Showing 45001 words to 48000 words out of 63435 words
zabura ta mike tana cewa,
"Don Allah ka yi hakuri Yaya Haydar, zan bude.... wasa nake.".
Ina! Ta makara, domin kofa ta balle. Shikadai ya san yadda yayi ya bude ta. Tana budewa ta fado timmm! A gabanta. Allah ya so ta ba a kan kafar ta ba.
Ta bude baki za ta yi kara don tsorata amma bai bata damar hakan ba, idanunshi kadai data kalla ta san cewa yau lamarin sai ya zarta na jiya, jikinshi yana masifar rawa, nata na yin na tsoro da tausayin kai. Rigar barcin jikinta tsaga ta ya yi tun daga sama har kasa...........
A wannan daren Muhaseen ta yi kuka har ta gode Allah. Data san haka auren yake da bata yarda ta amince ba. Ita ma Hanifah kwana ta yi kukan kishin mijinta, don duk tana jin sanda ya girgije kofa.
Kankanuwar yarinya ta haukata mata miji, ta sauya shi gaba daya. Ta mayar da shi mai arha, duk ajin nan nasa, ta mai da shi mara kunya da kawaici, alhalin a da ba haka yake ba.
Rungume yake da ita, tamkar ya tsaga kirjin sa ya sanyata su zama abu guda, ita tana kuka shi yana sauke numfashi mai nauyi (feeling satisfied and contented, ever), yanayi ne marar misali da bai taba tsintar kan sa a ciki ba a tsayin shekarunsa guda goma da aure, bai lura da rashin tausayin da ya yi ba, sai da ya ji jikinta ya dau zafi sosai.
Ta ce cikin kuka,
"Wallahi na fasa binka, baka jin tausayina, mugunta kake yi mini....ban gama warkewa ba, gashi bani da lafiya, ni wajen Mama zan koma...." Ta ci gaba da kuka sosai.
Shi dai bai tanka ba, bai kuma rabata da kirjinsa ba, sai da ta yi mai isarta tukunna. Ta shafeshi da hawaye da majina.
Ya sassauta rikon da ya yi mata, ya ce, "Duk ke kika jawo Muhaseen, na biki ta lallami kin ki, ke kika sa na yi miki muguntar, in ban zo wajen ki ba ina za ni?
Ita ta kore ni saboda ke, ke kin rufe min kofa, zina kuke so in je in yi ko me?"
Ya kai tafin hannunshi yana share mata hawaye.
Ya ci gaba da cewa, "Duk ranar da kika sake rufe min kofa, wallahi fin haka zan yi. Ni za ki rika garawa kamar gare-gare abin wasan yara?
Na yi kama da sa'anki? Ko da yake Mama kawai zan dinga gayawa kina rufe min kofa, in kin bini a hankali irin haka ba za ta faru ba.
Sonki nake Muhaseen da dukkan zuciya, ruhi da gangar jikina, 'to the extent that I cannot control myself (bana iya sarrafa kaina) akanki, ba zan iya raba makwanci dake ba in ba dole ba. Kada ki sake, kin ji? Nima ba zan sake irin hakan ba. I'm sorry....."
Ya fada yana mai jan sorrrry....din tun daga karkashin zuciyarsa. Ya sumbaci cikinta, sannan ya kara rungume ta.
"Kin hakura Muhaseen? Za ki bini?"
Ya fada cikin kwantaccen sauti a kunnuwanta.
Ba ta da yadda za ta yi, Yaya Aliyu ya bala'in sanin weakness dinta, ya koya matawata irin soyayyah a yau da bazata iya bari ba, ita mata san bogi kawai take yi da ta ke cewa za ta koma wurin Mama, alhalin ta zama cikakkiyar matar Aliyu, ta san wane ne shi, ta san me yasa mata suke kishin mazajensu. Don haka dole ta karbi lallashinsa, bambadancinsa da ban bakinsa. Don itama kanta tasan bazata iya zaman ba ta barshi. Da wannan sabuwar rayuwar da ya tsunduma ta, mai cike da abubuwa masu ban mamaki da bazata iya fayyacewa ba.
Ya sake cewa, "Za ki bini Muhaseen? Muhaseen ki taimake ni, na tuba, idan na kara to na yarda ki dawo wajen Mama..... Muhaseen don ALLAH!"
Ya fada cikin wata murya mai jan zuciya uwa lantarki.
Ba ta da zabi, ban da ta daga masa kai. Ya sumbaci idanunta dake lumshe, ya kara rungume ta.
"To kwanta in yi miki tausa".
****
Karfe tara na safe sun gama kintsawa, Danlami ya sa jakunkunan su a mota. Ya shiga dakin Hanifah da yake asabar ce tana gida don suyi sallama.
Tana zaune bakin gado tana shan Kuaker Oat, data dama da madarar peak, idanun nan sunyi mitsi-mitsi, gashin kanta a hargitse, kallo daya ta yi mishi ta dauke idonta.
Bai yi fushi ba da rashin gaishe shi, don dama ba dabi'arta ba ce gaida na gaba da ita. Ya zauna gefenta ya karbi kofin daga hannunta ya ajiye a gefe, ya kama hannuwanta biyu ya ce.
"Zamu tafi, babu matsala?"
A sanyaye ta ce, "Babu".
Ya karkace ya zaro kudi tun kan yai magana ta ce,
"Mai dasu, bani da bukatarsu, a saiwa amarya balangu, a gyara mata kofa!".
Dariya ya yi, (amma ko kadan bai ji kunya ba) sannan ya girgiza kai.
"To ai shi kenan, tunda gyaran kofa da balangu ne kawai ba sai an diba cikin kudinki ba, wannan hakkinki ne dole ki karba ko ke ce 'yar karuna, kuma idan na yi niyyar abu babu wanda ya isa ya sani in fasa, so karbi, in har fa kina son mu yi rabuwar arziki".
Ta ce, "Na ce maka bana so ko?"
Ya dora mata a kan cinyarta.
"Kina iya yin 'flushing' din su, ko ki bawa mai gyaran kofa, duk daya".
Ya mike ta bishi da kallon haushi, a ranta tana cewa.
"Allah Ya sa kar ku dawo, in huta da bakin cikinku".
Fita ya yi yana cewa, "Ki huta lafiya, ran uwargida ya dade, shugabar lauyoyin duniya. Wadda ta zabi aiki a kan auren ta. Ko da wannan aka barki kullum cikin kunci da bakin ciki za ki kasance".
Ta ce, "Ba damuwarka ba ce, tawa ce, in ma cikin kuncin nake meye naka ciki?" Ya fice yana yi mata dariyar da ta kara kular da ita.
Mama ce ta shigo ta ce. Lallai sai ta tashi ta shirya an raka su Airport da ita. Kamar ta yi kuka ta ce.
"Don Allah Mama ki yi hakuri wallahi bana jin dadi".
Mama ta ce, "To ai daga can sai mu wuce asibiti a duba ki tunda kan hanya ne, amma ayi ta zama da ciwo?"
Dole ba da son ranta ba ta shirya duk Mama na tsaye ta sa ta a gaba, ta rike mata jaka suka fita.
Ba karamin firgita ta yi ba da ta ga kyan da Muhaseen ta kara. Tana sanye da lesi ruwan hanta (maroon) da mayafi kalar adon lesin wato 'milk'. Kafarta wani arnen takalmi ne siriri baki mai igiya mai tsayin dunduniya samfurin 'channel' haka ma jakar da ta ke rataye da ita.
Far'a ta yi sosai da ganin har da Auntyn ta a 'yan rakiya, shima Aliyun sai kula ta yake a motar amma ta share su, hankalinta yana kan wayarta.
A ranta tana cewa,
"Munafuki dan abu kazan uba.....kawai". (wasu gunduma-gunduman ashar) zuciyarta ke ta lafta masa. Kamar ta shakeshi ya mutu kowa ya huta.
Sai da suka ga tashinsu sannan Danlami ya juyo dasu gida. Ta tattaro inata-inata ta yo sassan Mama tana jide su a dakin ta na da, wato dakin Muhaseen ta rufo sassan gaba daya.
Mama ta ce, "Lafiya?"
Ta ce, "Tsoro nake ji Mama ba zan iya zama a wannan katon gidan ni kadai ba".
Mama ta jinjina kai ta ce, "Kin fiya wauta Hanifah, shin don Allah meye ribar da kike ci a wannan aikin da kike wanda yake nisanta ki da mijin auren ki? Yana mai da ke koma baya a zuciyar mijinki?
Shin da gaske ne kina son mijinki ko ko takura miki a kai kika aure shi?"
Ta yi shiru, ita kanta ta fara ganin wautar kanta. Ta sallama mijin kenan? Duk dimbin soyayyar da take yi masa?
Amma ita bakin cikin da yake shaka mata ne ba za ta iya jura ba, amma ta yarda da gaskiyar Mama, yin nisa da take da Aliyu tauraruwarta take dakushewa a idanunsa.
Ta kwantar da kanta a kafadun Mama hawaye na zuba a idonta, ta ce, "Addu'a za ki yi min Mama, ina da kishi mai zafi. Ba zan iya jure ganinsu tare ba, gara dai muna yin nesa-nesa da juna.
Idan na bar aiki na bishi na nemi wani aikin a inda nake, shi ba zaunanne ne a wuri daya ba, na yi ta canza wajen aiki kenan?"
Mama ta ce, "Shin shi aikin dole ne? Ba za a iya hakura da shi ba tunda anyi karatun duniya a tsaya a nemi lahira?"
Ta ce, "Ina tunanin yin hakan nan da wani dan lokaci, amma ba yanzu ba. Na sha wuyar karatu Mama, ina so al'umma su amfana da ilimina, musamman kasar haihuwata (AREWA).
Yaya Haydar ba damuwa ya yi dani ba Mama....."
"Ki daina fadin haka". In ji Mama. "Baya son ki zai zauna dake har tsayin wannan lokacin?"
"Ko ya fara sona Mama yanzu ya samu wadda ya fi so.... Kema kin san haka Mama (ta yi murmushi). Kina bani 'hope' ne kawai!".
Ta sake yin murmushi. "Ina ji a jikina Mama kamar na kusa barin Haydar......amma ban san wane lokaci ne ba".
Mama jikinta ya yi la'asar, ta rungume ta, "Bana son irin wadannan maganganun na yanke kauna da gangan Hanifah.
Zan rantse Aliyu yana sonki, amma kuna da banbancin ra'ayi da akida. Ki yarda dani, ki karyata tunaninki. Shaidan ne yake son kashe miki gwiwa, ya saka miki was-wasi, ki bari Hanifah".
Ta ja hannun ta suka shiga cikin gida.
****
Sun sauka lafiya a Warri, direban office da wasu customs guda uku dake karkashin Aliyu su suka zo da mota suka kwashe su zuwa 'Camp' din su. Inda gidajen ma'aikatan custom yake, flat-flat ne hawa-hawa suna a (No. Thirty) hawa na farko.
Gidan Aliyu ya fi sauran gidajen kayatuwa da sabunta, kasancewar shi gidan (Controller) gaba daya kuma bai dade da shiga cikin shi ba.
Ko'ina kal-kal sai daukar ido yake kamar a kasar waje. Domin yaronshi John ya zo ya gyara gidan tun jiya, kukunsa Bicky ya yi cefane ya adana komai cikin 'freezer', ya kuma ajiye sauran kayan bukata kowanne a muhallinsa, irin su potatoes, plantain, albasa, busasshen kifi da sauran su, amma har kayan gwari (tattasai, tumatir, attaruhu) ya markada ya adanasu cikin dirkekiyar freezar kitchen din. Nama nau'i-nau'i kowanne ya yi masa ma'ajiya daban, ya samu takarda da salatif ya rubuta sunan kowanne a kan shi ya makala.
Aliyu ya yi kiran shi a waya ya ce ya zo maza ya sama musu abin da za su ci. Ya ja hannun Muhaseen ya kaita dakinta wanda ke shimfide da gado da shimfidu na alfarma.
Ko'ina a dakin 'marbles' ne fari sol mai daukar ido da sheki. Ta sunce ta shiga wanka shima ya nufi dakinshi ya yi nasa. Suka fito kusan lokaci daya, kowanne cikin sassaukar shiga.
Shi ruwan madarar jallabiya ce a jikinsa irin mai hade da hular nan, saidai bai sa hular ba, tana reto a bayanshi, gashinnan a kwance sai sheki yake ga sajensa kwance a gefe da gefen fuskarsa kamar balaraben Kuwait, ita kuma riga da zani na danyar 'super' shudiya ta sanya dinkin ya bi kirar jikin ta ya kwanta. Gidan duk ya gauraye da kamshin girkin Bicky, ya hadu da sassanyan kamshin Onde Vertige da ango da amaryar ke yi, sai ya ba da wani launin kamshi, mai sanyi da sanyaya zuciya.
Bicky ya jera musu komai a 'dining' ya gaishe su ya fita. Bayan Aliyu ya ba shi sallahun abubuwan da zai sayo ya taho musu da shi gobe.
Suka hau tebir, shi ya zuba ya tura mata, loma daya, biyu ta yi na stuffed cabbage ta aje cokali tana yamutsa fuska, salam ba gishiri balle maggi.
Ta ture plate din ta ce, "Ni dai a barni in dinga yin girki na da kaina".
Ya ce, "Za ki iya?"
"To meye amfanina cikin gidan in ban girka maka abinda za ka ci ba?" ta fada a sanyaye.
Ya ce, "Shi kenan zan sallami Bicky. Amma to wa zai dinga tayaki aiki? Wanke-wanke, shara da goge-goge?"
Ta ce, "Duk ni zan yi ai gidan bai kai gidanmu girma ba, gashi sabo kal, aikin shi ba zai wahala ba.
Don haka in dai don ta nice duk ka sallame su ka bar mai cefane, wanki da guga kawai".
Ya ce, "Ko? To ban yarda ba, don ba aikin wahala na kawo ki kiyi ba, amarci na zo dake kiyi".
Ta ce, "To a nemo mace, amma ban yarda da wannan Baturen mai kallon kurilla ba, da wasu idanuwansa irin na mage (kyanwa)".
Dariya ya yi, "Baki da dama Muhaseen".
Yau dai 'pillow-talk' kawai aka yi, (ko kinsan 'pillow-talk?' Tambayi ALIYU da MUHASEEN. Muhaseen tace in gaya muku (wani lokacine da ma'abota soyayyah suka zaba don tattauna abinda ya shafesu a lokacin barci, kansu na bisa pillow guda), don dukkansu sun gaji basu dade suna hirar ba barci ya dauke su.
Sai da safe ne ya kira Mama ya sanar da ita sun sauka lafiya. Sannan ya kira Hanifa ita ma, amma wayarta tana kashe.
Sai ya sake kiran Mama ya ce ta hada su. Ta karba tana mita,
"Ni Mama ki kyale shi, bana son damu".
Duk yana jinta, a fusace ta amsa,
"Ya aka yi?"
Ya yi kwafa ya ce, "Da ni kika yi! Idan ni dan halak ne ba zan sake kiran ki ba. Ni kike cewa na dame ki? Don na bugo in ji lafiyarki?"
Ya kashe wayar ya yi cilli da ita yana mamakin hali irin nata.
****
Cikin asibitin (Saudi-German) dake cikin birnin Jeddah, Dr. Bello Sajoh, ke warware bandejin dake like da idon patient dinsa, wadda ya yiwa operation sati biyu da suka wuce. Cike da tararradi.
Sauran likitocin ido da suka yi aikin tare suna tsaye a gefe-gefe tare da ma'aikatan jinya. Cikin rauni da fidda rai da kwantaccen sauti ya ce.
"Yaya Halimah aikin bai yi ba ko?"
A hankali ta soma kokarin bude idanunta, wani haske da ya dallare mata ido, ba shiri ta mayar da idanunta ta rufe.
Ta sake kokarin budewa a karo na biyu, tana kallon inuwar likitocin dake kanta dusu-dusu. A hankali idon ya ci gaba da washewa yana sabawa da hasken, har ta bude su tangararau.
Salati ta yi tare da godewa Allah, ta tashi daga kwanciyar ta rungume dan'uwanta tana ta yiwa Ubangiji tazbihi, gwanin Sarki wanda babu wanda ya kai shi hikima.
Zubewa ta yi a kasa ta yiwa Ubangiji sujjadah. Kai daga karshe rushewa ta yi da kuka, ta rasa wacce irin godiya za ta yiwa Allah wanda ya saukar da cuta tare da maganinta.
Sati guda ta kara a asibitin ana ci gaba da treatment dinta, kafin su ba ta sallama gaba daya da idanunta da koshin lafiya.
Dr. Bello kusan ya fi 'yar'uwarshi farin ciki, don saboda nasarar wannan aikin har girma aka kara mishi zuwa consultant a bangaren ido.
Suka wuce gidan Dr. Bello wanda ke nan cikin gidajen likitocin Saudi-German. Matarshi Dr. Saudah ta ci gaba da kula da ita har tsayin sati biyu.
Daga nan suka yi shirin tahowa Umrah su duka da yaransu biyu, Musbah da Miftahul-Khair zuwa cikin Makkah.
****
Tun tafiyar su Hanifah ba ta da lafiya, Mama ke ta jelen asibiti da ita. Abubuwa da yawa sun damu zuciyarta.
Ga kishi ga son mijinta. Ta soma nadamar irin wautar ta. Tana son yin sulhu da mijinta amma ta kasa kiran shi, shi kuma bai kara kiran ta ba, tun wulakancin da tayi masa.
Ciwon hanta ne (Hypertitis B) in ji likitoci, hantar ta ta huje tana bukatar ayi mata aiki, in har tana son ci gaba da rayuwa.
Mama tana cikin tashin hankali ba kadan ba, ta yi waya Innani ta zo suka ci gaba da jinyarta tare.
A rana ta bakwai da fara ciwonta kwana ta yi tana suma suna shafa mata ruwa tana farfadowa. Mama ta yiwa Aliyu waya a lokacin watannin su biyu da tafiya Warri, ta ce lallai ya zo ya sa hannu za a yiwa Hanifah aiki ba ta da lafiya sosai.
Haka ya tsallake aiyukansa suka taho. Ita ma Muhaseen din ba ta da lafiya, laulayin karamin ciki ne sai dai daga ita har Aliyun basu sani ba.
Ba karamin dadi ta ji ba da ya ce da ita za su taho gida, don in ya tafi aiki ita kadai yake bari a gidan, ta yi ta fama da amaye-amayen ta, sai mai aikinta Tina dake tayata ayyukan gida.
Yamma lis Danlami ya je filin jirgi ya debo su. Su Mama suna falo Hanifa tana ciki. Danlami ya shigo da jakunkunan su kafin su biyo bayansa.
Muhaseen ta fada jikin Mama ita ma ta rungume ta. Ta gaida Innani, sannan suka karasa dakin Mama wajen marar lafiyar.
Hankalin Aliyu ya tashi sosai da ganin halin da Hanifah ke ciki, ko wanda ke kanta ba ta sani ba. Ya ce da Mama a yau zai juya Abuja ya yi musu (bisa) dukkansu su wuce Jeddah a duba ta a can.
Cikin kwana biyu komai ya kammala. A daren ranar suka tashi zuwa Jiddah har Innani da Muhaseen.
Motar asibitin Saudi-German ta je ta dauko mara lafiyar a filin jirgi da yake tuni sun tattauna komai da likitocinta na gida Najeriya ta yanar gizo.
Suka nemi 'hotel' suka sauka, shi da Muhaseen daki daya, Mama da Innani daki daya. Bayan sun kintsa suka dawo asibitin.
Dr. Saudah Bello, ita ce likitar da 'case' din Hanifah yake hannunta. A ranar Aliyu ya sanya hannu aka shiga da ita dakin tiyata.
Suna waje cikin harabar asibitin, kowanne carbi ne a hannunsa ban da Aliyu, wanda ke ta faman safah da marwa daga nan zuwa can.
Bai san yana son Hanifah har haka ba, sai yau da rayuwarta ke hannun Ubangiji. Idanunshi sunyi jajir, a ranshi yana ta yi mata addu'a. Sabida dai yana zargin kanshi akan rashin yi mata adalci ga soyayyar data ke yi masa.
Asibitin basa bukatar 'yan jinya, suna da kwararrun ma'aikatan jinya. Amma Aliyu ya kasa barin asibitin, kullum a nan yake wuni har sun saba da Dr. Bello mijin Dr. Saudah, sabida yadda duk inda Dr. Saudan tayi Bellon na biye da ita kamar jela in bashi da aiki, yana tayata nata aikin, kasancewar shi Bahaushe shi da matarsa.
Basu barsu sun shiga wajen Hanifah ba sai bayan sati guda da yin aikin. Ta samu sauki sosai har tana zuwa toilet da kanta, kuma sun tabbatar aiki ya yi kyau yadda ake so.
Ita ma Hanifah ta saba da Dr. Saudah saboda yadda take kula da ita, kulawa ta musamman.
Bayan wata guda da yin aikin, Dr. Saudah ta basu sallama, ta gayyaci Hanifah cin abincin dare a gidanta dake nan cikin asibitin.
Shi kuma Dr. Bello ya