Danlami a harabar gidan ta ce ya kaita Darazo.
Ya ce,
"Ai zaman nan da kika ga na yi, Oga Aliyu nake jira ya fito, zan kai shi Airport zai tafi Abuja......."
Tun kan ya karasa ta yi gaba ta barshi a nan. Yau abin da ba ta taba yi ba tun tasowarta shi ta yi, wato shiga motar haya zuwa Darazo.

Kan azahar sun iso saboda gudun da suke yi. Innani na bayan gida lokacin da ta shiga, ta shige uwar dakinta ta kwanta a kan gadonta tana ta rasgar kuka.
Ta fito daga bayan gida ta yi alwala a gindin famfo ta tashi. Nan ta tadda takalmanta da katuwar jaka, ta shiga dakin ta cimmata.
Ta tsaya a kanta ta ce,
"Ke lafiya? Wani ne ya mutu?"
Ta yi mata shiru ta ci gaba da kukanta. Innani ta ce,
"Ai kuwa baki isa ki zo ki sani gaba da kuka ba, kuma in tambaye ki dalili ki yi min banza ba...."
Sallamar Alh. Abdullahi tasa Innani dakatar da fadanta, ta ce,
"Shigo, watakila kai ta yi maka bayanin wannan balaguron da ban san dalilin sa ba. Ta sani a gaba kuma sai kuka take, na yi tambayar duniyar nan ta yi kunnen uwar shegu dani".
Alh. Abdullahi ya ce,
"Auren kika kaso in ce ko?"
Ta girgiza kai, don tana tsoron Babansu, bashi da wasa ko kankani, duk girmansu kuma basu wuce ya sa tsabga ya zane su ba idan suka tabo shi.
Don haka cikin shesshekar kuka ta ce, "Aure ya kara, kuma da sanin Mama".
Ya ce,
"Au, to saboda ya kara auren ne da sanin mahaifiyarsa shine kika taho? To wajen wa kika zo? Wace ce uwarki a nan? Don ni dai Hajiya Maimunan na sani a matsayin uwarki.
Don haka duk wata matsalarki da mijinki ki neme ta. Kada ki kara wanko siririyar kafarki ki zo mana nan da irin wannan shirmen kin ji na gaya miki.
Don haka taso yanzun nan sawunki a likkafa in mai da mata ke, tun ranki bai baci ba. Ba a aure ke aka aure ki shashashar banza? Taso tun ban taka ki ba a dakin nan wallahi-tallahi...."
Jikinta yana rawa ta mike, Innani ta mika mata mayafinta ta biyo su da jakar. Har soron Karshe ta raka su suka shiga mota suka tafi.
Ta dawo cikin gida duk ranta a jagule, don ta san Hanifa da shegen kishi tun tana karama. A ranta ta ce,
"Allah ya basu zaman lafiya".

Ta kira Mama a waya suka gaisa ta ce, "Hanifah ta zo yanzun nan amma gasu nan a hanya tare da Alhaji".
Mama ta ce,
"Ai ki rabu da Hanifa kawai, halinta sai Allah ya sawwake. Wai Hanifa ta dubi tsabar idona ta ce na munafunce ta bana sonta na fi son Muhaseen.
Don haka ni na cire hannuna a kan wannan maganar ta je su karata ita da mijinta, ai ta san shi farin sani, ni nake sawa yake russunawa, amma tunda haka ta ce, ai shi kenan, ni din babu hannuna...."
Innani ta dinga ba ta hakuri kamar itace karama, kamar ta yi kuka. Mama ta ce,
"Uh-uh! Ni kam me zai sa raina ya baci tunda ba yau na san Hanifah ba?
Ba yau na soma shakar bakin cikinta ba? Don haka ni na zama 'yar kallo tunda har ta kaimu ga haka".
Suka yi sallama zuciyar kowannensu babu dadi.
Da suka iso Mama da Alh. Abdullahi gaisawa kawai suka yi, yasa Hanifa ta baiwa Mama hakuri.
Ta ce, "Ke za a baiwa hakuri tunda ke aka yiwa laifi.. Sai dai tunda bani na kar zomon ba, bai kamata a bani ratayarshi ba.
Da kin san yadda a kai daurin auren da kin sha mamaki...."
Ta shiga basu labarin duk yadda abin ya faru, da rikon da taiwa Muhaseen alhalin ba ta san ko 'yar waye ba, da yadda Allah ya bayyana mahaifinta da dangantakar Daddy da Dr. Omar wanda ita Hanifan ta san shi.
Mama ta kare da cewa,
"Kin san yarinyar nan Muhaseen ba bakuwarki ba ce, kin san halinta kin san ladabinta.
In nice ke aka yi min kishiya irin wannan ba zan daga hankalina ba, da dai a je a kwaso min wadda burinta ta kame miji ta kore ni.
Don haka ya rage naki ki kwantar da kai ki bi mijinki, ko ki yi ta rashin hankalin naki".
Haka Alh. Abdullahi ya tafi ya barsu Mama na ci gaba da yi mata fada. Ta rakata har sassanta ta koma lallashinta.
Sai dai fa Hanifa ta girgiza da jin cewa Muhaseen din da ta raina diya ce ga Dr. Omar, duk jikinta sai ya yi sanyi, don ta san ta fita gata da 'power' a cikin gidan nan nesa ba kusa ba.

****
Kwanan su Muhaseen uku a Dubai ana yi mata gyaran amarci daga aljihun Aunty Badi'a, sannan suka koma saye-saye, duk yawancin kayan gyara jiki ne da kayan kichin, don Daddy ya ce bai yarda wani cikin su ya sai wa Muhaseen ko cokali ba har shi Dr. Omar din, ya riga yayo odar komai daga Italy, ko gara ba zai karba ba. Tunda tare ya gansu.
Duk da haka sai da 'yan'uwa suka hada kudi masu dama suka dankawa Dr. Omar, sabida suma ba abinda baya yi musu kan hidimar rayuwarsu data'ya'yansu, musamman ta fuskar karatunsu, ya hada da nashi ya budewa Muhaseen account da Guaranteed Trust Bank.
Shi kuwa San-Turaki kyautar karsanoni bakwai ya yi mata, za a ci gaba da yi mata kiwon su a can Dukku.
Ranar laraba jirgi ya sauke su a Abuja, Aunty Badi'a na kunna wayarta wayar Aliyu na shigowa, ya gaya mata yana cikin Abuja.
Ta ce, "Muma saukar mu kenan munje Dubai".
Ya ce, "Me kuka je yi?"
Ta ce, "Inda ka aike mu".
Ya yi murmushi ya ce ta bashi adireshi. Ta yi text din adireshin ta tura mishi, suna unguwar (Ministers Hill) ne.
Kusan a tare suka iso, don suna shiga gida yana shigowa. Aunty Badi'a ta sa aka bude mishi falon baki, ta ce da Muhaseen ta yi wanka ta shirya ta zo ta kai mishi abinci da ruwa.
Ta lura sai wani lakai-lakai take wajen yin wankan da shiryawar kamar ba ta son zuwa, don dai ba za ta iya ce mata ba za ta je bane.
Ta karbi man tana shafa mata, ga lallenta ya fito ya yi bakikkirin ya yi kyau sosai. Jikin nan ya kara yin taushi kamar na jarirai, sai sheki take. Inda duk ta gitta wani lallausar kamshi ke tashi da ba za ka iya tantance na kowanne irin turare ne ba. Sakamakon wankan turare da ake ta yi mata a Dubai.
Atamfa super koriya shar da ratsin rowan goro ta bata ta ce ta sanya, ta karbi kallabin ta daura mata ya zauna cif a kanta kamar nadin inji.
Riga da siket ne, siket din ya kamata sosai daga sama ya bude daga kasa sosai, ya fidda 'shape' mai ban sha'awa.
Ta kara fesa mata turare, ta ba ta gyalen kayan shima ruwan goro, ta kamo hannunta suka fito.
Kai tsaye kicin suka nufa, Zulai mai aikin Auntyn na ta firar dankali suka gaisa, sannan Auntyn ta hada komi cikin kwandon kayan abinci ta rako ta dashi har kofar dakin baki, ta yi mata murmushi, sannan ta juya.
Ta dade a tsaye a kofar ta kasa shiga saboda wata mashahuriyar kunya da ta lullube ta, kunyar Yaya Aliyun da a yau ya tashi daga Yaya ya koma husband anya za ta iya shiga?
Tana kokarin juyawa, don ta rasa da idanun da za ta dubi Yayan da su. Ba ta yi zaton ya san da tsayuwarta a gun tun dazun ba, tana jinshi yana waya ne da harshen 'Araucano'.
Yasa hannun hagu yayin da na daman ke manne da waya a kunnensa ya dage labulen ya janyo ta da hannun hagun ta fado kirjinsa.
Kadan ya rage ta suma, saboda kunya da tsorata. A haka ya jata har tsakiyar falon, ta sulale ta zube daga jikinsa zuwa kan kilishi.
Ya gama wayarshi ya tura aljihun shudin wandon 'jeans' dake jikin sa. Ya dagota ya rungume a kirjinsa. Runguma mai karfi, kamar ya tsaga kirjinsa ya sanya ta.
Yana sakin wata ajiyar zuciya mai nauyi. Kafin ya sake ta ya dago habarta da hannun damanshi yana murmushi yana kallon kyakkyawar fuskarta da ta canza mishi baki daya.
Ta runtse idonta gam, jikinta yana rawa da karkarwa. Ya ce,
"Relax Muhaseen, ....feel free with me. Me ya yi zafi na wannan tsorata haka? Yaya Aliyunki ne, ba dodo ba!".
Dariya ya ba ta sosai sabida yadda yayi maganar cikin sanyin zuciya, sai da ta murmusa. Hannunta ya kama suka zauna a cikin kujera, ya soma ba ta labarin Gwaggo mai ban dariya, sai da ya ga ta ware sosai har tana kyalkyala dariya. Bai kuma kara kai hannun shi jikinta ba, don ta saki jiki da shi sosai. Ya ce,
"To dauko abincin da kika baro a bakin kofa za ki gudu, ki zo ki zuba min, yunwa nake ji".
Ta mike a nutse ta je ta kawo, ta zauna sosai a kasa tana zuba mishi, yana hilatar ta da hira, har tana ba shi labarin Dubai, ta manta da zancen wani aure can, ta dauka tana serving Yaya Aliyunta ne kawai as earlier.
Suka shantake da hira har tana tambayar Mama da Aunty Hanifah, ya ce,
"Suna gida, Mama ba ta san na taho ba, da ba za ta barni na zo ba".
Ta ce, "Saboda me?"
Ya kalli tsakar idonta yai murmushi bai ce komai ba. Ya zuba lemon 'Rani'(soft orange) a tambulan ya mika mata.
Ta ce, "Na koshi".
Ya ce, "Ki karba ki sha, me kika ci?"
Ta ce, "Bamu dade da cin abinci a jirgi ba".
Sai ya ajiye a gefe ya koma ya jingina bayan shi da kujerar falon, ya lumshe zara-zaran gashin idonsa, yana yiwa Allah godiya mara iyaka cikin zuciyarshi. So yake ya janyota ya dora ta a kan kirjinsa, ta ji irin bugun da zuciyarshi ke yi a kowacce dakika da sonta da kaunar ta.
Amma bai yi hakan ba, tunda ya samu ta saki jiki da shi wannan din na tafe nan gaba, insha Allahu.
Ba makasudin aurenshi da ita kenan ba, ya aure ta ne kawai don yana sonta, yana kaunar ta, yana son rayuwa da ita har zuwa karewar numfashinsa.
Bai bar gidan ba sai da aka kira magariba. Ya koma Hotel din Rock-view ya kwana, washegari ya wuce Gombe.
Ya hurawa ma'aikatan gidanshi wuta kan su yi maza su karasa ginin. Sannan ya koma gida, bai samu Hanifah a gidan ba, Mama ta gyara dakin amarya sosai, ciki daya ne like da bandaki, ba a zuba mata kayanta da Daddy ya yo (order) daga Italy ba sai kadan, kamin Aliyu ya karasa ginin shi.
Shi da Mama suka shiga dakin, ya yaba komai, kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login