Showing 117001 words to 120000 words out of 177624 words
light orange and milk colour, yayinda aka ƙawata jikin ƙofa da window'n da wasu irin haɗaɗɗun labulaye masu kyau, tsakiyar falon kuwa mamaye yake da wani haɗaɗɗen carpet Orange colour,, ga wani irin ƙaton tv plasma dake aje kan wani haɗaɗɗen glass,, falon dai ba'acika masa kayan ado ba amma kuma yaƙawatu sosai komai na falon me tsada ne,, direct wani ɗaki dake cikin falon aka wuce da Zahrah,, ɗakine me kyau wanda yaji royal furnitures milk colour, yayinda aka lailaye kan makeken gadon da wani irin zanin gado pink me kyawun gaske... Akan gado sukayimawa Zahrah masauƙi, Husnah dakanta ta haɗawa Zahrah ruwan wanka, koda tafito a bathroom ɗin hannayen Zahrah dake zaune kan gado ta kamo, haɗe da janta har zuwa cikin bathroom inda ta haɗa mata ruwan wanka...
Wani Turare ta bata tace inji Hajiya Shuwa, sannan kuma tayi mata bayanin yanda zatayi amfani dashi...
Zahrah tana fitowa a wanka Husnah ta shafa mata powder haɗe da lipstick, wani riga da sket na material marar nauyi Husnah ta bata tasanya, take tafito ɗas da'ita, a tsakiyar gado Husnah ta zaunar da Zahrah haɗe da rufe mata kanta da wani irin haɗaɗɗen mayafi me sheƙi da walwali, wasu turaruka masu ƙamshi Husnah takuma feshi jikin Zahrah dasu, take ɗakin yakuma ɗumamewa da ƙamshi,, sake matsowa kusa da Zahrah Husnah tayi cikin murya ƙasa ƙasa tace
"Dan Allah Zahrah karkice zaki ci gaba da wannan kukan naki, ki ɗan daure zuciyarki kinji ƙawata, kuma sannan kada ki hana Doctor haƙƙinsa, nasan zakiji tsoro amma please ki daure kinji ƙawata, banaje falo na amsa waya " Husnah taƙare maganar tana me miƙewa tsaye, idanu tayiwa Auntie Ladi suka fice a tare....
Tun Zahrah na jiran dawowan su Husnah hartasoma jin tsoro, domin kuwa gaba ɗaya gidan yaɗau shiru babu alaman akwai motsin wani mutum bayan ita,,, abun da Zahrah bata sani ba shine su Husnah wayo sukayi mata suka tafi suka barta, sunyi hakanne kuma saboda taƙaitamata wahalan kuka, domin sun san sunace mata zasu tafi zata ƙara fawan kukanta.....
Gyangyaɗine yasoma ɗaukarta, dan haka saita jingina bayanta ajikin saman gadon haɗe da lumshe idanunta da suketa tsiyayar hawaye...
A hankali yaturo ƙofar ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, yasake shiga cikin wata farar shadda sabuwa ƙal sai sheƙi takeyi, ƙamshi ne kawai ke fita ajikinsa, daganinsa kasan yana cikin matsanancin farinciki,, ledan dake hanunsa ya aje, haɗe da takowa zuwa wajen datake zaune ta jingina bayanta da saman gado,, zama yayi akusa da'ita haɗe da ƙiran sunanta,, cikin murya me sanyi da kuma alamar bacci ta amasa masa,, ahankali yasanya hanunsa ya ɗan jaye mayafin dake kanta, hawaye yagani kwance akan fuskarta, hanunta yakamo haɗe da jawota jikinsa, hanu yasanya yashiga share mata hawayen dake kan fuskarta.
"Ki daina kuka kinji my wife, bacci zakiyi ne?" yatambayeta yana me ƙaremawa fuskarta kallo,, fuska ta kuma kwaɓewa, haɗe da kaɗa kanta, cike da shagwaɓa tace
"Ina Husnah?"
Ajiyar zuciya yasauƙe haɗe da sanya hanu yashafi lallausan gashinta dayasha gyara
"Husnah kuma Zahrah?" yatambayeta cike da mamaki..
"Eh tacemin zata amasa waya tana zuwa kuma haryanzu bata dawo ba!" yanzuma dai asangarce tayi maganar,, murmushi yayi mata haɗe da cewa
"Kada kidamu Husnah zata dawo gobe, taso muje kiyi alwala idan munyi salla saikici abinci ko"
Jitayi gabanta yayi wani irin faɗuwa amma kuma yazatayi da rayuwarta babu yanda ta'iya haka tabisa kamar jela harcikin bathroom,, saida yayi nasa alwalan kafun yabata waje itama ta ɗauro alwala,, tana fitowa daga cikin bathroom ɗin ya miƙo mata wata lufaya, a ɗaɗare tasanya lufayan daya bata, hanunta yakama suka hau kan sallaya, shi yajasu salla raka'a biyu, suna idarwa yayi musu addu'o'i haɗe da kama kanta itama yayi mata addu'a... A tsorace ta zauna akan gado haɗe da sake takure jikinta waje ɗaya...
Wani ɗan madaidaicin carpet Dr.Sadeeq yashimfuɗa haɗe da cika tsakiyar carpet ɗin da kayan ciye ciye, hanu ya miƙawa Zahrah alamar tataho garesa, cikin ɗari ɗari haka ta shiga takowa zuwa inda yake, hanunta yakamo yazaunar da'ita acikin jikinsa, hijabin dake jikinta yasoma ƙoƙarin cire mata, da sauri tasake ƙanƙame jikinta, ganin haka yasanya shi yin murmushi, ya fasa cire mata hijab ɗin,, juice ya zuba acikin kofi haɗe da kai kofin bakinta, babu musu tabuɗe bakinta ta kurɓi kaɗan, aje kofin yayi, haɗe da yago gasasshen nama yakai bakinta,, kanta tashiga girgizawa alaman bazataci ba.
"Kiyi haƙuri kici kinji Baby na, kaɗan zakici bamai yawa ba!" yafaɗi haka cike da lallami,,, shida kansa yake bata kazan, bata wani ci me yawa ba tace masa ta ƙoshi, dakansa yatattara wajen yakai kitchine,, yana dawowa ɗakin yasameta tsaye ajikin mirror tayi jigum,, fargabane yacika mata zuciya, wani irin tsoro ne taji ya ɗarsu acikin zuciyarta wanda bazata iya misaltashi ba,,
Kaitsaye drower ɗin dake cikin ɗakin ya nufa, wata doguwar rigan bacci sleeping dress yaciro haɗe da ƙarasowa gareta,, "Kije kiyi brush, wannan kayan kuma kisanya kizo kiyi bacci" hanunta na rawa haka ta amshi kayan sumi sumi ta wuce cikin bathroom, tana kammala brush tasoma cire kayan jikinta, warware rigan da Dr. yabata tayi tashiga ƙaremawa rigan kallo, doguwar rigace na bacci me net, amma kuma tana da faɗin wuya sannan kuma rigan irin me nuna jiki ɗinnan ne,, badon tasoba haka ta sanya rigan ajikinta, hmmm sam bazata iya fita da wannan rigan gaban Dr. Sadeeq ba, saboda gaba ɗaya rigan ta bayyana breast ɗinta, yayinda komai nata yafito fili, hijabin da tayi salla dashi ta ɗauka ta sanya,, a ɗaɗare ta fito daga cikin bathroom ɗin,, zaune tagansa akan gado tuni yasanja kaya zuwa farar jallabiya, murmushi kawai Dr.Sadeeq kejifanta dashi, cikin zolaya yace "Meye narufe jikin da hijabi?"
Ƙasa takumayi da kanta, yanzu kam ko ɗan shagwaɓan ma takasayi masa...
Sarai ya fuskanci halin da take ciki, "Zoki kwanta" yafaɗi haka yana meyi mata nuni da kan gadon dayake zaune,, kamar wacce ƙwai yafashewa haka Zahrah ta zo ta kwanta akan gadon, gaba ɗaya ta takure kanta waje ɗaya,,, miƙewa yayi daga zaunen dayake haɗe da kashe wutan ɗakin ya kunna na bacci, Zahrah najin takusan alamar yakusa zuwa kan gadon taji bugun zuciyarta ya tsananta, yayinda ƙirjinta yashiga wani irin luguden duka,, kwanciyarsa akan gadon yayi dai dai da kusan ɗaukewar numfashinta,,,, da ƙyar ta'iya ƙwato numfashinta, haɗi sa soma sauƙe ajiyar zuciya a ɓoye, kusan minti goma da hawansa kan gadon amma kuma taji baiyi mata wani abu ba, hakan yasa taɗanji zuciyarta tayi sanyi. Shiru tayi tana me jin sauƙar numfashinsa ahankali, wani irin mugun tausayinsa ne taji yaɗarsu acikin zuciyarta amma kuma ita bata da yanda zatayi, tunaninta ne ya katse alokacin da taji sauƙar hanunsa a bayanta,, ahankali ya juyota tadawo tana fuskantarsa,, kallon fuskarta yashigayi batare dayace da ita komai ba, kusan mintuna 4 yayi yana kallonta, cikin wata irin murya wanda batasanshi da ita ba yace
"kicire hijabin nan saboda kiji daɗin baccinki ko"
babu musu ta cire hijabin daga jikinta sai dai kuma bahaka ranta yaso ba, bargo yaja ya rufa musu hanunta yakamo ta cikin bargon yariƙe acikin nasa, "Ki kwantar da hankalinki, nasan kingaji, kiyi addu'a, kiyi bacci me daɗi" yafaɗi haka cikin muryar raɗa, hanunta yasake damƙewa acikin nasa hanun haɗe da lumshe idanunsa, zai bartane kawai saboda tausayinta dayake ji, amma bawai don baya sha'awarta ba, hasalima baita ɓa jin matsanancin sha'awarta irin nayau ba, hakan yafarune kuma saboda baitaɓa samun kusanci me tsanani da ita irin na yau ɗin ba, da wannan tunanin bacci ya ɗaukesa,,,, Zahrah ma dai baccin ne yaɗauketa batare data shiryawa hakan ba,, ƙarfe ɗaya na dare wani irin zazzafan zazzaɓi yarufe jikin Zahrah take tasoma karkarwa haƙwaranta har haɗewa suke, suna ba da wani sauti, hakan yafaru ne kuma sakamakon sanyin AC wanda yayi mata yawa, acikin baccinsa yakejin hucin numfashinta nafita da sauri, a hankali ya buɗe idanunsa ya sauƙesu akanta, da sauri yatashi ya zauna haɗe da kamo kafaɗunta,, "Zahrah!" yaƙira sunanta a hankali,, tanajinsa amma bazata iya amsa masa ba domin kuwa ba iya zazzaɓi ba hatta kanta jinsa take tamkar anɗaura mata gungumen ice, yamata nauyi Da sauri ya sauƙa akan gadon, AC'n yafara kashewa, kana ya buɗe wata ƴar drower maganin ciwon kai da zazzaɓi ya ɗauko haɗe da goran ruwa,, yana zuwa ya ta data zaune, ɓalle maganin yayi yasa mata abaki haɗi da kafa mata goran ruwa, babu musu ta haɗiye maganin, ajiye goran yayi haɗe da hawa kan gadon, hanunsa yasanya akan wuyanta, zafi yaji zau kamar wuta, ajiyar zuciya ya sauƙe, haɗe da cire rigan dake jikinsa, cikin bargon yakoma, haɗe da jawota kusa dashi, ahankali yasanya hanunsa a bayanta yayi ƙasa da zip ɗin doguwar rigan dake jikinta,, cike da nutsuwa ya cire mata rigan,, Zahrah tana jinsa amma kuma ayanzu babu wani abu da zata iyayi wanda zata kare kanta,, bashi kaɗaiba har ita kanta saida ta sauƙe wani irin ajiyar zuciya me ƙarfi alokacin da zallan fatar jikinsu suka samu haɗewa waje guda. lokaci ɗaya yaji tunaninsa yasoma sauyawa, nutsuwarsa tafara gushewa, haka kuma idanunsa sun soma rufewa,, haɗewar jikin Zahrah danasa jikin baƙaramin feeling me girman gaske ya sauƙar masa ba, tunda yake aduniyarsa yau shine karo na farko, da ya fara haɗa jikinsa dana mace haka, yasan yataɓa rungumar Zahrah amma ba runguma irin wannan ba,,,, Zahrah kuwa baƙaramin jin daɗin jikin nasa tayi ba, jitayi gaba ɗaya nutsuwa yasoma sauƙar mata, sake maƙalewa ajikinsa tayi haɗe da cusa kanta acikin faffaɗan ƙirjinsa har yazamana laɓɓan ta suna gogan fatar wuyansa,, jin yanda take ƙara shigewa jikinsa shiya ƙara taimakawa wajen ƙara masa wutar sha'awarta, hannayensa duka yasanya a bayanta yasake riƙeta gam, numfashi kawai yake fitarwa akai akai shi kaɗai yasan meyakeji acikin jikinsa,, yana cikin wannan irin yanayin yaji sauƙar numfashin Zahrah ahankali yana fita da'alama baccine yakuma ɗaukarta,,, haka yarungumeta ƙam acikin jikinsa yayinda yacusa kansa acikin gashin kanta yana shaƙan daddaɗan ƙamshinta dake ƙara rikitasa,, bakaɗan ba ya yi jarumta wajen ganin ya ƙyaleta baiyi mata komai ba, haƙiƙa bakowani irin namiji bane zai haɗa jiki da mace ace ya iya daure zuciyarsa baiyi mata komai ba, balle ma mace irin Zahrah wanda irinsu basu da yawa acikin mata,, da ƙyar bacci ya'iya ɗaukarsa.......
*(Kuyi Haƙuri idan kunga typing error ina busy ne)*
*18/January/2020*
*Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*Editing is not allowed📵*
*CHAPTER 92 to 93*
Ƙiran sallan asuban fari akan kunnensa,, a hankali ya ware idanunsa akanta, baccinta takeyi cikin kwanciyar hankali da'alama zazzaɓi da ciwon kan dake damunta sun jima da kama gabansu,, baisan lokacin da murmushi ya ƙwace masa ba, komai na Zahrah me kyau ne, har idan tana bacci kyawunta baya ɓuya, kallon zara zaran eye lashes ɗinta daya kwanto aɗan ƙasan idanunta yayi,, ahankali ya zare jikinsa daga nata jikin, cikin sanɗa yatura ƙofar bathroom yashige, gudun kada motsinsa ya tashe ta daga daddaɗan baccin da take,, saida yafarayin wanka kafun ya ɗauro alwala,, tsayawa yayi yana kallon yanda taketa fidda numfashi a hankali, badon sallah yazama dole akanta ba, to tabbas da babu abun da zai sanya ya tasheta a dai-dai wannan lokacin, zai bartane tasha baccinta ta ƙoshi,, ahankali yashiga girgiza ƙafanta haɗe da ɗan ƙiran sunanta, cikin murya ƙasa ƙasa... Da yake bata da nauyin bacci, ƙira biyu yayi mata ta buɗe idanunta,, da sauri ta sake jawo bargo ta rufe jikinta, kana tasoma raba idanu, murmushi yakumayi mata haɗe da sanya hanu ya shafi gefen kumatunta.
"Kitashi kiyi sallah, ni na wuce masallaci"
Bata iya amsa masa ba haryafice daga cikin ɗakin,, kallon kanta tashiga yi gaba ɗaya gashinta ya watse yayi buji buji dashi, da'alama dai tasha juyi acikin bacci,,, tana shiga bathroom ta haɗawa kanta ruwa me ɗan ɗumi, wanka tayi itama kana ta ɗauro alwala (🤔Yadai dukanku wanka sai kace 🙊)....
Tana fitowa daga bathroom ɗin ta zura wata jan doguwar riga marar nauyi, haɗe da zura hijab ajikinta, kan sallaya tahau haɗe da dai-dai ta tsayuwarta...... Koda ta'idar da sallan saida tayi azkar kafun ta miƙe daga kan sallayan,, harta zauna akan gado, maganganun Hajiya Shuwa suka faɗo mata arai inda take ce mata _"Kada ta sake ƙamshi yabar jikinta, sannan kuma idan tayi sallan asuba kullum tana shafa turare aduk wani lungu da saƙo na jikinta"_ batasan mene manufar hakan ba, amma dai ta ɗau maganar kuma zatayi aiki dashi. Gaban mirror tanufa haɗe da ɗaukan ƴar ƙaramar hand bag ɗinta dake aje kan mirror'n wani ɗan kwalban body spray ta ciro daga cikin jakar, haɗe da fesawa ajikinta, daga kan wuyanta har zuwa bayan kunnenta, sosai turaren yake da ƙamshi, take ɗakin ya gauraye da ƙamshin turaren,, tana shirin maida turaren cikin jakarta, Dr.Sadeeq yaturo ƙofar yashigo bakinsa ɗauke da sallama,, cikin murya me sanyi ta amsa masa sallaman nasa,, direct inda take tsaye ya nufo, batayi tsammani ba saiji tayi ya buɗe hannuwansa ya rungumeta ta baya haɗe da ɗaura kansa akan wuyanta,,,, idanunsa ya lumshe haɗe da buɗe hanci ya shaƙi daddaɗan ƙamshin dake fita ajikinta cikin wata irin murya yace
"Good morning madam!"
Kunyan sane yakamata, saikawai tayi ƙasa da kanta haɗe da cewa
"Ina kwana"
"Lafiya ƙalau, yajikinki?" ya amsa mata yana me cusa kansa acikin wuyanta..
"Da sauƙi"
Ta mayarmai da amsa cikin ƙasa da murya...
"Ƙamshinki yamin daɗi sosai, kinyi sallah ne?"
Kanta ta ƙaɗa masa alamar "Eh" hanunta yakama yajata zuwa kan gado... Zama yayi kana ya jawota jikinsa,, ɗago fuskarta yayi haɗe da jefa idanunsa cikin nata. Sunanta yaƙira cikin wata irin murya me ɗauke da nutsuwa..
Kanta ta ɗago ta kallesa, ganin idanunsa tsaye cak akanta yasanya tayi saurin meda kanta ƙasa..
"Meyasa kikejin kunya na sosai ne?"
Yayi mata tambayar da bata tsammata ba,, jijjiga kanta tayi alaman
"babu"
Sake matseta acikin jikinsa yayi haɗe da kwantar da kansa akan kafaɗanta.
"Mallakarki danayi wata babban nasara ce dana samu acikin rayuwata Zahrah, inasonki ne da duka zuciyata, dakuma iya gaskiyata, banda niyar cutar dake acikin rayuwar zaman aurenmu, abu ɗaya nakeso kiyi mini shine, ki rage yawan tunani da kuma kukan nan dakikeyi, inajin tsoro kada su haifarmiki da wata cuta, yanzu nasan kina da buƙatar hutu ko, ki kwanta ki huta, kafun anjima sai kiyi break fast"
Miƙewa tayi daga jikinsa haɗe da hayewa kan gadon ta kwanta, amma kuma bata ɗauke idanunta akansa ba, bayan kamar mintuna biyar da kwanciyarta shima yatashi daga zaunen da yake, kan gadon ya hau, har Zahrah taji bugun zuciyarta yasoma ƙaruwa, sai kuma taga ya lulluɓe mata duka jikinta da blanket, agefe da ita ya kwanta haɗe da juya mata baya... Shiru ɗakin ya ɗauka babu abun dake tashi sai sautin fitar numfashinsu,,, bayansa ta kafe da idanu, yayinda a cikin zuciyarta take wani tunani na daban, haƙiƙa duk duniya babu wani namiji daya dace yazamo miji agareta sama da Dr.Sadeeq, ya cancanta ƙwarai, shi mutum ne wanda zaiyi wahala asamu kamarsa, Dr.Sadeeq kuwa lumshe idanunsa yayi bawai don bacci ya ɗauke sa ba,, shima wani tunanin yakeyi daban, baisan meyasa aduk sanda idanunsa zasuyi masa tozali da Zahrah yakejin matsanancin sha'awarta ba, wanda ada kuma ba haka abun yake ba, bazaice da bayajin sha'awarta ba, yanaji sai dai kuma bakamar wanda yakeji yanzu ba, jiya bakaɗan ba ya'iya daure zuciyarsa, amma daba haka ba tabbas da baisan wani irin aika aika zaiyi mata ba, a hankali yaji idanunsa sun soma rufewa da'alama dai shima bacci bai ishesa ba, ae dole ma jiya sunsha gajiya sosai,, cikin mintuna ƙalilan bacci ya ɗauki ma'auratan biyu, yayinda kowanne daga cikinsu da irin samfurin tunanin dake cikin zuciyarsa....
***
10:00 am dai-dai ta buɗe idanunta, haɗe da waresu akan haɗaɗɗen zanen POP'n da ya cika saman ɗakin, kallonta ta mayar ga inda take tsammanin ganinsa, amma sai dai taga wajen wayam babu shi babu alamarsa. Da sauri ta tashi zaune haɗe da maida kallonta ga wani ɗan madaidaicin agogon bangon dake saƙale jikin ginin ɗakin.
"ƙarfe 10 nakai ina bacci?"
ta tambayi kanta cikin yanayi naɗan mamaki.. A hankali tazuro ƙafafunta ƙasa, haɗe da miƙewa tsaye, ɗakalallen cikinta daya soma mata kukan yunwa ta shafa, haɗi da ɗan yamutsa fuskarta, direct ƙofar bathromm ta nufa, ɗan tsayawa tayi ta kasa kunnenta ajikin ƙofar, koda zataji ƙaran ruwa, amma saitaji shiru da'alama dai bakowa acikin bathroom ɗin, murɗa handle ɗin ƙofar tayi tashige ciki,, ruwan wanka ta haɗa yayinda ta cika turaren ƙamshi acikin ruwan, wankanta tayi cike da nutsuwa... Sanye da wani ɗan madaidaicin towel pink colour ajikinta tafito daga cikin bathroom ɗin, hatta gashin kanta ajiƙe yaƙe, still ƙaramin towel ne kuma riƙe ahanunta tana goge gashin kanta dayake ajiƙe,, daidai lokacin Dr.Sadeeq yaturo ƙofar ahankali yashigo, suman tsaye yayi ajikin ƙofar yana me ƙare mata kallo daga sama har ƙasanta, yayinda ita kuwa batasan ma da zuwansa ba, kanta kawai take aikin gogewa, saboda bataji motsin buɗewar ƙofar ba, shikuwa dama yabuɗe ƙofar ne ahankali gudun kada ya tasheta a baccin daya barta tanayi,, wani yawu ya haɗiye, haɗe da jan ƙafansa a hankali yafice daga cikin ɗakin batare daya bari ta ganshi ba,, yana fita yajingina bayansa da ƙofar haɗe da sauƙe wani irin ƙaton ajiyar zuciya,, lumshe idanunsa yayi haɗe da sanya hanunsa acikin tulin sumar kansa yashiga shafawa a hankali,, ashe haɗuwar Zahrah yawuce yanda yake zato yake kuma tunani, wannan wace irin haɗaɗɗiyar surace Zahrah'n sa ta mallaka,, lallai Zahrah mace ce cikakkiya tagaban kwatance,, da ƙyar ya'iya jan ƙafansa ya koma cikin falo, kwanciya yayi akan kujera haɗe da lumshe idanunsa da suka sauya launi lokaci guda...
Zahrah kuwa tana gama goge gashin nata tayi amfani da hand dryer wajen busar dashi mintuna kaɗan gashin yabushe tashafa masa mai,,, wani lotion me ƙamshi ta shafa ajikinta haɗe da murzawa fuskarta hoda da kuma kwalli, light pink lipstick tagoga akan leɓenta, take fuskarta ta tasake yin kyau,, gaban makeken drower'n dake kafe ajikin bangon ɗakin taƙarasa haɗe da buɗewa, kayane jere reras