Showing 42001 words to 45000 words out of 63435 words
falon, Mama ta ce ya kira Hanifa, sai gata ta fito da 'after dress' a jikinta.
Daddy ya yi musu fada sosai, na su zauna lafiya cikin amana da biyayya ga mijin auren su, ya ce su duka 'ya'yansu ne, babu wanda basa so a cikinsu.
Don haka duk wanda ya nemi takurawa dan uwansa to fa ba za su yarda ba. Jikin Hanifah ya kara yin la'asar.
Ita kuwa Muhaseen kuka take sosai cikin mayafinta. Don ji take kamar shi kenan an raba ta da Mama da Asabe ne. Mama ta rufe da doguwar addu'a suka shafa. Daddy ya mike, ita kuma ta kama hannun Muhaseen ta kaita har gefen gadon ta ta zaunar da ita, ta shafi kanta, ta juya ta fita, ta bi bayan Daddy.
Ita kuma Hanifah ta ce mishi sai da safe, ta nufi dakinta. Allah kadai ya san halin da zuciyarta ke ciki.
Mikewa ya yi ya bi bayanta, sai dai da ya murda kofar sai ya tarar ta rufe. Bai tsaya bugawa ba, ya juya ya nufi dakin Muhaseen.
Ya yi sallama, nan ya tarar da ita har yanzu kukan take. A hankali ya zauna a gefenta, kafadunsu na gugar na juna.
Ya bata lokaci kafin ya yi magana.
"Kukan ki na nuna kina cikin bacin rai ne, me aka yi miki? Ni ne baki son zama dani? Koko ni din ne baki so Muhaseen?"
Ya furta daga can karkashin makoshinsa, ta yadda ba don ta kasance cikin masu kyakkyawan ji ba, da ba za ta ji shi ba.
Da sauri ta girgiza kai, wato ba haka bane.
A sukwane ya ce, "To yaya ne?'
Ta yi saurin tsayar da kukan.
Ya kai hannun daman shi ya zare mayafin. A lokacin da take fadin.
"Ni na fi so in zauna a wajen Mama ne".
Ya ce, "To ni kuma fa Muhaseen?"
Ta yi shiru.
Ya ce, "Ni baki son zama dani?'
Ta girgiza kai.
Ya mika dogayen hannuwanshi ya rungume ta, yana shakar sassanyan numfashinta, ya kwantar da ita a hankali ya yi light off.
Ya ce, "Kwanta ki yi barcinki a jikina Muhaseen, I'm your husband.... (ni mijinki ne mahadin rayuwarki) na fi Mama bukatarki. Idan kuma sona ne bakya yi, to tashi in maida ki wajen ta..."
Ta yi saurin cewa, "A'ah!".
Ya janyo drower din jikin gadonta ya dauko turaren 'Onde - Vertige', ya feshe su, ya feshe shimfidarsu, ya sa 'remote' ya kunna A.C, ya ja lallausan bargo ya lullube su.
Ya ce,
"Ki yi barcinki Muhaseen, ni ba abinda zan miki. Feel free with me. Are you o.k?"
Ya fadi cikin wata sassanyar murya da ba ta taba jin ya yi magana da irin ta ba, murya ce da ta kasa amincewa cewa ta Yaya Aliyu ce, murya ce da ta ratsa har cikin kwanyar kanta. Ta bi ta kashe duk wata laka dake cikin gangar jikinta. Sabida taushin ta da sirantar ta.
Murya ce da ta tayar da tsigogin jikinta. Kukan ya tsaya don kansa, ba tare da ta yi wani kokari ko yunkurin tsayar da shi ba.
Ta samu kanta da sakin jiki sosai da kara kwanciya a jikin Aliyun. Al'amari ne da ko a mafarki bata taba katarin yin irin sa ba. Lallausar kamshin sa na ratsa zuciyarta, wata sabuwar rayuwa ce wannan da ko cikin mafarki mafarkinta bai taba hasaso irin ta ba. Wai ita ce yau cikin mayafi daya da YAYAN nata. Wannan wani abu ne da bata taba zato ba 'even in her imaginations'. Wani barci mai dadi ya soma fizgarta.
Karfe biyar na asubahi alarm da ya saita ya tashe su, suka yi alwala suka yi sallar jam'i su biyu, sannan ya ce da ita su kara da nafila ta musamman.
Suka yi addu'o'i masu yawa a kansu, 'ya'yansu da iyayensu. Sannan suka koma suka kwanta.
Sai labari ya sauya, domin Yayan ya birkice mata baki daya, duk rokonta, kuka, yakushi da cizonta, Yaya Aliyun bai tausaya mata ba, bai saurara ba, sai da ya bare AMANAR SA a leda.......!
Bai farga da aika-aikar da yayi ba, sai da ya lura Muhaseen ta sume masa. Daukar ta ya yi gaba daya bai aje ta ko'ina ba sai cikin 'Jacuzzi'.
Ta bude idonta ta soma yi mishi kuka duk ya rikice, domin kuka take sosai. Ta kankame jikinta ta ce.
"Ni dai ka fita zan yi wankana, kuma wallahi wajen Mama zan koma tunda kashe ni za ka yi".
Ta ci gaba da kuka sosai. Yana so ya yi dariya ya gintse. Ya karya kai, ya langabar kamar ba Yayan ba.
"So nake na gani ko kin iya wankan?"
Ta balla mishi harara ta ce, "Ni dai ka fita, wallahi in baka fita ba yanzun nan zan tafi in gayawa Mama abinda ka yi min, kuma wallahi ba zan dawo ba".
Ya yi saurin fita yana cewa,
"Na tuba, na bi Allah na bi ki. Kaina bisa wuyana, na fita". Ya fita ya ja mata kofar.
Ta dade a cikin kwamin tana kuka. Da ta gaji ta bude ruwan dumin ya fita, ta yi wankan tsarki yadda Mama ta koya mata na jinin haila.
Ta rasa kayan da za ta sa ta fito, sai ta kara saka kuka.
Kafin idonta ya kai ga tawul kala-kala dake jere a ma'adanarsu. Ta zari biyu ta daura daya, ta yafa daya, sannan ta fito tana ta kumburi.
Yana kwance cikin 'sofa' yana kallon ta ta gefen ido, ta bude wardrove ta zari doguwar rigar barci ta koma bandakin ta saka, sannan ta fito.
Ko kallon shi ba ta yi ba ta nufi gadonta za ta kwanta da niyyar da zakara ya yi cara ta tafi cikin gida.
Sai ta tarar ya cire wancan (bedsheet) din ya canza wani. Ta yi kwanciyarta kanta da jikinta duk ciwo suke.
Shi dai yana kallon ta zuciyarshi na harbawa, ji yake in bai maida Muhaseen cikin kirjinshi ba, zuciyarshi zata tarwatse..... (another taste of passion.......)
A kowacce dakika zuciyarshi kara harbawa take da kaunar MUHASEEN ta yadda har yake jin zai iya fansar ranta da ranshi, zai iya mallaka mata duk abinda ya mallaka a duniya.
Tasowa ya yi ya yaye bargon nata ya shige ciki, ya kamota ya makalkale ta. Kalaman da yake gaya mata a yau Muhaseen ta ce.
"Sirrinsu ne".
Shi kansa bai san me yake fada ba. Ta ce, "Don Allah ka cikani, za ka balla ni, rikon yayi min tsauri".
Bai cika tan ba, sai ya kara kankame ta. Cewa ya ke......
"Muhaseen na baki AMANATA da AMANAR rayuwata, raina fansa ne a gare ki, ki yi hakuri ki rufa min asiri ki zauna da ni. If not, I'll become shattered.......!
Ki rufe sirrina. Mama Uwarmu ce, ko ita Allah bai ce mu fallasa mata sirrin auren mu ba. Na hadaki da Allah ki yi hakuri. Ki yi ta dukana har sai kin huce bacin ran ki, amma kar ki gayawa Mama, ba zan sake ba!".
Ta ce, "To cika ni".
Ya sake tan, ya kwantar da kanshi a kirjinta, idanunshi a rufe. Yana shakar lallausar kamshin 'oud-abyad' dake tashi daga fatar jikin ta a hankali.
Sai tausayinshi ya kama ta, babba da shi, da ajinsa, da mukaminsa, da ilminsa, amma ya kwantar da kai yake rokon ta haka, kada ta fallasa sirrinshi ga mahaifiyarshi. Ita wace ce?
Ba ta san sanda hannunta ya kai cikin sumar kanshi ba, tana murza yatsunta a ciki a hankali. Saura kadan Aliyu ya sume.
"To na hakura ba zan gaya mata ba, amma kaima ka yi min alkawarin...."
Sai ta yi shiru.
"Alkawarin me? Fadi yanzu a aikata shi ko mene ne Muhaseen, komin tsaurinsa. Gida? Ko mota? Ko kujerar Makkahhh?"
Ta kyalkyale da dariya sabida yadda yayi maganar a sukwane, ta ce, "Allah ya sauwake in ce ka bani kudi, ni me zan yi da gida da mota?
Ni dai kawai kada ka kara auren kowa....ni da Aunty Hanifah mun ishe ka, wallahi bana son kishiya, sam bana son ta!"
Mamaki ne ya lullube shi, Muhaseen ta san KISHI, ta dandani ni'imar aure har ta san ta yi kishi a 'yan shekarunta da basu kai ga shiga ashirin ba. To nan gaba kuma fa? Idan ta zama cikakkiyar matar aure?
Rungumeta ya yi ya sumbaci shafaffen cikinta........
"Ga ni kashe ni Muhaseen! Idan na kara kallon wata, kallon da bai yi miki ba. Believe meee..... ke AMANATA ce..... da in na ci ta Allah zai hukunta ni, ki yarda don junanmu Allah Ya halicce mu, 'we are meant for each-other. And I'll remain yours forever ......, In sha Allahu!
Na fara sonki Muhaseen ba tun yau ba.....ba tun jiya ba, ba tun shekaranjiya ba, tun ranar da na fara ganin ki 'in rugs (cikin tsumma) na yarda cewa matata ce uwar 'ya'yana Allah Ya hada ni da ita.
Ki yi duba cikin wannan soyayyar ta shekara goma, ki so ni ko da rabin-rabin yadda nake son ki ne. Zan samu Muhaseen?"
Ta lumshe zara-zaran gassun idonta, ya soma sumbatar idanun yana cewa,
"Muhaseen don Allah!"
Sai ta rufe fuskarta da tafukanta tana murmushi ta ce.
"To ai ni dama ina sonka".
Ya kwaikwayi 'yar muryarta ya ce, "Ni ba wannan son nake nufi ba, so nake ki soni son MATA ga MIJINTA, ki bani dukkan AMANARKI, ki mallaka min zuciyarki da ilahirin gangar jikinki. Ki so ni har cikin kashi da bargo. Ki so ni son matar aure ga uban 'ya'yan ta.
Idan na samu wannan Muhaseen ko yau Allah Ya dauki raina bani da kaico, don na san inada wacce za ta dauwama tana yi min addu'a, ko da bani da 'ya'ya........."
Ta yi saurin toshe masa baki da tattausan tafin hannunta ta ce.
"Tare zamu mutu Yaya Haidar, insha Allahu!" (Sai hawaye....).
Ya sanya halshe yana side hawayen ya ce
"Haba Muhaseen, godiya zamu yiwa Allah ba kuka ba.
For me, (agareni) duk wasu mafarkaina na duniya sun gama cika, tunda na same ki Muhaseen, ke ai za ki haifa min 'ya'ya ko? Kuma za ki basu abinci daga jikinki don su tsotso kwakwalwarki da halayenki?
Ba za ki damu da canzawar structure din jiki ba? Wanda ke sanya duk miji mai hankali da imani kara kauna da tausayin matarshi?
Ban aure ki don jikinki ba Muhaseen, sai don ina son ki ke kanki. Za ki yi min wannan alfarmar Muhaseen ki haifa mini 'ya'ya?"
Ya kwantar da kai a kan kirjinta, yatsun hannunshi duka biyu cikin sumar kanta. Ba ta san lokacin da ta rungume mijinta ba, runguma (bery tight) mai nuna gesture din da ke cikin zuciya.
Ta ce, "Allah Ya bani Yaya Haydar, nima ina son 'ya'ya".
Ya ja bargo ya rufe su, ya dau 'remote' ya kashe A.C, babu wanda ya kara jin duriyarsu a gidan har karfe (12pm).
Sai sha biyu da kwata ya fito ya nufi dakinsa ya kintsa.
Tuni Hanifah ta fice, ga kuma kayan karin kumallo nan a kan 'dining' da alama daga wajen Mama suke ko tabawa ba a yi ba, wanda ke nuna haka ta fita ko ruwa ba ta sa a cikinta ba.
Zai iya rantsewa ya san jiya ko rintsawa ba ta yi ba. Tausayi ne sosai ya kama shi, ya wuce bathroom dinsa.
Ya fito cikin shiri ya dawo dakin Muhaseen, nan ya tarar ita ma ta yi wanka daure da tawul tana shafa mai a gaban mudubi.
Ya zagaya ta bayanta ya kwantar da kai a kafadunta, kyawawan fuskokinsu suka bayyana cikin madubin. Ya karbi man ya karasa shafa mata, ya bude wardrove, kaya ne a jere 'yan ubansu-ubansu, ya zabar mata wani bakin 'material' mai yarfen 'golden' ya ba ta ya ce.
"Ki yi maza ki shirya muje wurin Mama, gashi har Daddy ya fita".
Ta ce, "To laifina ne? Ba kai bane ko Yaya na yi kokarin in tashi sai ka sake makalkale ni?".
Dariya ya yi, ya sake makalkaletan, yasa ta a gaba sai da tasa kayan duk kunya ta isheta, ya kamo hannunta yana duban kyawawan yatsunta sunyi kyau sosai da bakin lallen da aka yi musu, sannan ya janyo ta zuwa 'dining'.
Abincin ma shi ke bata a baki, tana tayi mishi zumbure-zumburenta. Wanda ke sa shi nishadi kamar yayi yaya? Hakoransa farare kal duk a waje, ya kasa rufesu sai dariya yake, irin wadda bai taba yin irinta a rayuwarshi ba tun daga kuruciya har girma. A hakan dai suka tsatstsakura suka mike, hannunta cikin nashi har dakin Mama.
Bai kuma cika hannun ba har suka zauna gefe da gefen Mama, suka sanyata a tsakiya. Har suna hada baki wajen cewa "Mama kin tashi lafiya?"
Ta dube su ranta kamar takarda don haske, bata taba ganin Aliyun cikin wannan nishadin, walwalar da sukunin zuciyar ba, ta ce,
"Kai, ku kam baku da kunya wallahi. Ko da yake kai ka koyawa Muhaseen, da ba haka take ba".
Muhaseen ta yi saurin kai tafukanta ta rufe fuskarta. Shi kuma ya yi murmushi ya ce, "Mama in mun tsaya jin kunyarki wajen wa za mu je? Gobe insha Allahu jirgin karfe takwas zamu bi zuwa Porthercourt, ayi mana duk shirye-shiryen da ya dace".
Ta ce, "Za a yi, Hanifah kuma fa?"
Ya ce, "Ba haka take so ba Mama, ta yi ta aiki tana tara kudi, ni ba zan takura mata ba, Allah Yasa ta fi Bill Gate kudi".
Mama ta ce, "To ai shi kenan, Allah Ya kaimu".
Ita da Asabe suka shiga kicin a tare suka soma yi musu shirin tafiya. Kayan girki, soyayyar miyar attaruhu, dambun nama, cake, samosa, 'traditional spices' da sauransu.
Ga kuma kayan gara su alkaki, nakiya, dubulan, gireba, bakilawa da sauransu da aka kawo daga Dukku. Shi ya fito mata da duk kayan da ya kamata ta tafi dasu ta shirya su cikin babbar jakar lefenta.
Hanifah ta dawo da yamma, ta yi tunanin bari ta je ta gaishe ta don tun safe ba ta ganta a gidan ba.
Ta yi sallama a kofar dakinta daga ciki ta amsa, ta ce,
"Yes, come in".
Ta murda kofar ta shiga ta same ta a kan study-table da farin gilashi a idonta, takardu da manyan littattafan lauyoyi fal a gabanta.
Har kasa ta tsugunna ta ce,
"Aunty Hanifah mun wuni lafiya?"
Ta dan tsaida idonta a kanta tana nazarin ta, ita bata taba ganin inda kishiya ta durkusawa kishiyarta ba.
Ta tuno kalaman Aliyu,
"Don me za ki daga hankalinki don na auri Muhassen? Kamar wata annoba na kawo miki? Yarinyar nan a gabanki ta tashi, kin san dukkan halayenta, kin fi kowa sanin ladabinta. Da me za ta cutar dake?"
Sai ta ji zuciyarta na yin sanyi. Ta amsa gaisuwarta, a nutse ta ce,
"Mike ki zauna mana Mahaseen ga kujera nan".
Ta ce, "A'ah, ina sauri ne zan yi sallar maghariba, dama tun safe ban ganki ba sai yanzu Mama ta ce kin dawo, shine na ce bari in zo in gaishe ki".
Ta ce, "To, na gode, a kula da ango sosai 'amarya', kinga ni abubuwa sun min yawa".
Cike da jin nauyin sunan data kirata dashi ta ce, "Toh, sai anjima".
"Mu jima lafiya".
Tana shiga dakinta bayan ta yi sallah ta murzawa kofarta key, ba ta kuma zare shi daga jiki ba. Kada Yaya Aliyu yau ma ya zo ya nemi kashe ta.
Shi kuma da ya dawo sallah ya zo ya murda kofarta ya ji ta a rufe sai ya nufi dakin Hanifah. Yadda Muhaseen ta barta haka ya sameta. Ta zare gilashin idonta ta ba shi attention dinta.
Ya ce, "Ina Muhaseen ta yi ne kofarta a kulle?"
Ta ce, "Tun dazu ta bar nan, ko ta tafi kofar Mama ne?'
Ya ce, "Ai daga can nake ba ta can".
Ta ce, "To mai yiwuwa kulle kofar ta yi".
Sai ya matsa gareta ya rungumota ta baya, ya soma kissing, da abinda Aliyun ke cin lagonta kenan, yake mata cin kashin da ya ke so take shanyewa; ta dade da sanin cewa mugun dan soyayya ne shi wanda yayi bala'in lakantar hanyoyin kassara gabban diya mace ta hanyar gamayyar 'romancing' kadai ba sai an kai ga babban al'amarin ba. A da kam, 'she has no objection (bata iya bijirewa). Amma a yau sai ta yi namijin kokarin kwatar kanta, data tuna cewa da wata fa ya kwana jiya ba da ita ba, kuma cikin kwanakin waccan ne. A fusace ta ce,
"Kada ka yi haka, cin amana ne......."
Ya ce, "To ba ta kulle kofa ba? Ni kuma a bukace nake......." yanayin idanunshi kadai ya tabbatar mata da hakan, kodayake dama a yawancin lokuta haka suke. Amma na yau ya fi na kullum.
Ta balla masa harara tana mamakin rashin ta idon da namiji, wai me (sweet 16) ne da aka kawo mishi ita jiya, zai ce yana da bukatar mai (32 years). Ta manta an ce "a rashin uwa akan yi uwar daki". Tayi bala'in zuwa wuya. Ta ce,
"Ka ga, bi nan....".
Ta nuna mishi kofa.
Ya ce, "Ni kike kora Hanifahhh?"
Ta ce, "Na kore ka, nace na koreka din, kana kara taba ni zan rotsa maka 'crystal' din nan a tsakar kanka....."
Gwiwa a sage ya ce, "Toh?, me ya yi zafi? Na fita!".
Ya juya ya fita, don daga ganin kwayar idonta a juye, ya san ba cikin hayyacinta take ba, za ta iya yi masa abin da ya fi haka. Sabida bakin cikin da yake kunsa mata.
Ita ma Muhaseen din bai buga mata kofa ba saboda kunyar idon Hanifar dake haukace cikin mahaukacin kishi.
Ya koma dakinshi ya kwanta ya rasa inda zai sa kanshi, ya juya nan ya koma can, daga karshe dabara ta zo mishi, ya dau waya ya turawa Muhaseen text.
"Ki taimaki mijinki Muhassen ki bude mishi kofa.... ko kin zabi ki kwana cikin tsinuwar mala'iku ne?
Ya tura mata, nan da nan sai ga reply ya shigo.
"In bude ka kashe ni???".
Murmushi ya yi..........
"Don't you said we'll live and die together?"
Sai tace "Am not ready to die now.....".
Ta bashi amsa. Nan ma murmushi ya yi, ya tura...
"Shi kenan Muhaseen, ki barni ni in mutun....kuma idan kinga gawata da safen, ki tabbata alhakin mutuwata yana wuyanki".
Ta turo.
"You will not die now either.....it's not the high time... ka fasa haihuwar Yaya Haydar?"
"Ba kin ce ba za ki karba ba, zan haihu ni kadai ne?"
"A'ah (dariya).
"To ki bude kofa in baki BABY!"
"Na ki wayon..." (murmushi)
"Idan baki bude ba zan balla ta......" (sad face).....
[9/4, 12:59 PM] Asmau: Ta rufe wayarta ta tura cikin 'pillow' tana dariya, Yaya Haydar ya iya siye zuciyar diya mace cikin ruwan sanyi da dadadan kalamai, wadanda zaka yi mamaki ace daga bakinsa suke fitowa idan ka ganshi, to shi kansa bai san yana yi ba, (amma fa da Muhaseen kadai), ta yi kwanciyarta. Me za ta ji? Gir-gir-gir! Ana kokarin jijjige mata kofa.
Ta