Showing 27001 words to 30000 words out of 63435 words

Chapter 10 - Amanata HAUSA NOVE

ASMAU   

11 Nov 2024

19043

Gwaggo ya fesa mata labari mai dadi. Ai kuwa ta ce a zo a dauke ta ta duba Hanifah.
Mama kuma ta gayawa Innani, ita ma ta fesa wa mutanen Darazo.
Washegari Danlami ya je Kumo ya dauko Gwaggo, suka hadu ita da Mama aka yi ta jinyar mai ciki ana ririta ta.
Ko don wannan Hanifa ta yi sarandar barin cikin ta haifa musu, kada ta karya musu zuciya. Amma fa daga shi babu kari, don zuwa za ta yi a boye a cire mata mahaifar gaba daya. Tunaninta kenan.
****

Tsirfa iri-iri, su kuma da ta ce "Wash!" Za a ce, "Me ya faru?" Ta mai da Muhasin 'yar aikinta, daga ta yi mata dan-malele, sai ta toya mata dankalin Hausa, ta yi ta ci kamar Allah ya aiko ta.
Ba ta da abinci sai dankalin Hausa, kuma wai Asabe ba ta iya ba na Muhasin take so. Haka dai suke ta biye mata suna taya bera bari.
Satinsu biyu da zuwa jarrabawar su Muhaseen ta fito, ta ci makarantar 'yammata ta gwamnatin Tarayya dake Bajoga, Gombe, (FGGC Bajoga).
Sune first set wato daliban farko da sabuwar makarantar za ta dauka, za su fara karatu bayan sallah da sati daya.
Mama duk ta damu, ita dai ba ta so a barta a gida ita daya. Ta ce a maida ta Day School. Amma Muhaseen ta fi son makarantar kwana ita ma kamar yadda Yayanta yake so.
Dole ta sakar musu don sun rinjaye ta. Tun ana saura kwana goma Mama ta soma yi mata shirin tafiya.
Naira ta sha kashi wajen siyayyar Muhaseen, don su mantawa suke cewa ba su suka haifi yarinyar ba.
Naira dubu hamsin Aliyu ya baiwa Mama ta hada da tata gudunmawar ta yi mata siyayyar 'ya'yan gata. Muhaseen gigicewa ta yi sanda Mama ke nuna mata kayan, gashi sun hana ta yi godiya, amma sai da ta yin.
Ranar sallah sunyi hotuna duk gidan, anyi girke-girke na alfarma. Al'adar Daddy ce duk sallah ya gayyato abokansa da ma'aikatansa da abokan kasuwancinsa su ci abincin sallah tare.
Don haka yau ma kamar kullum, duk sun zo, sun cika falon baki. Aka shiga fiddo kabakin abinci iri-iri na gargajiya da na zamani, da abin sha kala-kala.
Mutum daya ne bai zo ba cikin wadanda aka gayyata, wato Dr. Omar San-Turaki Dukku. Duk Daddy ya damu, amma ba za ka gane hakan a fuskarsa ba.
Bai iso ba sai da aka gama walimar, amma ya yi waya ya shaidawa Daddy cewa tayar bayan motarsu ce ta fashe musu a hanya, Allah ya takaita babu abin da ya same su. Sai da aka canza tayar sannan suka samu suka karaso, don haka sanda suka iso duk jama'ar sun tafi.
Daga shi sai Daddy a babban falon bakinsa, suka soma hirar yaushe gamo irin ta shakikan abokai.
Kamin su gangaro kan rayuwar Dr. Omar, inda yake gayawa Daddyn har yanzu bai kara aure ba tun bayan rasuwar mai dakinsa Hafsatu. Shi yanzu tsohuwar matarshi ta lalle da suka rabu yake nema ruwa a jallo, har ya saka cigiyar ta a gidan rediyo da talabijin na Gombe da Bauchi, don ya tabbata alhakinta ne na wulakanta ta da abin da ke cikinta da ya yi Allah ya hukunta shi da rashin haihuwa.
Gashi a yau har ya manyanta, ba da, ba jika, balle magaji.
Daddy ya jinjina kai ya ce,
"Sau da yawa ku 'yan boko kuna da wata akida ta raina zabin iyaye, don kuna ganin kun fi su sanin abin da yake mai kyau a gare ku. Alhalin iyaye ba za su taba yin wani abu don su cutar damu ba, ba za su yi mana zaben da yake ba alheri bane a gare mu.

Tun a lokacin na gaya maka ko za ka kara aure, to ka bar Halima ka tausaya mata ka zauna da ita ko don albarkacin maraicinta. Amma ka yi kunnen uwar shegu dani don nima ka dauke ni dan kauye.
To yau wace riba ka ci, kuma dame ka burge da auren 'yar boko? Kai baka yi zaman jin dadi da ita ba har Allah Ya amshi ranta, kai baka haihu ba, kudin da kake samu basu amfane ka da komai ba, tunda babu wadanda ake nema domin su.
Sai dai ka yi ta tarawa tunda ba uwa ba iyali, karshenta ka mutu komai ya zama na baitul mali.
Don haka ina shawartar ka da ka nemo Halima ka bi ba'asin cikin da ta bar gidanka da shi. Baka sani ba watakila kwanka kenan a duniya, in ba haka ba wallahi-wallahi Umar hakki ba zai barka ka zauna lafiya ba".
Dr. Omar yasa hankici yana tsane hawayen da suka tsatstsafo masa. Ya yi nadama yau, har gobe ma yana yi. Ga matsayi, ga ilimin, ga mulki ga siyasa, amma ya kasa gano inda Halima ta shiga da tsohon cikinta.
Ko me ta haifa? Allah masani. Ya ce,
"Ka sani cikin addu'a Tobbacco, ina cikin wata jarrabawar Ubangiji. Aya iri-iri na ganta a rayuwata.
Na daki mace da tsohon ciki na saketa sakin wulakanci har uku, na wulakanta ta. Wadda na so ta haifa min 'ya'yan ita Allah bai bata ba.
Mahaifina har yau yana mai fushi dani saboda Halima, mahaifiyata ce kadai ta yafe min. Akwai wani makocina Malam Tanko wanda ya dauke ta a lokacin da na wulakanta ta, na nemi afuwarsa na kuma tambaye shi inda ta tafi ya ce wallahi-wallahi bai sani ba, don fakar idonsu ta yi ta gudu kada su kawowa iyayena abinda ta haifa. Amma yace 'ya macece.
Yanzu ban san ya zan yi ba, duk wata dabarata ta kare, don har kudi na sa masu yawa ga duk wanda ya kawo min labarinta amma duk a banza, yau shekaru biyar kenan ina cigiyar kamar malam ya ci shirwa".
Daddy ya ce, "Ba zamu fidda rai ba Dr. Omar, Allah (S.W.T) ya ce, "La taknadu min rahmatullah........." Ya kuma ce, "Inni gafurun rahimun".
Allah Ya ga zuciyarka ka gane kuskuren da ka yi har kana son gyarawa. To kada ka fidda rai, mu ci gaba da addu'a, kada mu gaza. Allah zai fiddo mana su insha Allahu a lokacin da bamu zata ba".
Har dare suna tare suna ta tattauna matsalolin rayuwarsu, sallah kadai ke tada su. Bayan sun dawo daga sallar isha Daddy ya yi kiran Mama a waya ta zo su gaisa da Dr. Umar, kuma a kawo abinci.
Mama ta yi lullubi ta dauki manyan 'warmers' guda biyu ta ce da Muhasin wadda suke aikin tare ta biyota da kwandon kayan marmari.
Suka yi sallama, Daddy ne ya amsa, shi Dr. Omar yana waya bai juyo ba sai bayansa take gani.
Dogon mutum bafillace, mai jiki kadan na hutu da jin dadi kamar dan shekara arba'in, amma a zahiri hamsin da biyu yake nema.
Muryarsa kawai ta ji yana magana da harshen turanci, sai ta ji tsigar jikinta na tashi. Ta dago da sauri tana kallon bayansa. Mama ta ce, "Jeki gida Muhasin ina zuwa".
Ta juya ta fita tana waiwaye. Ta so ganin fuskar wannan bakon mai sanyin murya da tada tsigar jiki tun ba'ayi tozali da shi ba.
Dr. Omar ya gama wayarshi wadda yake yi da mai girma Gwamnan Gombe a kan wata kwangila mai tsoka da yake so a ba shi, ya juyo ya amsa gaisuwar Mama, kasancewar shi mutum mai barkwanci yake tsokanarta da cewa.
"Maimuna da gaske dai kin kasa kin tsare kin hana Tobbacco daukar amarya, wai mene ne sirrin Gombawa ne?"
Dariya ta yi kadan ta ce, "Sirrin kake so ka sani Dr. Omar? To ka tambayi abokinka mana, ni ba zan sani ba sai shi din".
Ya juya ga Daddy, "To kai dan'uwa ka ji, me ya hanaka daukar sabuwa, wannan duk ta tsufa?"
Daddy murmushi kawai ya yi, ya ce,
"Don Allah ka zo ka ci abinci akwai inda zamu je fa".
Mama ta yi mishi sallama ta koma ciki. Ya dubi Daddy ya ce,
"Wai ina Haidar ne? Har yanzu yana Lagos din ne?"
Ya ce, "Yana can, amma yanzu yana nan sun zo hutun sallah shi da mai dakinsa. Nake jin yana 'side' dinsa bai san da zuwan ka ba da ka ganshi".
Ya ce, "Ai kuwa ina so na ganshi, don rabona da shi tun ranar daurin auren sa".
Daddy ya dauki waya ya kira shi ya ce ya zo dakin bakinsa yanzu.
Ko minti goma ba a yi ba Aliyu ya bayyana a falon cikin sallama. Kyakkyawan matashi mai kyau har da na ba da labari, yana sanye cikin kwalliyar sallar shi na farin yadin filted garai-garai mara kauri, amma ya baiwa naira na gugar naira har naira dubu saba'in baya. Engr. Aliyu Suraj kenan.
Dr. Omar ya mike tsaye ya tarbo shi ya rungume suka zauna a kujera, bai yadda da Aliyun ya tsuguna masa ba.
Ya ce, "Ya aiki, kuma ya iyali?"
Aliyu ya ce, "Alhamdulillahi Abba".
Ya ce, "To haka ake so, babu wata matsala in ce ko daga can wajen aikin?"
Ya ce, "Babu Abba, sai dai har yanzu ban samu 'transfer' dina zuwa Abuja ba, sun ce sai bayan na halarci wani 'course' na shekara uku a Tel-Abib. Har 'posting' din ya fito, wata mai zuwa zan tafi insha Allah".
Dr. Omar ya ce, "Ka je Tel-Abib din ka dawo, babu matsayin da ba za ka taka ba a wannan matakin. Ina yabawa da kwazonka Aliyu, Allah ya baka zuri'a dayyiba".
Aliyu na murmushi ya ce, "Ameen".
Ya kuma yi sauri ya gudu kada Daddy ya ce matarshi na da ciki yasa shi jin nauyin Dr. Omar.
Ai kuwa kamar ya sani, yana fita Daddy ya ce da Dr. Omar,
"Ai na kusa samun aboki ko amarya, Hanifahn na da juna biyu".
Dr. Omar ya yi hamdala ya ce, "Allah ya raba lafiya, ya bamu masu albarka".
Daddy ya ce, "Ameen".
Daga nan suka yi sallama Daddy ya shigo gida, shi kuma Dr. Omar a nan dakin baki ya kwana.
Da safe bayan sunyi sallar asuba ya wuce Bauchi, ko karin kumallo bai yi tare dasu ba, yana sauri kada ya makara a office.
****
[9/4, 12:57 PM] Asmau: Daga Mama har Daddy sun yanke shawarar kada a gayawa Aliyu Walida ta rasu. Muhaseen ta sha kuka har ta gode Allah.
Inda Allah ya taimake ta tana da hotunanta da wadanda aka dauke su tare ranar suna, da su ta koma makaranta.
Bayan rasuwar Walida da watanni biyar Hanifah ta soma karatu a Law School dake Lagos, ta girgije ta koma yadda take so kamar ba ta haihu ba, ta koma 'yar gayunta.
Sai dai har ranta tana son 'yarta, don ba yadda za ta yi ne. Allah ma ya so ta ba ta kai ga cire mahaifar ba.
Haka rayuwarsu ke tafiya, kowanne ya fuskantarwa rayuwarsa ci gaba. Ga Muhaseen, rayuwa na zuwar mata da kyakkyawan sauyi, ga ilimi ga girma ya fara shigarta, ga kyau ga tarbiyya, sannan ga nutsuwa irin ta daliban Bajoga
Yanzu haka sun fara (JSCE Exams), ya yin da Hanifah ta gama karatun ta, ta fito da kwalin cikakkiyar 'Lawyer' tareda takardar daukar aiki a (Lawyer's Chamber, Gombe State), saboda kyawun takardunta. Ana sanya ran dawowar Aliyu gida watanni biyar masu zuwa.
Sun dauka Aliyu bai san da rasuwar ba, amma ya sani tun sanda Danlami ya yi masa waya yana yi masa ta'aziyya. Amma tunda basu gaya mishi ba sai shima ya kyale su, kullum da hoton yarinyar yake kwana yana kallo cikin wayarsa, har kuka yake yi. Daga baya ya yi tawakkali ya ci gaba da yi mata addu'a.
Su Muhaseen sun gama jarabawarsu ta kammala karamar sakandire lafiya, sakamako na fitowa suka wuce 'senior section' a nan Bajoga.
Burin Muhaseen shine ta zamo 'yar jarida, ta dinga karanta labarai a gidan talabijin saboda tsananin kaunarta da news-caster Fatima Abbas Hassan ta NTA Abuja.
Sannan MU'AZZAM KANTI na CNN (Alkawari Bayan Rai) yana burge ta, kamar yadda Jamila Tangaza ta BBC London ke sanya ta cikin shauki.
Ga kuma kawar Sumayyah Abdulkadir, Badariyya Tijjani Kalarawi ta gidan rediyon Freedom da ke Kano, duk tana son su, suna sanya mata 'interest' akan 'mass-media'.
Don haka ta fi ba da himma a Hausa da Turanci, gashi a 'science class' take, don tana ganin sune za su kaita ga cikar burinta. Wato kwarewa a kansu zai sa ta zama 'yar jarida idan Allah Ya yarda.

*****




Shekara kamar kwana, a yau jirgin
'Argentina Airlines' ya sauke Engr. Aliyu Suraj Kumo, a filin jirgin saman Murtala Muhammed dake Lagos. Ba tare da ya fada a gida cewa zai iso ba.
So yake ya baiwa kowa mamaki, musamman Muhaseen, duk da bai da tabbacin tana gida ko tana makaranta.
Kwanan sa biyu da dawowa yana gidansa na Lagos, yana office yana ciccike takardun dawowar shi bakin aiki, ko waya bai musu ba. Ranar alhamis ya gama duk abin da yake yi, ya biyo jirgin (Bell-Biew) zuwa gida, Gombe.
Hanifah tana wajen aikinta ba ta dawo ba, don kullum sai shidda na yamma take dawowa. Mama da Asabe ne kawai a gidan, suna kitchin suna hada abincin rana.
Danlami da buzu maigadi suka yi sallama a kofar falon suka soma aje dankara-dankaran jakunkuna bakake wuluk a falon.
Mama da Asabe suka fito daga kicin, Mama na kokarin tambayar Danlami daga ina wadannan iyayen jakunkuna?
Sai ya sanyo kai cikin falon cikin bakaken 'suit' da bakin gilashin PRADA a idanunsa, dauke da sallama a bakinsa.

Gaba daya ya rikide ya juye ya koma (Argentinian), bai da maraba da su. Fari dan sardidi, wato ba mai kiba ba, sannan ba mai rama ba. A goshinshi tabon sujjadah ne ya yi baki sosai, ya fito rangadadau.
Gaba daya falon Mama ya amsa sassanyan kamshin 'Onde-Vertige'. Gashin kansa baki sidik na Fulanin usli, ya kwanta lambam a kan wuyansa sai sheki yake.
Karan hancinsa ya kara fitowa a tsakanin dara-daran idanunsa, ya kara kwarjini sosai na alamun hutu da kwanciyar hankali. Yana zuwa gaban Mama, rungume ta yayi, ya sumbaci goshinta.
Kunya ta kama Mama, duk da haka ba ta bar murmushi ba. Da daya kwal da Allah Ya bata, tana son shi sosai, in dai a kanshi ne aje fillacinta take a gefe, babu zancen fulako.
Ta ce, "Kai kam, baka kyauta ba, za ka taho amma ba za ka sanar damu ba. Gashi ba a shirya maka komai ba, ba a gyara gidanku ba. Mai dakinka bata nan, ina amfanin haka?"
Ya yi murmushi ya zauna cikin kujera ya sarke yatsunshi ji kake kas-kas, suna kara. Ya ce, "To ai ni Mama ba wajenta na zo ba, ke nake son gani, kuma gashi na ganki lafiya kamar yadda na barki, kin kara kyau kin kara kuruciya, sai Alhamdulillahi".
Dariya ta yi ta koma kicin, Asabe ma da take jiyo su daga kicin dariya ta yi. Ta fito tana yi mishi sannu da zuwa.
Ya ce, "Asabe ina 'yar gidanki ne? Ban ji duriyarta ba".
Ta ce, "Wai MUHASEEN?"
Ya lumshe ido, ya daga mata kai.
"Tana makaranta, ba ta dade da komawa ba. Idan ka ga Muhasein za ka sha mamaki, ta yi tsaho ta girma saura kadan ta kamo Hanifah".
Ya yi murmushi, wani abu na dukan zuciyarsa, ya ce,
"Ki ce gobe zamu tafi Bajoga".
Ta ce, "A'ah, sai ranar ziyarar dalibai ake zuwa, in ba da wata muhimmiyar larura ba".
Cikin ranshi ya ce,
"Ba zan iya ba Asabe, gobe zan je ko da za su kore ni".
Daddy ya dawo cin abincin rana kamar yadda ya saba, ya tadda bakon da bai zata ba. Ya bude baki yana dariya, da sauri Aliyu ya rungume shi ya daura kai a kafadun Daddy yana cewa,
"Alhamdulillahi".
Don haka farin cikin dake zuciyar wannan family a yau, ba zai fadu ba. Suka ci abinci tare, suka shiga tattauna hirar bayan rabo, yana baiwa iyayenshi labarin rayuwarshi a Argentina; Nasarorinshi, da matsalolin da ya gamu da su.
Muhimmi shine rashin iya harshensu, don ba Turanci suke yi ba. Shi kadai ne daga Nigeria cikin wadanda aka tura 'course' din daga ma'aikatun Custom na duniya.
Sai da kyar ya samu wani aboki mutumin Spain mai suna, Roy, ya iya Turanci, shine ya dage wurin koya mishi 'Spanish' da 'Araucano' da suke amfani da shi.
Yake basu labarin Argentina kasa ce da matasanta suka fi mai da hankali a kan sana'ar kwallon kafa na duniya, (world-cup) shima ya yi sosai, har karyewa ya yi, watanshi guda yana jinya, don ma suna da kwararrun likitocin kashi.
A lokacin ne Mama take sanar da shi Walida ta koma, tun bayan suna da kwana biyu, ya yi hakuri da sannu Allah zai ba shi rayayyu masu albarka, insha Allahu.
Sai ya yi murmushi ya ce,
"Na fa sani tun lokacin Mama, Allah yasa mai ceton mu ce".
Gaba daya suka ce, "Ameen". Har Daddy.

Barrister Hanifah Abdullahi Darazo, ta shigo gida a gajiye likis, tana sanye cikin bakaken kayansu na lauyoyi da hularsu, ta zagaya dan siririn mayafi baki a wuyanta, tana rungume da takardu da jakar hannunta.
Ba kowa a falo duk sun tafi sallar magariba. To amma kamshin da take shaka a falon ya sa ta kusa sumewa don dadi da farin ciki.
Ta watsar da komai dake hannunta a kasa, hada da takardunta kuwa, ta sheka da gudu dakin Mama. Mama na sallah, nan ta ga dakin fal sabbin jakunkuna da kaya iri-iri anyi baja-baja da su. Tuni ta nemi gajiyar dake damunta ta rasa, ko ba ta tambaya ba bakon Argentina ne.
Mama na yin sallama ai kuwa ta fada jikinta kamar wata karamar yarinya tana dariya. Mama ta ce,
"Kin ga daga ni bana son sakarci, maza tattara ku je ke da Asabe ku gyara gidan yadda ya sawwaka kafin Allah ya kaimu gobe a gyara sosai".
Ta mike daga jikin Mama ta fita da gudu tana kwalawa Asabe kira. Mama ta ce,
"Oh! Ni Maimunatu, Hanifah babu ta ido!!".
Cikin dan lokaci Asabe ta ci karfin gyaran gidan, da yake dama ba wani kura ya yi ba, don duk bayan sati biyu ana sharewa a goge ko'ina a wanke bayan gida a kunna turare a ko'ina. Ita kuwa uwargida sarautar mata ana can ana ta kalailace jiki kamar za a canza fata, zuciyarta kamar madara.
Karfe goma na dare Engr. Aliyu ya shigo, ya rufe ko'ina ya shiga dakinsa ya yi wanka, ya zuba pyjamas masu taushi yana fesa turaren barci (Dior, midnight poison). Ta turo kofar ta shigo.
Ta tafi da gudu ta rungume shi, shima ya shafi kanta ya ce, "Lauya, manya!".
Ta ce, "Controller kuma Engineer ai kune manya!!".
Ya ce, "Ko?'
Ta ce, "Kwarai, I terribly missed you Yaya Aliyuhh......."
Ya rungume

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login