Showing 18001 words to 21000 words out of 63435 words
suka barta daga ita sai halinta. Ta yi tsuru-tsuru a gefen gado, don ba ta san da fuskar da angon nata zai shigo ba.
Tana nan zaune cikin mayafi, tun tana duba agogo har ta soma gyanyadi. A nan ta bingire ta hau barci ba tare da ta ga keyar angon nata ba, dama kuma ta gaji sosai ta yi lis da gajiyar zirga-zirgar biki da ta sha.
Don haka take ta barci, ba ita ta farka ba sai karfe takwas na safe. Ta yi wanka ta dauro alwala ta ba da farali, ba ta da damuwar makarar tata don ba yau ta fara sallar asubahi da safe ba.
Ta yi kwalliya sosai cikin wani jan material da aka yiwa matsatstsen dinki riga da siket da kallabinsu. Ta yi kyau sosai, ita kanta ba ta san turare kala nawa ta fesa ba.
Ta fito falo tana saita talabijin, ya fito cikin shiri na wagambari mai launin sararin samaniya (sky blue), dinkin (boda) mai gajeran hannu, kanshi babu hula don har ba in wani 'occassion' bane bai fiya sata ba.
Sassanyan kamshin 'American Crew' shi ya fara bakuntar hancinta, kamin ta jiyo dakakken takun shi yana tahowa a kan 'marbles'.
Ta san wuce ta zai yi ba tare da ya kula ta ba, don haka zuciyarta ta ce
"Ki fara yakin kwatar 'yanci, tsoro ya kau, kun zama daya yanzu, ke halalin shi ce haka shima, don haka tsoro da kunya duk a ajesu a gefe'.
Don haka tana jin shi ya taho sai kawai ta rufe ido ta soma kuka ta durkushe a nan tana ta yi. Ta tare masa hanya, ya yi dan jim, sannan ya ce.
"Mene ne haka? Kukan me kike yi?"
Ta tsagaita kukan nata ta koma yi a hankali, kukkan kissa, mai raunata zuciyar namiji. Komai miskilancinsa kuwa.
"Ni tunda ka tsane ni to ka mai dani wurin Mama......".
Ya ce,
"Ai kin san hanya, ki tafi mana ko na daure ki? Kin san Allah, kada ki kara sani a gaba kina yi min kuka, don ba yankar naman jikinki nake ba. Kauce a nan tun ban yi kwallo dake ba".
Bai yi aune ba sai jin ta ya yi a jikinsa gaba daya ta mike ta rungume shi.
"Don Allah Yaya Haidar ka yi hakuri ka so ni, ko da da rabin-rabin son da nake maka ne. Ka yi tunani, ba fa ni na daurawa kaina kaunar ka ba, Allah ya jarabce ni.
Kada hakkina ya kama ka don Allah Yaya Haidar....."
Ta soma 'kissing' dinshi a duk inda bakinta ya kai, a wuya da fuskarsa. Ya gigice ya kidime. Karo na farko a tarihin rayuwarsa da jikinshi ya hadu da na mace, kuma matarshi ta sunnah.
Sabon al'amari ne da bai taba tsintar kanshi a ciki ba a gaba daya tsayin rayuwarshi. Ya kuma kasa yin wani motsi ko yunkuri na hanata. Amma ya kasa maida martani.
Sai da ta gama yamutsa mishi kaya sannan ta cika shi. Ya fice a hanzarce, ba tare da ya yi magana ba.
Ta-sani suka wuce shi da su Al'amin zuwa Darazo, daga nan sai Kumo, daga nan suka wuce Dukku ya yi ma Dr. Omar gaisuwar mai dakinsa.
Aminin Daddy ne sosai, tare suka yi karatun sakandire. Shi Dr. Omar ya wuce da karatu wanda har ta kai shi ga zama likitan Ilimi a jami'ar Bauchi, shi kuma Daddy ya fada kasuwanci.
Don haka bai samu dawowa gida ba sai karfe tara na dare. Kai tsaye cikin gida ya wuce wajen su Mama, can ya ci abinci tare da Muhasin da Mama. Ya kuma yi zamansa yana hira da Mama sai da ta kore shi tukunna.
Sanda ya shigo matar gidan ta yi barci, don ita dama barcinta karfe goma ne na dare, ko ta shirya ko ba ta shirya ba zai kwashe ta.
Tana mike cikin 'three seater' tana ta sharar barci ya wuce ta yana mamakin 'yar bingilar rigar da ta saka, wai ita ma nan ta iya abin jan hankalin namiji. Ya gyada kai ya wuce yana dariya yana cewa cikin ransa,
"Ai sha'awar ma Hanifah ba ta tasiri idan babu SO!".
[9/4, 12:57 PM] Asmau: Ya yi wanka kenan yana daura igiyar (pyjamas) dinshi ruwan toka. Ya yi addu'a ya yi light off, ya kwanta kenan sai ji ya yi ta banko kofar ta shigo, ta fada bayanshi ta makalkale shi.
"Yaya Aliyu tsoro nake ji.........".
Ta shige jikinshi sosai ya rasa ta cewa.
Ga lallausan kamshin amarci na fitinar hancinsa, ga tattausar fata kamar ta jariri yana ji a jikinsa. Sannan feeling din da Allah Ya halitta a tare da kowanne lafiyayyen dan Adam ya rinjaye shi. Al'amarin ya soma kokarin sauya salo, daga karami zuwa babba.
Sai da ta raina kanta ta yi dana sanin kankanbarta na kawo kanta inda ba'a nemeta ba. Lokacin da mai afkuwar ta afku, ihu ta saka tana zaginsa.
Bai juya mata baya ba, rungume ta ya yi tsantsan yana rada mata kalmar.
"I am sorry.....very sorry Hanifahhh.... And I can do anything right now to undo the hurt I caused you!"
Magana yake kamar ba Yayan ba, kuka ta ci gaba da yi tana kara kunna shi da salon kissarta.
Ko babu komi Hanifa ta yi daraja yau a idonsa, tunda ta kawo mishi kanta a kamilalliya, mai cikakkiyar alfarma, abin da bai zata ba.
Saboda yana yi mata kallon wadda idon ta ya bude da yawa. Ashe wayewar ba a nan take ba, kowacce diya mace da irin tarbiyyarta a zuci, yawanci yanayin rayuwa ke sa mata da yawa sarayar da mutuncinsu a waje.
Hanifah dai, koma dai yaya ne, ta shayar da shi mamaki. Ko don wannan abin bajintar da ta yi, ya yiwa kanshi alkawarin zama da ita cikin kowanne hali, ko da ya kara auren macen da yake so din watarana.
(Kalubale gare ku 'yanmatan zamani).
****
Tunda Muhasin take gidan ba ta taba dosar gidan Aunty Hanifah ba, domin ba ta bata fuska sam. Kai hasalima ta tsane ta, saboda kusancin ta da mijinta da yadda yake kula da rayuwarta. Ta warke sumul, ta zubar da sanduna.
Sai dai kuma tana dan dingisa kafarta ta hagu kadan. Aliyu baya son hakan, don haka ya soma tunanin kaita Jiddah a gyara kafar sosai.
To dan hutun nashi ya kare. Ranar lahadi ya bi jirgi ya koma Lagos, ita kuma Hanifa Danlami ya wuce da ita Bauchi ta koma makaranta.
Watanni ukku ya yi bai zo ba, sai dai kusan kullum yana waya da Mama ta ba ta suyi ta shan hira suna kwasar dariya.
Don Muhasin ba baya ba wajen magana. Idan ta yanko magana yana dadewa yana mamaki, don kalamanta sun girmi shekarunta.
Rannan take tambayarsa,
"Yaya Haidar?" Yace "na'am" "Wai matan ka nawa ne?"
Cikin mamaki ya ce,
"Me kika gani?"
"To na ga Aunty Hanifa baka tafi da ita ba, tana zuwa mana, to wa yake baka abinci a Lagos? Wa yake yi maka shara?"
Ya yi dariya ya ce, "Wannan ba matsala ba ce Muhaseen, ina da kuku (Jim), he's philipphino (dan Philipphine ne) ya fi Hanifah iya shara da girki".
Ta ce, "Abokin hira fa?"
Ya ce, "Ba hira na zo Lagos ba Muhasin, aiki na ke yi, tun safe har dare, wata ran ma a office nake kwana".
Ta ce, "Allah sarki Yaya na".
Can kuma ta ce,
"Idan ka dawo za ka dinga koya min karatun boko?"
Farin ciki ya kama shi,
"Da gaske kina son karatu Muhaseen?'
Ta ce, "Wallahi ina so".
Ya ce, "To, alhamdulillahi, yau kin shayar dani farin cikin da na dade ban yi ba, bani da lokacin da zan zauna in koya miki karatu, amma zan sa ki a makaranta".
A dokance ta ce, "Allah Yayana?"
"Na taba yi miki wasa ne?"
"A'a".
"To ina nufin abin da na ce. Ke dai ki mai da hankali, insha Allahu har jami'a sai kin je. Idan na zo karshen satin nan zan samu malamin da zai dinga yi miki 'lesson' kafin ki fara zuwa makaranta, don in sunyi miki interview ki ci".
Ta ce, "Allah ya kawo ka lafiya Yayana".
Hakan kuwa aka yi, a wannan zuwan da ya yi ya samu wani malami dan bautar kasa sunansa Kayode, Bayarabe ne. Suka tsadance zai dinga yi mata lesson tun daga A,B,C,D kullum da yamma. Ya sayo mata littattafai da tedt books, (children readers series) masu saukin koyon turanci da lissafi, Kayode ya soma aikinsa.
Asabar da lahadi kuma wani malamin ne daban da zai dinga koya mata karatun Alkur'ani da Hadisin Majma'ul Bahraini, Arba'una, Sirah, Tajweed da sauransu, shima da nashi albashin.
Mr. Kayode bai taba ganin hazikar yarinya mai kwakwalwa irin Muhasin ba. Duk abin da ya koya mata yau, washegari ya tambaye ta za ta kawo mishi babu gargada, ya yi waya yake baiwa Aliyu labari,
"Muhaseen is gifted...". Abin da yake yawan fada masa kenan. Aliyun na jin dadi a ransa.
Watanni biyar suka wuce, cike da ci gaba a rayuwar Muhasin, da nasarori ga Aliyu, cikin duk abin da yasa gaba.
Shima Malam Usaini yana yaba kwazonta, izifinta hudu kenan. Tana kuma iya kawowa a haddace ba tare da ta duba 'Alkur'anil- Azeem' ba.
Don haka a zuwan Yaya Aliyu wannan satin, makaranta ya kaita private. Sunyi mata duk gwaje-gwajen da ake yiwa dalibi kafin a dauke shi, kuma ba ta baiwa Yaya Aliyu kunya ba.
Aji biyar na firamare aka sanya ta. Sannan Mr. Kayode da Malam Usaini basu fasa yi mata lesson idan ta dawo ba.
Mama ma tana samun lokaci tana koya mata tsarki da alwala, da duk abin da dan musulmi ya kamata ya sani. Sai dai Allah ya saka musu da mafificin alherin sa.
***
A karshen shekarar aka yi bikin yaye su Hanifah. Aliyu bai samu halarta ba sakamakon tafiyar gaggawa da ta same shi zuwa Beijin din China. Mama da Daddy da Muhasin ne suka je mata can Bauchi, ta karbi kwalin LLB mai daraja ta biyu, suka juyo gida Gombe.
Kanta kamar ya fashe saboda ganin girman abin da ta yi, sai kuma jiran tafiya zuwa (Law School).
Satinta daya da dawowa gida Aliyu ya dawo. Akwatina uku cif ya takowa Muhasin da kaya fal 'yan ubansu-ubansu 'designers'.
Hanifah ta samu akwati daya, Mama biyu. Ta kasa boye mamakinta ta ce,
"Yanzu Muhasin ta fini kenan? Da za ka yi mata wannan uwar tsarabar ni ka hadani da 'yan wadannan?"
Wani irin tsinannen kallo da ya yi mata shi ya katse ta gabanin karasa babatun ta.
"......Kin aike ni ne?
To idan basu yi miki ba ki bani abina mana? Wawuyar banza, shashashar wofi! Ni na rasa me kika dauki yarinyar nan?
To ki ji in gaya miki tana matsayin kanwata ne, uwa daya uba daya. Kada ki kuskura in sake yi mata abu ki yi magana, don ni ba sa'anki bane. Kin ji na gaya miki".
Ta zumbura baki tana kunkuni, ya fita ya bar mata dakin yana cewa,
"Lallai yarinyar nan, kinga gadon barcina, da wannan ai da zagina kika fito fili kika yi kiri-kiri 'short and simple, stupid kawai".
Muhasin baki ya ki rufo, ta sa wannan, ta cire ta sa wancan. Mama na yi mata dariya. A haka ya shigo ya same su.
Ta ce, "Yayana Allah ya kara budi, na gode".
Ya ce, "It is my pleasure (jin dadina ne). Ta wani fannin kuma hakkina ne. Don haka kada in kara yi miki wani abu ki yi min godiya".
Hanifah tana wajen Mama, ya shiga dakinta yana neman safayar mukullan motarshi da ya ba ta ajiya.
Ya janyo lokar jikin gadonta kenan ya ga faket-faket din magunguna, ya dauka cikin mamaki yana dubawa. Pills ne (maganin tsarin iyali).
Ya kwashe su yana jinjina kai, takaici kamar ya kashe shi.
Ashe shi hotiho aka maida shi, yai ta bautar mace, yana ci da ita, yana sha da ita, yana daukar nauyin karatun ta mai tsada, yana biya mata bukatar ta, amma shi ba za ta iya daurewa ta haifa mishi 'ya'ya ba.
Ya kwashe duka ya zuba a aljihunshi yana cewa,
"Ba duka, ba zagi, ba tuhuma, amma kuma haihuwa sai kin yi ta, da izinin Ubangijin halitta".
Ya dau waya ya kira ta, "Ke kina ina ne? Ki zo ina da bukata....".
Tana so ta yi dariya, amma ta san ba ta isa ba, tayi kadan, don haka ta hadiye dariyarta ta ce, "Gani nan".
Dakinta ta fara shiga, ga mamakinta yau shine kwance a dakinta, yana waya ya yi kamar bai san ta shigo ba.
Yana kallon ta ta gefen ido ta jawo lokas tana ta dube-dube, fuskarta ta nuna ta shiga rudu.
Ya cillar da wayar ya fizgo ta ya ce, "Me kike nema ne?"
Cikin rawar murya ta ce, "Uhm...uhm! Panadol nake so in sha kaina na ciwo..."
"Zo in baki babban maganin ciwon kai, har ma da na ciwon jiki gaba daya".
Tana ji tana gani yau ba ta sha magani ba, gobe ma haka, jibi ma haka. Gaba daya ma a tsorace take da shi ta kasa sakar jikinta kamar da. Shikuma ya bi ya like mata kamar kaska yana ta addua Allah Ya bashi rabo albarkar Annabi, da ya ce "ku yi aure don ku hayayyafa in yi alfahari da yawan al'ummata ranar alkiyama".
A ganinta haihuwa ba tata ba ce yanzu da kuruciyarta. Da ta haihu nono zai fadi, shafaffen cikin da Aliyu ke matukar so zai yi tumbi ya yagalgale da nankarwa, sannan jikinta zai bude, to me ya yi saura da za ta burge Aliyun da tun fil'azal ba wani sonta yake ba, lallabawa take?
Don haka washegari ta tambaye shi fita ya ce, "Ina za ki?"
Cikin sanyin murya ta ce,
"Asibiti, an kwantar da Barrister Halisa zan je in duba ta".
Ya ce,
"To ki jirani bayan isha'i in dawo sai muje. Na gaya miki ban yarda ki dinga tukin mota ba indai ina nan, ko dai Danlami ya kai ki duk inda za ki, ko ki hakura".
Ta ce,
"Amma don Allah da can unguwa kake kaini da yau za ka ce za ka rakani?"
Ya girgiza kai, kamar ya yi dariya, ya ce, "Kika sani ko 'shopping' zan biya dake in yo miki?"
Ya rungumo ta yana 'kissing', kafin ya ce,
"Sai na dawo".
Ta bishi da kallon takaici, a lokacin da yake fita daga dakin. Dama kuma tana zargin shi da dauke mata magani, tunda dai shi magani ba zai dauke kansa ba, kuma ba kowa a gidan sai su biyu.
Ga wani kirki da yake yi mata kwana biyu, wai har zai sa ta a gaban mota su fita, bayan da ko kallon ta a dole yake yi kamar mujiya.
Bai dawo gidan ba sai bayan sallar isha'i, ya same ta a karamin falonta tana waya. Ba ta ga shigowar shi ba sam take fadin.
"Karya na yi dake, na kuma rasa ya zan yi da ita, cewa na yi zan je duba ki an kwantar dake a asibiti, don Allah in mun zo ki ce an sallamo ki ne..... na nemi 'pills' dina na rasa....shine nake so in je asibiti in samo wasu. To ya kasa ya tsare kwanakin nan ya hana ni fita....."
Ba karamar razana ta yi ba da ta daga ido ta ganshi a kanta. Wayar dake hannunta ta subuce ta fadi kasa, amma da yake lauya ce tuni ta waske, don ba ta da tabbacin ya ji ko bai ji ba.
"Ka ji ma wai an sallame ta ta koma gida...."
Zama ya yi a gefenta yana kallon ta a kaikaice, ya ce, "Allah ko? Juyo nan".
Ba ta yi musu ba ta juyo su kai facing din juna. Ya dauke ido a kanta, ya ja aji, kamar ba da mutum yake magana ba. Duk ta bi ta tsargu.
Can kuma bayan ya gama shaka, ya ce,
"To ke an ce kina sona, kema kuma kina fadi da bakin ki. To amma ina so in san wane irin so kike ikirarin kina yi mini?"
"Kamar ya ya?" Ta bukata cikin rashin fahimta.
Ya kara daure fuska, "Saboda ni dai na san in kana son mutum, to babban burinka shine ka hada jini da shi. Ni da na aure ki a bana son ki, ban kyamaci hada jini da ke ba sai ke?
Kike yi min asarar kwayayena masu muhimmanci a gare ni, kike yaudarata kina yi min asararsu. Don haka tattara ki tafi wajen Mama kamar yadda kike a da.
Ranar da kika soma sona, son gaskiya, har kike ganin za ki iya haihuwa dani, sai ki dawo. Ni ba bakon zafi bane, ba kuma sakarai bane da zan zauna da wadda ba za ta haifa min sanyin idaniya ba.....".
Ta soma kuka ta ce,
"Don Allah Yaya Haidar ka yi hakuri, wallahi ba haka bane, ni ba haka nake nufi ba.....
Wallahi Mama dukana za ta yi, don Allah ka yi hakuri ka yafe ni, wallahi ba zan sake sha ba.....!"
Ya ce, "Wallahi sai kin tafi...tunda ke munafuka ce mai ha'intar mijinta...Ki tashi ki tattara yanzun nan ki tafi tun baki sani na yi abin da zan zo ina dana sani ba. Kada ki sani in tsitstsinka igiyar da ba wani dadani da kasa ta yi ba".
Ta razana sosai, da yadda yake maganar; a fitittike, idanunshi a lumshe da tsagwaron rashin son wargi, kwayar idonshi a kaikaice, cike taf da rashin mutunci kuma ba sassauci, don haka ba ta kara magana ba. Ta share hawayenta ta mike ta nufi dakinta tana kuka.
Ta zauna gefen gado ta rasa yadda za ta yi. Ta ji takunshi yana tahowa, ai tuni ta zabura ta mike ta dauki mayafi ta yafa tana cewa cikin ranta....
"Gara dukan Mama, da rabuwa da abinda RAI da ZUCIYA ke SO!!!".
[9/4, 12:57 PM] Asmau: AMANA TA-2
Mama tana sassan Daddy don haka ba ta san da shigowar ta ba, sai da asuba ta shigo yin alwala a bandakin 'bedroom' dinta ta ganta tana barci a kan gadonta.
Ba ta tashe ta ba ta yi abin da za ta yi ta fita. Ba ta dawo dakin ba sai lokacin tafiyar Muhasin makaranta, wato karfe bakwai da rabi.
Nan ta iske ta ta tashi tana sallah. Ta sallami Muhasin da Danlami suka tafi, sannan ta dawo dakin ta taddata ta zuba uban tagumi a gefen gado.
Ta jawo 'stool' din madubinta ta zauna ta ce,
"Lafiya dai kika zo min daki kika kwana?"
Hawaye suka zubo, ta ce,
"Shine ya ce in taho".
Gaban Mama ya yi bala'in faduwa, ta ce, "Me kika yi masa?"
Cikin kuka ta ce, "Wallahi Mama ban yi masa komai ba".
Ta ce, "Um-um Hanifah, ruwa baya tsami banza....."
Ta ci gaba da kuka