Showing 54001 words to 57000 words out of 177624 words

Chapter 19 - SHU'UMIN NAMIJI completed Hausa novel

18 Jul 2024

37539

inda yake tsaye, cike da fari'a Dr ya amsa mata sallaman da tayi haɗe da cewa "Wato sai anjamin aji kafun a fito ko?"

Ɗan guntun murmushi Zahrah tayi haɗe da cewa "Bawani batun jan aji, ni a hakan ma inaganin na fito da wuri"

Shima murmushin yayi haɗe da cewa "Kinyi kyau!"

Still murmushi tayi, cikin son kawar da zancen da yayi na  cewa tayi kyau, tace "Lafiya kuwa naganka a dai-dai wannan lokacin?"

Gyara tsayuwarsa yayi haɗe da maida nutsuwarsa gareta "Maganar danazo miki da'ita Zahrah bata tsaye bace, yana da kyau mushiga mota, sai mu tattauna ko?"

Ɗan jim Zahrah tayi, haɗe da cije lips ɗinta, "Shikenan amma inafatan bazamu jimaba, kafasan banson fitowa waje da dare"

"Insha Allah, bazamu ɗau tsawon lokaci muna magana ba!"  Dr yafaɗi hakan lokacin da yayimawa kansa masauƙi a cikin motar tasa, bayan ya kunna ƙoyin wutar dake cikin motar take haske ya gauraye cikin motar.

Gyara zama Zahrah tayi, haɗe da tattaro duka nutsuwarta "Inajinka" tafaɗa a taƙaice.

Wani irin numfashi Dr yayi, haɗe da fitar da iska daga bakinsa, sai yanzu yakejin cewa, bazai iya furta abun da yakawosa ba, gaskiya yanajin nauyi, baisan tayaya Zahrah zata karɓi muradinsa ba,  kada maganar da zaifaɗa ma ta yazamo sanadiyar rugujewar nishaɗin da yake gani akan fuskarta yanzu,  "Ta'ina zanfara?" ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa.

"Lafiya kuwa, naga kayi shiru?"
Zahrah ta tambaya, cike da mamakin yanda yayi shiru, bayan yace akwai maganar da zasuyi.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe, haɗi da maida kallonsa gareta, saida ya tattaro nutsuwarsa kafun yace...
"Yazakiji idan wani yazo miki da batun soyayya a wannan lokacin Zahrah?"  abun da ya iya fitowa daga bakinsa kenan, domin a gaskia shikam yarasa ta'ina zai fara.

"So kuma? wani irin so?" Zahrah ta tambaye shi cike da mamakin kalaman nasa.

"So na Aure Zahrah!" yafaɗi maganar cikin ɗar ɗar.

"Au..r..e.. Kuma Likita? Aure fa kace,  dama akwai wani wanda, zaiji kwaɗayi da sha'awar aure na ne? hmmm a gaskia bana tunanin haka, domin kuwa babu wani wanda zai so ni da rayuwata, a yanda nake ɗinnan!" Zahrah tafaɗi hakan da'iya ka gaskiyar ta.

"Kada kice haka Zahrah, akwai mata masu rauni da yawa irin ki, amma an auresu, kuma anzauna dasu, ke me yasa zaki yanke ƙauna da...."

"Dan Allah kadaina min wannan zancen Doctor, banjin zan sake son wani ɗa namiji a duniyar nan"
Zahrah ta katse shi da ga maganar da yakeyi, ci gaba tayi da cewa
"taya kake tunanin zansake kai kaina tarkon da ya ruguzamin rayuwa, shi So ɗin dakake faɗa yanzu, shine ya ruguzamin rayuwa ta,  ya rabani da duk wani farinciki na rayuwata, shin idan kace min na sakeyin So, kamin adalci kenan? " Tuni hawaye sun gama wanke mata fuska.

"Kada kice haka Zahrah, kefa musulmace, kuma ke mace ce, nasan kina da sanin cewa,  kyautatuwar rayuwar ƴa mace shine aure, haka kuma rayuwar ƴa mace bata cika hundred percent sai da aure, haka kikeso ki ƙare rayuwarki ba aure? ko kin manta cewa cikar mutumcin mace shine a ganta gidan mijinta?  yin Aure shine burin kowacce mace ta ƙwarai,  nasan kema wannan shine burinki, kada shaiɗan yayi amfani da abun da yafaru dake, ya ruguza miki rayuwa, ya hanaki aikata sunna!" 

"Hakan shine burina amma ada,  wa zai aureni a yanzu? waye zai ɗaukawa kansa duhu? waye zai ɗauki sauran da wani yaci ya rage, sauran da wani ya tarwatsa, ya zuba ƙazantarsa, acikin cikinta, waye zaiyi hakan? bazan yaudari kaina ba, nasan babu wani wanda zai aureni a yanda nake, bantaɓa aure ba, amma kuma niba budurwa bace a yanzun, ya cuceni yariga ya karɓe abun da nake burin bawa mijina na sunna, waye zai yarda da haka?"

"Nine nan Zahrah, Nasan komai a kan ki, kuma zanyarda da duk wata ƙaddaranki, nine wanda zan sharemiki hawayenki,  kece damuwata bawai budurcin kiba, kiyarda dani dan Allah!!" Doctor Sadeeq yafaɗi hakan cikin jajircewa..

Kamar sauƙan aradu haka Zahrah taji sauƙan kalamansa a cikin kunnuwanta, cak ta tsaida kukan da takeyi haɗe da, da hangame baki tana kallonsa, gani take kamar ma baya cikin hayyacinsa, ƙaryane tayaya za'ace Namiji mai aji, kamar Doctor yace wai ya amince da ƙaddaranta zai aureta,  wannan ba gaskia bane,

"Kada kiyi shakka ko kokonto, ba yaudara'nki nake ba, dagaske nake har cikin zuciyata, don Allah ki bani dama Zahrah, burina da fatana kawai ki amince min!"

Kai Zahrah ta shiga girgizawa, cikin tsananin ɓacin rai da danasin sauraransa da tayi tasoma cewa " Nayi Babban kuskure, haka kuma na tabka nadaman baka daman shigowa rayuwata da nayi, ashe dukanku haka halinku yake, macutane ku azzalumai,  ashe bazaku taɓa sanjawa ba, dama ɗaya kawai idan aka baku, sai ku nemi shigo da manufarku, kaicona da abun da Zaid yayi mini baikasance IZNAH ga rayuwata ba, kaicona dana sake aminta da kai, kaicon zuciyata,  kafita a rayuwata dan Allah, kaje banaso nasake ganinka ko kuma  jinka, katafi kayi nisa da ni, kabarni na rayu cikin salama dan Allah!!" gaba ɗaya hawayen ɓacin rai yagama wanke mata fuska,  ƙoƙarin fita daga motar ta somayi, cike da tashin hankali Doctor Sadeeq ya riƙo hanunta, ko kaɗan baiyi zato ko tsammani ba, saijin sauƙar mari yayi akan kumatunsa,  Zahrah ce ta ɗaukesa da lafiyayyen mari, babu abun da ke kwance akan fuskarta banda tsananin ɓacin rai, 

"Koda wasa kada kasake ƙoƙarin taɓani, mayaudari, dama haka kuke bakuma zaku canza ba!!" fuuuuu haka Zahrah tafice daga cikin motar tamkar kububuwa.  

Tamkar statue haka Dr Sadeeq ya tsaya, komai nasa daina aiki yayi, sai numfashinsa dake fita da sauri,  ganin komai yake tamkar al'amara,  wai yau shine Zahrah ta mara da hanunta, a hankali yasanya hanunsa ya shafi kan kumatunsa inda Zahrah ta wankesa da mari, ko kaɗan baiga laifin Zahrah ba, kuma baiji zafin marin da ta masa ba, babban damuwarsa da tashin hankalinsa, shine yanda yaga Zahrah tana kuka wiwi, sannan kuma ranta yayi matuƙar ɓaci,  tabbas da yasan abun zai ɓaci har haka, to da baiyi gigin furta mata kalmar cewa zai aure ta ba, ko da na minti ɗaya ne bayason ɓacin ran Zahrah, yanzu yasan haka zata kwana tana kuka, maiyasa? maiyasa na kasa jurewa? ni nake burin faranta rayuwa da zuciyarta, amma sai gashi da kaina nasake ruguza farinciki'nta  maiyasa? yatambayi kansa da ƙarfi, cike da haushin kansa ya sanya hanunsa duka biyu ya daki siterin motar tasa, wani irin haushin kansa yakeji,  yayi dana sanin sanar da'ita abun dake cikin zuciyarsa,  "mai yasa na yarda nazamo LOSER?" ya tambayi kansa cikin ƙunan zuciya, yakusan 10 minute yana zaune a cikin motar, da ƙyar ya'iya tada motar yabar cikin unguwar tasu...

Zahrah kuwa tana shiga gida, kaitsaye ɗakinta ta wuce,  zamewa tayi a ƙasa, tashiga rera sabon kuka,  lallai tayarda cewa Ƙaddaranta mai girma ce, daga wannan sai wannan,  bata taɓa zato ko tunani'n haka zai fito daga bakin Dr Sadeeq ba, ko da wasa bata taɓa ayyana wani abu a ranta ga me da shi ba,  maiyasa zai zo mata da wannan maganar a daidai wannan lokacin? maiyasa zai sake maida ita uƙubar da tayi nasaran samun bakin fita daga cikinsa?   tabbas yanzu kam tayarda cewa duhu yasamu mazauni a cikin rayuwarta

"Bawanda zai soni a haka, shima nasan ba sona yake ba, wata manufarsa kawai yakeson cimmawa, ashe ƙaddarorina suna da yawa?" ta tambayi kanta cike da ruɗu.
Sanin bata da amsar bawa kanta, yasanya ta cigaba da kukanta, ganin hakan bazai fishsheta ba yasanya ta ɗauro alwala tazo ta fara gabatar da salla, haɗe da miƙamawa mai kowa mai komai duka lamuranta...

Koda Doctor ya isa gida, baije koda ɓangaren mahaifiyarsa bane, kai tsaye ɓangarensa ya nufa, gaba ɗaya jiyakeyi duniyar ta masa ƙunci,  saboda cimma muradinsa yasake sanya Zahrah a damuwa,  kwanciya yayi lamo akan gado, zuciyarsa cike da tarin tunanuka kala kala, gaba ɗaya kalamanta ne suke yawo a ƙwaƙwalwarsa, babu kalman da tafi tsaya masa a rai kamar inda takecewa " Natabka  nadamar baka daman shigowa rayuwata da nayi, katafi ba naso na sake ganinka ko kuma jinka!!"  wannan kalamannata sunfi komai ɗaga masa hankali,  sam shikam ya ma manta da marin da tayi masa,  saboda bai ɗauki marin a matsayin komaiba, shidai shiga damuwarta ne bayaso, baisan wani irin so yake mawa Zahrah ba, bayason ganinta a cikin damuwa, ba kuma yason ɓacin ranta, amma tayaya Zahrah zata fuskancin hakan?  Yanaso ya aureta yakuma inganta rayuwarta, ba budurci'nta bane abun so a gareshi ita kanta ce abarsonsa, haƙiƙa kowani namiji yana burin auren mace yasameta a budurwa, shima kuma yana burin hakan, amma son da yakemawa Zahrah, yasanya zai iya karɓanta a yanda take.. Haka Doctor yayita saƙawa da kuncewa, da ƙyar bacci ɓarawo yayi nasaran ɗaukarsa.

Ɓangaren Zahrah ma dai hakanne takasance da ƙyar ta'iya runtsawa a wannan dare....

*TURKEY*

*ZAID* ne zaune akan wata haɗaɗɗiyar kujera,  sanye yake da riga long slive, white colour yayinda wandon jikinsa ya kasance baƙi,  suit ne baƙi ɗaure a saman kayan nasa,   sosai yayi kyu a cikin shigartasa,  hanunsa riƙe yake da wani dogon kofi na glass, bakomai ne acikin kofin ba face giya, a hankali yake sipping giyar tasa, yayinda ya ɗaura ƙafansa ɗaya kan ɗaya,   gefensa kuwa Abid ne zaune shima dai irin shigar Zaid ɗinne a jikinsa, sai dai shi nasa kalan sun kasance blue,   "Lokaci fa yana tafiya Zaid, yakamata ace yau munkoma New York, amma bansan dalilinka nacewa muzauna anan ba, ni fa duk yanda instanbul takai ga haɗuwa da daɗin zama, batakaimin new york ba, kasan can akwai mata ƴan harka, amma ni gaskia nan a takure nake!" Abid yakai ƙarshen zancennasa cike da ƙosawa.

Kyakkyawan murmushinsa yayi haɗe da maida kallonsa ga wani kyakkyawan ruwa dake gudana a gefensu,
"Inason zaman Instanbul sosai Abid, domin yanayin garin yanasawa inajin shauƙin abar sha'awata!!"

"Bangane shauƙin abar sha'awan kaba? wai meke damunka ne? kusan tsawon watanni kenan dana fuskanci sauyawa a tattare dakai"

"Sha'awa nakeji Abid, matsanancin sha'awarta nakeji!"
Zaid yafaɗa cike da tsananin shauƙi.

"Sha'awa? wacece ita?" Abid ya tambaya cike da zaƙuwa, domin shikam yarasa wace irin macece Zaid ya kejin sha'awa'rta haka, ko da yaushe cikin maganarta yake, kuma ita kaɗai yakejin sha'awa.

"ZAHRAH NA!" Zaid yafaɗa cikin wata murya mai ɗauke da ma'anoni.

Dariya sosai Abid yasanya, hadda riƙe ciki,  "Zahrah fa kace Zaid, wannan villager girl ɗin, koba sugar baby'nka ba?" Abid yatambaya yana ƙoƙarin gimtse dariyar da ta tasomai.

" Tana da matuƙar mahimmanci a wajena Abid,  bantaɓajin irin abunda nakeji akanta ba, inason kasancewa da'ita a koda yaushe, inaso tazama ita ce mace guda ɗaya dazanna yin sex da'ita dare da rana,  sha'awarta tamun mummunan kamu Abid, kasan yanda nakeji kuwa ?"  Zaid ya tambayi Abid cikin sigar rashin wasa.

"Kokaɗan bansan ya kakejiba, amma kuma Zaid wannan ba sha'awa bane SO ne" Abid yafaɗi hakan da iya gaskiyarsa, domin shi abun da ya fahimta kenan.

Dariya sosai Zaid yashiga yi, haɗe da sanya hanunsa ya daki kafaɗan Abid.
"Shirmen banza, wai SO? menene SO Abid? kasan me kake faɗa kuwa, taya sha'awa zata zama SO, so fa kananufin wai inasonta ne, hahaha Abid ƙwaƙwalwarka ƙaramace, taya za'ayi nayi soyayya da'ita,  sha'awace kawai kuma da zaran na sakeyin sex da'ita nasan komai zai wuce,  tun farkoma danasan ban ƙoshi da'itaba, ai da banbari ta tafiba!!" yaƙare maganar yana mai ɗaga kofin giyarsa yakai baki.

Murmushi kawai Abid yayi, domin yafi kowa sanin cewa Zaid bayason gaskia, amma tabbas shikam anasa hasashen zuciyar abokinsa takamu da so, yana kuma da tabbacin idan har Zaid zaiyi sex da Zahrah sau ɗari, to wannan sha'awar bazata taɓa barinsa ba, saboda dama ba sha'awar bace So ne.

"Shikenan naji ba soyayya bane, sha'awa ce, amma kasan dai yanzu bazaka taɓa samunta ba ko, wataƙilama ta mutu, domin ina da tabbacin cewa baka shigeta da wasa ba"

"Dole zan sameta ne Abid, dole sai ta dawo gareni, kuma dole ta ƙara yarda da ƙudurina a karo na biyu,  aure baya ɗaya daga cikin tsarina, amma idan taƙi yarda dani, saina aureta!"

Saurin kallon Zaid Abid yayi jin abun da yake fitowa daga bakin Zaid ɗin, "Aure kuma Zaid? Abid yafaɗa cike da mamaki.

"Ƙwarai zan'iya aurenta Abid, ƴan matan tana burgeni fiye da zatonka, inason komai nata, tana da kyau na fili dana baɗini, ni nasan mai naji a cikinta Abid, bakuma zanso nasake rasata ba, sha'awarta yasa koda yaushe cikin tunaninta nake, na kuma gama yanke hukunci, nan da sati ɗaya zankoma Nigeria,  badon kowa ba sai don ita, nayi missing tattausan laɓɓanta masu zaƙi kamar zuma!!" Zaid yakai ƙarshen zancennasa yana mai lumshe idanunsa, da suka soma zama ja lokaci ɗaya.

Hangame baki Abid yayi yana kallon Zaid,  "Anya kuwa ba aljana Zaid ya haɗu da'ita ba?" yatambayi kansa,   tabbas baitaɓa ganin Zaid acikin hali makamancin wannan ba, gaba ɗaya Zaid ya sauya, yarage yawan yin sex da mata, a cewarsa wai bayajin daɗinsu, sannan kuma koda yaushe cikin tunani yake, to idan ba so ba meke da munsa ? Abid yakuma tambayar kansa.

A hankali Zaid ya buɗe idanunsa, haɗe da miƙewa tsaye kwalbar giyansa dakuma kofi ya ɗauka a hanunsa kai tsaye yanufi wani babban bene inda anan masauƙinsu yake,  da kallo kawai Abid yabisa har ya ɓacewa ganinsa..
Yana shiga cikin ɗaki  ya ɗaga kwalbar giyarsa ya kafa a bakinsa, saida ya shanye giyan tas kafun yayi wurgi da kwalba'r,   kaitsaye ya nufi inda ma'ajin zane zanen sa suke,  Caboard papers ne dayawa acikin wajen kuma duka ɗauke suke da hoton zanen fuskar Zahrah a jiki, wani ma iya bakinta kawai ya zana, wani ko iya idanunta ya zana,  yana yawan yin zanen ne idan matsanancin kewa da sha'awarta ya da mesa,   ɗaukan caboard paper'n dake ɗauke da zanen bakinta yayi haɗe da mannawa akan nasa bakin,   wani irin zubawa yaji tsikar jikinsa tayi, domin kuwa ji yayi tamkar itaɗince da gaske, zamewa yayi ya zauna a ƙasa daɓas, haɗe da warwatsa caboard paper's ɗin  akan jikinsa.

"Inakewarki Sugar Baby'na ,nayi missing komai naki, duk da cewa nasan kina fushi dani namiki da zafi, amma kiyi haƙuri wannan karon bazan miki da zafi ba, a hankali zan bi da ke tayarda zakiji daɗi har brain ɗinki, zakuma za ki saba da ni a sannu,  na miki alƙawari zandawo gareki!,  kina sona?"  yatambayi zanen fuskarta dake jikin wani ƙaton caboard paper,   "Nasan har yanzu kina sona ko Zahrah na?" still dai wannan zane yakuma tambaya,   murmushinsa mai kyau yakumayi, haɗe da sanya hanu yashafi gefen kumatunsa.
  " Kiyi murmushi Zahrah na, nakusa zuwa gareki, a yanzu zan iya sadaukar da komai na zuwa gareki,  amma fa banso kina yawan fushi, duk da cewa idan kina fushi kinfi  kyau !"
Haka Zaid yayita sambatun sa har bacci ya ɗaukesa a wajen.

Kwance take akan ƙirjinsa, yayinda fuskarta ke ɗauƙe da murmushi, a hankali ya matso da fuskarsa daf da tata,  cike da matsanancin sha'awa ya kamo lips ɗinta na ƙasa yashiga tsotsa a hankali,  cike da ƙwarewa yake cusa harshensa cikin bakinta, cike da soyayya ta soma tsotsan harshensa tana mai lumshe idanunta, a hankali yayi ƙasa da hanunsa zuwa ƙirjinta,  cikin salo yashiga shafa breast ɗinta, yanayin yanda suke sucking tongue ɗin junansu, shiyasanyasu suka fice a hayyacinsu lokaci guda,  ƙasa yayi da kansa zuwa ƙirjinta,  yana shirin ɗaura  bakinsa a kan nipples ɗinta kenan, taɓace masa ɓat, dai dai lokacin yafarka  a hargitse,    wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe, duk da cewa sanyin A.C na aiki a cikin ɗakin amma shi gumi yake haɗawa,  da ƙyar ya'iya miƙewa ya shiga bathroom haɗe da sakarmawa kansa shower. 

ba yau yafara wannan mafarkin ba, amma maiyasa Zahrah take gudunsa acikin mafarki, takan ɓacewa ganinsa a daidai lokacin da yake matsanancin buƙatar ta....


     *5/December/2019

*Voted,Comment, and Share please..... Follow me on Whatsapp and Wattpad @fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

           *SHU'UMIN NAMIJI !!*

      *Written By*
Phatymerhsardauna

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

         *WATTPAD*
   @fatymasardauna

*Editing is not allowed📵*

      *Chapter 48 to 49*

Yajima tsaye a gaban shower ruwa na dukansa, mafarkinsa na yau ne yatsaya masa a rai, duk da kuwa cewa ba wannan bane karo na farko, daya fara yin irin wannan  mafarkin.   Koda wasa baiyi niyar komawa America a yau ba, amma yanzu yaji ajikinsa cewa komawarsa can ɗin yafi masa, domin kuwa mararsa har ƙullewa take saboda sha'awa, gaba ɗaya kwana biyunnan da suka shuɗe baiyi sex ba. A gurguje ya shirya kansa, bayan yasanar da Abid cewa shima ya kimtsa zasu wuce America a yau.  Suna zuwa airport basu wani daɗe ba, jirginsu yaɗaga zuwa sararin samaniya....

Nigeria

Washe garin ranan da Dr yazo da dare yafaɗi muradinsa..

Tun tashinta takejin ƙunci a zuciyarta, hakanan take jin ta tsani komai na duniyar,  badon lecture'n da zasuyi yau mai amfani bane, to tabbas da bazata je makarantar bama.

Doctor Sadeeq ne tsaye a tsakiyar ɗakinsa, yayinda hannayensa duka biyu ke sanye cikin aljihun wandonsa,    shima kallo ɗaya zaka masa kafahimci cewa yana cikin damuwa, kallon sa yamaida kan agogon bangon dake saƙale ajikin bangon ɗakin na sa,  ƙarfe 7 da rabi na safe kenan, tabbas  yasan yau ƙarfe takwas suke da lecture,  yanaji a jikinsa cewa yayi mata laifi mai girma,  sannan idanunsa suna matuƙar son ganinta, to amma a yanda yakeji bazai iya zuwa gareta ba, "idan ma naje nace mata me?" yatambayi kansa.     " Nariga dana furta mata abun dake cikin zuciyata,  dole zanbata lokaci domin samun dawowar nutsuwar ta"   yafaɗi hakan a bayyane, wayarsa ya ɗauka haɗe da kutsawa cikin dialing call ɗinsa,  numbern drivernsa yashiga ƙira kai tsaye, ƙara biyu wayar tayi,  drivern yaɗauki ƙiran,  kasancewar driver'n yasan gidan su Zahrah, yasan ya kai tsaye, bai tsaya yi masa wani kwatance ba, yace masa yaje ya ɗauketa ya kaita makaranta, da "to" kawai driver'n ya amsa masa,   katse ƙiran yayi haɗe da cilla wayar tasa zuwa kan gado,
"Yasan balallai ta yarda tabi driver'n ba, domin yanayinta da yagani jiya, kaɗai ya isa ya tabbatar masa da hakan, amma burinsa ne ya bata ingantacciyar kulawa, shiyasa baiyi ƙasa a guiwaba wajen sa driver'n nasa kaita makarnta, saboda baiso ta hau wani abun hawa bayan nasa....

Ko kwalli, yau bata shafa ba, balle kuma uwa uba fawder,  zumbuleliyar doguwar riga ta sanya, haɗe da ɗaura ƙaton hijab akai,  kallo ɗaya zakayi mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login