Showing 108001 words to 111000 words out of 177624 words

Chapter 37 - SHU'UMIN NAMIJI completed Hausa novel

18 Jul 2024

37529

dai masu yin vedio suka ci gaba da ɗauka yayinda..... Hmmmm kamu dai yayi kamu  yakuma ƙawatar amma kuma sai dai sam amarya Zahrah ta kasa sakewa komai a ɗari ɗari takeyinsa,  abu biyune suka haɗe mata kunya dakuma rashin sabo, saboda bata taɓa zuwa irin waƴannan wajen ba, wannan ne karonta na farko, gashi kuma kamun yatara mutane sosai,  su Husnah sunyi rawa sosai sun raƙashe Amarya kuwa ae ko taka kafarta bata'iya ba gaba ɗaya nauyi da kunya sun hanata sakat.... sai gab da magrib aka tashi  daga kamu kowa yasamu abun arziƙi ankuma cika ciki da abinci na musamman da kuma lemuka...    Yanzu kam mota ɗaya Zahrah da Husnah harma da Suhaima suka shiga, yayinda Dr.Sadeeq shikuma yashiga wata motar ta daban...  Jingina bayanta tayi da kujera haɗe da kwantar da kanta akan kafaɗan Husnah, duk hiran da  Husnah da Suhaima keyi jinsu kawai takeyi, sosai sanyin AC'n dake cikin motar yake ratsata har hakan yaso sanyamata zazzaɓi, haka dama ita take matuƙar ta shiga  hayaniya to kanta sai ya ɗanyi mata ciwo, uwa uba kuma idan sanyi yayimata yawa saita ɗanyi zazzaɓi..  Harsuka isa gida Zahrah ko uffan batace ba duk da kuwa yanda su Husnah kejanta da hira, amma iya abun da take iyayimusu shine murmushi...  Fitowarta a wanka kenan,  sauri sauri ta zura wata doguwar riga me kauri ajikinta,,, kallon ta ta mayar ga Husnah wacce taketa faman chatting a wayarta sai nurmushi kawai take zubawa..

"Wai ke da waye ne haka?  a iya sanina dake ke ba mutum bace me yawan chatting da'alama dai munsamu ƙaruwa" Zahrah tafaɗi maganar cikin sigar tsokana... Dariya Husnah tayi haɗe da ɗage giranta sama.    "Ƙwarai kuwa tawan, wallahi ɗazu na haɗu da wani guy a wajen kamunki, ina tunanin ya kwantamin arai"

Dariya Zahrah ta sanya haɗe da neman guri ta zauna akusa da Husnah haɗi da kwantar da kanta akan kafaɗan Husna'n....

"Husnah kinsan ya so yake?"  tambayar da ta fito daga bakin Zahrah kenan..

Mamaki tambayar da  Zahrah tayi mata  ya bata amma kuma batasan menene dalilin dayasanya Zahrah tayi mata wannan tambayar ba...

"Eh zan iyacewa nasansa zankuma iya cewa  bansan saba, saboda banyi wani zurfi acikinsa ba, amma kuma ke kinsan bana yaudaran kaina Zahrah, duk wasu alamomin so nasansu, saboda hakane ma nayardarwa kaina cewa nakamu da soyayyar Yazeed so matsananci!" Husnah tafaɗi haka tana me wasa da wayar hanunta, da'alama sunan Yazeed kaɗai da ta ambata yasanyata cikin shauƙi..

Ajiyar zuciya me ƙarfi Zahrah ta sauƙe haɗe da ɗago kanta daga kan kafaɗar Husnah, hannayen Husnah takama cikin murya me sanyi tace da  Husnah "Wasu irin alamomi ne kesanyawa mutum yagane cewa yakamu da so?  sannan kuma inaso ki sanar dani menene hukuncin zuciyar da ta makance har take ƙoƙarin sake son wanda yacutar da'ita, wanda kuma baida wani amfani a wajenta"

Kallon mamaki haɗe da ɗaurewar kai Husnah tashiga yi mawa Zahrah, ƙwarai itakam maganganun Zahrah sun sanyata a duhu me Zahrah take nufi?

"Banfahimci inda kalamanki suka dosa ba Zahrah, zanfi fahimta idan har kika warware maganar tazama abu guda, amma kuma ni a ganina  babu amfanin  zuciyar da zata so wanda baida amfani a wajenta, sai dai kuma amma kinsan shi so wani zubin yakan makantar da komai naka ne tahanyar da baka isa kayi yaƙi dashi ba, amma kuma shi so kala kala ne, kowani so da'irin ƙarfinsa haka kuma da irin rauninsa, wani son yana fita, wani kuma sai ahankali zai fita, wani kuwa baya taɓa fita har gaban abada, amma shi wanda baya fita har abada shi ake ƙira da ƙauna, ita ƙauna kuma idan zafinta yatashi ƙona ka, to  ƙunan yakan kasance me tsananin zafi da raɗaɗi bakamar na so ba,   ina fata dai Ƙaunar Doctor ce tasanya kikamin wannan tambayar?" Husnah tafaɗi haka tana murmushi.. Wasu siraran  hawayene suka silalo daga cikin idanun Zahrah zuwa kan ƙuncinta.

"Zahrah kuka kuma?" Husnah tatambaya cike da mamaki domin ita sam bataga abun kuka  acikin maganar da sukeyi ba, hasalima ita Zahrah'n ce tafara ɗago maganar ba wai ita ba.

Hanu tasanya ta share hawayenta haɗe da sakin murmushi,  "Bakomai Husnah kawai dai idanuna ne tunɗazu sukeyimin zafi, kinsan ban saba da irin wannan kwalliyar da akamin ba, bacci ma nakeji bana ɗan kwanta, idan kingama ki rufe mana ƙofa" Zahrah tafaɗi haka fuskarta ɗauke da murmushin dole..

Har Zahrah  ta kwanta Husnah bata ɗauke idanunta daga kanta ba,  sosai ganin hawayen Zahrah'n yabata mamaki duk da kuwa cewa tana lure da'ita a ƴan kwanakinnan gaba ɗaya acikin damuwa take wuni, amma gudun kada ta dameta da tambaya yasanyata sharewa bata tambayeta ba, amma tasan damuwa kam akwai shi jingim acikin zuciyar Zahrah...

Kusan mintuna talatin hawaye na gangarowa daga cikin idanunta, amma kuma ko kyakkyawan motsi taƙi tayi gudun kada Husnah ta fuskanci cewa batayi bacci ba,, bazata taɓa bari kowa yasan damuwarta ba, ta yarda ta amince zata haɗiye duk wani damuwarta acikin rai da zuciyarta ita kaɗai, koda kuwa damuwartata zata kasheta,  tabbas wannan abun da takeji ba abu bane wanda zai ɓoyu ba, amma kuma zatayi iyaka ƙoƙarinta wajen ganin ta maidashi ɓoyayyen sirrinta a haka har baccin gajiya ya ɗauketa, tana bacci babu jimawa kuwa ƙiran Dr.Sadeeq yashigo cikin wayarta, ganin ya nace da ƙiran ne yasanya Husnah ɗaga wayar ta shaida masa cewa Zahrah tayi bacci, to kawai yace haɗe da ajiye wayar..   
Wani irin tausayinta ne yaji ya dirar masa acikin zuciyarsa, hakanan yaji yau soyayyarta yasake shiga zuciyarsa fiye da ko yaushe  yayinda tausayinta yakuma ɗarsuwa acikin zuciyarsa, yaso jin muryarta acikin wannan daren amma kuma hakan baisamu ba, haka yashare yashiga cikin abokansa suka cigaba da  sabgoginsu...... 

Kafe cak idanunsa  suke akan haɗaɗɗen zanen POP'n dake mamaye saman ɗakin wanda aka ƙawatasa da ado me matuƙar burgewa, a hankali yake fitar da numfashi me zafi daga cikin hancinsa,, ahalin yanzu ba ciwon da yakeji bane damuwarsa, yafi damuwa da ganin  Zahrah'nsa fiye da komai,  yanzu kenan saura kwana uku a ɗaura mawa Zahrah'nsa aure da wani bashi ba,   rumtse idanunsa yayi da sauri haɗe da haɗiye wani irin yawu me ɗaci daya tsaya masa a maƙoshi, abu kamar wasa saiga ƙwalla suna gangarowa daga cikin idanun Zaid,  hanu yasanya yashafa gefen fuskarsa inda yaji sauƙar ɗumin wani abu kamar ruwa,,  ruwan hawayen daya fito daga cikin idanunsa ya lakato ahanunsa koda yaga cewa hawayene ke fita daga cikin idanunsa sai yasaki wani irin murmushi me matuƙar ciwo,  rayuwa kenan babu yanda bata juyawa bawa, watarana kaga me kyau watarana kuwa kaga mummuna, ƙaddara kenan babu tayanda bata zuwarwa bawa, haƙiƙa SO babban cutane ga bawa musamman idan baka samu abun da kakeso ɗin ba, tabbas ya jarabtu domin ko a iya haka Allah yabarsa ya horasa horo mafi tsanani ma kuwa,   tabbas Zahrah itace rauninsa, rasata kuma shine abu wanda zaifiye masa komai ciwo acikin rayuwarsa, baisan wani irin zazzafar soyayya yakeyiwa Zahrah ba, ashe tun dama yaudaran kansa yayi  ba sha'awarta yake ba sonta yake, amma kuma saboda wani banzan tunani da kuma banzar hujjan sa yasanya ya kasa yarda da hakan,  idan yace zai  misalta irin tarin yawan nadaman da yayi kawo daga randa ya yiwa Zahrah fyaɗe  zuwa yau to tabbas yayi ƙarya, ya cutar da'ita, ya zalunceta, tabbas yasan bai kyauta mata ba, sannan kuma baiga laifinta da ta ƙishi ba tabbas shida kansa ya san cewa bai cancanci ta sake yarda dashi ba,  saurin rumtse idanunsa yayi haɗe da dunƙule hannayensa da ƙarfi, bakomai ne yasanyasa yin hakan ba  face tunowa da yayi  lokacin da idanunsa suka rufe ya shigeta da ƙarfin gaske yanajin wani irin ihun da tayi amma saboda bushewar zuciya irin tasa haka bai saurara mata ba,,  kansa yashiga duka da hannayensa biyu kamar mahaukaci, ihun da Zahrah keyi masa alokacin da zai keta mata haddine yashiga dawowa cikin kunnuwansa ji yake tamkar alokacin ne abubuwan suke faruwa,,,  ihu yashiga yi batare daya sani ba, gaba ɗaya idanunsa sun kaɗa sunyi jajur dasu,   Mum da shigowarta falon nasa kenan taji ihun Zaid na tashi daga cikin bedroom ɗinsa, cikin sauri hartana haɗawa da tuntuɓe tanufi ɗakin nasa,, kwance tagansa akan gado yaɗaura duka hannayensa akansa yana wani irin ƙara tamkar wani wanda aljanunsa suka tashi..

"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un, Zaid! Zaid!!" Mom taƙira sunansa cikin matuƙar ruɗewa,,   girgiza sa Mum tashiga yi  cike da ruɗewa sunansa kawai take ƙira, a tunaninta Zaid ɗin nata ya haukace ne, yanajin muryar Mom ɗinsa acikin kunnensa yatashi a zabure haɗe da faɗawa cikin jikin mahaifiyartasa,  abun mamaki saiga Zaid nan na kuka tamkar wani ƙaramin yaro, ita kanta Mum kasa motsi tayi haka ta tsaya kamar statue, wai da gaske Zaid ɗin tane wannan, kuka fa yake, anya kuwa ba aljanune suka shiga mata jikin ɗa ba?.
"Zaid" Mum takuma ƙiran sunansa cikin murya me sanyi domin kuwa itama tuni ƙwalla harsun cika mata ido...   "Please help me Mum, i don't want to lost her!"  abun da Zaid ke faɗa kenan yana kuka,,  mamaki marar misaltuwa ne yakuma kama Mum  wannan wace irin masifa ne ya ruski Zaid wace irin tsinanniyar soyayyace wannan datake shirin haukata mata yaro? lallai yazama dole tayi wani abu, bazata taɓa bari tanaji tana gani ɗanta ya rasa ransa akan wata ba, wai dama ashe haka so yake? idan kuwa haka so yake to sai dai muyi fatan Allah yarabamu dayin so me tsanani....

Kansa mum tashiga shafawa ahankali cike da tausayawa tace "Ka kwantar da hankalinka Zaid, kayi haƙuri kasamawa kanka nutsuwa, badai kana sonta ba?"

Kai Zaid ya kaɗa tamkar wani ƙaramin yaro.  

"Insha Allahu zata zamo taka, zaku rayu da'ita rayuwa ta har abada, kadaina damun kanka kaji my son!"

Mum ta ƙare maganar cike da lallashi..

Kansa ya kwantar akan kafaɗan mahaifiyartasa lokaci ɗaya yashiga sauƙe ajiyar zuciya irin dai yaro ƙarami yayi kuka ya ƙoshin nan.... Bayansa Mum take shafawa a hankali sai gashi cikin mintunan da basufi 10 ba Zaid yasoma fidda numfashi a hankali cike da nutsuwa da'alama dai bacci ne ya ɗaukesa, Mum tana tabbatar da cewa Zaid ɗin yayi bacci ta tattaro duka ƙarfinta  haɗe da  zameshi akan kafaɗanta ta kwantar da kansa bisa kan pillow'n sa haɗe da ja masa bargo ta rufeshi,   kallon fuskarsa Mum tashigayi cike da tsananin tausayinsa, tajima tana kallonsa kafun daga bisani tayi masa addu'a  ta shafa masa akan fuskarsa,  cikin sanyin jiki ta tashi tafice daga cikin ɗakin, gaba ɗaya zuciyarta tayi rauni......

*Washe Gari*

Tun safe kwararriyar me zanen lalle wanda Dr.Sadeeq ya ɗaukarwa su Zahrah bayan yabiyata maƙudan ƙuɗaɗe tazo gidan,, zanen jan lalle me matuƙar kyau aka tsantsarawa  Zahrah akan hanu da ƙafarta, abunka da farar fata take zanen jan lallen yafito akan fatarta yayi kyau sosai,,,   lokacin da ta wanke zanen lallen nata hakanan ta tsinci kanta da sakin murmushi ita kanta sosai zanen yayi mata kyau gashi ya ƙara ƙawata farar fatarta gwanin sha'awa. Wayarta dake ringing ta ɗauka haɗe da karawa akan kunnenta, cikin wata irin kasalalliyar murya taji yace "Amaryata"       murmushi tasakar masa me sauti haɗe da cewa "Umm"     Dr.Sadeeq dake zaune cikin motarsa yagyara zama haɗe da cewa "Ki ɗan bani aron minti 10 daga cikin lokutanki na yanzu inason ganinki"  ya ƙare maganar yana wani lullumshe ido kamar wanda yake a gabanta.     Ajiyar zuciya Zahrah tayi haɗe da cewa "Gani nan zuwa"  tana aje wayar   ta ɗauki wani haɗaɗɗen mayafi wanda aka masa ado da  fararen duwatsu ta yafa ajikinta yayinda haɗaɗɗen gashinta dayasha saloon ya bayyana kansa ta cikin mayafin..

Tana fitowa tsakar gida ta kalli Husnah wacce yanzu ake zana mata nata lallen, murmushi tayi mata haɗe da kashe mata ido ɗaya, dariya suka sanya su duka domin sukaɗai suka san ma'anar hakan.... Murmushi yayi haɗe da sauƙe ajiyar zuciya alokacin dayaga fitowarta daga cikin gida,,,  buɗe murfin motar tasa tayi tashiga bakinta ɗauke  da sallama,, cikin murya me ɗauke da kasala ya amsa mata sallaman haɗe da maida kallonsa gareta. Murmushinta dake ƙara mata kyau akoda yaushe tayi masa haɗe da ɗan tsaida idanunta akansa,,,,    shiɗinma kallonta yake batare dayace komai ba, azuciyarsa kuwa mamakinta yake ta yanda ta'iya tsaida idanunta akan sa a yau ɗin, bayan kuma yasani sarai batayi masa dogon kallo.  
"Namiki kyau ne ƴan mata?" yatambayeta yana me duban kansa,, dariya ne ya kwace mata amma kuma saitayi saurin sanya hanu ta toshe bakinta,   
"Wow! gaskiya wannan zanen lallen yayi kyau sosai!" yafaɗi haka yana me ƙoƙarin kamo hanunta, sam shi bai lura da zanen bama sai yanzu,,  saurin maida hannayenta cikin mayafin dake jikinta tayi haɗi  da  cewa "Sai an biya kuɗi me yawa sannan ake kallon wannan zanen"    murmushi yayi me sauti, ba ɓata lokaci ya sanya hanu acikin aljihunsa, kuɗi yaciro wanda baisan ko nawa bane, ya ɗaura mata akan cinyarta.
"Karki hanani gani please" yafaɗi maganar yana me marairaice fuska,   
"Naƙi wayon kuma ni wannan kuɗin sunmin kaɗan" tafaɗi haka cikin sigar wasa.

"Laluma aljihunsa yayi dama da hagu amma kuma yaji babu ko sisi,  kawai saiya marairaice idanunsa yana kallonta, dariya yanzu kam tashigayi, sai da tayi dariyarta ta ƙoshi sannan tace "Kasan baka da kuɗi kuma kakeson ganin zanen lallena?"
Jin shiru bai bata amasa ba yasanyata saurin ɗago kanta ta kalleshi, gani tayi ya zuba mata idanu kamar wani wanda bai taɓa ganinta ba, murmushi kawai tayi haɗe da kawar da kanta gefe, sosai takejin wani iri ajikinta idan yana kallonta.

"Zahrah na!"  yaƙira sunanta cikin wata irin murya me sanyi.  Zahrah bata iya amsa masa ba, sai dai ta dawo da kallonta gareshi..

Yabuɗe baki zaikumayin magana kenan wayarsa tasoma ƙara,,

"Hajiya"

shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayar, dakatawa da maganar yayi haɗe da ɗaukan wayar yakara akan kunnensa.. Hajiya dake zaune akan kujera cikin yanayi na ɓacin rai tace

"Kana'ina ne?"

"Ina wajen Zahrah Hajiya" yabata amsa cike da girmamawa.

"Kabar duk abun da kake kazo gida inason ganinka" tana kaiwa nan azancenta ta kashe wayar.

A hankali ya zame wayar daga kan kunnensa haɗe da sauƙe ajiyar zuciya kallon Zahrah yakumayi haɗe da ɗan sakin murmushi.

"Hajiya nason ganina yanzu, ki riƙe wannan saboda hidimar walimanki na gobe, maybe bazaki sake ganina ba sai bayan na angonce!" yafaɗi haka yana me miƙa mata wasu kuɗaɗe masu yawa daya ciro daga cikin wata ƴar loka dake cikin motar. 

"A'a ae bana buƙatar komai don mungama duk wani abun da zamuyi, kuma komai na walima yazama ready,  sannan kuma  inada kuɗi a wajena ka...."

"Shiiii kinsan banason yawan musu please ki karɓa kinji baby na, ki ajiye kobazakiyi komai dasu ba nasan zasu miki amfani wani lokaci" yafaɗi haka ta hanyar katseta daga maganar da takeyi batare daya bari ta ƙarisa ba,,   badon ranta yasoba ta amshi kuɗin haɗe dayi masa godiya kana ta buɗe murfin motar ta fice, shima tada motar nasa yayi yabar ƙofar gidan, zuciyarsa cike da mamakin ƙiran da Hajiya tayi masa, Allah dai yasa ba wata matsalan ne takuma kunnu kai ba,  idan dai har akan aurensa da Zahrah ne tofa shikam gaskiya sai dai kowama yayi haƙuri saboda ayanzu baijin zai iya sanja muradin sa...

Fuska ɗauke da mamaki Dr.Sadeeq ke cewa   "tafasa aurena kuma Hajiya?"

"Badole tafasa aurenka ba, wace uwa ce zata yarda da irin abun da katsiro dashi? tun ma ba'aje ko inaba kana nuna banbanci ƙarara, gashi  abanza ka jawo zubewar mutumcin dake tsakanina da Hajiya Furaira, yanzu da wani ido kakeso nasake kallonta!" Hajiya tafaɗi haka cikin ɓacin rai.

Sunkuyar dakai ƙasa Dr.Sadeeq yayi yana me hamdala acikin zuciyarsa da aka soke batun aurensa da Saleema, dama shi Allah yasani ko ya auri Saleema ba lallaine yakamanta mata adalci ba, saboda abun a bayyane yake yafi ƙaunar Zahrah fiye da kowacce mace a yanzu idan aka cire mahaifiyarsa dakuma ƴar uwarsa ta jini.

"Dama haka kakeso ai shikenan burinka yacika, gakuma kayan lefe dakuma kuɗin auren da kakai can sun dawo maka dashi, sai kaje kayi ta fama da wacce zuciyarka ta zaɓa ma ni tashi kabani waje !"

Sumi sumi haka Dr.Sadeeq yatashi daga gaban mahaifiyartasa  cikin sanyin jiki yafice daga cikin falon...

Yana shiga ɗakinsa yasaki wani irin ajiyar zuciya, wayyo Allah shikam daɗi kasheshi, dama yafi kowa tunanin yanda zaman nasu zai kasance saboda shi a tsarin rayuwarsa bai da niyar auren mace sama da ɗaya bare yanzu daya samu Zahrah yasan cewa ita kaɗaima ta'ishesa rayuwa,   yaji daɗin fasa wannan auren ƙwarai... 

*Zaid*

Gaba ɗaya jikinsa yaƙi daɗi duk yanda yaso koda a daddafene yaje yaga Zahrah hakan yagagara, saboda wunin yau ma gaba ɗaya  baiyishi cikin daɗi ba, kasancewar ciwon zuciyarsa yatashi yasanya Dr.Bilal ya dinga basa magani masu sanyasa bacci gudun kada ya matsantawa kansa  da tunani, haka dai yanaji yana gani tashi zaune ma yagagaresa, haka ya kwana yana begen ganin Zahrah....

*Friday*

Kowa dake gidansu Zahrah shirin zuwa wajen walima kawai yakeyi, yayinda amarya Zahrah tasha kyau cikin wani haɗaɗɗen sari da aka ɓata lokaci wajen naɗa mata shi ajikinta,  yauma dai meckup aka tsantsara mata akan fuskarta nagani na faɗa, take fuskar amarya Zahrah yaci gaba da walwali,,  motoci Dr.Sadeeq yaturo suka kwashesu har zuwa inda za'a gudanar da walima,,,   walima fa ya ƙayatar saboda Malami aka ɗauko na musamman yagudanar da wa'azi akan yanda ake zamantakewar aure, sanan kuma yaƙara da wa'azi me ratsa jiki  harsaida amarya tayi  kuka,,  bayan anƙare walima ne kuma aka soma rabon abinci  haɗe da kyaututtuka kamar su memo da kuma jaka wanda Dr.Sadeeq ne duk yayi su, sai dai babu hoton amarya da ango ajiki sai dai sunansu kawai.  Walima fa yaƙayatar kowa sai dai yace Alhmdlh haka  aka tashi a taron walima kowa yanacikin farinciki,, yayinda gobe asabar  kuma take ɗaurin aure💃.

*(Maza kuzo fa, mata kuma ku faɗawa Mazajenku su je ɗaurin auren😂 🙊Nidai baruwana Team Zaid kada kuga laifina Dr.Sadeeq ne yace ingayyaci kowa da kowa 😂💃😜)*

       *Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

        *SHU'UMIN NAMIJI !!*

     *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

            
           *WATTPAD*
    @fatymasardauna

*(Wannan fejin baki ɗayansa nakine My KHAIR74  kinasani nishaɗi sosai, kiyi farinciki marar iyaka kiji daɗinki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login