Showing 1 words to 3000 words out of 84568 words
💞💞soyayya da izza💞💞
Story and writing by
hadeexatou (Mrs KD)✍️✍️
yar amanar jajirtattu💪💪
Wannan labari kirkirarrene idan kinga wani abu Wanda yayi kamada naki to kiyi hakuri banyishi dan wani ko wataba
Page 1
______________Sauri takeyi tagama shiryawa tawuce islamiyya dan bata kaunar a taba lafiyar,
Saboda batasan amata dukan makara ko kadan murya najiyo daga waje tana fadin zuhura kiyi kifito kutafi maryam ta biyo miki amsawa tayi da, to inna ina zuwa, wacce aka kira da maryam ce, tace inna aida sauran lokaci inna ce tace amma ai garadai kutafi dawuri ko dan zuhura batasan duka ko kadan dariya maryam tayi tace wlh kuwa batasan duka zuhura ce tafito tanasa hijjabi tana fadin maryam mutafi inna dawo zanci abincin inna da to ta bita kawai, nan suka futa inda zuhura ke fadin maryam ki daga kafa kar malam isah ya dakemu kinsan halinshi baya afuwa aike zuhura wani zubin yana rangwantamiki zaro ido zuhura tayi tace a ina yake rangwantamin kijiki da wani zance kinga kiyi sauri kawai dariya tayi tace muje shugaban matsorata eh naji ai tsoro halak ne da haka harsuka isah makarantar sunkai sa a ba a fara dukan makaraba aji suka shige suka xauna sukafara karatu.
U S A
Kwance yake a makeken gadonsa idanunshi a rufe alamar bacci yake sanyin a .c dake fitowa daga dakin tare da wani daddadan kamshi dake tashi a bedroom din komai na bedroom din purple and white ne komai na dakin ya hadu fiye da tunani me tunani nikam canai aljanar duniya kirrrrrr3 wayace ke kara alamar kira seda takatse wani kiran yashigo sannan yafara laluben wayar irin name magagin bacci wayar yadauka yakara a kunne amma beyi maganaba jiyay ance am waiting for you jin muryar ya tabbatarmai da Ahmad ne abokinshi da kyar ya furta ok blanket din ya yaye ya sauko da kafarsa kasa wacce take fari tasss azuciyata nace wannan ko fura aka dama mun ai nasha mikewa yayi ananne naga siffar kyanshi ta daban da jiki wanda yanmata ke rububi farine tasss kai kace balarabene dago da fuskarshi yayi yanada idanu daidai yanada dogon hanci se dan karamin bakinsa me dauke da pink lips sumar kanshi bakace wuluk yayinda taketa sheki atakaicedai wannan gayen shi ake kira da handsome guy wanda duk macen data ganshi seta kyasa, toilet yashiga yasakarwa kanshi ruwa inda ya sauke ajiyar zuciya yakai kusan minti talatin yana wankan sannan yafuto daure da tawul a kugunsa yana tsane gashinsa da wani gaban mirror ya tsaya kana yadauki lotion me kamshi yafaragogawa a hankali ajikinsa seda yagama shafawa sannan ya gyara sumar kansa ya shafamata mai se sheki take gwanin sha awa wardrobe yanufa ya fudo da kaya kananun kaya ya dauko ligh blue t sheet da dark blue trouser a tsanake yagama shiryawa yadau agogonshi ya manna a tsintsiyar hannunshi kana yadau key din mota da phone dinshi yafuta a hankali yake takowa falon nikam se a nan naga haduwar falon ya hadu komai na more rayuwa akwai irinshine akacewa inbakaji tsoron Allah ba ibadama da kyar xakayi, karasowa falon yayi ya nemi daya daga cikin kujerun alfarma na falon ya xauna Ahmad ne ya kalleshi yace amma bakada mutunci wlh awana daya inajiranka kazo kasamugu ka zauna bayankasan ba zama nazo yiba be kalleshiba kuma be bashi amsaba idonshi nakan phone dinshi ahmad ne yace please Ammar tashi mutafi se lokacin yayi magana batare daya kalleshiba yace waika gajine yanda yay maganar inka kalleshi zaka rantse kace bashi yayiba Ahmad ne yace kaga katashi mutafi inason nashiga school da wuri mugama shirye shiryen graduation dinan Allah na matsu nakoma Nigeria kallanshi yayi yace ok muje fita sukai harabar gidan suka shiga motar Ammar suka wuce school.
A bagaren zuhura kuwa bayan suntaso daga islamiyya tashigo cikin gidan azaune ta tadda inna akan tabarma se dan autanta akan cinyarta halifa se Amira dake gefenta tana wasa tana shigowa hijabi kawai ta cire tafada dakin girki saboda yunwar datakeji ko abincimma bata ganiba tace inna ina abincina inna ce tace mata gashinan arufe daukowa tayi tafuto waje ta nemi gefen tabarma tazauna tabude abincin tafaraci shinkaface fara da mai dayaji tanaci tanayiwa inna hira can taji ta tauna tsakuwa furzar dana bakinta tayi tace kai inna duk tsintar da mukaiwa shinkafarnan amma haryanzu tsakuwar nanan inna tace eh aidai mun rage tace inna dan Allah kar a kara siyomana wannan shinkafar Allah idan na tauna tsakuwarnan jinake kamar hakurina yacire, inna tayi dariya tace ya zakiyi, in babanki yadawo se kije kifadamai kice yadena siyomuku me tsakuwa, yawwa inna islamiyya ance mukawo kudin wata inna kinsan watana uku ban biyaba inna ce tace to kibari babanku yadawo sekije kifadamai kona wata daya yabaki kikai tom wlh inna harkunya nakeji azo karbar kudin wata ban kawoba inna ce tace kiyi kici kitashi magariba ta kawokai amsawa tayi da to.
Tafiya suke bawanda yace kala se can Ahmad yace wai abokina ya maganar wannan yarinyar kuwa wacce fa, yafada atakaice patrishia mana Ahmad yafada yana kallonshi yace tomene hadina da itah Ahmad ne yace soyayya mana soyayya kuma, yes koba hakabane shiru yamai dan yasan soyake kawai ya taboshi dan yasan bayasan zancen mata Ahmad ne yace kasan hargurina tazo wai na taimakamata na shawokanka ka karbi soyayyarta towaikai wai meyasa baxaka karbi soyayyarta neba yace sabida banida time din wata soyayya yanzu kuma kozanyi bazanyi da baturiyaba saboda me Ahmad yafada yace saboda bana ra'ayi ammafa tanasanka sosai dan har tafi sabrin sankafa yace kaga abar maganarnan muyi shiru banasan surutu sosai you know shiru Ahmad yayi yadau phone dinshi yana dannawa
Wata farar matace zaune a daya daga cikin kujerun alfarmar dake falon farace tass kamar katabata jini yafuto tana da jiki irin na hajiyoyin nan kana ganinta kasan kudi ya zauna ko daga yanayin flour ma kasan akwai nera wayarta ta dauka da take gefenta contact tashiga ta danna dialing my son naga an rubutu ajikin screen din wayar bugu biyu yadauka daga daya bangaren naji ance hello mamy amsawa tai da my son how far fine mamy kin manta dani ko haba my son taya xa ai namanta dakai kasan harkokin business dina se a hankali jiya jiya nadawo daga dubai Allah mamy namatsu nadawo gida nagaji danan kasar mamy ce tace to ai kakusa saura wata daya ina Ahmad ne kinganshinan agefena Ahmad ne yace kace ina gaishe da ita, mamy yace yana gaisheki tace to ina amsawa Ammar ne yace inasu jawad da muhsin da nadra mamy ce tace duk sunan lpy mamy ki gaishemun dasu sosai da kowa na gidan to insha Allah zasuji daga haka sukai sallama mamy takashe wayar tana ajiyeta kan center table muhsin da nadra ne suka shigo nadrace ta rungume mamy tanacewa mamy I miss you mamy ce tace too yanzu yaya Ammar yakirawo yace yana gaisheku muhsin ne yace momy dan Allah ki kiramanashi mugaisa nadra ce tace mamy yaya Ammar yace ze tawomin da yar tsana me gashi dayawa mamy ce tayi dariya tace am ina jawad din kuma koba shi yadaukokuba nasandai na aiki bala direba muhsin ne yace shiya daukomu mamy yace zeje wani guri yadawone mamy ce tace ok kuje kucire unform kuje gurin iya lami ta hada muku lunch amsawa sukai da to suka wuce itama mamy bedroom dinta tanufa dan ta kwanta
Bayan yagama wayar ya kalli Ahmad yace wai haushina kakejine Ahmad ne ya kalleshi yace haushin me kuma Ammar yace ok yayin da yake shigar da motarshi cikin harabar makarantar kana ganin makarantar kasan se dan wane da wane parking space yanufa yafaka motar suka futa darect class suka nufa duk indaa suka gifta se an kallesu especially Ammar, can naji wata black America tana fadin gaskiya guy dinnan yayifa anya baxan gwadacewa inasansaba watace daga gefenta tace karma kisoma dan baze taba yaddaba aiko kallontama baxeba wata tafada, da turanci suke ta maganar Ammar nashiga class ya zauna ahmad ma xama yayi. sun dan jima school din daga bisani suka koma gida bayan sungama shirye shiryensu
💞💞 Soyayya da izza💞💞
Story and writing
By
Hadeexatu (Mrs KD)✍️✍️
yar amanar jajirtattu💪💪
Typing
Page 2
Yana komawa gida bedroom yanufa kayan jikinshi ya rage ya fada toilet ya sakarwa kanshi ruwa seda yagama wankan tsaf sannan yafuta yadau lotion me kamshi ya shafa ya feshe jikinshi da turarenshi me rikita lissafi sannan yasa kayan bacci yafada gadonshi karar wayar shice ta karade bedroom din patreshia ke yawo kan screen din wayar seda aka kira sau uku be daukaba still ba ai zuciyaba aka sake kira seda takusa yankewa yadauka yakara a kunnensa daga daya bangaren naji muryar mace dake magana da turanci, inda take fadin gani nazo gidanka kafuto mugaisa what meya kawoki gidana bance ki fita sabgataba why haba Ammar to mene dan nazo gidanka kawai inasan ganinkane shiyasa kasan nadade bangankaba kwana biyar fa wani tsaki yaja yana fadin seki tazama danni bazan fitoba kya gaji ki tafi to ai ba matsala sena shigo dakin tana fadin haka ta katse wayar bin screen din wayar yayi da kallo yana fadin yarinyar nanfa bata da hankali, handle din kofar da aka murda yasashi juyowa yana kallonta sanye take da doguwar riga iya gwiwa farace tass irin farinnan na turawa gashinta ya zuba kafadunta dasauri yamike yana kallonta wow baby na kanada kyau sosaifa saurin daga mata hannu yayi yana fadin waike baki da hankaline zaki shigomun har dakina matsowa tayi dab dashi numfashinsu na dukan na juna hannunta tasa gefen kuncinsa tana fadin baby kanada kyau sosai ka dan bani lokaci ko kadan ne inkasance dakai zan saka nishadi sosai ganin inda ta dosa yasashi tureta yana fadin futarmun daga daki ka tsaya kajimana nace ki futarmun daga daki ganin bata da niyyar futa yasashi kama hannunta yajata har bakin kofa ya hankadata ya rufe kofar wasu hawayene suka zuba daga fuskarta jakarta ta dauka ta fuce tana kuka yana rufe kofar yakoma kan gadonshi ya kwanta ya rufe idanunshi gaba daya tasahi awani yanayi na daban bude idonshi yayi yadau phone din yayi dialing number Ahmad seda takusa katsewa yadauka yanafadin abokina ya akai ne yana maganar yana futar da wani nishi kwance yake rigingine se wata budurwa dake kasanshi tana tsotsan penis dinshi yana futar da wani nishi yana kara tura kanta Ammar ne yace Ahmad kanajina kuwa magana zamui dakai akan waccen bazan yarinyar Ahmad ne yace abokina mubari se gobe ina duty ne shiyasa bana cikin hayyacina Ahmad wai bazaka dena wanan iskancinnakaba ko kittt yaji ankashe wayar Allah ya shiryeka Ahmad nima ameen nace toilet yakoma yayi wanka saboda patreshia gaba daya tasashi wani yanayi, Ammar mutum ne me karfin sha awa ko yaya mace ta rabeshi yana iya futa hayyacinshi shiyasa baya kula mata saboda gujewa sabon Allah lokaci da dama zuciyarshi na rayamai yabiyawa kanshi bukata saboda yanada kudin da ze iya neman mata goma a rana daya kuma yanada surar daze ja hankalin yammata Ahmad yasha fadamai kawai yafara harkanan dayake ta neman mata amma sedai yace mai mata basa gabansa. da haka ya kammala shirin baccinsa ya hau gado yaja blanket rufe idonshi yayi kowanne bangare na zuciyarshi da abunda yake sakamai dahaka har bacci yadaukeshi
Baba sannu da zuwa yayinda yakaraso cikin gida yawwa zuhura inna ce tace barka da dawowa malam amsawa yayi yana zama kan tabarmar dake gefe daya inna ce ta kawomai ruwa ta ajiyemai da abinci malam haruna ne yace zuhura ya makarantar amsawa tayi da lpy lau baba Masha Allah haka akeso baba zuhura tafada tana wasa da yatsun hannunta inajinki zuhura mene baba dama kudin watan makaranta ban biyaba harna wata uku shiru yayi sannan yace tom kibari karshen wata in an bani albashi sena baki kikai musu ko tace tom toya boko kinazuwa ko eh tace yace yawwa zuhurata kicigaba da kokari kinji amsawa tayi da to inna ce tace tashi kije ki gyaramuku gurin kwanciya tashi tayi tashiga daki inna ce ta kalli malam haruna tace malam wani tunani nake wanne tunani kenan tace anya malam bazan nemi ko wanke wanke neba tunda kaga dan albashin naka baya isarmu dubu gomafa iya kayan abinci yake siyar mana katse ta yayi da banyarda da wanan shawarar ba bazeyiwu kullum kina hanya ba kina barin yara a gida ki hakura kawai Allah ze kawo mafita to tace tana fadin Allah yakawomana mafita ameen yace zuhura futo ki dauke yaranna daga nan ki kwantar dasu to inna futowa tayi tadau halifa ta shigar dashi dawowa tayi tadau Amira tashinta tafarayi Amira tashi, inna ce tace kidauketa mana, Allah ina tayi nauyi dayawa malam haruna ne yace amira tafara nauyi ai, wanne irin nauyi kawaidai lalacine irin na zuhura kidauketa kikaita dakin, Allah ina bazan iya daukantaba tafada a shagwabe, malam ne yace batta nakaita to tace ta koma daki malam yarinyar nan tafiye lalaci wlh se kace wata sikila malam ne yayi dariya yace haba habiba sikila kuma kiga ya da kumarinta kice sikila tace ai yarce tafiya lalaci yanzu ace amira ta gagareta dauka, to ai tazama katuwa yar, malam kaima kake goyawa yarnan bayafa, yace ba dole nagoyamata bayaba, to ai shikenan inna tafada tana mikewa tashiga daki shima tashi yayi ya wanke hannunshi yadawo yadau amira yashigar da ita yadawo yashiga dakinsu
11:00 pm mamy ce zaune falo tanajiran shigowar jawad ba a dadeba se gashi yashigo yarone fari amma be kai Ammar ba yanada hanci shima sanye yake da kananun kaya da facing cap black hannunshi rike da makulin motarshi yana shigowa yaga momy a falo beyi tunanin ze gantaba tsayawa yayi mamy ce tace daga ina kake shiru yamata be bata amsaba jawad ba dakai nakeba ne in ina yafarayi am mamy dama dama naje birthday din abokinane to shine yacemun dan Allah na tsaya nadan jira agama mutafi tare shi birthday din 11:00 ake kaiwa ah ah dama dama dagamai hannu tayi tana fadin daga yau karna sake gani kakai 11:00 awaje amsawa da to yayi mamy tana kaiwa nan tabar gurin ajiyar zuciya yayi da batace zata hadashi da yaya Ammar ba dan yasan halinshi sarai
Wanene amar
Mahaifin ammar alhaji usman su ukune agurin mahaifiyarsu yayinda mahaifinsu kedamata uku hajiya zainab mahaifiyar alhaji usman tanada yaya uku alhaji nasir se alhaji usman se autarsu aisha se matarshi ta biyu hajiya maimuna tanada yaya biyar itace matarshi ta farko se matarshi ta biyu hajiya suwaiba se matarshi ta uku hajiya zainab wato mahaifiyar alhaji usman wato kakarsu Amar mahaifinsu mutum ne me tarin dukiya sannan former president ne ya raini yayanshi cikin so da kauna yabasu ingantacen ilimi dan kaf yaransa basuyi karatu a Nigeria ba haka kuma basa aiki a kasar sedai alhaji usman dake aiki anan kasa Nigeria shima ba kasafai yake zamaba dan kasuwane ba gasar da bashi da kamfanunuwa shiyasa ko ina ansanshi bayan yadawone daga karatu aka umarceshi daya futar da mata yayi aure to dama yanasan kanwar abokinshi Khadija wato mamyn su Ammar anan ne yasanar da mahaifinshi game da ita mahaifinshi yayi bincike annan yagano mahaifinta shine accauntan general of federation wato alhaji sunusi mamman, matanshi biyu hajiya zara'u tafarkon mahaifiyar mamyn su Ammar tanada yaya biyar Ibrahim se mukhtar se Khadija mamyn su Ammar se mufida sannan se dayar matarshi hajiya sakina tanada yaya hudu yusuf fiddausi maryam se Laila, anan ne akafara shirye shiryen biki inda akasa biki sati biyu aka kai lefe aka daura aure amarya ta tare agidanta na kaduna, Khadija macece kyakyawa ga gashi dan mahaifiyarta ta hada jinsi da larabawa haka shima alhaji usman farine amma bazaka sa shi sawun farareba yanada dogon hanci ahaka suna zaune yana matukar ji da ita haka kuma yana kula da ita yadda yakamata, a daga bisani tasamu ciki zokakaga murna gurin alhaji usman da sauran yan uwa yadauki son duniya yadorawa cikinnan ko futa kasashen wajen yadena yazauna wai ze kula da ita wata ranar alhamis tana zaune kan kujera ta Mike kafafuwanta yana mata tausa kamar an mintsineta tafarajin ciwon baya tafara cije lebe nan hankalinshi yatashi, kamata yayi yafutar da ita bakin mota yasata aciki ya hau ya fuzgi motar da karfin gaske sannu yake tamata harsuka shiga asibitin inda likitoci sukayo kanta suka shiga labour room yinkurin binsu yake wata doctor ta dakatar da shi haka yatsaya yanata safa da marwa gurin, wayarsa ya xaro daga aljihunsa ya shiga Kiran abokinsa mukhtar wato yayan khadija yasanar dashi halin da ake ciki annan ne yakira gida yana fadamusu hajiya zara'u ce ta tafi asibitin wato abokiyar zaman mahaifiyarta, takai kusan awa daya da rabi daga baya aka futo aka fadamusu Allah yasauketa lpy saboda murna ko tsayawa tambayar meta haifa beyiba yace zan iya ganinta tace ah ah semun gama gyarata ita da babyn hajiyya zara u ce tace likita meta haifa namijine likitan tafada dubu hamsin yaciro a aljihunsa yamikawa likitan karbatai tana washe baki tana kwararo gdy da addu a seda aka gyarata tsaf sannan suka shiga dan su ganta ita da babyn tabarakallah farine tass ga hanci irin na ubansa farin kuma yadauko na mahaifiyarsa nan suka koma gida kowa murna yakeyi yayinda kaka ninsa suketa dokin ganinshi daga na uwa harna uba kowa yana nunamai soyayya anan ne Khadija taroki alfarma asamata sunan mahaifinta beyi mata gardama ba akasamai sunusi ake kiranshi da Ammar, yafara girma inda suka koma London da zama dan haka anan yayi makaranta yana primary 5 Khadija tasamu cikin jawad inda akasamai sunan mahaifin alhaji usman muhmd ake kiranshi da jawad ta haifeshi acan kamarshi daya da mahaifiyarsa farine kuma se ya dauko na babansa inda yakasance ba faribane tass bawanda yasanshi a dangi kasancewar acan aka haifeshi seda Ammar yagama secondary yayinda jawad yake jss one a shekarne mahaifin Khadija alhaji sunusi Allah yamai