Showing 24001 words to 27000 words out of 63435 words

Chapter 9 - Amanata HAUSA NOVE

ASMAU   

11 Nov 2024

19037

gudu ta rungume shi ta baya, abin da ba ta taba yi ba.
A sanyaye ya juyo shima idanunshi sun kada sunyi jawur, ya rage tsawo shima ya rungume ta ba tare da ya san lokacin da ya yi hakan ba.
Hanifah na gefe tana kallon ikon Allah, takaici kamar ya kashe ta, ya yi ta maza ya sake ta ya ce, "Is o.k Muhaseen, makaranta ce ba wani waje ba, ko yaushe kike son ganin Mama za ki ganta, ba za ta wuce wata daya ba ta zo ta ganki ba.
Abin da nake so da ke Muhaseen shine, ki tsaya, ki yi karatu, sosai, yadda duniya za ta yi alfahari dake.
Ban da wasa ban da kawayen banza. Zan yi tafiya ta lokaci mai tsawo zuwa Tel-Abib, ba zan dawo da wuri ba. Sai dai kullum ki sanya a ranki cewa ina tare da ke, ina kallon yadda kike ba da himma wajen karatu. Maza jeki Muhaseen, Allah Ya hada fuskokinmu da alheri".
Tana kuka sosai ta juya ta tafi, tana waiwaye, tana tuntube, yana daga mata gira, yana murmushi. Da ta kara waiwayowa sai ta daga mishi hannu, ta juya ta bi Metron din dake jiranta, ba ta kara waiwayowa ba.

****
"Nifa bana son tafiyar nan cikin Yahudawa, makiya addinin Allah da musulmi, wanne irin 'course' din arziki ne da sai a Isra'ila za a yi shi? Ba Turai ba, ba Amurka ba, kuma har tsayin shekaru uku. Ni dai ban amince ba".
Daddy kenan, yake magana da gudan danshi Engr. Aliyu Suraj Kumo, wanda ke zaune a gefen Daddyn bisa carpet ya sunkuyar da kai yana wasa da 'yan yatsun kafafun shi.
A sanyaye ya ce, "Tunda baka so Daddy sai a bari, dama kasashe biyu ne suka bani zabi, ko Isra'el ko Argentina, inda nake so nan zan zaba".
Daddy ya dan saki fuska ya ce, "Ko da na ji, amma me ake da Isra'ila makiyanmu? Makiya Manzonmu? Duk wani musulmi wanda ya yarda da Allah daya ne neman tsari yake daga sharrin su, amma ba ya tura kanshi cikinsu ba".
"To Daddy ka amince da Argentinan?"
"Na amince ka je, amma tare da matarka ko?"
"Ya ce, "A'ah, ka manta da lalurar ta ne Daddy? Za ta zauna a Lagos saboda za ta fara karatun ta a Law School".
Daddy ya ce, "na manta kam. Amma sai bayan ta haihu za'a je karatun ko?'
"A'a, Daddy ba za su jira ta ba, sai dai in dagawa za ta yi zuwa shekara mai zuwa".
Daddy ya ce, "Sai dai a dagan, don ni ba zan bar mace mai yaron ciki ta tafi wata uwa duniya ba, wa zai kula da ita?"
Aliyun ya yarfar da hannu, "Sai yadda ta gani".
An daga tafiyar Hanifa Law School sai bayan ta haihu, za ta zauna nan wurin Mama har sai Allah ya sauke ta lafiya.

Ranar lahadi, sha biyar ga watan Aprilu, Aliyu ya tashi zuwa kasar Argentina, cikin rakiyar iyaye, matarsa da kakarsa, kowa ya juyo gida, cike da dimbin kewarsa.
Ga iyayensa shi mutum ne da suke alfahari da haihuwarsa. Gashi dai shi daya kwal, amma ya cike musu gurbin 'ya'ya goma. Basu taba kukan rashin wadatar 'ya'ya ba
Yana yi musu biyayya tamkar ya kwanta musu.
Ga matarshi shi miji ne abin alfahari, duk da tana da yakinin ba wani sonta ne yasa yake zaune lafiya da ita ba face biyayyar iyaye, amma kuma bai taba wulakanta ta ba, balle ya tauye ta ta wani bangare.
Duk da yana da zafi, amma yana kwatanta adalci cikin auratayyarsu. Da wuya ya yi mata fada sai dai ya bita ta ruwan sanyi ya ladabtar da zuciyarta da kuruciyarta.
Don haka bayan sun dawo rakiyar shi daga Airport, kowannensu sukuku yake, babu wanda ya nemi abincin dare, kowanne dakinshi ya nema, kewa kamar ta kashe shi. Kada Gwaggon Kumo ta ji labari.
Don haka washegari da sassafe ta tada balli a maida ta Kumo, gidan babu dadi, tunda babu Gadanga kusar yaki.

****








MUHASEEN A FGGC BAJOGA


Rayuwar Muhasin a makaranta, rayuwa ce da ta zo mata da sabon sauyi ta kowacce fuska. A gida komai Mama ke mata, sabanin a nan da kowa shi zai kula da kanshi.
Muhasin jaruma ce a fannin karatu, bata wasa. Ga son tsafta, kullum sai ta wanke uniform dinta ta goge. Gadonta kullum tsaf-tsaf abin sha'awa. Ba ruwanta da kowa karatu kawai take.
Mama ta san principal dinsu Hajiya Ramatu, da yake 'yar Gombe ce, tare suka yi makarantar sakandire. Don haka ita aka bawa amanar Muhaseen tana kula da ita sosai.
Kullum ka'ida ne kafin ta shiga aji sai ta je ofishin Hajiya Principal kamar yadda suke kiranta sun gaisa, ta tambaye ta ko tana da matsala?
Sai ta ce, "Babu". Hajiya kuma ta ce,
"To maza tafi aji Muhaseen kada malami ya riga ki shiga".

Ranar visiting Mama ce ta zo, Danlami ya kawo ta. Ta yo mata girke-girke masu dadi, soyayyun kaji fal bokiti. Ita Muhaseen ba ta damuwa da rashin kirkin Hanifah, tana sonta sosai.
Don haka yau ma sai da ta tambayi Mama ya jikin Aunty Hanifah? Ta ce ta ji sauki tuni, tana gida. Ba ta gaya mata cewa kin zuwa ta yi ba.
Muhaseen ba ta da wata takamaimiyar kawa, sai dai tana gaisawa da 'yan dakinsu da 'yan ajinsu.
Haka kawai ne dai ba za ta kula ka ba, idan ba wata hulda ce ta hadaku ba. Don haka da yawan 'yan dakinsu suke daukar ta wata mai girman kai, kasancewar ta kyakkyawa kuma 'yar masu da shi sosai, ko daga irin abincinta da kayan amfaninta.
Hatta bargonta abin kallo ne, domin takanas Mama ta taho mata dashi daga Dubai. Duk da cewa yawanci daliban duk 'ya'yan masu akwai ne da manyan 'yan boko.
Kasancewar FGGC Bajoga sabuwar makaranta a lokacin, tana da tsari mai ban sha'awa da hazikan malamai, wadanda dukkanin su 'degree holders' ne (masu digiri), da edperience a kan koyarwa. Basu yarda dalibansu suyi magana da Hausa ba sam, don haka cikin dan lokaci harshen Muhaseen ya juye da turanci zallah, ko gida ta zo hutu duka rabin maganarta da Turanci ne, ko da wa take magana kuwa. Ita babu ruwanta. Ko Goggo ce.

Sunyi hutun karshen shekara ta zo gida ta tarar Aunty Hanifah ta haihu kwana uku da suka wuce, an samu 'baby girl' mai kyau kamar ubanta.
Sai dai ta yi duhun Hanifa, ga suma yalala a kanta, yarinyar ta shiga ran Muhaseen sosai, ko don kamanninta da mahaifinta.
Ta bi ta like a dakin da Hanifah ke jego, tana faman daukan jaririya, da mikawa baki masu zuwa barka.
Amma Hanifan haushinta take ji kamar ta shake ta, duk sanda kawayenta suka zo sai ta kore ta, har wasu daga ciki kan ce,
"Haba, ke kuwa ki kyale ta mana, yarinya mai son kanwarta". Sai ta yi tsaki ta ce,
"Ta fiya kankanba ne".

Duk gidan babu wanda ya san Hanifa ba ta baiwa baby nono sai madara, don idan Mama ko Gwaggon Kumo suna tare da ita, sai ta kara ta a jikinta kamar tana ba ta nonon.
Tuni an tutturawa angon karni hotunan baby ta waya. Ranar talata aka yi suna, baby ta ci sunan Gwaggon Kumo (Hassana), kuma Gwaggon ta roke su kada su rufe su kira ta Hassanarta.
Amma Mama ba ta iyawa, don haka take kiranta Walida. Maijego da jaririyarta sun sha gata, kayan baby har rasa inda za a zuba su a kai da turamen atamfofi.
Ba daga abokan Daddy ba, ba daga kawayen Mama ba, ba daga Dr. Omar ba, ba daga kawayen maijego ba, balle kuma daga Mama da Daddy.
Shima uban baby kudi ya turo masu yawa ya ce ayi musu duk abin da ya dace.
Bayan suna da kwana biyu Walida ta tashi rannan da dare ta soma kuka. Tun tana yi kadan har ta shiga callarawa iya karfinta.
Hanifah ta fito daga toilet ta cirota daga cikin 'net' sai ta ga wata kumfa tana fitowa daga bakinta. Ga madarar data bata kafin ta shiga wanka tan dawowa ta hancinta.
Ta sureta da gudu zuwa dakin Mama daga ita sai tawul a daure iya cinyoyinta. Mama na zaune tana lazimi Hanifah ta shigo da ita tana faman mimmikewa ta dora ta a cinyar Mama tana ihu.
Mama ta ce,
"Suhbahanallahi!" Ita ma ta gigice ta ce da Hanifah, "Sako riga maza mu tafi asibiti".
Ta jefa 'yar a baya ta goya, ta suri mayafi ta yi waje. "Danlami! Danlami". Kawai take kira. Ya taho da gudu ya jawo mota, tun bai san abin da ya faru ba. Hanifah ta fito riga daban zani daban mayafi daban suka tafi.
Suna tafe a hanya Mama ta ji jikin yarinya dake goye a bayanta ya saki, sannan kirjinta ya daina bugawa. Saboda tsoro da firgici sai ta ki sakkota kada ta je ta ga abin da ya fi karfinta. Ba ta sauke ta ba sai a hannun likita.
Da sauri yasa abin awonsu a kirjinta ya kama tsintsiyar hannunta. A sanyaye ya dube su ya ce, "I'm sorry.....she is no more!"
Wata kara da Hanifah ta saka ta sulale nan a gaban likita ta sume. Nurse biyu suka shigo suka dagata suka dora a gado suka shiga ba ta taimakon gaggawa.
Mama ta share hawayenta da gefen mayafinta, ta kunshe gawar 'yar ta dauka ta yi waje, ta samu Danlami a waje ta ce,
"Mu tafi. Allah Ya karbi abinSa".
Ya yi salati ya sanar da Ubangiji ya ce, "Wayyo ubangidana, babu rabon zai ga abin da Allah Ya ba shi, Allah ya kawo wasu masu albarka, ita kuma Annabi Ibraheem ya san da zuwan ta".
Mama ta ce, "Amin".
Duk dauriyar Daddy sai da ya yi hawaye, Walida ta yi kwanan keso. Washegari da safe aka yi jana'izarta. Mama ta je asibiti ta taho da Hanifah, ta farfado sai kuka take tana sambatu.
"......Dana sani da na baki nono. Yanzu haka zuciya kika hadiya saboda na hanaki nono, kaicona!"
Mama ta yi turus, tana sauraron ta, ta ce, "Me kike cewa Hanifah?"
Ta rushe da kuka ta ce,
"Ban taba bata nono ba Mama, gashi yanzu ina dana-sani......."
"Saboda me kika hanata?"
Ta yi shiru ba ta yi magana ba. Mama ta sake tambaya a fusace,
"Na ce me ta yi miki kika hanata abincin ta?"
Ta share hawaye ta ce,
"Tsoro nake kada nonon ya fadi ya yi min kishiya...."
Mama ta ajiye mayafi ta rufe ta da duka titim-titim ta ko'ina, ta soma ihu Nurse suka shigo da gudu suka rike Mama suna ba ta hakuri, fadi take
"Ku barni in kashe yarinyar nan, kafin bakin cikinta ya kashe ni.....". Ta fashe da kuka.
Doctor da kanshi yake baiwa Mama hakuri, cewa take
"Ina amfanin boko? Boko bai yi ba kam, in dai haka wasu shashashai suka dauke shi".
Ta gaya musu abin da Hanifah ta yi. Duka suka hada baki "Kash! Kin yi kuskure Hanifahh, babu wani likitan duniya da zai baki shawarar kada ki shayar da danki nono. Wai don kada halittar ki ta sauya.
Yana da sinadari masu matukar amfani ga rayuwar jariri, balle sabuwar haihuwa. Shine abincin da Allah ya halatta masa ya tsaftace shi, ya zamar dashi kariya daga cututtukan da ke saurin kashe jarirai.
Namiji ba dan goyo bane Hanifah. Ko nonuwanki ne suka fi na kowa tsini a duniya in ya so kara aurenshi zai yi wallahi baki isa ki hana shi ba.
Ban da wauta irin taki 'ya'yan da za ki haifa masa ma ai sune darajarki da tutarki a zuciyarsa. Nan gaba kada ki sake wannan kuskuren".
Mama tana kuka ta ce,
"Don Allah ku rabu da ita, baku san halinta bane. Ai haihuwar ma ba da son ranta ta yi ta ba. To kuma suman me da kukan me za ki yiwa mutane yanzu? Ba haka kike so ba? Sai ki ci gaba da gayunki da bokon ki, babu mai yi miki kashi da tumbudi, shi kuma ya zo in samo mishi mai kaunar shi ta haifa mishi sanyin idaniya".

****
[9/4, 12:57 PM] Asmau: Su Muhasin ana tsaka da jarrabawar fita primary, don haka zama bai ganta ba ita da sabon malaminta Hamisu. Shima dan bautar kasa ne daga Katsina, don Kayode tuni ya gama ya koma garinsu Abeokuta.
Sam ba ta jin wuyar jarabawar saboda Hamisu har ya fi Mr. Kayode iya lesson, don shi Bahaushe ne yana fassara mata kalmomin da ba ta sani ba da harshen Hausa.
Suka yi jarrabawarsu lafiya suka gama, sai jiran sakamako. Shi kuma Malam Usaini ya ci gaba da ba ta karatun addini sosai da Alkur'ani a cikin zaman jiran fitowar jarrabawar.
Sau biyu ma yake zuwa, da safe da yamma. Don har albashi Mama tasa Daddy ya kara masa.
Don mutanen Ikko yau watanninsu uku ba a ga keyarsu ba, sai dai kusan kullum suna waya, kuma Mama tana kiran Muhasin ta ba ta wayar su yi ta hirar su da Yayan nata tana ba shi labarin jarrabawarsu, da irin yadda ta tsarge ta, da kyautar kwamfutar yara da Uncle Hamisu ya ba ta saboda kwazon ta, in ji shi.
Ya ce, "To me kike koya a cikin kwamfutar?"
Nan da nan ta ce dashi, "Akwai games da yawa, akwai Cartoons, akwai National Anthem, akwai Mavis Beacon....Dictionary......Encarta da abubuwa da yawa".
Ya ce, "Kai! Allah ya sakawa Malam Hamisu da alheri, har babur zan saya masa insha Allahu".
Ba su zo gida ba sai da Azumin Ramadhan ya kama suka tattaro suka taho. Ranar kuma sunyi waya sun sanar da Mama tahowar su.
Don haka yau Mama buda baki na musamman take shiryawa a gidan. Tun karfe biyun rana suka fara aiki su duka ukun, Mama, Asabe da Muhasin. Basu kammala ba sai karfe biyar da rabi na yamma.
Muhasin ta yi wanka ta shirya cikin Pakistan riga da wando da mayafinsu 'yan kasar India, kalar deep orange, ta sha kunshi jawur dashi a 'yan yatsunta. Ga kitso yiri-yiri, don Mama ba ta taba barinta tasa relaxer a kanta ba sai dai a yi mata kitso.
Ta yi kyau kamar Ba'indiyar gaske, tana yanayi da (Priyanka Chopra) sosai, musamman idan ta yi dariya, duka gefen kumatunta lotsawa suke yi ciki sosai ka ji kamar ka sace ta ka gudu.
Karfe shida da rabi Danlami ya shigo da jakunkunansu, sun iso kenan. Da gudu Muhasin ta yi waje tana yi musu sannu da zuwa.
Wata harara da Hanifah ta jefa mata sai ta kashe gwiwarta, amma ba ta fasa karbar jakar Computer dake hannun Yaya Aliyu ba.
Binta yake da kallo cikin mamaki, yarinya kamar kazar Agric, kamar ana janta saboda tsayi. Ta cika sosai a watanni hudu da ya kwashe bai ganta ba, kyau kamar sai ka wanke hannu kafin ka taba ta. Murya mai zaki kamar mazarkwaila.
Ya kama hannunta ya rike cikin nasa ya ce, "Kin kara girma Muhaseen......."
Ta yi dariya ta ce, "Wallahi kaima ka kara tsaho".
Suka shiga falon Mama suna dariya abinsu, kai da ganinsu ka san yau cikin farin ciki suke.
Ita ma Mama bakinta har kunne. Tana tsaye tana kallon kofar da Aliyu zai shigo, watakila ba don ya girma ba yau da goya shi za ta yi.
Bai zauna ba a gurguje suka gaisa ya nufi masallaci don Daddy ya je Umarah tun farkon Azumi. Haka yakeyi duk shekara ya shiga halwa. Ita Hanifah dakin Mama ta yi ta kwanta don ashe wai ba ta da lafiya.
Sai da aka idar da sallah sannan ya shigo, aka hadu gaba daya a 'dining' aka yi buda baki da girkin Mama da yai 'missing' har yana zuba santi.
Don girkin Hanifa sunansa "A ci kar a mutu". Abin da ta kware a kai shine, dafa Indomie da soya kwai. Amma ko dankali ta soya wani danye wani ya soyu za ka ji.
Yake baiwa Mama labari. Ta ce, "Ni ai bani da laifi, Allah Ya gani ba yadda ban yi da Hanifa ba kan ta dinga bina kicin amma sai ta ce karatu za ta yi, kamar ita ta fi kowa son boko.
Don haka ina ganin zan baku Asabe ku tafi da ita, ba girkin da ba ta iya ba. Na gargajiya dana zamani. In kuma bakwa so to ka dauki kuku wanda ya samu 'training' din makaranta a kan girke-girke".
Ya ce, "Ba zan rabaki da Asabe ba Mama, don tunda na taso na ganku tare. Tana yi miki komai saboda Allah da zuciyarta daya, kuma tana son Muhasin, ita ma Muhasin na sonta, ko Muhaseen?"
Ta ce, "Kwarai, amma ba ka ce 'boarding school' zan je ba? Ku tafi kawai sai Mama ta nemi wata, in na zo hutu in dinga taya ta kamar yadda nake taya Asabe, ko Mama?"
Ta ce, "Haka ne Muhasin, su je kawai, da ya dinga zama da yunwa ko bin gidan abinci, ana cin kudinsa a banza kullum ta Allah".
Ya yi murmushi ya ce,
"Zan yi tunani kafin mu koma, don muna nan har bayan sallah insha Allahu".
Tunda suka zo Hanifa ba lafiya, haraswa take ta kelayawa a kan carpet din Mama. Muhaseen na aikin gogewa da fesa room fresh, daga baya ma carpet din ta fita dashi daga dakin gabadaya. Sabida karni. Har ruwa aka kara mata leda biyu.
Mama take tambayar sa "Kun je asibiti kuwa a kan wannan haraswar ta Hanifa?"
Ya langabe kai ya ce, "Oho mata! Ba yadda ban yi da ita ba muje amma ta ki don kar ayi mata allura".
Mama ta ce, "Ka ji shirme, ni bari in kaita yanzu".
Ta shiga daki ta same ta tana kwance tana faman tsirtar da miyau cikin 'tissue', ta ce, "Tashi maza ki shirya mu tafi".
Ta ce, "Ina zamu Mama?"
Ta ce, "Inda kika aike ni?"
Sai ta yi shiru ta mike tasa after dress ta bi bayan Maman.
Gwajin fitsari na farko da aka yi mata ya nuna tana da shigar karamin ciki wata biyu. Mama ta hau hamdala tana godewa Allah.
Ita kam Hanifa fuskarta ba yabo ba fallasa, ba ta farin ciki, don ta sanyawa ranta cewa da ta haihu jikinta ya canza, dan guntun son da Aliyu ya fara yi mata, dainawa zai yi.
Don haka ta kudircewa ranta cewa ko ta haihu ba za ta yi shayarwa ba, kada mamanta su rankwafa, don su kadai ne abin da Aliyu yake so a jikinta.
Ai yau Mama sai da ta karbi goron albishir a wajen Daddy, shi kam Aliyu ya yi hamdala a ransa, amma bai nuna mata wani dokinsa ba.
Ya san ba so take ba, don dai an fi karfinta ne kawai, sai ya sa ido sosai a kanta.
Daddy da kansa ya bugawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login