Showing 51001 words to 54000 words out of 63435 words
ce ta raka su har cikin gidansu tare da Asabe don ta gyara musu. Muhaseen tana ta kumbure-kumbure, ita wallahi ba ta son turaren Yaya Aliyu, tashin zuciya da kwannafi yake sa ta.
Mama ta ce, "An ji".
Hanifah ta ce, "Zan kwashe duk turarukan in boye, tunda ya ce ba zai daina fesawa ba, ga turaren ya riga ya kama komi nashi".
Bai shigo gidan ba sai karfe sha daya na dare. Hanifah ce a falo cikin kayan barci tana nazarin takardunta. Kallo daya ya yi mata ya dauke kai ya wuce dakinsa yana rike da falmaran din Spanish-suit din dake jikinshi bakake.
Tuni Muhaseen ta yi barci, yana kokarin rufe kofa ta rike murfin kofar tana murmushi ta ce, "We are sorry...!"
Sai kuma ta rungume shi tana kissing dinsa passionately, abin da Muhaseen ba ta iyawa.
Tun yana daurewa, yana ciccijewa har ya bada kai bori ya hau. Ba don komi ba sai don tsabar matsuwar da yake ciki ta lokaci mai tsawo. Don haka ya saki, ya rage zafi da ita, amma gamsuwar shi a auratayya na ga MUHASEEN, mace daya tamkar dubu, mai tattare da wasu sirrikan da daga shi sai Ubangijinsa suka sani.
Amma haka ya yi hakuri, ya jure. Tun kan ta bude kofa ya tsufa a Airport shi da Hanifah, saboda yana so ya nuna mata fushinsa.
Da ta yi sallar asubah, ko lazimin da ta saba yi yau ba ta yi ba saboda gajiya. A nan kan sallayar barci mai dadi ya yi awon gaba da ita. Ba ta farka ba sai karfe goma na safe.
Ta yi wanka ta shirya ta fito, falon wayam! Dakunan jama'ar gidan a kulle, sai kayan karin kumallo a kan tebir. Ba ta tsaya ba ta nufi sassan Mama watakila ko suna can.
Mama ce kadai a falon tana waya, tana zaune cikin kujerun falonta. Ta zauna a kusa da ita tana raba ido. Mama ta kashe wayar ta dube ta da murmushi ta ce.
"Sai yanzu?"
Ta ce, "Tun fa dazu na tashi Mama na tsaya wanka da shiryawa ne".
Mama ta ce, "Break fast fa?"
Ta ce, "Bar ni kawai Mama, yau (mandako) nake son ci".
Yadda ta yi maganar tsakaninta da Allah ya bala'in baiwa Mama dariya. Ta yi dariyarta ta more ta ce.
"Mandako Muhaseen?"
Daidai lokacin da Ummanta ta fito daga daki da Aliyu a hannunta yana rigima. Muhaseen ta karbe shi tana rarrashinsa:
"Yi shiru mai sunan Yayana,...... duk mai suna Haydar baya kuka, jarumi ne cikin kowanne hali....."
Mama ta ce, "Zo ki tayani dariya Hajiya Halimah, yau masu ciki mandako suke son ci".
Umma ta yi murmushi ta ce, "Lallai aiki ya same ku".
Mama ta mike tana cewa, "Kwarai kuwa, bari in taso Asabe ta tafi kasuwa siyen rogo da kuli-kuli".
Ta dubi Ummanta ta ce, "Umma haihuwa da wahala?'
Ta ce, "Ba wani wahala kina barci ma za ki tashi ki ga abinki kusa dake".
Muhaseen ta yi dariya, "Uhm-uhm! Umma kada ki zurmani da wayo na".
Ta ce, "Kin san hakan kika tambaye ni? To neman baki ne ko me?"
Mama ta dawo Asabe na bayanta. Asabe ta ce, "Kada ki damu uwar dakina, yanzun nan mandako zai kammalu, bari ki gani. Mama kawo kudi".
Mama ta zaro gudar N500 a jakarta ta ba ta, da saurinta ta tafi.
Umma ta yi dariya ta ce, "Mama da Asabe masu daurewa karya gindi, in ban da haka duk abincin da ke tebirin nan babu wanda mai ciki za ta iya ci sai an tashi takanas an je kasuwa?"
Mama ta ce, "To meye abin wahala a nan? Kowanne ciki da irin laulayin sa, wallahi in ma garin za a bari a nemo mandako, yau sai an nemo shi".
Muhaseen ta yi dariya ta yiwa Umman gwalo a keyar ta, ta ce, "Mama yau Aunty Hanifah sammako ta yi ne? Shima da na tashi ban ganshi ba".
Ta dube ta cikin mamaki ta ce, "Bai gaya miki yau zai koma Warri ba tare da Hanifah?"
Wuta ta daukewa Muhaseen, wani kululun bakin ciki ya taso ya tokare a wuyanta. Kishi na bala'i ya turnike ta.
Mama da Umma suka zuba mata ido ganin yadda yanayinta ya sauya lokaci daya, kawai sai ta mike ta yi dakin Mama ta kwanta rub da ciki tana kokarin hadiye kishinta ko don albarkacin Mama kada ta ce tana kishi da Hanifah.
Mama da Umma suka bita da kallo,. Mama ta ce, "Yanzu haka tana barci suka tafi, bai yi mata sallama ba, kadan da halinsa, in dai shi ne".
Umma ta ce, "Can ta matse musu".
Ta dauki danta tana makala mishi pampers. Mama ta yi niyyar bin Muhaseen daki ta tambaye ta basu yi mata sallama bane? Sai kuma ta fasa ta shige kicin tana cewa a ranta tunda baki gaya min ba bari in kyale ki.
Ba ta fito ba sai da cikinta ya soma kiran mandako, ta fito dakin Mama tana mika sannan ta nufi kichin, nan ta tadda Asabe tana dunkula mata mandako.
Ta yatsina fuska ta ce, "Kin yanka albasa a ciki?'
Ta ce, "A'ah".
Ta ce, "To marmasa shi ki yanka albasa a ciki kadan sannan ki dunkula".
Asabe ta ce, "To ranki ya dade".
Mama na jinsu tana dariya.
[9/4, 12:59 PM] Asmau: Tasa mandakon ta a gaba da gwangwanin (Mountain Dew) a gefe tana ci kamar Allah Ya aiko ta. Nan da nan ta tashi dashi duk yawansa fal katon plate. Ta kora lemonta ta mike ta nufi sassan su, ta debo 'yan kayan amfaninta ta koma sassan Mama,ta ce ita ba za ta iya kwana ita kadai a can ba, za ta taya su Abubakar kwana.
Umma ta ce, "Ba ta yarda ba, ta tafi dakin mijinta ta kwanta, ba ta san ladan dake cikin hakan ba".
Ta marairaice fuska ta ce, "To Umma don Allah yau daya dai ki zo muje dakina ki tayani kwana, daga yau ba zan kara ganinku ba sai an dade, don Allah Umma...."
Ta kama baki, "Yau ni Halima na ji abin da ya fi karfina, in tafi dakin mijinki in kwana Muhaseen? Ina kika taba jin wata uwar kirki ta yi haka?
Ga Abubakar nan da Usman ki tafi dasu ki bar mani Aliyun saboda yana rigima cikin dare".
Mama ta sako baki, "Ke kuwa Umma don Allah ki je ki tayatan, in kunya ce babu mai ji daga ni sai ku, ki yiwa Allah ki taya ta, in kun tafi gobe za ta dade bata ganku ba, don sai Allah ya sauke ta lafiya zamu zo".
Dadi ya kama Muhaseen ta rungume Mama, "Yauwa Mama tayani rokonta ko Asabe ba za ta san kina can ba".
Suka sanyata a tsakiya da naci da magiya dole suka samo lagonta, ta shiga daki ta dauki abin da take bukata, Muhaseen ta dauki Aliyu ta kama hannun Abubakar da Usman suka tafi, murna kamar ta kashe ta.
Wannan ne ya sanya ta manta da bacin ran abin da Yaya Aliyu ya yi mata. Domin kwana suka yi hira da Ummanta.
Ta daga ido tana kallon irin daular da Mama ta shirya a wannan daki, sai rabar A.C ke tashi da sassanyan kamshin turaren wutar 'touch-me' dake hayaki a hankali cikin 'burner'.
Ta rasa wace irin godiya za ta yiwa wadannan kariman mutane. Wai yau ita ce da Muhaseen dinta cikin wannan rayuwar da ko a mafarki basu taba hasaso irin ta ba. (To ina ruwan Allah? Yarzuku man yasha'u bi gairi hisabin).
Duk yadda Muhaseen ta yi Umma ta hau gadonta ta kwanta Umma ta ki, blanket mai laushi ta shimfida ta dora filo. Muhaseen na kwance rigingine gefen gadonta tana fuskantar ta suna hira, su Abubakar duk shimfida ta yi musu a kasa, a cewar ta ba a hawa gadon mace mai aure, babu kyau.
Ta ce, "Bana so in bar garin nan ban je Billiri na gaida Hajiya Ta-fisu da Maigari ba, gashi gobe zamu tafi in Allah ya kaimu".
Muhaseen ta ce, "Ai Billiri ba nisa har da ni za'a je, zamu iya zuwa da safe mu dawo da azahar, tunda jirgin ku sai biyar na yamma zai tashi. Nima ina so in ga Hajiya Ta-fisu wadda ta yi miki jego na".
Umma ta ce, "Idan kin tambayi mijinki ko?"
Ta ce, "Mama ba za ta hanani zuwa ba, ni ba zan masa waya ba....." Sai ta balle da kuka.
Umma ta ce, "Ke kam, ban san yaushe za ki daina kuruciya ba, da abinda ya isa, da wanda bai isa ba duk ki bare baki kina musu kuka".
Cikin kuka ta ce, "Umma ko sallama bai min ba ya dauki Aunty Hanifah suka tafi. Ban san laifin da na yi masa ba".
Umma ta ce, "Wannan ne abin kuka? Don ya dauki wadda ya ga damar tafiya da ita sun tafi? Ke baya tafiya dake? Sai kin masa laifi zai dauke ta? Ban da abinki ma ke da kike fama da kanki in ya kwashe ki ya tafi dake ya zai yi dake? Ina zai je kasar Inyamurai ya nemo miki abubuwan da kike son ci?"
Ta yi shiru. Can kuma ta ce, "Ni ba don bai tafi dani bane na ji haushi, Umma ko sallama bai min ba ni shine abinda ya bani haushi, in ba laifi na yi masa ba me yasa zai min hakan?"
Umman ta ce, "Sai ki yi mishi waya ki ce ka tafi bamu yi sallama ba, lafiya?"
Ta zumburi baki, "Allah Umma yana sane, ni ba zan kira shi ba. Suyi ta tafiya duk inda za su, su fi jirgi sauri, nima ba na huta jarababben Turaren shi ba?".
Umma ta ce, "Baki da wayo, shi miji lallaba shi ake, ba a mishi girman kai da zafin kai. Balle ke mai kishiya, ba a nuna mishi an gundura da shi, shi ma sai ya daina yi dake duk son da yake miki ya rungumi mai kula da shi".
Ta yi dariya ta ce, "Da dan gaskiyar ki kam Umma. Kinga Aunty Hanifah aiki fa take, ba yadda ba a yi ba ta aje aikin ta ki, amma da ta ga ya tafi dani shine yanzu ta watsar da aikin ta bishi, ni za a yiwa wayo?" tayi kwafa "To da wayo na!".
Umma ta yi dariya ta ce, "To ai kin gani, haka nake so ki daina shirme, ki dinga bin komi a hankali ba da fushi ba.
Yanzu dai ki yi mishi wayar ki tambaye shi yadda suka isa, kada ki nuna kin ji haushi. Ki kwantar da kai ki tambaye shi me yasa baka yi min sallama ba? In laifi na yi I am sorrry....."
Ta kyalkyale da dariya ta ce, "Umma yaushe kika iya turanci?"
Ta ce, "Sanda ubanki ya haife ki".
Ta sake yin dariya ta ce, "Ni kin tuna min ma, ban kira babana na gaya mishi yadda muka iso ba".
Ta ce, "Au, Uba ya fi miji?"
Ta ce, "Sosai ma, amma ba miji irin nawa ba;
He is like an angel to my life Ummahh ......., ya so ni tun ina cikin tsummokara na, ya kula dani a sanda na rasa ki. Ya tsaya tsayin daka ya dora ni a kan turbar ilimin da na ke buri, ya mai dani MUTUM.
Ina son shi sosai Umma, shi yasa nake KISHIN sa.....Umma na ji haushi da ya dauki Aunty Hanifah ya barni, duk da ya san bani da lafiya".
Umma ta ce, "Ki yi mishi uzuri Muhaseen, baki da masoyi a duk duniyar nan daga iyayenki sai shi. Ki ji abin da nace dake, ki kira shi ki ba shi hakuri".
Ta ji kunya sosai, ta ce, "To".
Umma ta juya ta gyarawa danta kwanciya ita ma ba'a jima ba barci ya dauke ta.
Muhaseen ta lalubo wayarta a karkashin pillow, hoton fuskar Yayan da ta sa a fuskar wayar yana murmushi, shi ta fara yin tozali da shi. 'Shower' ya fito kanshi da fuskarshi jike da ruwa yana yarari, singileti ne fara tas kawai a jikinsa, a haka akayi hoton, siraran lebbansa dauke da murmushi.
Ta lalubo sunan "HAYDAR DINA... ta soma kira, ta yi kara har sau uku bai daga ba. Daga karshe ma da ta ci gaba da kira sai ta ji ya kashe wayar baki daya.
Duk inda hankalin Muhaseen ya ke in yayi dubu ya kai kololuwar tashi, wani dunkulallen abu ya zo ya tokare ta a makoshi. Tabbas Yayan fushi ya yi da ita, to laifin me ta yi masa?
Sai ta sake dabara ta rubuta mishi text ta tura. Fiye da awa daya bai dawo mata da reply ba.
Sai ta tura wayar karkashin filonta, ta kwanta sosai tana kuka a hankali. Soyayyar mijinta na kara tunzura kukanta.
A wannan ranar yadda ta ga rana haka ta ga dare. Ta rasa inda za ta tsoma ranta ta ji sanyi. Me ta yiwa Yaya Aliyu haka da har yai irin wannan fushin da ita?
Don haka da ta tashi washegari idanunta sun kumbura sun kuma yi jajir, kanta na ciwo sosai, a haka suka yi shiri Danlami ya kwashe su a mota suka dauki hanyar Billiri, har da Mama.
Tambayar duniyar nan sun yi mata a kan me ya samu idonta amma ta ce ciwo yake. Mama duk ta damu, ita kuwa Umma hidimar 'ya'yanta kawai take a motar.
Da kwatance da tambaya aka nuna musu gidan maigarin Billiri. Yana zaune a soro da 'yan jikokinshi suna cin abinci suka yi sallama a zauren. Ya amsa ya basu izinin shigowa tare da shimfida musu tabarmar kaba.
Suka zazzauna aka gaisa. Umma tana murmushi ta ce, "Baba maigari baka gane ni ba ko?"
Ya dube ta sosai yana nazari, kamar ya san fuskar. Ta katse tunanin shi da cewa, "Halimah ce makauniya Babar Muhaseen, wadda ta zauna a nan wajen ku 'yar Baddo mai rasuwa".
Maigari ya mike tsaye cikin al'ajabi ya ce, "Halimatu ke ce? Ina Muhaseen?"
Ta nuna mishi ita da dan yatsanta. Muhaseen ta matso tana gaishe shi. Ya ce, "Allah da iko Ya ke, ku kama ta mu shiga ciki wajen Tafisu".
Murmushi ta yi ta ce, "Da idanuna Baba maigari".
A zabure ya juyo cike da mamaki ya ce, "Ikon Allah, ina kuka fada Halimatu duk tsayin wannan lokacin?"
Ya yi musu jagora suka shiga ciki har dakin Tafisu, cewa yake "Fito Tafisu ga Halima babar Muhaseen yau Allah Ya kawo ta".
Da gudu ita ma ta fito ta rungume Muhaseen, don kallo daya tayi mata ta gane ta, ta kama hannun Umma suka shiga dakinta, ta rasa inda za ta saka su.
Maigari ya kara gigita ta da al'ajabi da cewa, "Da idanunta fa, tas take ganin mu".
Ta rafka salati ta rungume Halimah tana yiwa Ubangiji tasbihi.
Sauran jama'ar gidan duk suka shigo aka gaisa kowa na mamakin yadda Halima ta koma kamar Baturiya, ga 'ya'ya abin sha'awa, ga idanuwa ras, iko sai Ubangiji!.
Sun dade suna hira tare da maigari da Hajiya Tafisu. Ta sa Muhaseen ta dauko katuwar jaka da ta ciko da sittiru musamman saboda Hajiya Tafisu. Nata daban na maigari daban, shadda-shadda da jallabiyoyi da yadiddika masu tsada.
Haka na jikokinta suma daban. Ta basu labarin rayuwarta bayan ta barsu da yadda ta rabu da Muhaseen. Haduwarta da dan'uwanta da aikin da ya yi mata, da aurenta da Alh. Idris duk ta gaya musu.
Ba wanda bai yi al'ajabi ba. Ta ce su shigo Gombe suyi (passport) shekara mai zuwa za ta tafi dasu su sauke farali insha Allahu. Kuma su ga muhallinta.
Tsaraba sosai irin ta kauyen fulani Hajiya Tafisu ta hada musu ita da Mama, kwan zabbi, kindirmo, manshanu, takanda (Rake mara kauri) da kayan kamshin gargajiya aka rabu cike da kaunar juna da yiwa juna addu'ar alheri.
Sanda suka iso Gombe Alh. Idris ya iso yana tare da Daddy shi da Dr. Bello da Dr. Saudah. Wajen karfe uku na rana, don haka basu bata lokaci ba aka yi sallama Danlami ya kwashe su a Jeep din Daddy har su Muhaseen sai Airport.
Basu baro filin jirgin ba sai da jirgin su ya daga. Muhaseen ta rungume Mama tana kuka sosai, Mama na shafa bayanta tana lallashinta, suka taho gida.
****
BAYAN TAFIYAR UMMAH HALIMAH
Sai me? Kadaici da damuwa suka yi mata sallama, don ma Asabe na debe mata kewa da hirarrakin kauyensu masu ban dariya.
Muhaseen ba ta yi fushi ba, a karo na wajen hamsin ta sake kiran number Yayan, amma ya ki dagawa.
Bayan tana ganin suna yawan yin waya da Mama, amma bai taba cewa a bata ba. Ita Mama ta yi zaton suna waya tunda akwai waya a hannunta.
Hanifah ta kira ta sau biyu ta ji lafiyar jikinta, ita ma ba ta nuna mata komai ba ta saki ranta suka yi hira sosai.
Ta ce, "Haka Porthercourt ke da dadi amma kika ki tahowa Muhaseen?"
Hawaye ya ciko idonta saboda kishi mai tsanani da ya kamata, wato hakan ya gaya mata cewa ita ta ki zuwa, amma sai ta ce, "Na fi son nan din ne Aunty Hanifah, ko don irin abinci na".
Suka yi sallama ta aje wayar ta rufe fuskarta da tafukanta biyu tana kuka a hankali.
Wasa-wasa sai da suka cika watanni biyu Aliyu bai nemi Muhaseen ba, in ta kira shi ba ya dauka. Wannan hukunci yayi tsaurin da Mahaseen bazata iya jurewa ba. Don haka hakan ya shafi walwalarta da sukuninta a cikin gidan gabadaya.
Tun Mama ba ta gane ba har ta fahimci Muhaseen na cikin matsananciyar damuwa, a zuciya da fuskarta da yanayin jikinta.
Ta yi sanyi sosai, duk walwalarta ta ragu. Bata da aiki sai kwanciya, abincin ma ba sosai take ci ba. Zuwa wannan lokacin cikinta ya cika watanni hudu, amma girmansa yana baiwa Mama tsoro, ya turo ta karkashin zaninta sosai. Kamar na watanni bakwai. Laulayin ya ragu, daga mandako aka koma cin dafaffiyar masara, kullum sai Asabe ta dafa mata, akalla guda goma. Ta sa a gaba ta yi ta gaigaya kamar ta cinye totuwar.
Mama ta murda kofar dakinta a hankali a wani marece, sai ta taddata tana waya da Ummanta tana kuka, tana gaya mata har yau Yaya Aliyu bai neme ta ba, kuma in ta yi tedt ba ya replying, haka in ta kira shi baya dauka, ta rasa laifin da ta yi mishi.
Mama ba ta ji abin da Umman ta ce ba, amma ta lura lallashinta take. Domin tana ta share hawayenta da bayan hannun ta. Sai ta juya ta maida kofar ta rufe a hankali, ba tare da Muhaseen ta ji shigowar ta da fitar ta ba.
Ta zauna a gefen gadonta ta dauki wayarta ta kira shi, bugu na biyu ya daga yana kokarin gaisheta ta dakatar da shi.
"Me Muhaseen ta yi