Showing 48001 words to 51000 words out of 63435 words
gayyaci Aliyu, shi kuma ya tattaro su Muhaseen da su Mama duk suka yi shiri suka shiga motar Dr. Bello suka taho gidansa.
Muhaseen sanye take da bakar abaya mai kauri da mayafinta siriri. Baka ganin komai sai shatin kyakkyawar fuskarta da tafukan hannayenta wadanda ta kawata da zobban farin zinare guda uku, da kuma zanen jan lallen 'Rani' akan yatsun hannunta zara-zara, ban da haka hatta kafarta cikin bakin cober shoe take maras tsayin dunduniya.
Ya yin da Hanifa natibe dressing dinmu ta yi, wato atamfa super ruwan hoda da mayafi kalar kwalliyar atamfar.
Aliyu manyan kaya ne a jikinshi, farar shadda har da babbar riga. Su Mama ma duk atamfa ce a jikinsu da ganinsu dai ka ga cikakkun 'yan Nijeriya. Ban da Muhaseen, wadda ta saje da Larabawan Jeddah.
Dr. Bello ya danna kararrawa Dr. Saudah ta bude, matashiya kyakkyawa da ba ta fi shekaru talatin ba, amma cikakkiyar likitar fida ce 'yar asalin garin Maiduguri daga kabilar Shuwa.
Bakinta cike da far'a ta bisu da runguma daya bayan daya. Ta kama hannun kawarta Hanifah ta kuma rungumo kafadar Muhaseen suka isa kayataccen falonta.
Hira sosai ake yi a falon tsakanin Dr. Bello da Engr. Aliyu. Dr. Saudah da Hanifah da su Mama.
Ita dai Muhaseen tunda suka shigo falon gabanta yake faduwa, ta daga kai tana kallon tangamemen hoton dake arewa maso kudu na dakin. Dr. Bello ne da Dr. Saudah rungume da wata mace mai tsananin kama da Ummanta.
A lokacin da Dr. Saudah ta shimfida ledar cin abinci, ita da mai aikinta suka shiga jera abinci nau'i-nau'i cikin 'yan kananan tangaraye.
Muhaseen mikewa ta yi ta isa ga wannan hoton, ta kai hannunta tana shafa shi a hankali, wannan idan ba Ummanta ba ce, to kuwa kanwarta ce.
Ba tare da Dr. Saudah ta lura da halin da take ciki ba ta ce da ita,
"Kina kallon 'family picture' dinmu ne? Wannan Yayar Doctor ce Aunty Halimah, tana aure a makotanmu garin Abha....."
Sai ta durkushe a nan ta rushe da kuka, cewa take, "Ummata ce, wallahi Ummata ce......" Sai ta zube a wajen ta sume.
Likitocin gaba daya suka tsallake abincin suka yo kanta da gudu. Dr. Saudah na shafa mata ruwa a fuska. Shi kuwa Aliyu ciccibarta ya yi ya dora a kan cinyoyinsa yana kiran sunanta. Ta yi doguwar ajiyar zuciya ta bude idanunta tana kallon su.
Sai ta fashe da kuka ta rungume Dr. Bello tana cewa, "Kai ne Bello kanin Ummana?"
Ya ce, "Ni ne Muhaseen, ki yiwa Allah godiya, kin zo gida!".
Kowa ya cika da al'ajabi da mamaki, kudurar Ubangiji ta wuce haka. KUN FA-YA-KUN ne fa, wanda in ya ce "kasance" sai ya "kasance".
Dr. Bello rike yake tsam da Muhaseen kamar mai jin tsoron kada wani iftila'i ya ratsa ya raba su.
Wannan abinci kowa kasa cin shi ya yi, jikin Hanifah ya kara yin sanyi sosai. Mama da Dr. Bello ke magana yana ba ta labarin irin neman Muhaseen da suka rika yi lokacin da Allah ya hada shi da 'yar'uwarsa a Gombe ya zo ganin wani likita abokinsa a babban asibitin garin Gombe.
Ya ce,
"Ganinta na yi a gefen titi tana ta kuka, ga idanunta a bude amma ba ta ganni ba. Sai da na kama ta na tura ta a mota na ce da ita, kwantar da hankalinki nine dan uwanki Bello Allah Ya hada mu".
Sai muka rungume juna muna ta kuka, musamman da ta bani labarin rasuwar mahaifinmu da Innarmu Baddo. Na gaya mata dalilina na rashin dawowa Dukku bana kasar ne ina KL (Kuala-Lampur) ina karatun likitancin ido har tsayin shekaru bakwai.
Malamin da mahaifinmu ya kaini hannunsa a Maiduguri babban malami ne sosai, yana samun alfarmomi daga gwamnatin garin Maiduguri, sabida tarin ilminsa da yadda ake girmamashi.
Gwamnan Borno mai ci a lokacin ya ba da (form) din mutum goma ga Malam Goni ya rabawa almajiransa guda goma, gurbi ne na yin karatun likitanci a Kuala-Lampur.
Nine mutum na farko da malam ya sanya sunana. Domin mahaifina tunda ya kawo ni bai kara zuwa ba. A lokacin ni kuma bani da wayon da zan kawo kaina Dukku tun daga Maiduguri.
Shekaru biyar muka kwashe muna karatu muka zo gida hutu. Malam bai barni na koma ba sai da auren diyarshi Saudah gata nan. Muka taho tare ita ma ta fara karatu a can da yake ta samu (scholarship) itama.
Ban dawo Maiduguri ba sai da na zama cikakken likitan ido. Na tura takarduna neman aiki ta yanar gizo a asibitoci daban-daban. Ciki harda nan Saudi-German.
Ita Saudah ba ta kare nata karatun ba, don haka can na barota lokacin da (Saudi-German) suka kirani interview, ba da dadewa ba na fara aiki tare da su.
Na zo Nigeria ne ta'aziyyar Babanmu Malam Goni, wanda Allah Ya karba bayan gajeruwar rashin lafiya. Na wuce Gombe wajen wani abokin karatuna Dr. Ahmad Rasheed, inda Allah ya yi haduwa ta da ita a gefen titi a makance,.
Dama zuwan nan da na yi wajen Dr. Rasheed Dukku zai rakani in je gare ta da mahaifina, sai take gaya min rasuwar babanmu tuntuni, tun ranar da ya kawoni.
Ta kuma gaya min labarin aurenta da dan Turaki, da abin da ya yi mata, da batan diyarta Muhaseen.
Mun yi yawon ofisoshin 'yan sanda na Gombe har ba adadi da gidan marayu amma bamu samu Muhaseen ba. Dole muka hakura na yi mata bisa ta residence permit muka taho Jeddah.
Wata guda na share ina binciken matsalar idanun Yaya Halimah, cikin kwamfuta da sauran kayan aikinmu, kwayar idonta ba ta fashe ba, wasu jijiyoyi ne suka tsittsinke, jini kuma ya taru ya kwanta a karkashin idanunta.
Umrah na yi musamman a kan al'amarin ni da Saudah, na yi dawafi ina rokon Allah ya bani nasara a kan aikin da zan mata.
Da hankali ya nutsa muka yi mata aikin ni da sauran manyan likitocin ido na Saudi-German. Cikin ikon Allah, Allah Ya bamu nasara muka shawo kan matsalar.
A yanzu zancen nan da nake muku Yaya Halimah ta yi aure a garin 'Abha' (probince of Asir) da wani babban dan kasuwar Najeriya da Saudiyyah. Suna zaune a Abha, ta Saudi-Arabia. Yaransu uku duk maza, Abubakar, Usman da Aliyu. Suna zuwa Umrah duk karshen wata, kuma suna zuwa nan Jeddah duk sanda suka zo, muma muna zuwa akai-akai. To kun ji".
Ya sake kama hannun Muhaseen ya rike sosai cikin nashi ya ce,
" 'Ya ta Muhaseen mu godewa Allah, da ya hadamu ya takaita wahala, gobe insha Allahu za ki ga Ummanki".
Ta sake kwanciya sosai a jikinshi tana kuka da dariya gaba daya....har da majina take sharewa, wadda ta hadu ta jike da hawayen; idon Umma ya bude....za ta ga Ummanta....har kanne an mata....me za ta ce da Ubangijinta ban da ta yi maSa sujjadah?
Don haka ta kai gwiwoyinta kasa ta yiwa Allah sujjadar. Tace (sajadat wajhy lillazee fadaras-samawati wal ardhi hanifan wa ma kana minal mushrikeen).
****
[9/4, 12:59 PM] Asmau: Dukkansu nan gidan Dr. Bello suka kwana, basu koma masaukinsu ba. Aliyu ne ya koma ya debo musu kayansu, shima a nan dakin bakin Dr. Bello ya kwana.
Duk wadda ya kira cikin matan nasa sai ta kashe waya, ita Muhaseen sabida kunyar Mama, ita kuwa Hanifah ta lafiyar jikinta take, ya yi kwafa ya ce, "Da ni kuka yi".
Yau kam Muhaseen ko rintsawa ba ta yi ba, kwana ta yi sallah tana godewa Ubangijinta. Sai ta ga daren ma kamar yayi tsaho gari ya ki wayewa. Da suka yi kalaci ne Mama ma ta baiwa Dr. Bello labarin rayuwar Muhaseen tare dasu, da yadda a kai ta zo hannun su, karatunta da ganin mahaifinta, da kuma yadda aurenta da Aliyu ya kasance.
Dr. Bello ya ji dadin rayuwar da Muhaseen ta yi tare dasu, musamman tushen ingantaccen ilmin da suka dora ta akai.Ya yi ta yiwa Mama godiya. A ranar ya nema musu (entry bisa) suka tafi garin Abha cikin babbar motar 'Golf' din Dr. Bello.
Umma Halimah, tana kwance a falonta tana kallon tashar Al-jazeera, da yake ranar makaranta ce su Abubakar duk suna makaranta.
Alh. Idris ya je Riyadh kan harkokinsa ta ji ana danna mata kararrawa. Sannan kiran Dr. Bello ya shigo, ta daga ya ce da ita suna kofar gidan ta.
Da matashiyar budurwar ta fara tozali, mai tsananin kama da Umaru, wanda kamanninsa ba za su taba bace mata ba.
Wani irin feeling ne take ji a kan yarinyar, yana sauka a zuciyar ta, duk da cewa bata taba ganinta ba. Ta kasa dauke ido a kanta, sannan ba ta bata hanya ta wuce ciki ba. Muhaseen ta rungume ta tana cewa,
"Umma! Umma nah!"
Muryar 'yar diyarta Muhaseen, wadda ta bace mata tun tana da shekaru goma, ko mutuwa ta yi ta dawo ba za ta mance muryar Muhaseen din ta ba. Suka rungume juna suka rikice da kuka.
Dr. Bello ne ya yi musu jagora suka shiga falon. Muhaseen ta kasa sakin Ummanta, tana kallon irin daular da Ummanta ke ciki abin kamar a mafarki.
Babu wanda cikin su bai share hawaye ba saboda tausayin Halima da diyarta. Sai da suka gama koke-koken su sannan ta soma entertaining bakinta, tana yi musu sannu da zuwa.
A take tai kiran maigidanta ta ce ya zo ya tayata murna, yau ga 'yarta Muhaseen Allah Ya bayyana ta.
Kan ka ce meye wannan Hajiya Halima ta cika gabansu da cima iri-iri karshen kwadayinka. Ita da masu yi mata hidima.
Ba ita kadai ce matar Alh. Idris ba, akwai uwargida a gida Najeriya. Yaranta su Abubakar suka dawo makaranta suna ta yi musu kallon bakunta.
Usman ya tafi da gudu jikin Dr. Saudah yana cewa, "Aunty Dr. baki zo da su Miftahul-khair ba?".
Ta shafa kansa tace, "Suna makaranta shi yasa, sai anyi hutu zan kawo muku su, in sha Allahu`".
Ta yi musu nuni da Muhaseen wadda ke ta kallon kyawawan yaran tana murmushi ta ce, "Ga Auntyn ku Muhaseen, yau Allah Ya kawo mana ita!".
Duk suka juyo suna kallon ta. Abubakar ya ce, "Ke ce Yaya Muhaseen da kullum Mama take bamu labari?"
Ta jawo shi ta jingina da jikinta ta ce, "Eh, Abubakar Saddik, nice Yaya Muhaseen".
Sai Usman ma ya taho gare ta, Aliyu sai zare ido yake, duk ta hada su ta rungume su hawayen kauna da farin ciki na ziraro mata.
Aliyu da Dr. Bello fita suka yi don Aliyu ya ga gari, bayan sunyi sallah sun ci abinci, sune har da wucewa Da'if da Tabuk, don sai dare sosai suka dawo.
Lokacin su Mama sun dade da yin barci, sai Muhaseen da Ummanta wadanda suka raba dare suna bawa juna labarin rayuwarsu.
Yadda Dr. Bello ya basu labari haka Ummanta ta maimaita mata. Ita ma ta ba ta labarin rayuwarta a gidan su Aliyu bayan ya kade ta da mota, da yadda ya taimaka wajen inganta rayuwarta positibely. Karatun da ta yi, haduwarta da Baba Umaru, da yadda aurensu ya kasance, har zuwa yadda suka hadu da Dr. Bello da matarshi Dr. Saudah.
Ta ci gaba da ba ta labarin Dr. Omar, ta sanar da ita ya yi nadama sosai, in kin ganshi yanzu Umma dole ya baki tausayi, duk da mukaminsa, da matakan girman da ya hau a rayuwarshi. Yet, he's incomplete, ba Da, ba jika Ummah.
Ta kare da cewa, "Umma ki yafewa Dr. Omar don son Annabi da godiyarmu ga Ubangijin da Ya hada mu, ya kyautata rayuwarmu. Ta hanyoyin da bamu taba zato ba.
Ko wannan kadai aka duba sakayya ce bayyananniya Allah Ya yi mana, tunda shi yanzu bashi da da ba jika sai ni din da ya sheganta, nice din dai kuma ba shi da abin son da ya wuce ni.
Umma ki yi duba ga irin rayuwar da kike ciki da 'ya'yan da Allah Ya baki, da miji da idanu, ki yafe masa!!!".
Murmushi ta yi, "Na taba ce dake na kullaci Babanki? Dai-dai da rana daya ban taba kullatarsa ba. Na yafe mishi duniya da lahira, Allah Ya yafe mana baki daya".
Muhaseen ta fada jikinta, kai ka ce yarinya ce 'yar karama. Umman na kara rungumeta. Ta yi murmushi ta ce, "Mijinki kyakkyawa da shi, har ya fi ki kyau, dan gaye, mai kirki.".
Ta ji kunya sosai ta sunne kanta a kafadunta. Ta ce, "Umma Yayana ne fa?"
Ta ce, "Kuma 'darling' ko?'
Suka kyalkyale da dariya gabadayansu.
Ta ce,
"Ga kishiya mai hankali Allah Ya hadaki da ita, ko ido ba ta iya budewa ta kalli mutane sosai".
Ta ce, "Tabdi! Aunty Hanifan? Lallai baki santa ba. Yanzu ne da ta ga ta kusan mutuwa ta shiga makarantar ta-nutsu".
Ummanta ta sake yin dariya ta ce, "Baki da dama Muhaseen, har yanzu bakin yana nan cau, kamar mazarkwaila".
Ta ce, "Umma in baka bude baki kana magana sai a raina ka".
Haka suka yi ta shan hira suna dariya abinsu. Kamar wasu kawayen juna.
Washegari Alh. Idris tun basu tashi ba ya iso. Ai kuwa su Aliyu sun ga tarbar girma kamar a hadiye su. Godiya suke ta yi har babu bakin yinta.
Mama ta ce don Allah su daina, ita Muhaseen diyarta ce ko da Aliyu bai aure ta ba, Allah ne ya hadasu, ba mutum ba.
Washegari dukkansu suka nufi Makkah da niyyar aikin Hajji, don an fara sauke Alhazai. Shi dai Aliyu ya zubawa Hanifah da Muhaseen ido, tunda duk sunyi mishi kaura, kowacce ta likewa uwarta, musamman Muhaseen wadda ba ta da koshin lafiya.
Wani irin ciki Allah Ya hadata da shi mai gudun kusantar da namiji, don haka duk wata hanya da ta san za ta sadata da angon nata gudunta take.
Ta kashe waya ta boye, tsakaninsu sai in an hadu wajen cin abinci, shima din tana toshe da hanci ba ta son kamshin 'American Crew' da ya kama jikinsa, ko bai fesa ba..
Ita kuma Hanifah gani take ba ta gama murmurewa ba. Mama ke kula da Muhaseen, Dr. Saudah na kula da Hanifah.
Daga Mama har Innani babu wacce ta yi tunanin kawaicin da Aliyu ke yi. Fisabilillahi a takure yake matukar takura kuwa. Don haka ya yi kaura ya koma Hotel shi kadai ya bar musu gidan da suka sauka. Duk kasar ta gundire shi. Ya yiwa Daddy waya ya sanar da shi duk halin da suke ciki da bayyanar Hajiya Halima.
Daddy ya ji dadi sosai duk da yana Italy, har magana ya yi da Dr. Bello yana ta yi mishi godiya.
Daddy ya ce, "Babu komai Muhaseen diyarsa ce, domin shi amini ne tun na kuruciya da mahaifinta, balle kuma yanzu da ta zama diyarsa baki daya".
A take shi kuma ya fesawa Dr. Omar, ya gigice ya kidime, amma da ya tuna saki uku yai mata sai murnarsa ta koma ciki. Gashi Daddy ya ce ta yi auren ta har da albarkar 'ya'ya.
Kuka ya rinka yi, kukan nadama.......wadda AL-AMEEN BELLO MAKARFI ya kira NADAMA MARA AMFANI (Duba Siradin Rayuwa).
Gaba daya suka tattaro suka taho gida Najeriya bayan kammala aikin Hajji. Innani an sako dallelen hakorin Makkah.
A Abuja jirgi ya sauke su suka kwana gidan Badi'a kamar ta goya Muhaseen, sun sha hirar yaushe gamo.
Washegari suka kamo hanya aka sauke Innani da tsarabobinta rankata-kaf a Darazo. Daga nan suka shiga Dukku.
Gidansu ya rushe ya zama kango. Umma Halima dai gidan Malam Tanko ta sauka dakin Ta-Birni ita da 'ya'yanta. Alh. Idris yana tare da Dr. Bello a gidan saukar bakin da suka kama. Su Muhaseen suka wuce (family house) dinsu wato gidan Turaki.
Turaki ya tura su Hajiya Dijah gidan Malam Tanko lallai a zo mishi da Halima. Ya kuma kira Dr. Omar ya ce lallai ya baro duk abin da yake yi ya zo.
Yau sai ga Dr. Omar da Halimar da ta firgita shi, rantsewa za ka yi Muhaseen kanwar ta ce ba diyar da ta haifa ba.
Turaki ya yiwa Halima fada sosai a kan abin da ta yi, yana raye, ta tsallake shi ta jefa kanta a uku.
Ya ce, "Na dauka za ki dauke ni uba Halima kamar yadda Sajoh ya dauke ni? Ko me Umaru yai miki na dauka nine mutum na farko da za ki nema? Tunda ni na kulla auren ku?
Kin yi wauta Halima, nan gaba kar ki sake maimaita irin ta. Allah ya albarkaci 'yarku, ki yi hakuri ki yafe masa".
Ta ce, "Babu komai, ni tuni na yafe masa".
Ya ce, "Me zai hana ki koma dakin ki Halimah?"
Ta yi wani murmushi na jin nauyi, ta ce, "Aure nake har da yara uku a kasa, tare muke da maigidanama".
Sai jikin Turaki ya yi sanyi. Shi Dr. Omar dama tuni ya sani. Ya yi musu addu'a, ya kuma ce a kawo yaranta ya gansu.
Ya dinga shafa kan su Abubakar yana cewa, "Masha Allah, 'yan samari masu babbar riga".
Ya kawo alheri mai yawa ya basu ya kuma ce da Halimah har gobe shi Babanta ne, duk wata matsala da take da ita ta neme shi, kada ta yi la'akari da wai ba ta auren dansa, tsakanin shi da Malam Sajoh ya wuce haka.
Ta yi godiya ta mike yana ci gaba da sanya mata albarka.
Ya mai da hankalinsa ga Dr. Omar wanda ke sunkuye da kai a gabansa ya ce, "Wata daya na baka ka samo mace 'yar mutunci ka aura, wannan zaman naka haka ya isheni. Tashi ka bani waje tun baka ga fushina ba".
Ya mike jikinshi babu kwari ya fita. Wa zai aura? Duk wani tanadin rayuwarshi na yanzu, ya yi shi da Halimahh ne, zai iya kare sauran rayuwarsa a haka, tunda ya rasa Halima.......!
** **
Kwanan su uku a Dukku suka tattaro suka taho Gombe. Alh. Idris ya wuce wajen iyalinsa a Maiduguri ya bar Umma tare dasu, shi kuma Dr. Bello yasa aka rushe gidansu aka fara yi masa ginin zamani don su rika sauka idan sun zo.
Ya kuma yiwa Ta-Birni da Malam Tanko alkawarin kujerar Hajji idan Allah Ya kaimu shekara mai zuwa.
Shi da Dr. Saudah hotel suka kama a Gombe. Mama ta sauki Umma Halima a dakin Muhaseen na da, sauka ta alfarma.
Asabe ta rungume Muhaseen tana tayata murnar ganin Umman ta. Umma ta kori amaryar da uwargidan da suka like mata ta ce, "Suje su yiwa mijinsu tausar gajiyar hanya".
.
Shi ko inda suke bai kalla ba, shiri ma yake gobe zai wuce Porthercourt ya nemi ta uku a can ya aura, tunda ya lura duk sun daina son shi. Kamar a kansu aka fara ciwo a duniya.
Mama