Showing 69001 words to 72000 words out of 177624 words

Chapter 24 - SHU'UMIN NAMIJI completed Hausa novel

18 Jul 2024

37569

ace tayi hankali,  domin sarai yanzu tasan  salon yaudaran maza baida ƙarshe, suna iya yimaka komai don su samu biyan buƙatarsu, wannan yana ɗaya daga cikin babban dalilin da yasanya ta amince da auren Dr Sadeeq, ko ba komai idan ya aureta ta tsallake wani babban siraɗi na daga yaudaran da Maza sukeyi mawa ƴan mata a wannan zamanin.

Ƙaran wayartane yakatseta daga tunanin da takeyi,  cikin sanyin jiki ta ɗaga ƙiran nasa, haɗe da kara wayar akan kunnen ta.

"Barkanki da hutawa My Princess!"

Dr Sadeeq yafaɗa cike da tsantsar kulawa.

Ɗan guntun murmushi tayi haɗe da cewa "Kaima barkanka dai ya aiki?"

Ɓata fuska yayi tamkar dai tana ganinsa haɗe da cewa "Aiki ba daɗi kokaɗan, ya kundawo a super market ɗin kenan?"

"Eh" tabashi amsa a taƙaice. Domin tsabar gajiyan da ta kwaso har wani bacci bacci takeji.

"Naga kamar kingaji da yawa, ki samu ki ɗan huta, zuwa anjima zanzo gida, inaso na samu Baffa, idan yabani dama zanturo magabata na ayi maganar auren mu,  domin banso akai nanda wata ɗaya ban mallakeki ba!" yaƙare maganar cikin yanayin shauƙi.

Wani irin bugawa taji zuciyarta tayi, sakamakon jin abun da Dr Sadeeq yace. Wani irin yanayi ta tsinci kanta ciki, wanda baza'a ƙirasa da farinciki ba, ba kuma za'a ƙirasa da yanayin baƙin ciki ba.

"Zahrah na!" yaƙira sunanta jin cewa tayi shiru batace dashi komai ba.

"Umm" ta'amsa masa a kasalance.

"Naji kinyi shiru, ko dai bakiyi farinciki da hakan bane?"
Yajefo mata tambayar da batayi zaton zai mata shi a yanzu ba..

"A'a nayi farinciki mana, kawai dai kainane ke ɗan min ciwo" tafaɗi haka don ta kare kanta, gudun kada yafuskanci wani abu.

"Ayya kiyi haƙuri, anjima idan zanzo zan tahomiki da magani ko, yanzu ki kwanta ki huta, nasan ma stress ne, insha Allah zuwa anjima zaki ji ki normal" yafaɗi hakan cike da kulawa.

"To" kawai ta'iya cewa dashi, haɗi da zare wayar akan kunnen ta.

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauƙe,  haɗe da share ruwan hawayen da suka fito daga cikin idanunta.   "Yazama dole nakoyi soyayyarka Dr Sadeeq, domin bayan kai babu wani wanda zai bani kulawa kamar haka, ya Allah kamin maganin matsalolina!" tafaɗi hakan a bayyane, bayan ta ɗaga idanunta zuwa sama.

Da ƙƴar ma ta'iya cusa abincin da Inna ta bata, domin kuwa hakanan taji zuciyarta ta cunkushe.

Kwanciya tayi akan katifarta tana ƴan tunani, take bacci ɓarawo ya siɗaɗo ya ɗauketa, batare da tashiryawa hakan ba....

Zaune yake akan wata haɗaɗɗiyar kujera, wanda take ita kaɗaice kuma na mussaman acikin bedroom ɗinsa, dake cikin guest hause nashi.  ɗan ƙaramin table ne aje a gabansa, wanda samansa ke ɗauke da zungureriyar kwalbar wine da kuma glass cup.

Wayar sace riƙe a hanunsa, gaba ɗaya hankalinsa akan wayartasa yake, murmushine ɗauke akan fuskarsa, yayinda yake playback  ɗin vedi'on daya mata ɗazu fitowarta daga cikin shoprite, batare da ta sani ba.

Harzuwa yanzu bai tantance mai yakeji a jiki da zuciyarsa ba a game da Zahrah, abu ɗaya yasani shine, yasan cewa "yana matuƙar buƙatarta a kusa dashi, fiye da tunanin mai tunani,  yakuma ɗauki haka, amatsayin fitinanniyar sha'awarta da yake" sake playback ɗin vedion yayi bayan yakai ƙarshe akaro na barkatai domin kuwa yayi playback ɗin vedi'on yafi sau goma daga zamansa a wajen zuwa yanzu.
Wani irin sanyi haɗe da kewarta ne suke ratsa zuciyarsa alokaci guda.

"A hankali zankuma cimma burina akanki Zahrah, akaro na biyu ma ina da tabbacin cewa zanyi nasara akan ki, domin niban kasance Loser ba, bakuma zantaɓa kasancewa Loser ba, har abada !" yafaɗi haka cike da son ƙarfafamawa kansa guiwa.. A taƙaice dai haka Zaid yayita playback na vedio ɗin da yayi mawa Zahrah yana kallo, zuciyarsa cike da nishaɗi, abu ɗayane zai hanasa zuwa gareta a yanzu, shine plan ɗin daya shirya mata, bakuma zai je gareta ba, harsai ya tabbatar da cewa ta gama rufzawa cikin tarkonsa, da ya ɗana mata a karo na biyu....
(😲)

Doctor Sadeeq ne tsugune a gaban Baffa Amadu, wato ƙanin mahaifinsa. Bayan ya gama kora masa bayanin duk abun dake faruwa, hatta fƴaɗe'n da akayimawa Zahrah bai ɓoye masa ba, domin kuwa a yanzu Baffa Amadu shine Uba a garesu, kasancewarsa ƙanin mahaifi'nsu.

Ajiyar zuciya Baffa Amadu yasauƙe, haɗe dayin gyaran murya irin tasu ta manya...

"Haƙiƙa kazo da babbar magana Sadeeq, amma kuma duk na fahimceka, bakuma zanyi ƙasa a guiwa ba wajen ganar da mahaifiyarka dakuma ƴar uwarka,  amma kuma kasan  dole sai an haɗa da haƙuri, kasan su mata koda yaushe tunaninsu baya zurfafa, bakuma ko da yaushe suke gane abun da ake so  su fahimta ba, amma tunda kakawo matsalan nan wajena, ka kwantar da hankalinka, ni nan zanje har gida na samu mahaifiyartaka, zamu tattauna akan matsalan!"

Wani irin sanyin daɗi ne yashiga huda zuciyar Dr Sadeeq, sai yanzu yakejin nutsuwa na sauƙar masa, yanzu fatan sa ɗaya, shine Allah yasa mahaifiyarsa ta amince, amma tabbas Zahrah itace burin ran sa...

Daga haka sukayi sallama da Baffa Amadu, bayan ya tabbatar masa cewa lallai zaice yasamu mahaifiyartasa da batun...

Cike da farinciki Dr Sadeeq yabaro gidan Baffan nasa, kai tsaye gidansu ya nufa....

Zama yayi dirshan akan kujeran dake falonsa, haɗe da soma cire safar ƙafansa, fuskarsa cike take da annuri dagani kai kasan yanacikin farinciki...

Turo ƙofar falon nasa akayi da ƙarfin gaske, wanda hakan yatilasta masa ɗago kansa da sauri, don ganin ko waye.

Dammm haka yaji ƙirjinsa yabuga, sakamakon ganin fuskar Hajiyarsa da yayi babu ko ɗigon annuri akanta, saima wani irin mugun kallo da take jifansa dashi.

Cike da girmamawa yace "Hajiya Barkanki da....."
Saurin ɗaga masa hanu tayi, alaman batason jin komai daga garesa..

Cikin ɓacin rai da tuƙuƙin zuciya Hajiya tasoma cewa....

"Lallai ka haifu Sadeeq, tunda har zaka iya kai ƙarana wajen ƙanin mahaifinka, yanzu akan wata watsatstsiyar yarinya, ka ke neman ka bijirewa auren ƴar uwa kuma aminiyata da aka baka? Ashe dama wacce kake ikirarin kana so ɗin, ba cikakkiyar mace bace, sauran layine? kaban mamaki ƙwarai Sadeeq,  amma bakomai ni na sakema har haka ta faru,  kuma tabbas zanɗauki ƙwaƙƙwaran mataki akan ka, daga kai har sakaryar yarinyar da ka bawa soyayyarta amanna,  bansan cewa rashin hankalin naka har yakai haka ba, ashe har zuwa kamun ƙafa wajen mutane kakeyi, akan cewa azo a bani baki, nabarka ka auri wacce tagama raba budurcinta ga mazan layi, hmmm wallahi kasaurari hukuncin da zan yanke, kuma tun wuri ka gaggauta cire tunanin auren wannan yarinyar aranka, domin kuwa bamai yi wuwa bane!" fuuu haka Hajiya ta juya ta fice daga falon nasa ranta amatuƙar ɓace...

Kalmar "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!"
Shine abun da yafito daga bakin Dr Sadeeq, wanda yasanya hannayensa gaba ɗaya ya dafe kansa...     "Me yasa Aunty Raliya? meyasa zakimin haka?" yatambayi kansa cikin takaici dakuma ɓacin rai.   Tabbas yasan Aunty Raliya ce ta sanar da Hajiyansa komai, domin kuwa lokacin da yake gaban Baffa Amadu ta ƙirasa, bai ɓoyemata ba kuma yashaida mata cewa yana gidan Baffa Amadu'n, ashe ita harta gane mai yakawosa, shine kuma tasanar da Hajiyarsu komai...   Take idanunsa suka kaɗa sukai ja,, ba abun da yake masa ciwo kamar aibata Zahrah da akeyi, kowa idan yatashi sai yajefeta da sunan wacce ta watsar da mutumcinta a waje, alhalin kuma itama ba laifinta bane, ƙaddarace dakuma tsautsayi, domin kuwa shi kansa sheda ne akan abun da yafaru da'ita, tunda har kusan haukacewa tayi.  Rasama me yake masa daɗi yayi, da wanne zaiji ne? da soyayyar Zahrah, ko kuma da fushin da Hajiyarsa keyi dashi. Gaba ɗaya ma ji yayi zazzaɓi nason kamasa don haka kawai sai ya koma ɗakinsa ya kwanta, ba abunda yake ambata sai sunan Allah, domin kuwa shi kaɗai ne zai iya kawo masa ɗoki,, dama kuma mu dashi muka dogara shine mai kowa kuma mai komai, sarkin da babu kamarsa, Allah kenan buwayi gagara misali, maiyin duk yanda yaso mai kuma ƙwacewa da kuma bayarwa alokacin da yaso, ga kuma duk wanda yaso.....

Zahrah kuwa tunda ta faɗa duniyar bacci ba'ita tafarka ba, sai gaf da'ana ƙiraye ƙirayen sallan magriba..  Kaitsaye banɗaki ta wuce taje tayi wanka haɗe da ɗauro alwala tazo ta kabbara sallan magriba.

Kayanta marar nauyi tasanya haɗe da ɗauƙan wayarta dakuma ledan da kayan siyayyanta ke ciki, tafito farfajiyar gidan nasu, zaune ta iske Inna tana faman ƙoƙarin kunna redio'nta, wanda koda yaushe take tare dashi kamar jaraba.

"Barka da dare Inna" Zahrah tafaɗa lokacin da tayi mawa kanta mazauni a kusa da Inna'n.

Inna bata amsata ba, saima kafe ledar dake hanun Zahrah'n da tayi da ido, Allah Allah take taga mene acikin ledar, domin  dama bakinta ya bushe neman abun lasawa takeyi,  kasancewar tuwo ta tuƙa abincin dare, bakuma tajin cinsa, tafison tasamu ƙwalam taɗan lasa, like o'o da o'o lol.

Tun Zahrah batakai ga buɗe ledar ba inna tayi gajen haƙuri haɗe da fusge ledar daga hanun Zahrah tashiga dubawa.

Ganin cewa tarkacen su Chocolate's da kuma su biscuit's ne acikin ledar yasanya Inna jan uban tsuka haɗe da bankamawa Zahrah harara.

"Aikin kenan gayyar tsiya, mutum yasan bakacin abu, amma saboda tsinannen baƙinciki dakuma mugunta, ko da yaushe shiyake saya bini bini, bazai sayo abun da duka gida za'a amfana ba mcheeww!"  cikin ƙufula Inna taƙare maganar, domin kuwa ita duk wannan shirmen banzan basonsu take ba, tafiso taga daƙwalen kaza, kokuma gasheshshen nama mai zafi,  yauwa tanan tafi kauri, amma kwata kwata kayan kantin nan ita ba zaɓinta bane.

Da ƙyar Zahrah ta iya danne dariyan Inna dake cikinta aciki.

Buɗe ledan tayi gaba ɗaya haɗe sa sanya hanunta taciro wani ɗan madaidaicin cake wanda daganinsa kasan yasha madara.

"Ungo wannan Inna shikan nasan zaki iyaci, saboda kema nasayoshi" Zahrah tafaɗi haka tana mai miƙamawa Inna cake ɗin.

"Yauwa kokefa, amma da kya bani wasu tarkacen banza" 

Take Inna ta ɓare cake ɗin, tahau ci har lumshe idanu take, domin dai sosai cake ɗin yamata daɗi.

Murmushi kawai Zahrah tayi haɗe da gyara zamanta, tasoma latsa wayarta....

Wani yarone yashigo cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama, atare Inna da Zahrah suka amsa masa.

"Wai ana ƙiran Zahrah a waje" inji cewar yaron..

Wani irin faɗuwa Zahrah taji gabanta yayi harsaida tasanya hanu ta dafe ƙirjinta......

(🤔Miye Zaid yake sake shirya mawa Zahrah ne wai readers🧐.

Hajiya problem🤣 Team Dr saiku shirya kuyo gangami kuzo kuyi banbaki ga Hajiya kozata haƙura 😜)

(Ina jin bacci amma haka nayi tƴping ɗinnan, idan kunga tƴping eror kuyi haƙuri saboda typing ɗin dare nayi)

*Voted,Comment,and Share please..... Follow me on Wattpad @fatymasardauna

9:51 pm.....

(kuyi haƙuri banyi posting da wuri ba naje makaranta ne)
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

               *SHU'UMIN NAMIJI !!*

    
        *Written By*
  *phatymasardauna*

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

              *WATTPAD*
         @fatymasardauna
          〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

*Editing is not allowed📵*

    
     
       *CHAPTER 59 to 60*

Wani irin faɗuwa Zahrah taji gabanta yayi har saida ta sa hanu ta dafe kirjinta daya fara dukan uku uku.....

"Jekace tana zuwa" Inna tace da yaron,, bamusu yaron yajuya yafice daga cikin gidan...

"Yadai lafiyanki kuwa naga kinwani dafe ƙirji?" Inna tatambayi Zahrah, wacce lokaci ɗaya yanayinta ya sauya.

"Bakomai" Zahrah tafaɗa a taƙaice domin kuwa ko tayi ƙoƙarin ganar da Inna halin da take ciki tofa bazata gane ba...

"Tashi maza kije, ba kyau yin watsi da baƙo, wata ƙilama da alkhairi yazo miki, domin na lura keɗin baki da ƙashin tsiya" Inna tafaɗi hakan lokacin da ta miƙe daga zaunen da take.

Cikin sanyin jiki Zahrah takoma ɗaki ta ɗauko ƙaton hijab ɗinta ta sanya.

Tun kafun ta ƙarasa fita daga zauren gidannasu zuciyarta tasoma bugawa, wanda batasan dalilin hakan ba.

Wata mota ce tagani fake a ƙofar gidan nasu, kasancewar akwai hasken wuta, yasanya har kalan motar tana'iya hangowa.

Tsayawa tayi cak daga inda take, domin bazata sake tabka babban kuskuren da ta tabka a baya ba,  batasan waye ba don haka bazata ƙarasa ba, idan wanda ke cikin motar yagaji ya fito, ya isketa daga inda take tsaye...

Cikin hanzari wani wanda baza'a ƙirasa da suna matashi ba,  bakuma za'a ƙirasa da suna tsoho ba, yafito daga cikin motar hanunsa ɗauke da wani kwali, yayinda aka ɗaura wani kyakkyawan flower a saman kwalin... Ganin yanufota kaitsaye yasanya ta ɗan sake ja da baya..

"Sannu da fitowa ranki shi daɗe" mutumin nan yafaɗa..
"yauwa sannu" Zahrah ta bashi amsa a taƙaice...

" dama saƙone aka bani nakawomiki" wannan mutumin ya kuma faɗa cikin rusunawa haɗi da girmamawa, duk da kuwa cewa shiɗin ba yaro bane, domin yakusan haifar  Zahrah'n ma, domin itama bawani yawan shekaru ne da'ita ba...

Cike da tsananin mamaki Zahrah, ta saki baki da hanci tana kallon mutumin dake tsaye a gabanta, yana miƙomata saƙon dake hanunsa...

"Wayekai?" shine kawai abun da ya iya fitowa daga bakinta, saboda gaba ɗaya kanta ya kulle...

Murmushi mutumin yayi haɗe da cewa "Ba'a bani daman sanar  dake koni waye ba, kawai dai an umarceni dana kawomiki wannan saƙon, sannan dan Allah kada kice bazaki ansaba, saƙone mai mahimmanci, yanada kyau ki karɓa, sannan daganinki ke mai ilimi ce, kinsan bakyau maida hanun kyauta baya!" mutumin yafaɗi haka still yana mai sake miƙo mata kwali da flowern dake riƙe a hanunsa...

Kai Zahrah tashiga gyaɗawa, cike da tsarguwa tace " Kana da girma da kuma mutumcin da bazanyimaka gardama ba, amma kuma saidai kayi haƙuri, bazan karɓi abu daga wanda bansani ba, bankuma san menene nufinku a kai na ba" tafaɗi hakan da iyaka gaskiyarta....

"Hakane, amma ki ceci aikina, domin wanda ya ban saƙonnan nakawo zuwa gareki ya tabbatarmin da cewa, idan har baki karɓi saƙon ba, to abakin aikina, kitaimaka, ina da iyalai, kuma da aikina na dogara" mutumin yafaɗi haka cikin rauni.

Zaro idanu Zahrah tayi haɗe da jinjina maganar mutumin aranta, lallai kuwa kowaye ya aikosa yacika ɗan jin kai,  ita kuma irin mutanen da tafi tsana kenan a rayuwarta wato mutum mai jin kansa....

Cike da kokonto haɗi da zullumi tasanya hanu ta karɓi abun da mutumin ke miƙomata.

"Zankarɓane kawai saboda kai, domin na fuskanci rashin karɓana zai iya sanyaka acikin matsala, amma koma waye ya turoka kace masa injini ya sanja hali, domin wannan ba hali mai kyau bane" daga haka tasakai tayi komawarta cikin gida..

Cike da murna'n cewa ta karɓi saƙon wannan mutumin yakoma mota haɗe da yi mata key yabar area'n unguwar tasu....

Zahrah tana shiga gida kaitsaye ɗakinta ta wuce, yayinda Inna ta rakata da  idanu...

Zama tayi akan katifa, haɗe da tsurawa kyakykyawan kwalin nan idanu, ba iya shi kaɗai bane, abun ɗaukar hankali, hadda wannan haɗaɗɗen flower'n dake samansa ma abun burgewane, alal haƙiƙa ma ita flower'n ne yafi ɗaukar hankalinta....
Cikin sanyin jiki tasa hanu ta ɗauki flower'n haɗe da matso dashi kusa da fuskarta....lokaci ɗaya ta zabura haɗe da wurgi da flower'n gefe, take idanunta suka kaɗa sukai jajur dasu, jitayi kanta yafara juyawa,  tabbas bazata taɓa mantawa da wannan ƙamshinba har abada kuwa, ajikin mutum ɗaya tasan wannan ƙamshi, bayan shi kuma batasakejin ƙamshin a jikin kowa ba,, hannayenta ta sanya duka biyu haɗe da dafe kanta dayake sara mata,, tabbas irin ƙamshinsa fulawar nan keyi, take taji wani irin tsanar flower'n  ya cika mata zuciya,  san nan kuma tsanarsa tasake dawo mata sabuwa fil, cike da ɓacin rai ta ɗauki flowern haɗe da fita waje da'ita, ko son ganinta ma batason yi,   kai tsaye wajen da suke aje  shara ta nufa, cike da tsanar  flower'n ta jefa ta cikin kwandon shara, haɗe da furzar da yawu akan flower'n duk wani abu da zai tuna mata da Zaid ta tsanesa...
Ranta a ɓace takoma ɗaki, ita dai Inna dake zaune a tsakar gidan haka ta saki baki galala tana ganin ikon Allah..

"Wallahi na tsaneka, tsana mafi muni, bantaɓajin tsanar wani a raina sama da wanda nakeyi maka ba,  ya Allah kada ka sake haɗa fuskata da tasa!" tafaɗi hakan a bayyane, kuma cikin tuƙewar murya...
Gaba ɗaya ƙamshin da taji flower'n nan nayi ya ɗaga mata hankali,  sabuwar tsanar Zaid yasake ɗarsuwa acikin zuciyarta...
Lallai da zataga wanda yasanya akawo mata flower'n nan da ta gargaɗesa da kada ya sake kawo mata komai nasa, don bata so, domin kuwa duk wani abu da zai sanya tayi tunanin Zaid bata ƙaunarsa, koda sunansa nema batason ji"

Kwanciya tayi lamo akan gado, tana mai da numfashi, ji takeyi gaba ɗaya ta tsani ɗakin nata, domin kuwa ɗakin gaba ɗaya ya ɗau ƙamshin turaren dake jikin flower' ɗin nan....

Wayartace tasoma ƙara alamar shigowar ƙira, ganin Dr Sadeeq ne me ƙira yasanya ta ɗaga wayan, cikin son ɓoye damuwarta..

"Inaƙofar gida" abun da Dr Sadeeq yafaɗa kenan, a cikin wayar, domin kuwa shima dai yauɗin yana cikin damuwa....

Babban tabarma ta shumfuɗa musu a tsakar gida, kafun tanufi ƙofar gida don yi masa iso..

Kusan tare suka shigo cikin gidan, tana gaba yana biye da'ita a baya.. Gaba ɗaya yagama karantar yanayinta, ya kuma gane cewa tana cikin damuwa.

Zama yayi akan tabarman da ta shumfuɗa musu,  haɗe da tanƙwashe ƙafafunsa.. Gaba ɗaya nutsuwarsa ya miƙa zuwa gareta, ta hanyar zuba mata idanu....

Gyara zama Zahrah tayi haɗe da ɗaga idanunta ta saci kallonsa, aikuwa karab idanunsu suka sauƙa akan na juna.. Cikin son basarwa tace " Sannu da zuwa, ya hanya?"

Ajiyar zuciya ya sauƙe haɗe da lumshe idanu..."Hanya ba daɗi duk nagaji da tuƙin ma, i hope you will find a driver that will take me home" cikin zolaya yaƙare maganar..

Kallonsa tayi kawai,  haɗe da yin ɗan murmushi, shiru tayi batare da tace dashi komai ba...

"Meke damunki naganki haka, ko dai ciwon kanne?" Yatambayeta cike da kulawa..

"No bashi bane, ka wai dai gajiya ne, baisakeni ba haryanzu" tafaɗi hakan a taƙaice...

"Kansa yajinjina, haɗe da sake lumshe idanunsa,  shi ɗinma ƙarfin haline kawai yasa sa yazo, amma tabbas damuwar dake damunsa tana da yawa.

"Meke damunka, naga gaba ɗaya kamar baka cikin farinciki?" Zahrah ta tambaya cikin siga da yanayi na nuna damuwa..

Wani irin sanyin daɗi yaji a zuciyarsa, badon komai ba, saidon kulawa da yasamu daga gareta.

Gyara zamansa yayi haɗe da bata duka nutsuwarsa...."Bazan ɓoyemiki ba Zahrah, tabbas inacikin damuwa, kuma duk akan kine,  Ina tsananin sonki Zahrah, ina da burin baki farinciki a cikin rayuwarki,  amma sai dai na  haɗu dake a ƙurarren lokaci, inafata zaki fahimci abun da zance dake?"

Cike da ɗaurewar kai Zahrah take kallon Dr Sadeeq, domin kuwa sam ita bata fahimci inda kalamansa suka dosa ba.

"Mahaifiyata ta zaɓamin matar da zan aura, yanzu haka maganar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login