Showing 36001 words to 39000 words out of 63435 words

Chapter 13 - Amanata HAUSA NOVE

ASMAU   

11 Nov 2024

19033

ka ce dan karamin 'palace' ne. Kalar 'marbles' din ruwan madara, haka gadon da labulaye duk 'milk and choculate' ne.
An manna mata karamar 'Plasma' daga kudu maso gabas din dakin, komai sai daukar ido yake.
Ga wani lafiyayyen bed-sheet da Mama ta shimfida shima milk and choculate. Mai kananan pillows. Baka ga kallo ba sai a toilet "Jacuzzi" shima da duk kayan kawar dake cikinsa ruwan madarar ne, Komai ya zauna a muhallinsa kai ka ce Turawa ne suka shirya komai ba Mama ba, ko'ina sai tashin kamshin sabunta yake.
Ya zauna a gefen lafiyayyen gadon ya dubi Mama yana murmushi ya ce,
"Mama kina ji da Muhaseen sosai, ni ko tsinke baki canza min ba".
Ta ce, "Ka bani ajiya ne?"
Ya ce, "A'ah, wai hakkin makwabtaka ai ko?"
Ta ce, "To ban yi niyya ba".
Ta sashi gaba suka fito ta rufo dakin, har da murza key. Ya bi bayanta yana yi mata dariya.
Ranar lahadi tun safe Gwaggo ta iso da tawagarta, za su tafi Abuja dauko amarya. Su Innani da sauran 'yan'uwan Mama duk a nan suka kwana.
Karfe sha daya na rana motoci biyar suka tashi tafiya Abuja a jere reras, duka bakaken 'Cruisers' duk 'yan dauko amarya ne.
Muhaseen ko kukan nan da amare ke yi in za a tafi dasu ita ba ta yi ba. Ba don komai ba sai don ita ba ta ga wani bambanci ba don an maida ta wurin Mama, dama Abujar ta ishe ta, ga Aunty Badi'a ta hanata sakat da ciye-ciye da jike-jiken magunguna duk ta kosa ta tafi.
Don haka Yaya Khaula na cewa ta taso za a tafi ta gyara lullubinta ta mike ta sunkuya tana daura (flat cover shoe) dinta a kafafunta.
Aunty Badi'a ta ce,
"La'ilaha illallahu! Yanzu Muhaseen ba za ki yi kuka ba?"
Ta ce, "Ina zani da zan tsaya kuka, ba wajen Mamata bane?"
Badi'a ta yi dariya ta tafa hannuwa ta ce, "Ko? To a gaida Mama, amma idan labari ya sauya, wayata a bude take, a bani in sha".
Ta ce cikin rashin fahimta da rashin baiwa zancen muhimmanci,
"Wane labari ne kuma zai sauya ban da abinki Aunty Badi'a? Ba inda zani wanda ya wuce wurin Mama. Ba abin da zai kai ni sassan Aunty Hanifah balle ta yi min rashin kirkinta".
Ita dai Badi'a dariya take, don ta lura sam-sam Muhaseen ba ta san me aure ya kunsa ba. Ita kuma ba za ta tsaya bata lokacinta wajen yi mata bayani ba.
A ranta ta ce, "Ki je in ta yi wari zamu ji".
Ta kamo hannunta ta gyara mata lullubi suka shiga motocinsu Gombe ta diba. Badi'a na rungume da ita.
A Dukku suka tsaya don ta yi sallama da Turaki da mahaifinta. Addu'a sosai Turaki ya yi mata, sannan ya kawo littafi mai kunshe da addu'o'i na tsarin jiki da kariya daga magauta ya bata.
Dr. Omar yana gefe zaune cikin carpet yana danna wayarshi, ta kai idanunta a hankali inda yake ta ce.
"Ina wuni?"
Ya yi saurin dagowa ya dube ta, bai amsa ba, sabida yadda muryarta ta doki dodon kunnensa ba don ya zata ba.
Turaki ya yi kiranta gaban shi, ya kama hannunshi ya hada da nata ya ce,
"Ku yafi juna haka Muhaseen, ki yafewa mahaifinki, kuruciya ke dibansa a wancan lokacin. Amma a yanzu ki dube shi sosai, babban mutum ne ba yaro bane. Ki yafe masa kin ji Muhaseen?".
Hawaye suka zubo mata, na tunawa da Ummanta, inda take cewa, .......
"Ban baki wannan labari don ki kullace shi ba, sai don hankalinki ya kwanta".
Sai ta fada jikinsa tana kuka ta ce, "Na yafe maka Daddy, nima ka yafe mini".
Ya ce,
"Ni baki yi min komai ba Muhaseen, ni ne mai neman afuwarki. Allah ya yi miki albarka, ya zaunar dake lafiya a dakin mijinki, ya baku zuri'a masu albarka".
Ya kamo hannunta zuwa wajen su Badi'a, har da shi aka taho Gombe kawo amarya.
****

Tarbar girma kuwa sun ganta a wurin Mama da 'yan'uwanta su Innani. Duk abin nan da ake Hanifa tana dakinta ta kulle ba ta shigo sassan Mama ba, har su Innani ba ta zo inda suke ba, don duk fushi take dasu, don wai basu kaunar ta.
Su suka kulla aka yi mata kishiya da Muhaseen diyar cikinta kuma yarinyar da ta tsana fiye da kowa a duniya. Don ta tabbatar tuntuni daman Aliyun na son ta, ko daga irin kallon da yake yiwa yarinyar ma wanda ya sha ban-ban da wanda yake yiwa sauran mutane wanda ita Muhaseen din sam ba ta san haka ba.
A nan Gombe 'yan Dukku suka kwana, sai washegari da safe suka hau motocinsu suka koma.
Sai Aunty Badi'a wadda za ta bi jirgin karfe biyu na rana zuwa Abuja, ita da yaranta hudu, Anas, Husna, Jamila da autarta Nusaiba.
Bayan sunyi wanka sun shirya sassan amarya da uwargida suka nufa ita da Mama. Tuni Hanifa ta fice, don ranar litinin ce tana da ayyuka da yawa.
Suka shiga dakin amarya komai a gyare (neat and tidy), suka kara kunna turare a 'burner', suka yi 'yan gyare-gyare suka koma sassan Mama.
Saura kadan dariya ta kwace musu, ganin Muhaseen da tsintsiya da abin sharo yana tana ta gyara dakinta dake nan kusa da na Mama.
Mama ta dube ta tana murmushi ta ce, "Muhaseen aiki ake yi ne haka?"
Ta ce (ba tare da ta juyo daga sharo yanar da take yi ba), "Eh, Mama dakin ya yi kura sosai, ga yana. Hala tunda na tafi Abuja ba a share ba?".
Mama ta ce, "To ai ke yanzu baki da bukatar dakin, don tashi za ki yi ki koma dakin mijinki".
A nutse ta juyo, "Mama ni dai na fi so in zauna nan a wajenki".
Mama ta karasa ta rungumeta ta, sakamakon yadda tayi maganar da zuciyarta daya, ta ce, "Shi kenan Muhaseen gyara dakin ki, duk inda kike so nan za ki zauna, ni ba zan hanaki ba".
Aunty Badi'a tayi dariya har ta gode Allah. Da gaske Muhaseen ba ta san mene ne aure ba. Na farko dai ba ta da kawaye na jiki, sannan ba ta karance-karance da kallace-kallace. Gashi ta hadu da wata irin Uwa mai gudun bacin ranta, to ya ya za a karke da shi angon? Anya ba za su hadu su kware shi ba ita da Mamanta?
Za ta so ganin karshen wannan diramar ta Mama da 'ya'yanta. To amma babu lokaci maigidanta yana ta kiran ta a waya.
Don haka karfe daya dai-dai tasa yaranta a gaba suka tafi Airport. Danlami ne ya kaisu, sai da ya ga tashinsu sannan ya dawo.
Muhaseen ita da Mama da Asabe suka shiga kicin suna shirya abincin rana, da yake basa yin 'lunch' sai 3pm.
Lokacin ne Daddy yake dawowa gida cin abincin rana. Da suka gama ta shiga dakinta ta yi wanka, ta shafa lotion dinta (FaceRain) ta fesa deodarant spray din fahrenheit, ta zuba doguwar riga (Omanis) ruwan shanshanbale. Kunshinta ya fito sosai ya yi bakikkirin. Ta taje kanta ta kame shi da ribbon kalar kayanta, ta nada dankwali a kanta kai ka ce bakuwa ce daga Beirut.
Ta dauko wayarta za ta fito don ta tambayi Mama inda ta ajiye mata 'charger'. Tana kokarin fita, shi kuma yana sawo kai, sai suka yi karo garam...!
Ta yi saurin ja da baya ta bashi hanya tana cewa,
"I'm sorry Yayana....ban ga tahowar ka ba".
Ya limshe ido. Ya jingina da kofar ya harde hannuwansa a kirji yana murmushi yana ta faman kallon ta, kamar yau ya fara ganinta, gabadaya ta canja mishi, kallonta kawai yakeyi, da kauna da mamaki, idanunshi a lumshe, kansa a langabe jikin kofar.
Sanye yake da bakin wandon 'Jeans' da 'shirt' fara samfurin 'BVulgari', gashin nan a kwance bakikkirin da shi na fulanin Kumo yana sheki kai ka ce relaxer ya ke sa mishi.
Ga mikakken hancin kamar karas, irin na Mama. Ya zauna sosai a tsakanin lumsassun idanun shi kai ka ce saurayi ne mai tashen ashirin da bakwai. Kai ita a rayuwarta baki daya ba ta taba ganin mutum mai kyau da sigar Yaya Aliyu ba, dole Hanifah ta haukace da kishin abinta.
Ta dauke idonta cike da kunya ta ce, "Ka shigo mana Yayana, wucewa zan yi".
Ya ce, "Waye Yayan naki? Yayan nan, ya fita a bakin ki Muhaseen......."
Ta yi shiru. Ya kauce ya ba ta hanyar ya ce, "Wuce".
Ba ta san yasa mata kafa ba, saura kadan ta kifa, sai ya dagata gaba daya bai dire ta ba sai a gadonta.
Hannuwanta ya rike da hannun damanshi, yayin da ya yi amfani da na hagun wajen tallafo kanta, a hankali ya soma 'kissing' dinta gently, tun daga bakinta, sassan wuyanta, har zuwa yatsar kafarta............
Duk wasu kafofin sadar da jini cikin gangar jikinta sun daina aiki, sun karbi sakon sassanyar 'kiss' da Aliyu ke turawa a kowacce kusurwa mai bukatar hakan a jikinta.......
Ta bude baki za ta yi kuka sabida dimaucewa, ya yi saurin toshe mata baki yana girgiza mata kai, idanunshi sun canza launi daga yadda ta sansu, sun zama a shagide, kuma a juye da tsimin soyayyar shekara goma! Wadda ta taso gabadayanta a yau, ta soma warware kanta.

Wasu irin kalamai yake gaya mata cikin kunnuwanta da kananun shekarunta da dan turancinta ba za su iya fassarawa ba. Zuciyarta ke karbar sabon al'amarin da bata taba ji cikin gangar jikinta ba. Ya ci gaba da sumbatarta yadda ranshi yake so, ko motsi ta kasa, ta zamo 'pale' cikin wannan unexpressable moment da Aliyu ya jefa ta. Bakidaya ta manta a inda suke......

Can a tsakar kanta ta jiyo muryar Mama na kwala mata kira. Ta hada karfinta wuti guda ta ture Aliyun da ba shi da wani sauran karfi ko katabus ta mike. Ta lalubi dankwalinta ta daura ta fita da sauri saura kadan ta kifa

"Wato wannan shine abin da ake cewa AURE!"

Muhaseen ta fada a ranta.
"In haka ne auren abu ne mai nauyi kwarai, da sai an kai zuciya nesa sabida GIRMAN sa, wanda yafi karfin tunaninta, hankalinta da tsinkayenta.
Ba don komi ba sai don kunya da matsayin data bawa Yaya Aliyun na YAYAN TA. Amma kuma ai is so sweet; zuciya da gangar jiki na karbarshi. A shekarunta ta goma sha takwas (18), sai ta ji hakan ya sa ta kara son mijinta kuma Yayan nata; mahaukacin so kuwa. Wanda bata taba yiwa wani mahaluki a duniya kwatankwacinsa ba.
Ya kuma samu wani matsayi na daban a zuciyarta da bazata iya kwatantawa ba. Wanda har ta ji a yau tana KISHIN Aunty Hanifahhh....., kishi kuwa ba dan kadan ba!!!
[9/4, 12:57 PM] Asmau: Ki duba ki ga jiya na dawo bayan tafiyar shekara uku da doriya, amma a ce matata washegari ta tafi aiki tun bakwai na safe har magariba.
Yarinyar nan ba ruwanta da halin dana wuni balle ta yi tunanin ta bani abinci. Tsakanina da ita sai dare, a hadu wajen kwanciyar barci.
Ba ta san ta kula da komai nawa ba balle ta alkinta, sannan tana fita da dan figigin mayafi cikin taron maza ta yadda har ba za ka bambance ta da mara aure ba.
Don haka aiki bana so, na soke shi. Sai ta zaba; aurenta ko aikinta!"
Ya aje kofi ya mike zai fita.
Mama ta ce,
"Koma ka zauna".
Ta dubi Hanifah wadda har zuwa lokacin sharar ido take. Mama ta ce,
"To ke kin ji, me kika fi so a ciki?"
"Mama ni duk ina so, auren da aikin".
"A'a, taura biyu ba ta tauno Hanifah, ya ya kuna matsayin ma'aurata amma shi yana gabas ke kina yamma saboda aiki? Idan don albashi ne ki fadi nawa kike dauka ya dinga baki duk wata, tunda baya so, amma ki tsaida hankalinki waje daya".
"Ni fa Mama ba don kudi nake aiki ba, ra'ayina ne da sha'awa. Amma na yarda ayi min 'transfer' zuwa can Lagos akwai 'branch' din mu". Mama tace
"anyi ba'a yi ba!"
Ya balla mata harara ya ce,

"To ni kuma Mama zan kara aure!".

Ita da Maman suka dago a zabure suka dube shi, sai dai firgitar ta fi yawa ga Hanifah, wadda ta ji kamar ya daba mata wuka a kahon zuci.
Mama ta ce, "Bana son rigima ka ji ko, 'yar matsalar da ba ta fi a warware ta ba cikin dan lokaci. Ka yi yaya da mata biyu kai da ba zaune kake waje daya ba?"
Ya yi wani irin murmushi ya ce,
"Sai in sa amaryar a gaba mu tafi, duk inda na dauke kafa ta maida tata. Ta bani kulawar da nake nema.
Ita kuma uwargida sarautar mata shugabar lauyoyin duniya ta zauna a (Magistrate Court) na garin Gombe, duk sanda ta samu lokaci sai ta kai min ziyara, don jaurar nan ta ishe ni, ba zan iya zuwa ba sai bayan watanni uku-uku. That is final!" Ya mike ya fita.

Mama ta dube ta cikin takaici,
"To ai kin gani irin abubuwan da nake gaya miki kina kunnen uwar shegu dani, kin san dai yadda aka lallaba aka yi auren nan, maimakon ki kwantar da kai ki yi ta biyayya, 'a'ah, sai ki yi ta wauta.
Mazan yanzu ana lallaba su ana kula dasu ma ya aka kare balle kana hutsanci? Ke kika sani, sai ki je ki gyarawa kishiya daki, don ni ban isa in hana shi aure ba saboda ina son ki, tunda Allah ya halatta masa".
Mikewa ta yi ta fada jikin Mama tana kuka,........
"Don Allah Mama ki hana shi, wallahi na hakura......."
Mama ta yi dariya ta gode Allah ta ce, "Ina! Kin baro gini tun ran zane, na rantse da Allah yanzu ba zai saurare ki ba. Da dai ba shi din bane".
Ta yi ficewarta ta tafi wajen Daddy ta barta tana koke-koken ta. Da ta gaji ta nufi 'side' dinta tana cewa a ranta.
"Wallahi ba zan bar aikina ba saboda da namijin da ba alkawari ne da shi ba, ko ina aiki ko bana yi ba fasa rashin mutuncinshi zai yi ba, balle wannan shugaban marasa mutuncin". Ta yi tsaki ta banko kofa.

Satinshi biyu da dawowa ya tattara ya koma bakin aikinshi. Sun ninka mishi albashi da sauyin wurin aiki, an mai da shi Niger Delta. Ya barta tayi ta lauyacinta, amma fa maganar karin aure, babu gudu babu ja da baya.

****




Sanda Muhaseen ta zo hutun karshen shekara wanda daga shi za ta shiga aji biyar na sakandire, Yaya Aliyun baya gida yana can Warri. Sai dai kusan kullum suna waya idan ya kira Mama tana hada su suyi ta hira, daga baya ma da ya kira Mama ko dagawa ba ta yi za ta bata.
Ya yi mata alkawarin waya mai kyau idan ta gama aji biyar, yanzu kam bai sonta da rike waya saboda tana hana karatu.
Ita dama bata sa a ka ba, duk da yadda hankalin mutane manya da yara ya raja'a a kai, ita sam ba ta dame ta ba, don karatun dake gabanta kadai ya ishe ta.

Muhaseen ta yi suna a FGGC Bajoga saboda hazakarta, ta kai ta kawo duk malamai da dalibai babu wanda bai santa ba.
Don haka a farkon shigar su aji shidda aka ba ta dankwalin 'Head Girl', wato shugabar dalibai na shekarar baki daya.
Yayan ya cika alkawari kamar yadda ya ce, ya saya mata waya mai kyau da tsada, sai dai ba ta zuwa da ita makaranta sai dai in ta zo hutu.
Da suka shiga aji shida kuwa basu kara zuwa hutu ba saboda shirye-shiryen SSCE, har sai da suka gama gaba daya.
Ranar da suka rubuta takardar karshe (Geography) makaranta ta shirya musu send up party. Sun sanya gown na education.
Duk 'yan'uwa da iyaye sun hallara. Sai dai Muhaseen ba ta cikin walwala duk da ga Daddy da Mama har da Asabe sun zo mata. Ba don komi ba kuwa sai don rashin halartar Yayanta, wanda ya ce da Mama ba zai samu zuwa ba, sakamakon ayyuka da suka yi mishi yawa. Amma so yake kawai yayi 'surprising' Muhaseen.
Bayan shugabar makaranta Hajiya Ramatu Ibraheem Alkaleri ta bude taro da addu'a. MUHASEEN ALIYU SURAJ, ita ce farkon wadda aka kira.
Cikin tsaftataccen Turanci ta yi sallama ta gaida iyaye, 'yan'uwa da malamansu. Ta yabi hazakar malamansu da yadda suka sadaukar da kansu don mai da su masu amfani ga al'umma.
Ta godewa iyayensu wadanda suka dauki nauyin dawainiyar karatunsu tsayin shekaru shidda ba tare da gazawa ba. Ta yi musu addu'a da fatan alheri, ta yi sallama ta koma sansanin dalibai 'yan'uwanta ta zauna.
Ita ce wadda aka fara kira domin karbar kyautar dalibar da ta fi kowa iya lissafi, iya Turanci, tsafta, sarrafa 'Computer' da 'Sport' daga hannun kwamishinan ilimi na jihar Gombe. Dr. Omar Abdallah (San-Turakin Dukku).
Kamar an ce da ita daga kanki, ta daga kai a hankali ta dube shi. Anyi sa'a shima ya dago don ya kalli wace ce wannan hazikar yarinyar.....?
Sai kyaututtukan dake hannunsa nade cikin wrapping sheet suka subuce suka zube a kasa.
Ta maimaita sunan shi da ta ji an kira....... Dr. Omar San-Turakin Dukku....gashi kamarsu daya, haske kurum ta fishi. Omar shine (UMARU),..... San-Turaki shine kakanta,..... DUKKU shine sunan garin su mahaifiyarta. Idan har memory dinta yana 'recalling' abubuwa dai-dai yana kuma aiki sosai.... to tsinkayenta gaskiya ne. Wannan shine BABA UMARU!.

Sai ta watsar da kayan ta sulale ta zauna a kan gwiwoyinta, numfashinta na sassarfa tana nuna shi da dan yatsanta ta kasa cewa komai.
Daga can cikin dakin taron Controller Aliyu Suraj, ya keto jama'a ya fito gaban dakin taron cikin shiga ta alfarma. Farar shadda kal babbar riga, 'yar ciki da wando da hular kube a kanshi.
Ya kamata ya mikar da ita tsaye ba ta fasa nuna mutumin da ke amsa sunan Umar San-Turaki Dukku da hannayen ta ba. Ta tafi luuu! Ta fada kirjin Aliyu, ba ta kara sanin inda kanta yake ba.

****










Ta farfado ne ta ganta a cinyar Mama, ga su nan dukkansu zagaye da ita, Mama, Aliyu, Daddy da Dr. Omar dake ta hawaye yana yi mata firfita da gefen babbar rigarsa.
"Bana haufi ke 'yata ce Muhaseen, ke ce kwaina da na wulakanta a duniya. Ina Halimatu? Don Allah, ina take?"
A sukwane ta tashi zaune ta yi bayan Mama ta buya,
"Bana sonka, bana sonka! Ni ba 'yarka ba ce, ka je

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login