Showing 3001 words to 6000 words out of 63435 words
zancen a tsakaninmu amma ya ki amincewa. A cewarsa hakkin su ne ya sanar da su. Koda kuwa bazasu dauki wani mataki ba. Ni kuma na kudire daga wannan rana na bar garin Dukku kenan har abada!
Ba don komi ba sai don in tsira dake, domin na tabbata muddin San-Turaki da Iya Ramatu suka ji karbar ki za su yi, tunda saki uku Umaru ya yi min, babu zancen a gyara.
Burina kawai in bar garin Dukku in yi nisa da duk abin da zai raba ni dake Habiba-Muhasin. Don haka Mal. Tanko na fita Ta-Birni ta shiga wanka na lalubo ki a shimfidarki na goya ki, na yafa mayafin Ta-Birni, na dauki sandar da Mal. Tanko ya saya mini ina dogarawa da ita na lallaba na fice.
Ina zuwa zaure na ji almajiri yana bara, na yi kiran shi na tambaye shi ko ya san tasha? Ya ce, "Eh, ya sani". Na roke shi ya taimake ni yai min jagora ya kai ni ya sanyani a motar Billiri.
Niyyata in je in nemi Inna Baddo, in gaya mata abin da ya same ni, ta taya ni jimamin rashin Baffa, ta taya ni rainon ki. Idan kika yi kwari sai in kara gaba zuwa duk inda Allah ya kai ni.
Cikin sa'a muna zuwa motar Billiri saura mutum guda. Yaron nan ya sanya ni, alhalin na san bani da ko sisi.
Sai da mota ta fara tafiya mai mota ya lura ni ban ba da kudi ba, ya ce, "Baiwar Allah ina kudinki?'
Ban san sanda kuka ya kwace min ba, na ce, "Ka barni in je Billiri a motar ka sadaka fisabilillahi. Bani da ko sisi".
"Zancen banza kike Hajiya, kin san baki da kudi kika shigo mana mota?"
Gaba daya jama'ar motar suka maido hankalinsu kan mu. Ya soma kokarin tsai da motar yana cewa.
"Wallahi sauke ki zan yi. Ku nakasassun nan kun dauka kowa ma mai matacciyar zuciya ne irinku? To ni na abinci nake nema halalina ba masu bara nake taimako ba".
Yana kokarin bude murfin motar. Daga can baya wani mutum da ban san ko wane ne ba ya ce.
"Haba bawan Allah, ka dubi jaririn dake bayanta, ka dubi lalurarta, zaka sauketa a wannan kungurmin dajin? Wai me yasa mutane da yawa bamu da tausayi ne?"
Ya kirgo kudi a aljihunsa ya bashi. Mai mota ya amshe ya kalmashe yana cewa.
"Yanzu na ji magana, kai da kake da tausayi baka san zafin nema bane. Sai ki yi hattara, in yau wani ya biya gobe babu mai kallon ki".
Ya ja motar aka ci gaba da tafiya.
Na juya ina yiwa mutumin godiya, duk da ba ganinsa nake ba. Ya ce babu komai. Mutanen motar babu wanda ya sanya mana baki, har aka iso kauyen Billiri.
"Baiwar Allah ki fito an zo".
Muryar wanda ya taimake ni ne. Na daddogara na fito ya kama karshen sanda ta yana cewa, "Ina kika nufa ne?"
Na ce, "Gidan su Inna Baddo".
Ya yi dariya ya ce,
"Ai ba a sanin sunan mace, da dai kin san sunan maigidanta ko mahaifinta ko samarin gidan".
Wata sabuwa! Na ce,
"Wallahi ban sani ba. Don Allah ka taimaka ka sama min makwanci cikin tashar nan inda ba zamu cutu ba, zuwa wayewar gari sai in shiga gari in yi ta tambaya".
Tausayi ya kama shi, ya ce, "Kawo 'yar kina ji tana ta kuka".
Kememe na ki sakkota na ce,
"Nono take bida, ka samar min inda zan zauna sai in ba ta".
A raina na ce, in baka ka yi kwallo da ita? Kamar yadda Umaru ya yi kwallo da ni, itama ta makance?
Ai babu ni babu namiji, gaba daya na hada na yi musu jimillah, basu da adalci da imani cikin zukatansu.
Ya ce, "To wuce muje in kai ki gidan Mai-gari, za su baki makwanci har zuwa lokacin da za ki ga wadda kike nema, amma bai kamata ki kwana a tasha da wannan jaririyar sabuwar haihuwa ba".
Na yi masa godiya har da hawayena, ya kama gefen sandata yana yi min jagora har gidan Maigari.
A zaure Maigari ne tare da wasu dattijai guda biyu. Mutumin ya umarce ni da in tube takalmina mu shiga.
Sai a lokacin ne na tuna ashe kafata ko takalmi babu. Ya zube yana kwasar gaisuwa, nima na yi yadda na ji ya yi.
Sannan ya yiwa maigari bayanina yadda muka hadu daga Dukku har zuwa nan, da cewa da na yi zan kwana a tasha. Shi kuma shine ya ga dacewar ya kawo ni nan gare shi don kada na fada mugun hannu.
Maigari ya ce, ya kyauta kwarai. Sannan ya juyo gare ni.
"Jini ya taru cikin idanunki, me ya same ki? Ga idanunki a bude, amma ga dukkan alamu ba kya gani".
Na yi shiru ban amsa ba.
"Sakko yarinyar".
Na sauke, amma na kankame ban baiwa kowa ba, na soma kici-kicin sanya mata nono a baki, ta kama a hankali.
Suka ci gaba da tattaunawar da suke yi da jama'arsa, daga bisani ya sallame su, shima mutumin da ya kawo ni sallama ya yi mana zai tafi.
Ya ce, in an kwana biyu zai bullo ya ji ko na samu ganin Baddon. Shi kuma maigari ya ce in tashi mu shiga ciki.
Babban gida ne mai sassa daban-daban, wanda ke kunshe da matan aure hudu da 'ya'yansu, jikokinsu da surukansu.
Wajen uwargida Hajiya Tafisu maigari ya kai ni, ina ji yana yi mata bayani da rokon ta taimake ni kamin a binciko wadda na zo gurin ta. Ya kuma ce dani in saki jikina in yiwa Haj. Tafisu bayani sosai, kada in ji ko dar, a kyakkyawan hannu nake, inda ba za a cutar dani ba.
Hakkinsu ne taimakon jama'a ba nice ta farko ba. Na yi musu godiya ina hawaye. Tafisu ta ce, "Bani 'yar". Ita da yake macece na mika mata ke.
Ta ce, "tubarkallah, Kyakkyawa da ita". A take ta mike ta saki labulaye ta rufe kofa, ta baki ruwan dumi ta goya ki ta fita ta dafa ruwa ta yi min jagora ta dinga zabga min ganyen dalbejiya wadda suke da bishiyarta a nan cikin gidansu, amma mu can Dukku da runhu akeyi.
Sannan ta barni ta ce in yi na sabulu. Kema ta wanke ki da sabulun salo data aika jikanta ya sayo mata, ta lullube ki cikin kayan saki ta miko min ke, ta ce in ci gaba da baki nono.
Ta fita ta kawo min tuwon dare, tuwon dawa mai sulbi da miyar karkashi, ta wadata da yajin daddawa da man shanu.
Na kuwa kama ci kamar Allah ya aiko ni. Don har na manta rabona da abinci. Na ci na koshi na sha ruwa, hankalina ya dawo jikina.
Wani daddadan barci ya soma fizgata, daga ni har jaririyata, ta yi min umarnin in hau gadon bononta in kwanta ita za ta kwanta a na katakon, da yake gado biyu ne a dakin. 'Yan jikokinta kuma ta yi musu shimfida a kasa.
Bayan mun yi sallar asubahi da duku-duku Haj. Tafisu ta sake yi min wanka, ta kara gasani ta bani kayan 'yarta nasa.
Haka baiwar Allahn nan ta ci gaba da kula damu ba tare da ta san ko ni wace ce ba, har na fita wanka wato kwana arba'in.
A ranar ne kuma muka zauna na ba ta labarina, na kuma kwatanta mata Inna Baddo. Ta ce,
"Baddo da yawa a garin nan, ba zan iya ganewa ba.
Amma bari Dillaliya Dije ta zo, ba wanda ba ta sani a garin nan ba. Ki yi hakuri kuma ki kwantar da hankalinki, wata rana sai labari.
Ni na gaya miki wata rana sai Umaru ya nemi abin da kika haifa da kafafunsa da hawayensa".
Muna zamanmu mai dadi a gidan Maigari kowa ya shigo gidan nan sai ya tanka ki saboda kyau da koshin lafiya.
Haj. Tafisu tana shan tambaya a kanmu, amma ta ce ni din 'yar'uwarta ce.
Rannan muna zaune tsakar gida da yammaci, kina zaune jikin Asabe daya daga cikin yaran gidan, aka yi sallama ana cewa, "Gafaranku dai masu gida, ga 'yan kunnaye da awarwaro ko da mai saya?"
Na yi saurin dagowa na dubi sashen da maganar ta fito, ko mutuwa na yi na dawo ba zan mance muryar Innata Baddo ba.
Baddo na Baddon Bello, mai son mu mai kaunar mu. Ban san sanda kuka ya kece min ba. Na ce,
"Inna Baddo!!!"
Ta yi hanzarin dubana da mamaki da tsoro, ta ce, "Halimahhh?"
Na ce, "Na'am Inna".
Ta sauke kayan dake kanta ta iso ta rungumeni ta ce, "Ke da wa kika zo?"
Sam-sam Inna Baddo ba ta lura bana gani ba, saboda idanuna a bude suke tas. Jinin da ya kwanta cikin su har ya washe. Ina kuka sosai nake gaya mata "yau watannina uku a Billiri ina bulayin neman ki Innata".
Na juya ga Haj. Tafisu na ce,
"Hajiya Alhamdulillahi, yau Allah ya takaita mana wahala, ga Inna Baddo da na zo wurinta".
Ta ce, "To, Alhamdulillahi, bari in je in fadawa Maigari".
Tare suka dawo da shi, Inna Baddo ta gaishe shi cike da girmamawa, ta yi ta zuba mishi godiya shi da mai dakinshi.
Ya ce, "babu komai".
Sai kuma kewa ta kama mu ni da Haj. Tafisu, ta ce, "To yanzu Halima in kin tafi sai yaushe?"
Inna Baddo ta ce, "Kada ki damu Hajiya, Halima bazata bar garin nan ba ta yi miki sallama ba".
Suka hada min sha tara ta arziki, muka fito muna hawaye Haj. Tafisu ta kasa rabuwa da ke da kyar ta yadda ta baiwa Baddo ke ta goya ki.
Ta ce da Inna Baddo, "Ki kama ta ki yi mata jagora, ba ta gani".
Inna Baddo ta yi salati ta sanar da Ubangiji, ta kamo ni ta rike ta soma kuka. Nima sai ta karya min zuciya muka yi ta yi.
Ban taba jin tashin hankalin da ya same ni a kan idanuna ba sai yau. Hannuna ta ja muka tafi, muna yiwa jama'ar gidan bankwana.
Tun bayan rasuwar Baffanmu Inna Baddo ba ta kara aure ba, tana tare da gyatumar ta Inna Larai a gidansu na gado, don uban ya dade da rasuwa, tana saide-saiden ta don samun na abinci.
Ta yiwa Larai bayanina, sannan ta nemi labarin abin da ya rabo ni da gida. Na kwashe kaf na gaya mata ban rage komai ba.
Ta ce, "Bai cuce ki ba Halima, Umaru kansa ya cuta. Da sannu za ki ga sakayyar da Allah zai miki, insha Allahu tun daga nan gidan duniya.
Gara da kika taho, dan nima ban laminci a rabaki da 'yarki ba sanyin idaniyarki, da kika ci wahalarta ke kadai ko sannu baki samu ba. Nima ba wata wadata ke gare ni ba, amma ba zan gaza komai a rikon ki ba.
Allah Ya iya mana, bani ita nan in soma gwada mata nonon Akuya, yana sa yara saurin wayo da saurin girma, musamman in kin hada shi da waken suya".
Nan ta shiga hidima da mu da iyakar iyawarta.
Zamanmu a Billiri tare da Inna Baddo, zama ne mai dadi da fahimtar juna da taimakekeniya.
Domin dai duk da na rasa idanuna, ban kwanta a daki na ce sai Inna Baddo ta min komai ba. Da safe tana sai da waina da taushe, ni nake taya ta ayyukan, gashi tana samun ciniki sosai. In yamma ta yi kuma ta tafi tallan kayan koli da 'yan kunnaye gida-gida haka take bi.
Yayin da za ta goya ki ta tafi dake. Tsakanina da ke sai shan nono. Inna Baddo ta dauke min komai na rainon ki......."
Ta tsaya tana share hawayen da suka tsatstsafo mata da gefen mayafinta. Muhasin ta kasa shiru ta ce.
"To yanzu ina Baddo ne muke kwana a karkashin gada?"
Ta yi wata ajiyar zuciya mai karfi ta ce, "Kin fiya ci da zuci Muhasin, a sannu ai zan gaya miki".
Ta ci gaba da cewa.
"Shekararki takwas da haihuwa Allah ya yiwa Baddo rasuwa, ta dawo daga cin kasuwar Ladin Makoli, wata motar shanu ta bige ta a wajen ta rasu.
Mu dai muna zaune tare da Larai aka dinga sallama, aka shigo da gawarta. Jina na yi kawai ana zuba min ruwa saboda sumewa na yi. A lokacin har an hadata an kaita gidanta na gaskiya.
Tun daga wannan lokacin abubuwa suka tsaya. Na yi burin a ce da idanuna in ci gaba da sana'ar Baddo ta sai da waina, (masa) haka Allah yake ikonsa.
Ga jinyar Larai da ta hau kaina, don ita ma tun daga lokacin ba ta kara lafiya ba. Yau ciwon kafa gobe hawan jini, har ya zamanto Inna Larai sai dai a kwantar a tayar, tunda babu kudin zuwa asibiti.
Dan jarin da Baddo ta mutu ta bari aka tattara aka bawa Larai, dasu muke samu mu ci abinci.
Kan ka ce meye wannan babu ya kare, aka koma cin gayan tuwo. Wata ran ko gayan ba za a samu ba sai a sha ruwa ayi hakuri.
Gashi ke baki san babu ba, kin saba ki ci waina da taushe da koko kullum ta Allah, haka za ki sani a gaba ki yi ta ihun ba za ki ci gayan tuwo ba.
Daga karshe ma shi kansa gayan tuwon gagara ya yi. Wata ranar litinin na tatso nonon akuya wanda ya zama abincinmu, na tada Larai zaune ina ba ta.
Sai na ji ta yi nauyi a hannuna, sannan madarar tana dawowa ta hancinta. Na kura mata ido duk da ba ganinta nake ba, na dora hannu na a kirjinta, na tabbatar ba ta numfashi.
Na kwantar da ita na rufe mata idanunta, na yi lullubi na tafi gidan maigarin Billiri na sanar da shi rasuwar Larai.
Haj. Tafisu ce ta wanke ta, maigari ya sallace ta aka yi jana'izarta.
Bayan rasuwar Larai da kwana uku Haj. Tafisu ta zo gidan ta samu a gaba ta ce mu koma wajen ta, ko mu yi mata bayanin inda dangina suke ta kai ni.
Nan kuka ya dawo sabo. Na ce da ita bani da kowa, sai kanina Bello da aka kai karatun almajiranci Maiduguri.
Daga ita har maigidanta suka ce, to mu zauna tare dasu. Na ce, "A'a, tafiya zamu yi". Suka kada suka raya amma na ki. Don na san rikon mutumin da ba naka ba a wannan zamanin ba karamin abu bane. Gara in nemi na kaina in dogara ga Allah in tafi duk inda Allah Ya kai ni.
Haj. Tafisu tana kuka ina yi muka rabu. Ta ce, "To yanzu Halima ina za ku je? Yadda duniyar nan ta lalace, satar dan mutum ta zamo kamar satar kaza, ke ba ido ba, ke ba dangi ba".
Na yi murmushi na ce da ita,
"Kada ki damu Hajiya, duk inda na fada ba zan manta daku da alkhairin ku gare ni ba.
Wata rana insha Allahu zan zo mu gana muddin ina raye".
Ta tattara mana 'yan tsummokaranmu cikin Ghana Must Go, ta kawo naira dubu uku ta bani ta ce in yi kudin mota, Allah ya hada fuskokinmu da alheri.
Kika kama sandata kina yi min jagora, da yake tuni ke kike min jagora zuwa duk inda zamu. Yara sa'o'inki a Billiri kin sha kuka a kan su, kan kiranki da suke yi 'yar makauniya, don ke kam baki yarda a kirani da wannan sunan ba, dalili kenan da kullum kike cikin hawaye a yawancin lokuta.
Da muka zo tasha muryar 'yan kamasho na ji suna fadin, "Ina za ku je? Gombe, Kano, Katsina ko Bauchi?"
Ban san sanda bakina ya furta Gombe ba. Don na sha jin labarin karamcin mutanen garin wajen girmama bako. Na biya su kudin su na karbi canji muka fada motar Gombe. Aka sauke mu a nan tashar Dukku muka fara bara.
Ke kika sama mana wannan karkashin gadar muke kwana. Ganin muna samun na abinci bamu taba wuni bamu samu abin da za mu ci ba, da abin da zamu batar ba, na yanke shawarar mu yi zaman mu a nan.
Ga kuma bayan gida (toilet) da masallaci a nan din na matafiya, ke kike min jagora ki shigar dani bayan gida ki sama min ruwa, mu yi lalura mu yi alwala mu je masallacin mata mu yi sallah. Zancen wanka dama babu shi, mun ma manta yadda ake yin sa.
Ba tsana ba tsangwama, don duk wanda ke cikin tashar nan ya sanmu, yau shekaru biyu kenan. Haka duk sanyi duk ruwan saman da ke zuba, bamu fasa kwana karkashin gadar nan ba. To kin ji wannan shine tarihinmu".
Muhasin da ta yi shiru tana sauraron mahaifiyarta, ta ce,
"Insha Allahu Umma sai nima na yi karatun boko na zama soja, nasa an kama Baba Umaru. Sai na zama likita, na baki maganin ciwon ido. Sai na zama Alkali, na hukunta Baba Umaru wata rana....."
Umma Halimah, ta yi murmushi ta ce, "A'a, Muhasin, ni tuni na yafewa Baba Umaru. Ina rokon Allah nima Ya yafe mani, ko ba komai ya zamo silar da na same ki.
Don haka bana bakin cikin komai a rayuwa, tunda ina da ke. Ki yi hakuri ki yafe masa Allah yana son bayinsa masu afuwa".
Muhasin ta yi shiru, ba ta ce da Umman komai ba, wanda ke nufin, ba ta dauki nasihar ba.
Tayi suntum cikin fushi, zafin rai da kunar zuci, jikinta har rawa yake, idanunta sun kada sun yi jawur. Ta cokano baki, tayi kankan da 8
[9/4, 12:57 PM] Asmau: ****
Ya kai gwauro ya kai mari a tsakiyar kayataccen falon sa, yana rike da waya yana ta faman kira amma ya ki shiga, shegiyar matar nan mai sanyin murya ke ta gaya masa (is switch off). Kamar ya yi kuka a lokacin da Haj. Maimuna uwargidansa ta shigo tana rike da tata wayar tana turo 'troller' din kayan abinci.
Ta isa ga 'dining' wanda aka yiwa mazauni a gefe guda na falon ta soma jera 'warmers' da farantai da cokulla, da sauran kayan da ke cikin 'troller' din a kan 'dining' din.
Ta juya ga maigidanta a hankali ta ce, "Har yanzu bai bude wayar ba?"
Ya ce, "Kyale ni da ja'iri, yana sane ai ya kashe wayar saboda kar in neme shi. Karo na uku kenan suna kama min kaya suna jawo min asara, sannan gashi duk ya hana kananan ma'aikatan karbar cin hancin da nake aika musu, na kuma gargade shi da ya fita harkar kayana in har ya na so in shirya da shi, amma kin gani.
Yanzu Inspector Nura yake cewa sun kara kama min kaya a Lagos. To wallahi wannan karon ba zan dauki asara ba, ke da danki za ku biyani naira na gugar naira har naira miliyan