Showing 54001 words to 57000 words out of 63435 words
maka?"
Ya runtse idonshi kirjinshi na bugawa, da ambaton sunan 'Mu-ha-seeeen' da Maman tayi. Suna mafi soyuwa a gareshi.
Da Maman ta ji shiru, ta dauka aje wayar ya yi, sai kuma ta ji a hankali cikin sanyin muryarsa ya ce, "Cewa ta yi na yi mata laifi?"
Mama ta ce, "Ban sani ba, amma ka yi a hankali ba'a barin mai juna biyu cikin damuwa, duk abinda ka yi mata ai Allah Yana gani, idan ka boye mini. Kai da bakinka ka fada Muhaseen AMANA ce, Allah Ya baka, haka ake rikon AMANA?"
Cikin mamaki ya ce, "Ciki Mama? Don Allah Mama da gaske?" Ta yi tsaki ta kashe wayarta.
Ture tulin takardun dake gabanshi ya yi, akwai 'file-file' na mutane da yawa dake kan layin ganawa da shi. Amma haka ya tsallake komi ya basu hakuri, ko gida bai koma ba, direban shi na office ya wuce da shi filin jirgi.
Shap, ya manta ya baro Hanifah a gida. Sai da ya sauka a filin jirgin saman garin Gombe ya bude waya ya kira ta ya ce, "Ina Gombe, yanzu na sauka".
Takaici ya kama ta, ta ce, "Amma ka san ni kadai ce a gidan ko?"
Ya ce, "To me zai ci ki? Kina cikin 'Camp' karkashin kulawar sojoji da makotan kirki?"
Ya kashe wayarshi ya kira Danlami cikin dan lokaci ya iso suka taho".
Mama ba ta zata ba ta ji sallamar shi a falonta, tana bisa carpet tana nazarin wani littafin girke-girke na Turanci (FROM MY KITCHEN) Na Hadiza Umar Dogon Daji uwargidan Jelani Aliyu.
[9/4, 12:59 PM] Asmau: Ta aje littafin ta dube shi domin ya yi mata bazata. Ta sa mishi ido har ya karaso cikin 'uniform' dinshi makale da anininshi mai dauke da sunanshi da 'rank' din (Controller Aliyu Suraj Kumo). Kayan sun karbeshi sun mishi kyau, sun kara mishi kwarjini ainun. Cikin ranta take yiwa Allah tazbihi, domin ita kanta kwarjinin Aliyu da zatin shi yana bata tsoro, don haka ne kullum ta ganshi addu'ar neman kariya daga sharrin mutum da aljan take yi mishi a zuciyarta.`
Har ya zauna kusa da ita Mama ba ta yi magana ba, ya kama hannunta ya rike cikin nashi cike da damuwa, don ko sallamarshi a ciki ta amsa ta.
"Mama in laifi na yi miki ki yi hakuri ki yafeni".
Ta ce, "Ni kuwa laifin me za ka yi mini Haydar? Ina dai son in san laifin me Muhaseen ta yi maka?"
Ya yi wani miskilin murmushi ya ce, "Rabu da Muhaseen Mama, tunda ta ga Ummanta shi kenan ta daina SO na".
Mama ta yi dariya sabida yadda yayi maganar cikin sanyi? Ta ce, "Ya ya a kai ka san ta daina son ka, alhalin baka shiga zuciyarta ka gani ba?"
Ya lumshe ido ya bude su ya ce, "Mama kiri-kiri ta nuna mini, ko ganina ba ta son yi. Ko inda nake ta daina zuwa, ta daina kula ni, ko kiran ta na yi a waya sai ta kashe wai ba ta son turarena. Ina ruwanta da turare na?
Da can ba ta san ba ta son turaren nawa ba sai yanzu? Har ta koyawa Hanifah, suka hade min kai tun a Saudiyyah. Da muka dawo ita Hanifah ta zo inda nake ta bani hakuri na kuma karbi uzurinta na rashin lafiya ne, amma Muhaseen fa? Kulle kofarta ta yi Mama, don ba ta son ganina.... shine na bata fili ta sarara ni kuma in je in nemi ta uku in aura, wadda zata so ni yadda nake son ta, ta darajanta son, ta kimanta shi, ta kula dani yadda zan kula da ita, tunda Mahasin bata yi dani yanzu......tunda ta samu Ummahnta".
Mama dariya take ta ce, "Wai don Allah duk girmanka zaka ce baka san alamomin mace mai juna biyu ba? Muhaseen ba ta da ishasshiyar lafiya duka cikin laulayin ciki ne.
Ga damuwa duk da bata fada min ba, kowa da irin yadda juna biyu yake zuwa masa Aliyu. Ai sai ka tambaye ta dalili ko? Ka bata damar yi maka bayani, amma ba ka yi fushi da ita ba, nawa Muhaseen din ta ke?".
Ya kai yatsunshi cikin sumar kanshi yana murzawa yana murmushi, ya dan kau da kai ya ce, "Tana ina ne?"
Mama ta ce, "Inda ka ajiye ta".
Dakinta na da ya fara lekawa, ba ta nan. Sai ya nufo dakin Mama. Daga can karshen gadon Mama ya hango ta tayi linkif cikin bargo mai taushi da 'yan makarantar kwana ke kira 'locomotion' tana barcin ta sadidan.
Ya karasa ya tsaya a kanta yana kallon ta da idanun rahama da kauna. Duk kuma sai tausayinta ya rufe shi da ya tuna tana dauke ne da babynsa karkashin mahaifarta tsayin wani lokaci ba tare da ya bata kulawarshi da soyayyarshi ba. A daidai lokacin da take matukar bukatar hakan
Daidai kanta ya zauna, ya dauki kanta ya aza a cinyoyinshi. Ta rame kwarai ta yi fari sosai, jikinta ya kara taushi da sulbi sosai, duk ta dashe kamar jikin jariri sabuwar haihuwa.
Ya janye bargon ya dora hannu a kan cikinta ya tasa sosai kamar ya wuce watannin shi, yayi mamaki sosai, ko da yake shi bai ma san ko wata nawa bane.
Ya dage 'yar yaloluwar rigar barcin ya sumbaci cikin sannan ya rungume ta.
Muhaseen na barci tana mafarkin wai ga Yayan ya dawo ya rungume ta, ta kuwa kara gyara kwanciya sosai a jikinsa itama ta kara rungume abinta, tana sauke sassanyar ajiyar zuciya.
Sai dai kuma juyawar nan da za ta yi sai ta ji dan karfen aninin jikin 'uniform' din sa ya soke ta, sannan sassanyan kamshin Onde-Vertige dake tashi a hankali daga jikinsa ya mamaye numfashinta.
A hankali ta bude ido, ta tabbatar ba mafarki take yi ba; Aliyun ne da gaske, kwance rungume da ita kamar zai balla ta. Don ma katon cikin ya tokareshi.
Don dadi sai ta fashe da kuka, amma da ta tuna abin da ya yi mata sai ta soma kokarin zame shi ta mike. Ya yi saurin cafko hannunta ta fado kan kirjinshi.
Ta bude baki za ta yi ihu ya yi saurin toshe bakinta da nasa. Sai da ya yi 'kissing' din ta yadda ranshi yake so sannan ya sauka a gadon ya kwantar da kai a cinyoyin ta, kwalla ta cika masa ido.
Ya ce, "Ki yafe ni MUHASEEN, ban kyauta ba, ban sani ba, ban san kina dauke da babyna ba Muhaseen, don Allah ki yi hakuri. Duk na dauki laifin koma na mene ne na dora a kaina".
Cikin kuka ta ce, "Wato ba don ina da cikin ba da ba za ka zo ba? Sai ka ci gaba da wulakanta ni? Me na yi maka? In ka daina sona ne sai ka....."
Ya sake toshe mata baki da tafin hannunshi na dama, "shiiit, talking rubbish muhasin, ba haka bane fushi na yi saboda nima kin daina sona, tunda kika samu Umma... ba ruwanki dani, balle halin da nake ciki, in na ce zan zano miki laifuffukan da kika yi min a Saudiyya wallahi sai na kwana ban gama ba.
Amma dai yanzu na HUCE..., so let the bygone be bygone. Tashi mu tafi gidanmu, na gaji sosai, kuma ina son hira da Baby na".
Ya mike yana murmushi ya mika mata hannu, ta zumbura baki sannan tana kunkuni, tana kauda kai "Ni ba inda zan je...."
"Kada ki yi min haka Muhaseen, saboda ke na baro dukkan ayyukan dake gabana, ko sallama ban yiwa Hanifah ba....this is not the kind of wellcome I deserve....!"
Dole ta mike da tsinin cikinta, ji yake kamar ya tsaga kirjinsa ya sanya ta. Ya dauki zani ya daura mata a karkace, ya sanya mata hijabin sallar ta ya duka ya ce.
"Hau in goya ki".
Dariya ta yi ta harare shi idanunta cike da kauna mara algus, ta yi gaba ta kyale shi. Ya biyo bayanta yana cewa,
"Ki tsaya mu jera, don Mama ta san kin huce".
Ya kama hannunta suka fito falo. Maman ma ta yi hayewarta saman Daddy ta rabu dasu, sai ya ciccibe ta itada zungureren cikinnata, bai ajiye ta a ko'ina ba sai a katafaren gadonsu.
A wannan ranar Muhaseen ta ga kauna 'yar usuli daga Yayan nata, hadi da sassanyar soyayya mai tsayawa a zucci.
Abinki da mace mai yaron ciki, sai hakan ya kara armasa al'amarin, cikin su babu wanda bai yi kuka ba, sabida soyayyar dan uwansa.
Motsi kadan za ta yi ya ce, "Ya ya ne?"
Hatta numfashi ji yake kamar ya yi mata, lallashi, tausayi da tattali kamar ya haife mata jaririn.
Washegari bayan sun kintsa sassan Mama suka nufa.Daddy da Mama suna bisa table suna karya kumallo.
Daddy ya bishi da kallon mamaki, don bai san a gidan ya kwana ba. Mama ke mishi bayanin cewa ai tun jiya ya zo.
Suka kwashi gaisuwa suka zauna aka ci gaba da yin kalacin tare da su. Sai da suka kintsa ya ce, "Mama in babu matsala zamu tafi Warri".
Mama ta kama haba, ta ce, "Da wa? Ba dai da Muhaseen ba?".
A razane ya dago ya dube ta.
Ta ce, "Yarinyar da yaron ciki wanda ya fi girman watanninsa zan baka ka hau jirgi da ita?".
Ya dukar da kanshi kamar ya ce, "Wayyo Allah!"
Ya ce, "Mama babu matsala tunda ga Hanifah ma a can na san za ta kula da ita, nima ba zan dinga yin nisa ba".
Muhaseen kanta na sunkuye. Daddy ya ce, "Ina ruwanki? Mutum da matarshi kin fishi son ta ne? Ni kam bana jin dadin wannan mulkin mallakar da kike yiwa mutane a kan Muhaseen, alhalin baki fisu iko da ita ba".
Mama ta sha kunu ta ce da Muhaseen, "To ke kina so ki bishi ne ko kuwa?"
Kanta a kasa ta ce, "ni Mama duk yadda kike so, haka za a yi".
Ta ce, "Bana son gulma, kun gama kulla tafiyar ku can a daka ke da mijinki. In yadda nake so ne ki yi zaman ki tare dani in kula da ke har sai Allah ya sauke ki lafiya kin yi arba'in sannan ko ma gaba da Fatakwal ne ku yi ta tafiya".
Daddy ya ce, "To basa son kulawar taki, Allah shine mai kula da bayinSa. Ku tashi ku tafi, jirgin karfe nawa za ku bi?"
Aliyu kamar ya rungume Daddy, ya ce, "Ban sani ba sai mun je zan duba, don sai na yankar mata tikiti ba da wanda na zo zamu yi amfani ba".
Duka suka ce, "To Allah ya sauke ku lafiya".
Ya ce, "Ameen".
Mama ta ce, "Ya maganar aikin Hanifah?"
Ya ce, "Har yanzu dai hutun rashin lafiya take. Ban san me ta yanke ba".
Daddy ya ce, "Ina neman alfarma?'
Ya dago ya ce, "Ta mece ce Daddy?"
Ya yi dan shiru, sannan ya ce,
"Ka bar Hanifah ta yi aikinta".
Ya ci gaba da rarrashin shi. Ya ce, "Ka duba muhimmancin aikinta ga al'umma, gashi ta sha wahala ta yi karatu mai wahala, ka yi hakuri don Allah".
Ya ce, "Shi kenan Daddy. In zan zo hutun karshen shekara zamu taho gaba daya, lokacin komi na ginin ya kammala sai ta zauna a gidan ta koma aikin.
Ita ma Muhaseen makaranta zan sa ta in ta haihu, don Dr. Bello ya roke ni suna so ta yi karatun likitanci ba wanda take so ba, har ya fara nema mata gurbi a Jami'ar Sarki Abdul'aziz.
To amma Daddy? Daya ta yi gabas, daya ta yi yamma, ni na yi kudu, ya ya zan yi?"
Daddy ya dafa kafadun shi yana murmushin bada kwarin gwiwa, ya ce, "Haydara! Wannan shine "cigaba", wanda zamani ya kawo, wanda bashi dashi yanzu ko kallo bai ishi duniya ba, ba kwanciya a gida ba, hakuri za ka yi ka daure, kada ka danne musu 'yancinsu, ka basu dama su amfani al'umma kai kanka abin alfaharinka ne, kuma taimakon 'ya'yanka watarana.
Don munyi maganar da Dr. Omar ma ya ce ya samar mata gurbi a ATBU na ce zan yi shawara da kai. Don ban san ra'ayinka ba".
Ya ce, "Shi kenan a bari ta haihu din kafin nan 'transfer' dina zuwa Abuja ya fito, sai ta yi karatun a can, ko bana nan ga Badi'a".
Daddy ya ce, "Hakan ya yi, Allah ya taimaka".
Ya ce, "Ameen, don Allah Daddy kasa ido a kan aikin gidan nan don ma'aikatan suna wasa don sun ga ni ba mazauni bane".
Daddy ya ce, "Insha Allahu kan ku dawo komai ya kammala, kuna dawowa za ku shige gidanku da yardar Allah. To yanzu me za ka ce da Dr. Bello?"
Ya ce, "Hakuri zan bashi Daddy, ba zan iya nisa da Muhaseen ba balle 'ya'yan da za'a haifo mana daddy.....".
Ta dago da sauri tana mamakin rashin kunyarsa, sai ta bige da cewa, "Ni Daddy na fi son Bauchin sai in zauna a gidan Baba Umaru, tunda ka ce ya kusa aure har an sa rana".
Juya kwayar idanunshi ya yi yana yi mata wani kallo a kaikaice wanda ita kadai tasan rikicin dake cikin kallon nasa, ba shiri ta yi shiru.
Daddy ya ce, "To kai ka ji, ya za a yi?"
Ya ce, "Rabu da ita Daddy tana shirme ne".
Ta shagwargwabe fuska, "Allah Daddy ba shirme nake ba da gaske nake".
Ya ce, "A'a kam, nima wannan karon ban yadda dake ba, tunda mijinki ya ce ga yadda yake so, baki isa ki ce a'ah ba".
Ta ce, "Shi kenan Daddy.... Tayi narai-narai da ido kamar zata fashe da kuka".
Mama ta ce, "Ga Asabe nan ku tafi da ita na baku aronta zuwa lokacin da za ku zo hutu don ta rika kula da abincin da Muhaseen ke so, don Hanifa ba ta iya abin arziki ba, ita kuma Muhaseen in ta ji kamshin girki, to ba za ta ci ba".
Ya ce, "Babu matsala".
Ya mike yana cewa, "A gayawa Asaben ta kintsa".
Don murna Muhaseen rungume Mama ta yi tana yi mata godiya.
Shi ya hada mata kayanta cikin 'troller' din sa da duk abin da za ta bukata. Babbar murnar Muhaseen (tafiya da Asabe).
Suka yi sallama da kowa, Danlami ya debe su sai Airport, Porthercourt ta diba. A cikin jirgin ma Muhaseen rungume take a kirjin Aliyu, lokacin da jirgin ke rugugin tashi don kar ya jijjiga ta.
****
A WARRI
Suna sauka Aliyu waya ya dauko ya kira direban 'office' dinsa Mr. Jamoh ya debe su zuwa gida.
Hanifah na kitchen tana dafa abincinta (Indomie) ta ji ana danna kararrawa. Ba ta bude ba saboda tsabar tsoro sai da ta tambaya, "Wane ne?"
Asabe ta ce, "Nice Asaben Mama".
Ta bude ta dube su tana dariya ta basu hanya suka shige tana mamakin girman cikin Muhaseen, ta karbi (handbag) dinta da 'troller' din hannun Aliyu.
Ta ce, "Cewa za ka yi amarya ta yi kira, shine ka manta da uwargida ita kadai a gida ka tafi ka dauko ta?"
Ya ce, "To laifi ne?"
Ta ce, "A'a, ai ni na ji dadi, musamman saboda kadaici ya dame ni, ga ni ba gwanar bin gidajen makwabta ba. Sannun ku da zuwa Muhaseen, kun sha hanya ya Mama?"
Ta juya ga Asabe, "Asabe ya hanya?"
Ta ce, "Kowa da komi lafiya, a bani masauki in rage mara ta".
Ta yi dariya ta ce, "Dauko kayanki".
Ta ciccibo rindimemiyar tsohuwar jakarta Hanifa ta kaita Baskwata. Muhaseen kwanciya ta yi a doguwar kujera saboda gajiya.
Shi uban gayyar bai tsaya ba, dakin shi ya wuce ya yi wanka ya sauya kaya ya fice da sauri, don tsallake ayyukanshi ya yi ya tafi Gombe.
Hanifah ta zo tana yi mata magana cewa ta tashi ta shiga dakinta ta kwanta sosai ta huta, sai ta tarar har ta yi barci. Sai ta wuce ta kyale ta.
Aka shiga kitchen wai za a yiwa maigida da baki abinci, aka debo Indomie shida da kwai goma sai ga Asabe.
Ta kalli abin da take yi ta yi dariya ta ce, "Aunty Hanifah Indomie za a dafa mana ne?"
Ta ce, "Eh wallahi, kin san ta fi sauri".
Ta yi murmushi, "Hutar da kanki, matsa ki gani".
Ta dau katuwar tukunya ta dora ruwan zafi, ta ce, "Akwai samobita ko farar shinkafa?"
Ta ce, "Duk akwai, zo ki gani".
Ta bude mata 'store' dake shake da nau'i-nau'i na kayan abinci, amma abin takaicin ko buhunhunan ba'a bude ba balle a dafa, ta ce, "Gasu nan".
Ta diba kofi hudu ta wanke ta debi fulawa da za ta daure tuwon da ita, nan da nan ta mulmula lafiyayyen tuwon shinkafa fari tas da shi, ta nade malmala-malmala a leda.
Cikin kayan da suka zo dasu ta debi garin kuka da daddawa, tuni Hanifa ta gudu ta barta, ta debi kaji biyu a 'freezer' ta tafasasu da wadatacciyar albasa, garlic, maggi da dan gishiri da traditional spices, ta kada kuka mai shegen dadi.
Ta kammala ta debi 'warmers' ta juye, yadda dai Mama take yiwa Daddy, ta ware na Muhaseen ta kai mata dakinta.
Sauran ta aje a 'dining' ta canza shimfidar gado, ta share ta goge ko'ina sai sheki yake. Ta fesa room fresh ta kunna split ta rufo mata dakin.
Da ta fito falo Muhaseen ta tashi tana mika, ta ce, "Uwar dakina an tashi?"
Ta yi murmushi, ta rakata daki ta shige toilet dan ta yi wanka da alwala, nan ta ga food flasks a gefe Asabe ta ajiye mata.
Ta yi wanka ta yi sallar magariba da isha, sannan ta caba adonta da riga da wandon India (deep orange) tasa dryer tana busar da gashinta da ta wanke da kumfar head and shoulder. Sannan ta zauna a nutse tana cin tuwon. Asabe ta leko tai mata sai da safe ta dauki nata abincin ta wuce baskwata.
Daga bakin kofa ya tsaya yana kallon ta yana murmushi, cikin uniform dinsa yake, idanunshi sun kankance sun nuna gajiya da bukata. Ya karasa shigowa ya je toilet dinta ya wanke hannun shi yayi 'brush' ya fito, ya sa hannu a tuwon suna ci tare.
Ta yi mai wani kallo kamar na jin haushi kamar kuma na soyayya, ta ce, "Ya ya za ka zo ka cinye min tuwo na? Naku yana dining".
Ya ce, "Namu ni da wa?"
Ta ce, "Kai da Aunty Hanifah mana, kafin in zo ba tare kuke ci ba?"
Ya ce, "To ai yanzu kin zo, kada ki kara cin abinci ke kadai. Tare zamu dinga ci in har ina gida, in bana nan ku ci tare".
Ta ce, "To".
Da suka kammala da kanshi ya kwashe kayan ya kai kicin ya dawo falo ya zauna, sai ga Hanifa ta fito. 'Shirt' din 'gucci' ce fara kal a jikinta da bakin siket din (versace) wanda bai kai kasa sosai ba, ta zauna