Showing 57001 words to 60000 words out of 63435 words

Chapter 20 - Amanata HAUSA NOVE

ASMAU   

11 Nov 2024

19047

kusa da shi.
Ya dube ta sosai ya ce, "Ya batun aiki?"
Ta ce, "Tunda ka ce baka so ina zaton ai mun wuce wannan maganar".
Ya dan harareta. Ya ce, "Daddy ya ce ki ci gaba da aikin ki, Allah Ya taimaka".
Ta rungume shi tana godiya sai ga Muhaseen ta fito. Ganinsu haka sai ta koma kamar ta rusa ihu don kishi. Jin rufe kofar ta ne yasa suka dubi kofar.
Ya ce, "Muhaseen!"
Daga ciki ta amsa a wahalce, "Na'am".
Tuni ya fahimci abinda ta ke ciki. A raunane yace
"Zo mana!"
Sai da ta kwashi mintuna biyar tana fama da zuciyarta sannan ta bude kofar ta fito.
Hannunta ya kamo ya zaunar da ita a gefen Hanifah, shi ya tsaya a kansu. Ya dubi Hanifah,
"Me kuka tsara game da girki?"
Suka dube shi cikin rashin fahimta.
Ya ce, "Ina nufin wace ce za ta fara karbar girki, kuma kwana nawa-nawa za ku dinga yi a tsayin watanni uku da zamu yi?"
Hanifah ta ce, "Duk yadda ka ce".
Muhaseen tsakanin ta da Allah ta ce, "Ni na yafe, na barwa Aunty Hanifah duk wata ukun, bana jin dadin jikina".
Ya balla mata harara, "To ni ban yafe ba, ko ke kika fi kowa ciwo? Ita ce ma mara lafiya ba ke ba. Cikin watanni hudu kacal ki ce ba za ki iya daukar larurar mijinki ba? Kina ina masu ciki wata tara ke tare da mijin su suna hidimta masa, kokuwa don ke Mama ta shagwabaki?
Don haka na raba muku girki kwana biyu-biyu, Muhaseen za ta fara yau".
Hanifah ta ce, "Ba komi".
Nan suka ci gaba da hira Hanifah ta mike ta ce, "Na barku lafiya, lokacin shan magani na ya yi".
Muhaseen ta ce, "Allah ya tashe mu lafiya"
Ta ce, "Ameen".
Ai tana rufo kofa ya suri Muhaseen dinshi yai dakinsa. Brush suka yi, suka kuskure da 'mouth-wash' din 'listering', dakin suka dawo suka kwanta rigingine suna hira yana yi mata tausa a kafafunta da suka fara kumbura, sun yi jawur sun yi suntum.
Ya ce, "Muhaseen muyi hira, me kike so ki haifa mana? Mace ko namiji?"
Ta yi wani irin murmushi ta ce, "Duk wanda Allah Ya bayar, daya ne".
Ya ce, "Ni baby girl nake so mai kama dake, in sa mata sunan Mama, ko kin fi son namiji?"
Ta ce, "Na ce maka ni duk wanda Allah Ya bayar".
Ya ce, "Ba wani nan, namiji kike so don kisa masa suna Dr. Omar".
Ta kyalkyale da dariya ta ce, "Kai haba, ba a sa Daddy ba za a sa Baba Umaru?"
Ya ce, "Yap, sai in ba namijin bane".
Ta ce, "Ni dai addu'a za ka ke yi min Allah Ya raba mu lafiya, ni kadai na san bidirin da ake a cikina".
Dariya ya yi yace, "Ya fara motsi ne?"
Ya fadi can kasan makoshinsa yana kara mannata a jikinshi.
Ta ce, "Tun yaushe?"
Ya dora hannu a kan cibinta, ya kuma kasa kunne "Bari mu ji".
Ya kara kasa kunne ta ture shi tana dariya, ya yi maza ya rungume ta sosai, ya yi light off, yana warware mata sirrin soyayyahhh.....!

Haka rayuwarsu ta kasance a Warri, cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali. Asabe zaune take dasu tsakaninta da Allah, tana kula dasu da cikinsu, su kuma suna kula da mijinsu kowaccensu da zuciya daya.
In ma da kishin, to kowacce ba ta nunawa 'yar'uwarta sai dai ta nunawa mijin. Haka Aliyun ke so, yadda duk ya tsara, babu mai cewa a'ah. Wannan ya fi komi dadi ga Controller Aliyu Suraj Kumo, wannan shine cikar mafarkansa. Wato mallakar AMANAR SA Muhaseen!
Ya yi kyau ya yi kiba, ya kara haiba da kamala, kowa ya ganshi ya san yana cikin kwanciyar hankali a gidansa. Ga naira na kara zaunawa, ga addu'a da albarkar iyaye baibaye dasu. Aliyu mutum ne wanda ya san hakkin iyalansa, yake kulawa da tattalinsu cikin kokarin yin adalci, duk da soyayyar shi a kan Muhaseen mai karfi ce ta yadda har wani lokacin yake sha'afa ya bayyana ta gaban Hanifahh.
Ga Hanifah, yanzu ba wannan ne a gabanta ba, ciki take nema Allah ya ba ta ruwa a jallo, babu. To shi Allah ana mishi wasa ne? Ta yi nadamar wautar ta, kullum tana tebirin likita suna kuma gaya mata lafiyarta kalau Allah ne bai kawo lokacin ba.
Tattali da kulawar da Aliyu ke wa cikin Muhaseen shi ne ya kara tunzurata. Ashe ma mijin ya fi son ka in za ka haifa mishi da? Wannan dana-sani da yawa yake. Bature ya cucemu, da akidojinsa na banza wanda muka ara muka yafa babu gaira babu dalili. Mun manta Manzo (SAW) cewa yayi "muyi auren don mu hayayyafa, yayi alfahari da yawan al'ummarsa ranar alkiyama.
Ta yi nadama sosai, kullum cikin damuwa take. Muhaseen ce take ba ta baki ta ce,
"Lokaci ne Aunty Hanifah!"
****
Dr. Omar ya kawo musu ziyara shi da amaryarsa Dr. Salwa da ya aura, mijinta Minista ne ya rasu a hadarin mota, tana da yara hudu duk mata ta aurar dasu.
Mace mai kirki da far'a sosai, kyakkyawa ajin karshe, kamar ta hadiye Muhaseen. Kwanansu biyu suka koma Gombe.
Sarkoki ne na daham da 'yan kunnaye da manyan warawarai na 'white gold' ya kawowa Muhaseen tsarabar Umrah da suka je da amaryarsa.
Ita ma Hanifa ya ba ta sarka da dan kunne. Ya kuma ce da Muhaseen motarta tana gidan Daddy tana jiranta, ta yi maneji da ita kamin wadanda ya yo oda daga 'General Motors' su iso.
Ya yi musu addu'a sosai suka rabu Muhaseen na ta shagwaba yana rarrashinta, wai ita sai sunyi mata sati.
Ya ce ta yi hakuri yana da ayyuka ne da yawa, in ya samu lokaci zai dawo.
Kullum tana waya da Turaki tsoho mai ran karfe, suyi ta kwasar hira. Haka Aunty Badi'a, duk cikin danginsu ta fi shiri dasu. Turaki ya gaya mata shanunta uku sun haihu. Ta ce da sun dawo za ta zo ta gansu insha Allah.
Watanni uku kwarara wadanda suka yi dai-dai da cikar cikin Muhaseen watanni bakwai. Amma in ka ganta sai ka tausaya mata, kai ka ce gobe za ta haihu. Cikin ya yi girma ya yi fadi da tsini, ko mikewa da kyar take yi shima sai asabe ko hanifah sun kama ta. Sallah kuwa sai a zaune.
Aliyu ya dauki annual leave din shi suka tattaro suka taho gida Gombe jiran haihuwa. Suka tare a sabon (bungalow) da Aliyu ya gina a Federal Lowcost, kowacce part dinta daban, shima maigidan haka. Sai su shekara basu hadu ba saboda tsarin gidan in basu nemi junan su ba. Mama ta hakura ta barwa Muhaseen Asabe, ita ta nemi wata. Duk da tasan bazata taba samun kwatankwacin Asabe ba sai dai ayi maneji.
Ita ma Hanifah an samo mata wata bazawara daga Darazo Iya Abu, tana yi mata aikin gida idan ta tafi office.
Da cikin Muhaseen ya cika watanni tara, Mama ta sawa Aliyu rigima lallai ya tarkato Muhaseen ya kawo mata ita dakinta, ta kuma hana su yin 'scanning' ta ce babu kyau. A barwa Allah ikon Sa.
Dole haka ya daure ya kai mata Muhaseen, don shi kansa bata iya tsinana masa komai, sai dai kullum ya tare a dakin Mama dashi ake rainon cikin. Ba ya tafiya sai Mama ta kore shi.

Ranar wata asabar Muhaseen ta idar da sallar asubah a zaune kamar yadda take yi, ta ji kafafunta sun rike. Ta muskuta za ta gyara zama ta ji baya ma ya rike, da wani irin gigitaccen ciwo da bata taba ji a rayuwarta ba.
Mama ta shigo tana mita,
"Ni kam ka ishe ni wallahi, ba kuma za ka shigo min daki ba, wannan binbini har ina? Tashin mu kenan daga barci, ko gwauro ne kai sai haka. Yarinya na ta kanta ka hanata sakat. To wallahi ka fita a idona haydar tun bamu sa kafar wando guda ba".
Ya idasa shigowa cikin dakin yana cewa, "Mama ni ganinta kawai zan yi, in sumbaci Baby in yi musu addu'a, sai in tafi ba zama zan yi ba".
Ta yi banza da shi. Ya raba ta gefenta ya shige. Ta fice ta rabu da shi don kullum ya zo da irin launin rashin kunyar da zai kunso yayi a gabanta, muhasin din bata ko kulashi don ta-kanta take. Sanye yake cikin rowan tokar shaddah 'excelsior ' dinkin Mohammed kanshi babu hula, sumar nan baka wuluk ta fulanin usli kamar wani balaraben Marocco.Ya karaso dardumar Muhaseen ya sunkuya yana yi mata magana cikin kunnen ta, sassanyan numfashinsa a fuskarta, kamshin 'albaan' din bakinsa a hancinta, yau bai fesa turaren ba da bata so amma kamshi yake na musamman mai kwantar da zuciya,
"barka da asubah sarauniyar zuciyata, dare tsaho yake yi min idan na laluba babu ke. Makwancin fadi yake yi min. Rayuwar 'seem to be difficult, without you life is vile', idan na rintse ido barcin baya zuwa HABEEBAH!!! (karo na farko a rayuwarsu da ya taba kiran sunanta na asali). Ya ga sai wani uban gumi take hadawa tana yamutsa fuska, kamar tana hadiyar allura, dai-dai sanda Mama ta shigo dakin, ya ce,
"Ya ya dai? Kike wannan gumi haka da sanyin safiyar nan?"
Mama ta yi saurin juyowa ta ce, "Mene ne Muhaseen?"
Ko magana ta kasa sai nishi take idanu a warwaje. Mama ta figo mayafi ta yafa ta figowa Muhaseen din, ta ce, "Kama ta maza muje, ina zaton haihuwar ce".
Sai kawai ya dauke ta da ita da tirtsetsen cikin nata yai waje, Mama ta rufo musu baya. Ya sata a motar da ya zo Mama ta shiga baya kusa da ita.
Ya ja motar ya yi ribas aguje maigadi ya yi saurin wangale gate ya hau titi aguje.
Ko kafin su iso General Hospital Muhaseen ta fice daga hayyacinta. Ba ta san inda kanta yake ba, balle wanda ke kanta
Da gudu ya shiga asibitin ya turo Nurse suka zo da gadon daura marasa lafiya aka shiga da ita dakin haihuwa.
Nakuda gadan-gadan amma faya ta ki fashewa. Wuni guda ana bu daya. Aliyu ya kasa ya tsare ya ki fita daga dakin haihuwar duk da korar da likitoci ke masa.
Idan ya dubi Muhaseen tana murkususu sannan tana kiran sunan Allah da sunan shi, sai ya kara gigicewa.
Ya yi gumi kashirban, idanunshi sun kada sunyi jawur, yana tallafe da kanta. Cewa yake da Dr. Adam shi dai su cire cikin baya so ya hakura.
"Ka yi hakuri, haka haihuwar fari take, musamman da ya kasance ba da daya ne a cikinta ba".
Ya zaro ido daidai lokacin da Muhaseen ta yi wani nishi mai karfi ta kankame shi sai ga lafiyayyen baby ya fado, unguwar zoma ta yi sauri ta dauke shi, mintuna biyar a tsakani sai ga kyakkyawan Hussain ya fado, amma Muhaseen ba ta daina murkususu da ihu da salati ba.
A'a! Kowa al'ajabi ya ishe shi, likita ya latsa cikin ya ce, "Da saura..."
Aliyu yace "da me....?" Likita yace "da saura!"
Aka kara ledar ruwan nakuda, fiye da rabin awa sannan sankaceciyar budurwa ta biyo baya, suka zaro mahaifa, suka shiga ba ta taimakon gaggawa domin sumewa ta yi sabida azaba.
Tuni Nurses sun kwashe 'ya'yan suna shirya su. Shi kuwa rungume yake da Muhaseen yana kuka sosai, yana kallon 'ya'yan da take ta haifo mishi, suna callara kukan isowa duniya lafiya cikin koshin lafiya. Har aka yi mata dinki aka shirya ta, aka tura ta dakin hutu, barci mai nauyi ya dauke ta.
[9/4, 12:59 PM] Asmau: Su Mama suna wajen dakin haihuwar ita da Daddy da ta yiwa waya, da Gwaggo da Asabe, Nurses uku suka fito rungume da jarirai a cikin tattausan farin 'showell' suna murmushi, suka mikawa Gwaggo daya, Mama daya, Daddy daya.
Sai Mama ta zube a wajen ta yiwa Ubangiji sujjadah, shi kuwa Daddy sai hawaye, Asabe guda ta rangada ta hada Hassan da Hussaini ta rungume, don Mama farin ciki ya hana ta dauka.
Shi kuwa Daddy bakin shi ya ki rufuwa da kyakkyawar amaryar shi dake hannunsa mai kama da Muhaseen jajur da ita, da girmansu kamar ba tripple ba ('yan uku).
A take Mama ta buga waya Saudiyyah, Daddy ya bugawa Dr. Umar, Asabe ta kira Hanifah dake office, ita kuma Mama ta kara bugawa Innani.
Cikin awannin da basu gaza uku ba asibitin ya cika taf da mutanen Dukku da 'yan'uwan Mama da jama'ar Gwaggo daga Kumo.
Aunty Badi'a ce kawai ba ta iso ba, duk da jirgi ta biyo sai dare ta iso. Har zuwa lokacin Muhaseen barci take, barcin wahala sadidan da ta dade ba ta yi irin shi ba.
'Ya'ya kuwa Dr. Umar ya hana a dauka, duk me son ganinsu ya gansu cikin gadonsu, an jere su cikin 'pink' din kayan sanyi an rufe kafafunsu da 'socks' abin sha'awa, sai addu'ar Allah Ya raya cikin tarbiyyar Islama.
Daddy da Dr. Omar su suka yiwa jarirai khutbah a kunnuwansu da addu'o'in kariya daga zina a al'aurarsu. Shi kam Aliyu bai bi ta kan 'ya'yan ba, sai da Muhaseen ta bude idon ta, ta ganta rungume a kirjinsa. Ga iyayensu zagaye dasu. Amma shi ko a jikin sa.
Kunya ta kama ta, ta zame ta kwanta a kan 'pillow'. Ya yi saurin rankwafawa gareta ya ce, "Ba inda ke ciwo Habeebah??"
Ta ce, "Alhamdulillahi sai rashin karfin jiki".
Ya kira Nurse suka cire ruwan da ya kare suka makala mata wani, duk hannuwanta sun kumbura da hudar allura abin tausayi.
Ta shafi cikinta cikin rada ta ce da shi, "Ina baben?"
Murmushi ya yi, bai ce komi ba. Mama da Daddy, suka karaso da jariran a hannunsu, Dr. Omar da 'yar budurwa suka jera mata su a gabanta.
Sai ta fashe da kuka don dadi, shima Dr. Omar kuka ya saka, yana share ido da babbar rigarsa, ya dafa kanta yana ta tofa mata addu'a, yana shi mata albarka, yana kuma godiya ga Allah da ya ba shi tsahon ran da ya dau jikokinshi tun da sauran karfinsa.
Kwanansu biyu aka basu sallama domin daga maijego har yaranta suna cikin koshin lafiya.
Gidan Mama ya cika taf da dangi ba masaka tsinke, su Innani duk sun iso da abin arzikin su. Aunty Badi'a da Hanifa an kasa tsaye an kasa zaune, sune tsaye akan komi. Mama ce ke mata wanka da runhu, Gwaggo na wanke angwayenta da kishiyarta.
A ranar kauri, wato kwana biyar da haihuwa, mutanen Saudi-Arabia suka iso, amma babu Umma. Dr. Bello da Dr. Saudah da Alh. Idris, Abubakar, Usman, Musbah da Muftahul-khair. Aliyu yana can wajen Umma. Matar Dr. Umar ma ta zo ana gobe suna.
Ranar suna Turaki aka kawo Gombe shi ya radawa yara suna Suraj da Umar, sai Maimunatu, don ya ce basu da abin da za su biya Daddy da Mama rikon da suka yiwa Muhaseen.
Aunty Badi'a ta soma kiran Maimuna da (Leena), Suraj (Taufeek), Umar (Arfat). Sai kowa ya kama.
Suna kam an yi shi sunan dangi, ba irin abincin da ba a ci ba, ba irin zanin da Muhaseen ba ta daura ba. Ba irin abin alherin da basu gani ba daga 'yan'uwa da abokan arziki da iyayensu.
Hanifah ta yi, Oga ya yi, su Mama sunyi, Dr. Umar ya yi, Dr. Bello da Alh. Idris sun yi. Turaki ya yi, to haka 'yan'uwa da abokan arzikinsu, sai fatan Allah Ya raya. Ya albarkaci 'yan ukku cikin tarbiyyar Islama.
Kayan jarirai sai a 'store' aka loda su aka kulle, kudi kuwa a 'account' dinta na G.T ake ta loda su. Turamen manyan atamfofi da lesuka akwati-akwati, jaka-jaka haka ake dora daya kan daya.
Aunty Badi'a da ba ta rabo da tsokanar Mama, washegarin suna ta ce za ta tafi da masu jego Abuja, in sunyi arba'in su dawo.
Wani kallo da Mama tai mata sai da ta koma ba ta hakuri tana dariya, ta ce, "Wasa nake Maman Muhaseen, ni na isa?"
Ta yi dariya ta ce, "Ke dai kika sani".
****

Dr. Bello ya shigo dakin Muhaseen inda take jego wato dakinta na 'yammatanci, ya zauna a kan kujera tana bakin gado tana shayar da Arfat.
Lecture ya shiga yi mata sosai a kan yadda za ta kula da lafiyar jariranta. Ya ce ta daure ta dinga shayar dasu sosai, in suka shiga wata hudu sai ta kara musu da wata madara ta musamman da zai kawo mata, ba a samun ta a nan sai a can Saudi. Ruwan nono ba zai wadacesu ba.
Ta ce, "To".
Sai kuma ta fashe da kuka ta ce, "Saboda Allah me na yiwa Umma zan sha wannan wahalar amma ta ki zuwa ta ga lafiyata, balle ta jikokinta?"
Ya ce, "Ki yi hakuri, kunya take ji, amma ai za ta zo daga baya idan mutane sun ragu".
Ta tura baki tana kumburi, ya shiga rarrashinta har ta huce, amma ta ce ita lallai Umma ta zo nan da wata daya in ba haka ba ita ma Saudiyyah za ta bita ta kai mata 'ya'yan.
Ya ce, "A'a, ba yanzu ba, sai sun yi kwari Mahasin".
A haka su kai sallama ya dauki su Taufeek hotona a wayarsa, ya karbi 'account number' dinta na G.T zai zubawa su Arfat kudi.
Dr. Saudah ta rungume ta ta sumbaci goshinta, ta shafa kan Arfat sannan suka sa 'ya'yansu a gaba suka yi sallama da kowa. Alh. Idris na jiransu a Airport suka tafi.
Kowa ya watse taro ya lafa, sannan ne Aliyu ya samu damar shigowa yana ganinsu yana tayata hidimar yaran.
Mama ta ci gaba da yi musu wanka ita da Gwaggo, su Asabe ne 'yan dora ruwa da kwashewa. Hanifa kullum ta taso aiki tana nan. Ita da Ogan suke haduwa ayi ta raino, in ta fita ya hada 'ya'yan da matarshi ya rungume ya samu 'yar nutsuwa, yadda ranshi yake so kawai su koma gidansu don Mama ta sa masa ido ta takura masa ta hana shi sakat da kora. Har sha biyun dare suke kaiwa sai Daddy ya kore su ya ce zai rufe kofar gidansa.
Sun gama wanka, sunyi kiba sunyi kyau, kamar sunyi wata uku. Taufeek da Arfat 'photocopy' ne na ubansu, yayin da Leena ta debo komi na Muhaseen shi yasa Aliyu ya fi sonta.
Mama ta hana su komawa ta ce lallai sai sun yi wata uku, yadda Muhaseen da Asabe za su iya kula dasu. Kamar ya yi kuka, ya ce, "Mama ba sai a dauki mai raino ba a hada da Asabe? Hutu na ya kusa karewa, Abuja zamu koma 'transfer' dina ya fito".
Mama ta ce, "Allah ya sanya alkairi, sai ka fara tafiya. Amma ba zan baku jarirai uku ku kaisu bariki ba su yi kwari ba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login