Showing 12001 words to 15000 words out of 63435 words

Chapter 5 - Amanata HAUSA NOVE

ASMAU   

11 Nov 2024

19029

a falon, Mama na kicin, sai mai aikinta tana goge 'tiles' din falo. Ya wuce dakin Mama ba ta nan, don haka ya bi ta kicin.
Ya tadda tana tukin tuwo, kamshin turarensa ne ya sanya ta juyo ta dube shi. Ita kanta Aliyu yana mata matukar kwarjini a lokutta da dama, har ta dinga tambayar kanta anya! Ita ta haifi wannan sardidin Balaraben?

Kyakkyawa ne na karshe, ma'abocin ado; dana ce ado a nan, ina nufin; na suttura da na zuciya. Babu komi cikin zuciyarshi sai alheri ga kowa. Wato dai; Babu kyashi, babu hassada. Ba shi da abokin fada, ba a taba kawo mata karar shi ba tun yana yaro.
Yana jin kanta, kamar diya mace ke gare ta. Shi din nan har girki yake taya ta, da sauran ayyukan cikin gida, tun yana karami har girman sa.
A wannan zamanin samun da mai halayyar Aliyu-Haydar da wuya. Bai dauki rayuwa da zafi ba, yana bin komi a hankali. Duk da cewa ya tashi cikin gata, amma bai taba daukar gatan nasa a matsayin tabbataccen abu ba.
Ta juyo ta dube shi idanunta cike da kauna irin ta Uwa ga dan ta. Ya amshi muciyar zai tuka mata tuwon, ta yi dariya ta hana shi.
Ta ce, "Goggo ta iso".
Ya ce, "Kai Mama shine baki taso ni ba, gashi har na makara sallah".
Mama ta ce, "Ita ta ce in kyale ka, ba ta yarda a katse maka hutu ba, don ta san in ka tafi kai da hutun kun yi hannun riga kenan".
Ya yi dan murmushi ya juya ya fita ya nufi dakin saukar Goggon.
Ya yi sallama Gwaggo ta amsa tana daga kishingide a gefen katifarta, ya idasa shigowa dakin ya zauna kusa da ita.
Ta ce, "Sai da ta taso ka ko?"
Ya ce, "A'a, ba ruwan Mama ni na tashi da kaina. Kun iso lafiya?"
Ta ce, "Alhamdulillahi, ya ya aikin?"
Ya ce, "Komi lafiya, ya ya wajen su Malam Sani (Kaninta)?"
Ta ce, "Kowa lafiya".
Ya ce, "Daddy ya ce baki da lafiya, gashi kuma na ganki ragas, kin dai ki mutuwa mu ci gumba".
Ta yi dariya ta ce, "Dan nema, dani da kai wa ya san gawar fari? Ka ganni nan daram, sai na goya 'ya'yanka insha Allahu".
Ya basar ya ce, "Me ke damun ki ne Gwaggo? Ki yi briefing dina (takaita min) abin da ke damun ki don in san me zan gayawa likita in mun je".
Gwaggo ta ce, "Meye wani birifil? In za ka yi min Hausa ka yi min, in ba za ka yi min ba to ka yi min yarena (Fulfulde)".
Ya dara sosai ya ce,
"Ina nufin ki takaita min abin da ke miki ciwo, ni ban iya wani Fulfulde ba".
Ta ce, "Kowa ya bar gida Aliyu.....'
Ya ce, "In gidan zai yi adalci, to kada ya barshi.....".
Ta soma gaya mishi nan na ciwo, can na ciwo. Ya ce,
"Dakata-dakata, ai cewa nai ki takaita".
Suna haka Daddy ya yi sallama a kofa. Gwaggo ta yi mishi izinin shigowa. Ya shigo yana cewa, "Ke da maigidan naki ne?"
Ta ce, "Sam, ai ni tuni na guntule auren tunda ya ki ya yi min kishiya".
Nan da nan ya sauya fuska. Daddy ya gyara zama ya ce,
"Ban da abun ki Gwaggo, wacce mace ce take son kishiya? Gara da Allah Ya kawo ki, ki tambaye shi dalilin sa na kin aure, don mu har yau mun kasa gane kansa".
Nan da nan ya mike yana cewa,
"Daddy zan leka wajen Al-Ameen ya min (tedt) cewa ya iso kasar yau, mun jima bamu hadu ba".
Ya ce, "Za ka gudu dai, saboda kada ayi maka zancen aure, Allah Ya shirya. Manzo (S.A.W) dai ya ce, "Aure sunnata ne, wanda ya ki sunnata baya tare dani".
Kamar zai yi kuka ya ce,
"Daddy ku yi min auren, da duk yarinyar da ta kwanta muku, ni bana son kowa!".
Ya sa kai ya fita. Farin ciki ya kama Daddy, haka Gwaggo.
Ta ce, "Kaga ga Safara'u 'yar gidan Sani, bana ta gama sakandire, yarinyar na da nutsuwa, gata son kowa kin wanda ya rasa. Ka yiwa Kawun naka magana".
Dariya Daddy ya yi ya ce,
"Gwaggo, dan birni ai sai 'yar birni, 'yar kauye sai dan kauye. Mamarshi ta yi mishi mata tuni, diyar yayarta da ta ke riko, Hanifah.
Kinga ita a jami'a take, sannan ta san dukunkunannen halinsa za ta iya fin kowa hakurin zama da shi, tunda ta san halinsa. Gida daya suka tashi".
Gwaggo ta ce, "To Allah Ya tabbatar da alheri, kada a tsaya bata lokaci tunda dai an samu ya yi na'am".
Ya ce, "Haka ne Gwaggo, bari in kira Maimuna".
Ya yi waya ya kira Mama. Ta baro aikin wajen mai aikinta ta taho. Ta samu waje gefen Gwaggo ta zauna.
Nan Daddy ya ba ta daddadan albishir cewa Aliyu ya basu wuka da nama, su aura mai wadda suka ga ta dace, shi kuma ya zabi Hanifah.
Mama kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha don murna. Ta ce,
"Masha Allahu, abu ya yi dadi. Na ji dadi sosai, sai a aikawa mahaifinta can Darazo".
Haka suka ci gaba da tattaunawa. Su wane ne wadannan 'family' din ne?????????

****





ASALIN SU
Sun bullo daga Kumo, ta jihar Gombe. Malam Sama'ila malamin buzu ne, kuma daya daga cikin dattawan garin Kumo, wadanda ake ganin kima da mutuncin su, shine mahaifin Alhaji Surajo.
Duk da cewa ba halinsu daya ba, domin Surajo mutum ne mai wuyar sha'ani wasu lokutan, gashi da fada da rashin barin ko ta kwana. Duk da haka ya tsaya ya yi karatun addini sosai a wurin mahaifinsa kamin Allah ya dau ransa. Ya kuma ba shi babban jari ya ce ya je ya gwada duk irin kasuwancin da ya kwanta masa.
Surajo bai yi karatun boko ba, sanda ya shigo garin Gombe neman na kai Allah ya hada shi da wani Alh. Sule Mai-Taba, suka fara sana'ar sayar da taba.
Kanti guda gare su a babbar kasuwar Gombe suna sayar da taba nau'i-nau'i, kuma suna samu sosai, babu irin tabar da basa shigowa da ita Gombe daga Lagos.
Da abin yai gaba suka soma rarraba ta ga kananan 'yan kasuwar taba dake sauran garuruwa. Da suka yi karfi suka koma safarar ta da kansu daga kasar Amurka da Ingila.
Sanda Surajo ya fara karfi mahaifin shi Malam Sama'ila ya rasu, shi kadai ya haifa tare da mai dakinsa Gwaggo Hassana, duk haihuwar da ta yi bayan ta Surajo mutuwa suke tun basu shekara ba.
Shi kadai Allah ya bar mata, suka gaji abin da Malam Sama'ila ya mutu ya bari. Tangamemen gida da gonaki biyar, garken shanu da sauran dabbobin kiwo.
Surajo ya ci gaba da kula da gyatumarsa bayan rashin Malam Sama'ila, har zuwa lokacin da Allah ya hada shi da Maimuna.
Maimuna diya ce ga ubangidan shi Alhaji Sule, ta kammala karatunta na sakandire, Alh. Sule ya wanke ta ya ba shi auren ta. Mace mai ilimin addini da na boko kwarai da gaske, mai kyau matuka. A lokacin ya gama ginin katafaren gidanshi da yake gini a unguwar Shango Estate.
Shekaru biyu da auren su Maimuna ta haifi santalelen danta Aliyu Haydar, gata na duniya Aliyu ya gani a wurin iyayensa da kakanninsa; Gwaggo Hassana da Alh. Sulaiman.
Idan aka yi hutun makaranta wani lokacin yana Kumo wajen Gwaggo, wani lokacin yana wajen kakanninshi na wurin uwa. Sai dai kuma tun haihuwar Aliyu, Maimuna ta samu matsalar da dole aka juya mata mahaifa, haihuwa sai dai ta ji ana yi a makota.
Amma hakan bai sa Alh. Surajo ya taba tunanin kara aure ba, domin Maimuna jarumar mace ce, wadda ta sadaukar da kanta ga mijinta da danta.
Tana mishi biyayya da soyayya ta gaskiya kamar ta kwanta ya bi ta kanta.
Gwaggo Hassana ce ma ta taba dosar shi da zancen ya kara aure, ya ce,
"Na roke ki Gwaggo, kada ki kara wannan tunanin. Maimuna ta wuce in mata kishiya don in tara 'ya'ya, wanda Allah ya bani na gode, Allah ya albarkace shi".
Daga ranar ita ma Gwaggo Hassana ba ta kara tayar da zancen ba har inda yau ke motsi.

Hanifah, diyar Yayar Hajiya Maimuna ce wadda ke aure a garin Darazo, ta ba ta rikonta tun tana shekara biyar don ta dinga debe mata kewa, don Aliyu halinsa sai shi.
Kai shi magana ma wannan aiki ce ja a wurinsa. Baya furuci sai wanda ya zamo lazim, ba ya magana mara ma'ana ko mara muhimmanci.
Lokacin da Hanifa ta dawo gidan su yana da shekara goma sha biyar, aji biyar a sakandire. Ita kuma aji uku na firamare. Ba ruwan shi da ita harkar karatun shi kawai ya sa a gaba.
In ko ta sake ta shiga shirginsa yanzun nan za ta ci dan banzan duka. Don haka take dari-dari da shi, tun tana kankanuwa.
Aliyu ya yi dukkan karatunshi a jami'ar Maiduguri, kafin ya tafi zuwa 'Lancaster'. Sanda ya soma aiki da hukumar 'custom' ne suka hadu da Shareekah, diyar ubangidansa Controller Tajuddeen Olayemi.
Mahaifinta Bayarabe ne, mahaifiyarta mutuniyar Bendel, dukkansu Musulmi ne. Sun dade suna soyayya, sun aminta da juna, daliba ce a jami'ar Lagos mataki na uku.
Da abin yai nisa har iyayenta sun sani. Ba karamin jin dadin hakan Controller Tajuddeen ya yi ba, saboda yadda yake kaunar Aliyu kamar dan da ya tsuguna ya haifa, saboda hazakarsa da kyakkyawar zuciyarsa.
To amma kuma me? Bayan ya kai zancen gida Mama da Daddy duk da basu so ba, amma suna kaunar Controller Tajuddeen, saboda rawar kaunar da yake takawa a rayuwar dan nasu wajen ciyar da shi gaba kusan kowanne lokaci a kan aikinsa, ba za su iya cewa basa son hada jini da shi ba.
Aka kai kudin gaisuwa ga mahaifinta da tambaya kamar yadda yake a al'adar Hausa-Fulani, aka sa lokaci kowa cike da ganin girman dan uwansa.
Shareekah kyakkyawa ce, baka (black beauty), don sai an tona sosai cikin mata kafin a samu mai kalar fatarta. Kullum kanta cikin karin gashi yake, don haka ba za ka iya sanin tana da gashi ko ba ta da shi ba.
Ta ce da shi za ta yi tafiya zuwa Muzambikue an tura su "edcursion" kasancewarta dalibar 'geography' daga makaranta za suyi sati daya.
Tun dai da suka dawo Shareekah ba ta kara zama lafiya ba, ciwuwwuka iri-iri, haraswa, kasala, zubar da miyau da sauran alamomin mace mai juna biyu, ta kuma ki yadda kowa ya kaita asibiti har shi din kuwa.
Don ita a tunaninta sauyin waje ne kawai ya janyo mata. Ba ta ankara ba daga ita har iyayen sai ga ciki ya bayyana tororo wata shida, kowa yana gani.
Ashe ba wani 'edcursion', da uban ya rufe ta da duka kamar ya halaka ta kan sai ta fadi inda ta samo cikin, ba ta rufe ba ta ce,
"Michell ne (tsohon saurayin ta) suka fita hutawa kasar Johannesburgh ya yi mata fyade.
Tana kuka sosai tana rokar mahaifinta ya rufa mata asiri kada Aliyu ya ji, zai fasa auren ta, za ta je a zubar da cikin ko ta wanne hali.
Controller Tajuddeen har kuka ya yi, ya kuma kira Aliyu ita ma ya kira ta ya gaya mishi komai a gabanta.
Sannan ya kirgo kudin gaisuwa da na tambaya da iyayenshi suka kawo ya ba shi. Ya ce ya je Arewa ya nemi wata cikin kabilarsa. Ba zai aura mishi baragurbi ba.
Aliyu ya ce, "Ba zai karba ba, ya barwa Shareekah duniya da lahira".

Wannan ne dalilin da yasa Aliyu ya tsani 'ya'ya mata, ya alkawarta ma ranshi ba zai kuma son mace ba. Tunda su din mayaudara ne, maha'inta ne.
Duk soyayyar da Shareekah ke nuna mishi ashe a fuska ne kawai. Shin ya ake soyayya ta gaskiya? Ya ya take? Shin ma akwai ta ko babu? Does it really edist?

Wadannan sune tambayoyin da Aliyu-Haydar ke yiwa kanshi a kullum.
Ya tattara 'file' din mace da al'amarinta da ita soyayyar kanta ya aza a gefe, ya fuskanci al'amuran ci gaban rayuwarshi.
Muhimman abubuwan da ke gaban Aliyu-Haydar sune, aikinsa, kula da iyayen shi da gyatumar kakarshi Goggo Hassana.
Duk wata kankanba da giringidishin da Hanifah ke yi a kansa ya sani, bai taba daga ido ya dube ta da sunan so ba, share ta yake kamar bai san Allah ya yi ruwan tsirar ta ba.
Har kuma zuwa yau da ya yi furucin da ya zo ya dame shi, wato baiwa iyayenshi dama su aura mishi duk wacce suka ga dama, don ya ga farin cikinsu. Wanda ko kaffara ba zai yi ba, idan ya rantse cewa Hanifah za su zaba masa ba wata ba.
Ba zai iya dorar da komai a kan Hanifah ba, wato kyawun halinta ko akasin haka. Don ta tashi a gabansa, tunda ba sakar mata fuska yake ba balle ita ma ta saki jiki da shi.
Mama dai ta sha gaya masa cewa shi Hanifah take so, tun abin yana ba shi haushi har ya koma ba shi mamaki. Allah ya kawo mu wani zamani da wai mace ce za ta budi baki ta ce tana son namiji, a ganinsa karshen wulakantar da kai kenan ga 'ya mace.
Duk feleken da ta ke masa dai na nuna 'caring' ba ta taba tarar shi fuska da fuska ta ce 'ina sonka ba'. Sai dai ya ji a bakin Mama. Wannan ne ya bar mata dan guntun mutunci a idanunsa.
A wannan daren dai Aliyu barcin shi gashi nan ne, rabi da rabi. Bai ankara ba ya ji kiran asubahi a kunnuwan sa. Ko masallaci bai iya ya je ba, yana ta tunane-tunane kan subutar bakinsa, ya ba da farali ya koma ya kwanta, sannan ne ya samu barci mai dadi ya yi awon gaba da shi.
****




WASHEGARI
A makare Aliyu ya tashi misalin karfe tara na safe, shaf ya manta zai kai Gwaggo asibiti. A gurguje ya yi wanka ya kintsa cikin shirt da wando samfurin ARMANI, ya fesa turare ya yi cikin gida a gurguje.
Bai tadda kowa a falo ba sai Mama tana waya, ga dukkan alama da Hanifah take wayar, don yana jin yadda Mama ke lallashinta wai ta baro gidan bikin haka nan ga Yayanta a gida kuma akwai albishir.
Wani haushi ya kama shi, ya yi gaba dakin Gwaggo. Ya taddata ta kintsa shi take jira, ya zauna a gefenta kamar yadda ya saba. Ta dora hannu a kan kafadun shi ganin yana ta huci shi kadai.
Ta ce, "Wa ya tabo min Zakin Manzo? A'ah, saki ranka, wannan fushin bai yi maka kyau ba".
Ya ce, "Tashi muje Gwaggo, I got lot to do...."
Daddy ya shigo shima cikin shirin fita, ya zube ya gaida Gwaggo ta amsa fuskarta a sake. Ta ce, "Zamu wuce asibitin".
Ya ce, "To, sai kun dawo, a yiwa likita bayani sosai, ku je General Hospital can ne 'file' din ta yake".
Ya kai duban shi ga Aliyu ya ga yana ta huci amma bai fasa gaida Daddyn ba. Ya ce, "Gwaggo ya ya ne ke da angon naki? Wa ya tabo miki shi?"
Ta ce, "Haka nan nima na ganshi".
Da yake Daddy lallabashi yake kada ya botsare ya ce ya fasa auren, sai ya dube shi da murmushin lallashi, yana son ya ji damuwar shi.
Aliyu ya mike ba tare da ya ce komi ba, ya doshi kofa, ya ce, "Gara mu tafi Gwaggo rana tana yi".
Ta yafa mayafinta ta mike da kyar, Daddy ya yi saurin riko hannunta har jikin mota. Aliyu ya bude mata kofa ta shiga baya ya rufe, ya zaga ya shiga mazaunin direba suka fita a harabar gidan.
Shima Daddy tasa motar ya shiga ya nufi inda za shi. Gidan ya rage daga Mama sai mai aikinta Asabe.
Bayan sun fito daga asibitin gudu sosai Aliyu ke yi a kan titi, Gwaggo ta soma fada, ita fa idan ba zai daina gudu ba to ya sauke ta ya sa ta a Keke-Napep.
Bai daina gudun ba, kuma bai ce komi ba. Wannan halin shiru din na Aliyu na matukar ba ta haushi, yana ji kana magana amma ya yi kamar bai san kana yi ba.
Tsautsayi....wanda an ce...ba ya wuce ranarsa!. Wata yarinya ce ta tsallako da gudu da kwanon bara a hannunta, ta baro uwarta da takewa jagora a daya titin. Duk kokarinsa na kauce mata, da kwarewar sa wurin sarrafa sitiyari sai da ya kwashe ta ya watsar a gefe.
Gwaggo ta yi salati ta sanar da Ubangiji, ta ce, "Ka gani ko?
Ka ga abin da nake gaya maka amma ka yi kunnen uwar shegu dani. Maza samu wuri ka tsaya".
Ya yi parking a gefen titi, shi kansa zuciyarsa ta tsinke da ganin yarinyar jina-jina kwance a gefen titi, har mutane sun rufe ta.
Ya fito shima ya keta jama'a ya isa gare ta. Wani daga cikin mutanen dake wajen ya hau sirfa masa zagi yana cewa,
"Ku masu kudin nan kun mai da jinin talaka kamar na kiyashi, ku sanya hancin mota ku buge wanda kuka ga dama saboda takamar za ku saya mishi magani. To Allah Ya isa....!"

Aliyu ya daga kai ya dube shi, bai ce da shi komi ba. Ya dauki yarinyar ya sanya a bayan mota. Wani tausayi ya kama shi ganin yadda kanta ya fashe jini na zuba, ga alamar karaya a kafafunta da ke reto.
Ba tare da hankalinshi ya kai ga mahaifiyarta ba, wadda ke tsaye har zuwa lokacin a daya titin tana jiran diyar tata, ba tare da ta san abin da ya faru ba.
A guje ya ja motar ya nufi wani pribate hospital da ita. Don ya san na gwamnati ba za su karbe ta ba har sai sun bata lokacin neman 'report' din 'yan sanda da sauran su. Likitoci uku ne suka rufu a kanta suna kokarin ceto numfashinta.
Aliyu da Gwaggo suna zaune a harabar asibitin, kan wasu kujerun siminti. Kar ka so ka tona fargabar dake zuciyoyinsu. Idan yarinyar ta rasu a dalilin su yaya za su yi?
Gwaggo ta ci gaba da yi mishi fada a kan gudu da mota kamar ta ari baki, amma bai tanka mata ba. Don ya fita shiga damuwa.
Awanni uku cur suna zaune sannan likitocin suka fito, aka turota a keken tura marasa lafiya zuwa dakin aminity wanda Aliyu ya biya.
Likitan ya kira shi ofishinsa, ya yin da Gwaggo ta shiga dakin da aka kwantar da yarinyar tana ta hirji cikin ranta. Haka kawai tsautsayi ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login