Showing 30001 words to 33000 words out of 63435 words
ta jikinshi yana rawa, itama haka, suka lula duniyar da suka bari tsayin shekaru uku har da doriyar watanni biyar. Kamar basu taba sanin juna ba sai yau. Da kyar ya yi 'light off' ya bar 'dim light'. Basu kara bi ta kan komai ba sai sauke tsohon bashi.
****
Washegari ya yi shiri ya nufi Kumo wajen Gwaggo, ya ga tarba kamar a goya shi, kamar yayi kuka sabida tausayin tsohuwar da yadda ta damu da shi. Ta kawo fura ta ji kindirmo babu sukari, da dambun nama da soyayyun kaji duk ta dire masa. Sun ci tare sun koshi. Sun sha hira. Ta sa aka rakashi wajen sauran 'yan uwa duk ya gaishesu ya yi musu ihsanin da ya saba, daga nan ya nufo Bajoga.
Kai tsaye ofishin Hajiya Ramatu ya nufa, ita tasa aka kirawo Muhaseen, ta tsaya a kanshi yadda Muhaseen ba za ta hango shi ba, shi kuma ya juya yana waya ya baiwa kofar shigowa baya.
Hajiya Ramatu ta ce,
"Muhaseen meke damun ki ne na ganki duk a yamushe?"
Ta yi rau-rau da ido, sai hawaye....... "Ciwon mara nake yi Hajiya, ga jini yana zuba daga jikina. Amma wai su Yasmin sun ce lafiyata kalau, suma suna yi".
Hajiya Ramatu ta rungumo ta ta ce,
"Allah sarki diyata, da gaske suke lafiyarki kalau, in ce ko sun koya miki yadda za ki yi amfani da 'Always pad?"
Cikin jin kunya ta ce, "Eh'.
Ta ce,
"To ki kwantar da hankalinki, girma ne ya zo miki, yanzu abin da za ki kula da shi shine, ba ke ba wasa da maza, ba kwanciya a jikinsu, ba yin hannu dasu, duk yadda kuke dasu. Ke ko hannu kada ki yarda ki kara hadawa da kowanne namiji, in ba haka ba, ciki zai fito a jikin ki".
Ta zaro ido abin dariya har ta baiwa Hajiya Ramatu dariya, ta ce,
"Hajiya ko dan'uwana ne?"
Sai ta kauce, a lokacin Yaya Aliyu ya gama wayar shi da yake yin magana da harshen (Araucano), ya juyo yana murmushi yana jinsu. Hajiya Ramatu ta ce,
"Ko wannan ne!".
Sai ta hangame baki ta kasa rufewa tana dariya, ga kuma hawaye a idonta. A tsaye yake kyam cikin koriyar shadda 'getzner, dinkin Mohammed. Dogon matashin nan ma'abocin ilhama, kwarjini da cikar zati, wanda cikin barci ko a farke, dare ko rana, tsufa ko kuruciya, fuskarsa ba za ta taba bace mata ba.
Hajiya Ramatu ta ce,
"Rufe bakin kada kuda ya fada....."
Sai ta fada jikin Hajiya Ramatu tana dariya. Yau ji ta yi Yaya Aliyun ya yi mata nauyin gani a ido. Ga dai tsayi ya kara, ga kirjin shi ya kara fadi, shi kadai amma kwarjininsa ya cika ofishin.
Ga wannan kamshin da ba ta jinshi a jikin kowa, in ba shi ba, yana tashi a hankali. Ta kai siraran tafukanta ta rufe fuskarta tana dariya, farin ciki fal fuskarta da zuciyarta, bakinta ya ki rufuwa ta ce,
"Yaya Aliyu sannu da zuwa....yaushe ka dawo?"
Zama ya yi a cikin kujerun 'cushion' na ofishin, ya kasa dauke ido a kanta. Gaskiyar Asabe ne. Muhaseen din da ya tafi ya bari ta kara girma, ta zama budurwa mai zati, 'yar shekaru goma sha shidda, ko'ina a jikinta hutu ke Magana, kugunta ya fito, kirjinta ya ciko, fatar jikinta ta kara taushi kamar ba ta taka kasa, ga hanci, ga ido. Ji ya yi kamar ya mike ya rungume ta ko ya samu sauki a cikin zuciya da gangar jikinsa.
Hajiya Ramatu ta fita ta barsu, sai ya taso ya dawo gaban Muhaseen ya zauna, ya rasa inda zai sa kansa. Soyayyar dake kwance male-male cikin zuciyarsa ta Muhaseen, bai san adadinta ba. Wadda kuma ba zai ce ga ranar da ta soma tofo cikin zuciyarsa ba. Yau ta fito muraran, a fuska da cikin kwayan idanunsa.
Wallahi-Wallahi!! Tun ranar da ya fara ganinta, ta dishe hasken ko wacce diya mace daga idanunsa. Ita kadai ce yake gani cikin mafarkansa a matsayin matar da yake so, uwar 'ya'yansa kuma matarshi har a Aljannah.
Mika hannu ya yi zai kamo nata, sai ya tuna da wa'azin da malamarsu ta gama yi mata yanzun nan, ya yi saurin mai da hannayen shi baya ya sarke su.....
"Tell me how much you missed me Muhaseen....... ".
Dariya ta yi,
"Kaima dai Yayana ai ka san ba zai fadu ba!".
Ya daga gira, cikin kallon ta,
"Wani lokacin sai mu yi ta hasashe na mafarkanmu Muhaseen, kowa da irin mafarkansa.
Wannan ranar tana daga cikin renakun mafarkaina. Abin nufi, ranar da zan yi tozali dake kin mallaki hankalin kanki, ko na ce rana ce da na zaba na gaya miki wasu maganganu masu muhimmanci, da mafarkaina na kullum, ko kin san mene ne mafarkan nawa?"
Ta girgiza kai, duk da ba wani fahimtarsa ta yi ba. Shima sai ya basar, ya dauko wata maganar daban.
"Yaya karatun? Meye labarin bayan rabo?'
Wannan karon ma dariya ta yi,
"Karatu alhamdulillahi, ni da nake makaranta ina nake da labari? Kai zan tambaya, kana ganin 'yan kwallon kafa a Argentina?"
Ya yi murmushi ya ce, "Sosai ma kuwa, nima na shiga na yi lokacin da ake World Cup".
Ya fiddo wayarshi yana binciko mata hotuna wadanda suka yi suna ball din, da wadanda ya yi tare da manya-manyan 'yan kwallon Argentina.
Tana ta gani tana dariya ta ce, "To ka ce ma ashe course din kwallo ka je?"
Ya ce, "Oh-oh, oh-oh! Meye gamina dasu? Na dai yi sha'awa ne lokacin da nake 'free' . Amma ina ruwan ma'aikacin 'custom' da kwallo?"
Haka suka yi ta hira yana biye mata curiosity dinta (kwakkwafinta) ba tare da gazawa ba.
Hajiya Ramatu ta shigo ta ce,
"Aliyu ka zo ka tafi, Muhaseen za ta koma Hostel an tashi daga class, gashi ka janyo mata rashin darasin karshe".
Ya ce,
"Babu komai Hajiya, ai AMANATA ba daga nan ba, na san gobe za ta karba wajen kawayenta ta kwafa, ba za ta bari darasin ya wuce ta ba".
Ta tafi tana waiwayon shi, yana murmushi yana daga mata hannu. Bai daina kallon hanyar da ta bi ba, sai da ta kulewa ganinsa.
Ya lumshe ido a hankali, ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya mike tsaye, ya yiwa Hajiya godiya da sallama ya juya ya fita.
Sanda ya iso gida yamma ta yi sosai. Hanifah ba ta dawo ba, ya yi kwafa yana cewa a ransa, wannan aikin barin shi za a yi, wallahi ba zai yiwu ba.
Sai gata ta shigo cikin kayanta na lauyoyi, tana cilla jakarta sama tana cafewa, sam ba ta lura da tsayuwarshi a gefe ba, don har waka take yi ta zabiya Nancy Agram.
Ya ce,
Look! Ni fa ba sa'an ki bane, da za ki dinga fita tun sassafe ki dawo sanda kika ga dama, don haka wannan gantalin na soke shi daga yau, tunda babu rashin ci babu rashin sha, balle zanin daurawa.
Don haka yau ce rana ta karshe da za ki kara fita. Ki rubuta resignation letter ki yi zaman aure cikakke irin na kowacce macen mutunci".
Ta harare shi ta zumbura baki,
"Kaima wasa kake.....".
Tasa kai ta yi shigewar ta dakinta tana rage kayan jikinta. Ya bita har dakin yana cewa,
"To ki kara fita ki gani, tunda wasa nake, ai kin san dama sa'an wasanki ne ni, go ahead.
Amma wallahi duk ranar da kika kara sa kafa kika fita daga gidan nan ki wuce Darazo in kin dawo, o.k?" Shima ya juya yai tafiyarsa.
Ai kuwa ta fashe da kuka, ta biyo bayansa tana fadin
"Me kake nufi? Kana nufin karatun da na kwashe shekara goma ina yi ya tashi a banza ko me? To wallahi ban yarda ba, ai dama na san neman hanyar rabuwa dani kake shi yasa ka biyo ta nan.
Babu Darazon da zani, don a nan na tashi na ganni. Sai dai in tafi inda na fi wayo". Ko tanka mata bai yi ba, ya banko kofar dakinsa.
Ta kulu iyakar kuluwa, ta koma dakinta ta rasa abin yi, sai ta tsinke da kuka. Ta yi mai isarta ta gaji, daga karshe ta lallashi kanta don ta san ko kukan jini za ta yi ba zai zo ba balle ya lallashe ta. Ta ce cikin ranta
"Ai yana da na gaba dashi, dole a kwato mata 'yancinta".
Da safe ta yi shirin ta za ta fita, amma tana jin tsoro. Ta koma cikin falo ta zauna tana sharar hawaye.
Ya fito cikin shirinsa, riga da wando samfurin 'Marc Jacobs', bakake masu ratsin fari. Ya yi masifar kyau, har ta samu kanta da binshi da kallo.
Wani masifaffen SO na kara keta zuciyarta, har ta samu kanta da tausayin kanta, kan soyayyar wanda bai san tana yi ba, yana zaune da ita ne kawai don biyan bukatarsa, amma babu burbushin soyayya, ko kadan babu!
Tana kuka kashirban ta kira Mama a waya ta fara gaya mata, Mama ta ce
"Ki zo yanzu gashi nan a dakina sai in ji matsalar".
Ta yi sallama a bed room din Mama, yana zaune a gefen gadon Mama yana shan 'tea' a dan kankanin 'mug'. Bai dago ya kalle ta ba sai Mama ce ta amsa mata sallamar.
Ta zauna a kan stool din madubi tana share hawaye da gefen gyalenta.
Mama ta ce, "Duk me ya yi zafi har da kuka haka, me ya faru?"
Ta ce cikin rishin kuka,
"Wai cewa ya yi na daina zuwa aiki, in ajiye shi".
Mama ta dube shi cikin mamaki,
"Don me?
Ya za ka ce ba za ta mori iliminta ba? Ga aikinta mai tushe daga addini na taimakon wanda aka dannewa hakki. An sha gwagwarmayar karatu shekara da shekaru, amma a kare a zaman gida?"
Kamar ba zai yi magana ba, can kuma ya ce, "Ni kuma a wane matsayi nake Mama?"
Ta ce, "Kamar ya ya?"
Ya ce, "Sunan auren namu nake so in sani, jeka-nayi ka, ko me?
[9/4, 12:57 PM] Asmau: Ya fada daga can bakin kofar shigowa falon, ashe tuntuni yana tsaye yana kallonsu yana murmushi, kuma duk sai kunya ta kama ta, ta ga kamar ta yi wauta.
Ta juya ta tafi dauko mayafin duk suka mike suna sallama da Mama, godiya ta ki karewa a bakin su.
Ita ma ta dauko nata mayafin tana cewa, "Ai ban ga ta zama ba, dani za a tafi kada ku rike min 'ya daga bada aro".
Aka sa dariya gaba daya. Aunty Badi'a ta ce, "Ni da har zamu wuce Abuja ta ga 'yan'uwanta ashe ba za a bani ba Mama".
Mama ta ce, "Don dai 'yan kwanaki biyu ko uku ai ba za a hanaki ba, tunda an gama makaranta".
Ta ce, "A'a, hutu za a zo min na wata uku, kwana biyu sunyi kadan Maman Muhaseen".
Mama ta ce, "A'a, in wannan ne kam ba za ki samu ba, sai ki yi hakuri da wanda ya samu". Aka kara yin dariya.
Motocin suka jera reras har garin Dukku. Muhaseen na motar Yaya Aliyu ita da Aunty Badi'atu da Hajiya Antu, ita ce a gidan gaba. Mama na motar su Yaya Khaula, kowa cikin annashuwa.
Lokacin da suka iso gidan San-Turaki wato family house din su, hannunta na cikin na Badi'a, ta ki sakinta har turakar San-Turaki Abdullahi.
Nan suka tadda Daddy da Dr. Omar, ai da ganinsa Muhaseen ta ja baya ta rushe da kuka. Daddy ya ce,
"Ke bama son sakarcin banza, za ki shigo ko karkashin gadar za ki koma?"
Shi kam Dr. Omar cewa ya yi,
"A'a, bari in fita tunda dai ni kadai ne wanda ba a son gani, to alhamdulillahi".
Shi haushin Daddy ma ya ji da ya yi mata tsawa. Yarinya a kan gaskiyarta ta. Ya share idonsa da hankici, don farin cikin da ke cikin zuciyarsa ba zai taba kwatantuwa ba.
Bukatarshi ta duniya ta gama cika saura guda daya shine, Allah ya nuna masa Halima kafin ya dau ransa, ko ba ta komawa auren sa ba, to ta yafe masa abin da ya yi mata ko ya samu rangwame wurin Ubangiji.
Farin dattijo mai farin gemanya, ya tsufa tukuf, domin a kalla ya yi shekaru dari, amma da jin sa da ganinsa tangararau. Yana kishingide a kan tuntun amma saboda ganin jikarsa diyar Halima, sai ya yunkura ya tashi ya zauna yana cewa.
"Ya ki Muhaseen rabu dasu, wurina ai kika zo ko? Ba wurin babanki mara kirki ba, to taho mu gaisa...."
Da sauri ta karasa gare shi ta zauna a kan traditional carpet irin nasu na sarauta da ake yi mahadin tuntun da ya kishingida na fata, ya dora hannu a kanta yana ta sa mata albarka.
Turaki yasa aka kirawo Mal. Tanko da mai dakinsa Ta-Birni ya ce su zo su ga bakwainin da suka ceta diyar Halima yau Allah ya kawo ta da kafafunta, uwar ce dai har yanzu ba a ganta ba.
Ta-Birni ta rungume Muhaseen tana hawaye tana cewa,
"Halima bata kyauta min ba, shammata ta tayi ta tafi, da ba zan barsu suje ko'ina ba".
Duk ihsanin da Dr. Omar ya yiwa Mal. Tanko don ya wanke kanshi, Mal. Tanko ya ki amsa, ya ce,
"Ni ba don kai na yi ba sai don Ubangiji da hakkin makwabtaka.
Ka tuna abin da na gaya maka a wancan lokacin cewa.....wata rana sai ka nemi 'yar Halima da kanka, a lokacin da nadama ba za ta yi maka amfani ba.
Yanzu ina amfanin haka? 'Yar da ka haifa ba ta son ganinka, sannan bokon bai baka abin da Halima ta baka ba".
Shi dai Dr. Umar ya yi lakwas, ko me aka ce ya yi amsawa yake ya bada hakuri abin gwanin ban tausayi.
Turaki ke tambayar Daddy ko Muhaseen ta fidda miji? Don gata nan zokaleliya da ita. Daddy ya ce,
"Ita bata san wannan ba, karatu take yi a saninsa. Sai dai a tambayi Aliyu don shine amininta.
Turaki ya juyo ga Aliyu wanda duk hayaniyar da ake bai tofa tashi ba, kyawawan idanunsa na kan Muhaseen, wadda ke kwance jikin tsohonta ya ce,
"Ali wane ne gwanin amaryar tawa?"
Kai tsaye ya ce,
"Babu kowa sai NI ranka ya dade".
Duka basu fahimce shi ba. Turaki ya ce, "Kamar ya ya sai KAI?"
Ya yi kasa da kansa ya ce,
"Ni nake son Muhaseen.....ni zan AURE TA!"
Mama ta yi saurin dagowa ta dube shi kansa na kasa bai yarda ya hada ido da ita ba. Don ita yake gani a matsayin mahaifiyar Muhaseen.
Turaki ya ce,
"Kai wannan abu ya yi min dadi, (da yake tuni ya san Aliyu, don duk sanda ya zo wajen Dr. Umar sai ya zo ya gaishe shi kafin Dr. Umar ya koma Bauchi tun yana yaro).
Ita kuwa Muhaseen fiddo ido ta yi waje abin dariya, amma ba ta ce komi ba. Ya dago yana yi mata kallon don't you lobe me? Ta yi saurin dauke idonta ta sunkuyar da kanta, duk wata gaba ta jikinta ta yi la'asar.
Ita kuma Mama dadi ne ya rufe ta, amma kuma a ranta tana cewa a hada Hanifa da Muhaseen kishi ai bai yi ba, kuma ita Hanifa za ta yi blaming cewa da amincewarta.
Don haka ta bude baki ta ce,
"Idan ita din ta amince ko? Ko fin karfi kake so ai mata, da tun farko baka fada ba sai yau?"
Daddy ya harari Mama don ya gane 'yarta Hanifah take tayawa kishi. Ya ce,
"Ai kuwa yanzu ne ya dace ya fada, a gaban madaura aure, bari ki gani...."
Ya kaikaice ya zaro kudi a aljihunsa ko kirgawa bai yi ba ya kaisu gaban Turaki ya ce, "Ga kudin tambaya...."
Ya sake kaikaicewa ya zaro wasu ya ce, "Ga kuma sadaki, Allah ya ja da ran Turaki.... zamu iya shafa fatiha yanzu?"
Turaki ya yi murmushi dadi ya rufe shi, amma sai ya ce,
"Abi a hankali Surajo gaggawar ta mece ce? Kai da 'yar ka? Amma kamar yadda Maimuna ta fada ne a bari a ji ta bakin yarinya, gaggawa daga shaidan ce".
Aunty Badi'a da ta fi kowa karadi da farin ciki da son Muhaseen farat daya ta ce, "Muhaseen ai kina son shi ko?"
Ta yi saurin kai gyalenta ta rufe idonta kamar ta ce da kasar ta tsage ta shige saboda kunya.
Aliyu sai wani irin murmushi yake wanda bai taba yin kwatankwacin sa a rayuwarshi ba. Daddy ya ce,
"Tunda ta rufe ido ai fulakon kenan. Bari in kira Dr. Omar".
Ya dauko wayarshi yana neman layinsa, Turaki ya ce duk matan su shiga gida yanzu za su daura auren ALIYU da MUHASEEN".
Badi'a ta kaikaice ta rangada wata zazzakar guda, suka mike suna rige-rige wajen jawo Muhaseen su fita, wadda har zuwa lokacin ta kunshe fuskarta cikin gyale har tana tuntube da dokin kofa. A haka suka yi cikin gidan dakin Maman su Khaula wato uwargida Dijah.
Karfe biyar na yammacin ranar ta litinin iyaye da 'yan'uwa, da mutanen garin Dukku, suka shaida Muhaseen ta zama matar Aliyu Suraj Kumo, a kan sadaki mai albarka, wato mafi kankanta.
Washegari mata suka zarce da yinin biki. A can waje kuma fadar San-Turaki maroka ke ta zuba mashi kirari shi da Dr. Omar suna kwasar rabonsu, domin kyauta ta bajinta Turaki ke ta yi ta karsanoni da kujerar Makkah.
Shi kuwa Dr. Omar kyautar baburan Lifan yake ta yi ga matasan garin Dukku talakawa, ana ta busa algaita da kade-kaden kalangu irin nasu. Ana ta fidda kabakin abinci ga mabukata da mahalarta bikin. Wai a hakan ma don bikin ya zo ba cikin shiri bane, ba a yo gayya ta nesa ba.
Aunty Badi'a ta roki Mama ta ba ta amarya ta wuce da ita Abuja in ya so bayan sati daya sai a je can a taho da ita Gombe.
Mama ta ce sam ba ta yadda ba, ita za ta gyare 'yarta. Amma Daddy ya roke ta ya ce a barsu suje, wannan mulkin mallaka har ina? Ita Mama gani take kamar kwace Muhasin Badi'a ke son yi.
Badi'a ta ce,
"To ban da abinki Haj. Maimuna, ai 'ya ta ta riga ta kara zama 'yarki, mu 'yan kallo ne".
Mama ta yi murmushi. Kanta ya fasu. Aliyu ne ya dauke su ita da Daddy suka wuce Gombe don fara shirye-shiryen tarbar amarya.
****
Hanifah na gida ita kadai ba ta san me ake yi ba. Don ita tun safe har yamma tana kotu. (Ina ruwan Alkaliya mai Shari'a).
Ya dai yi mata text cewa sun tafi Dukku
an gano iyayen Muhaseen, amma ba ta taba kawowa ranta cewa Dr. Omar ne mahaifin Muhaseen ba, don ta san shi farin sani, shi ya samo mata aiki.
Shima Aliyun