Showing 57001 words to 60000 words out of 177624 words
kasan cewa tana cikin damuwa da ƙunci.
Koda tayi mawa su Baffa sallama, suma sun fahimci cewa yanayinta ya sauya, amma sai suka share babu wanda ya tambayeta.
Tana kai ƙofar gida zuciyarta tayi wani irin bugawa, sakamako'n ganin motar Dr Sadeeq, da tayi fake a ƙofar gidan nasu, tsayawa tayi cak ganin cewa driver'n sane yafito daga cikin motar, saɓanin shikansa Dr ɗin.
Cike da girmamawa Mudi driver ya ƙaraso inda Zahrah ke tsaye.
" Ranki shi daɗe barka da safiya! dama yallaɓoi ne yace nazo na kaiki makaranta, shi ba zai samu daman zuwa ba, wani aiki ne ya riƙesa, kawo jakar na karɓamiki" Mudi driver ya ƙare zance'n nasa yana mai ƙoƙarin karɓan jakar dake riƙe a hanunta. Saurin ja da baya tayi haɗe da fusge jakarta, cike da ɓacin rai tace.
"Kakoma kace masa bana buƙatar kulawarsa koda kaɗanne, ka kuma ce masa injini yafita a rayuwata, saboda bana buƙatarsa!" tanakai ƙarshen zancennata tasakai tayi tafiyarta.
Da kallo kawai Mudi driver yabita. "Uh ni naga bala'i, daga taimako kawai, to Allah ya kyauta" Mudi yafaɗa yana mai komawa cikin motar, key yayimawa motar haɗe da nausata kan hanya, tabbas zai koma ya shaidawa uban gidansa, duk abun da tace a faɗamai..
Cikin ikon Allah tana isowa bakin titi tasamu mai taxi, bawani ɓata lokaci tashiga yaja sukayi gaba, bayan ta sanar masa inda zai kaita.
Tun shigowarta cikin ajin, Husnah ta lura da mugun sauyawan da fuskar Zahrah'n tayi, domin kuwa kowa ya kalli idanunta, zai fahimci cewa tayi kuka har ta ƙoshi. kasancewar Zahrah'n na shigowa malami yashigo, yasanya Husnah bata samu damar tambayarta komai ga me da sauyawarta ta ba.
Koda aka fito daga lecture, kan dakalin da suka sama zama, yauma sukai mawa kansu masauƙi.
"Wai meke damunki ne Zahrah? gaba ɗaya kinsauya, bayan jiya ba haka muka rabu dake ba, sannan kuma na kula cewa, yau ba Dr bane ya kawoki, maike faruwa?" Husnah ta tambaya cike da kulawa, ga ƙawarta ta.
"Inacikin matsala Husnah! a she a yanzu babu wani, wanda zai taimakeka don Allah sai don biyar buƙatar kansa? na ɗauki yarda ta na basa, na ɗaukesa tamkar ɗan'uwa, na'aminta dashi, nayi saurin yadda haɗi da sakewa dashi, bantaɓa zaton haka zata faru ba, ashe shi abun dake cikin zuciya da ruhinsa daban ne, wani abune saɓanin tunani na!" Zahrah tafaɗa tana mai share ƙwallan daya gangaro daga cikin idanunta.
"Banganeba, kinsani a duhu, maikuma ya sake faruwa? ki faɗamin !" Husnah tafaɗi hakan cike da zaƙuwa, don ta ƙosa taji menene matsalar ƙawarta ta.
"Kinsan abun da yafaru dani Husnah, Zaid yaci mutumci na, ya ƙwaci budurcina da ƙarfin tsiya, ya halaka min rayuwa, shin kinaga akwai wani namiji dazai soni tsakani da Allah, bayan yasan abun da yafaru dani?" Zahrah ta tambayi Husnah.
"Haryanzu banfahimci inda kalamanki suka dosa ba Zahrah, zaifi kyau ace kiwarwaremin komai!" Husnah tafaɗi hakan cikin rashin fahimta.
"Ba gaskiya bane Husnah, bai faɗawa kansa da zuciyarsa gaskiya ba, baizamanto gaskiya ba, soyayyar da yakemin ba gaskiya bace, Husnah bazan yaudari kaina ba, domin nasan babu tayanda za'ayi cikekken namiji mai aji da lafiya kamar Doctor Sadeeq, yace wai ni yake so ya aura! ina kokonto akan al'amarin !" gaba ɗaya hawaye sun gama wanke mata fuska, lokacin da takai ƙarshen zance'n nata.
Nannauyar ajiyar zuciya Husnah ta sauƙe, domin kuwa sai yanzu ta fahimci inda matsalar ƙawartata take, dakuma abun da ke damunta.
"Doctor da kansa yace zai aure ki Zahrah?" Husnah ta tambaya, bayan ta aza hannayenta duka akan kafaɗun Zahrah.
Kai kawai Zahrah ta'iya gyaɗawa, alamar "eh''
"Ba wasa bane Zahrah kamar yanda kika ɗauka, haka kuma ba yaudara bane kamar yanda kike tunani, har yanzu keɗin mai kyauce, kuma haryanzu keɗin haɗaɗɗiyar mace ce abar so ga kowani irin namiji, ba'akanki a ka faraba, baikuma dace ki ɗau hukunci mai tsanani gawanda baiji ba bai gani ba, kina tunanin Doctor Sadeeq yaudaranki zaiyi ?" Husnah ta tambaya.
"Ƙwarai kuwa Husnah, ke kanki kinsani, namiji kamar Dr ba sa'an aurena bane, ko lokacin danake ɗauke da mutumcina yafi ƙarfina, balle yanzu danake fanko, inaso kisani wannan karanbani'n shi na tafka a karon farko, yazo yazamemin babbar matsala, domin kuwa nayaudari kaina, na sawa zuciyata soyayyar wanda har gaban abada yafi ƙarfina, yakuma yi mini rata, na yaudari kaina danaƙi amfani da tunanin cewa Zaid yafi ƙarfina, bazan taɓa yarda nasake aikata haukan dana aikata a baya ba Husnah!" Zahrah tafaɗa cike da raunin murya dana zuciya.
"So baitaɓa zama haukaba Zahrah, kada kicemin kin wulaƙanta Doctor saboda abun da Zaid yayi miki, kada ki yarda da tunaninki nacewa gaba ɗaya maza mayaudara ne, kowa da irin halinsa, kuma masu irin halin Zaid basa ɓoyuwa a kamanni da halaye, soyayyarsa ce kawai tarufe miki ido, har ki ka kasa hango mummunar manufarsa a kanki, yana da kyau ki nutsu kiyi tunani, inada tabbacin cewa Dr Sadeeq, ba zai taɓa cutar da rayuwarki ba, kema kuma yakamata kisan hakan, kada tunaninki ya gushe ki kasa tantance fari da baƙi, wlh ni ina da tabbacin cewa Dr Sadeeq ba mutumin banza bane, bakuma zan ɓoyemiki ba, tabbas idan kika tsaya wasa da damarki, to zata miki mummunan suɓucewa, haƙiƙa Dr Sadeeq haɗaɗɗen gaye ne, wanda ko wacce mace zatayi fatan samunsa a matsayin mijin aurenta, nasan idan nace miki kiyi soyayya yanzu na haɗaki da babban aiki, amma zai kyautu ace ki koyawa zuciyarki soyayyar Dr Sadeeq, shawara nake baki Zahrah, idan kuma har kikayi amfani dashi, bazaki taɓa danasani ba, dan Allah ƙawata kiyi tunani mai kyu!" Husnah tafaɗi hakan cikin son ƙarfafawa Zahrah guiwa.
Hawayen dake zuba daga cikin idanunta ta sanya hanu ta share.
"Bazan iya ba Husnah, bazan iya taɓa sake son wani ba a cikin rayuwata, kada ki ga laifina, nasan Dr Sadeeq yafi ƙarfina, yana da asali, yana da ƴan uwa, yanada gata, yana da kuɗi, yanakuma da ƴancin da zai zaɓi matar aure wacce ransa keso, nikuma fa? idan kikayi dubi da tushena, to ban cancanta da zama inuwa ɗaya da shi ba, nifa yanzu banda wani ƴancin da zan iya zaɓin mijin aure da kaina, sbd akwai nakasa acikin rayuwata, dole sai mai tawakalli ne zai iya aure na, to maiyasa zansanya kaina a cikin wahala? balallai farincikin da Dr Sadeeq ke ƙoƙarin bani yakasance dauwamemmeba, nafaɗamasa yafita a rayuwata Husnah, a yanzu bana buƙatar kowani namiji, zaifi kyautuwa a gareni nayi rayuwata ni kaɗai, nayarda da ƙaddarata, amma kuma yazama dole na kiyaye sake jefa kaina a haɗarin soyayya!"
Rungume Zahrah,
Husnah tayi ajikinta, sosai tausayin ƙawarta ta ya kamata, haƙiƙa Zaid yacutar da rayuwar Zahrah, ya rabata da duk wani sukuni nata, amma a kwai Allah.
"Haƙiƙa dole zakiji ciwo Zahrah, amma yana da kyau ki zurfafa tunani, ni ina da tabbacin cewa Dr Sadeeq auren ki yakeso yayi bada wasa ba, amma abun da kikayi masa baki kyauta ba, ki basa haƙuri, koda kuwa bazaki auresa ba, yayi babban ƙoƙari acikin rayuwarki, kiyi nazari, amma kuka ba naki bane, kuma yana da kyau rama halacci da alkhairi !"
Gaba ɗaya Zahrah jitayi jikinta yayi laƙwas, take marin da ta shararawa Dr Sadeeq akan fuskarsa ya dawo mata, wani irin faɗuwar gaba taji, ko kaɗan batayi tunanin zata iya kai hanunta jikinsa da sunan duka ba, amma a daren jiya ɓacin rai yasanya idanunta rufewa, harta iya ta mare sa batare da tayi tunanin komai ba, tabbas komai yayi mata bai cancanci mari daga gareta ba.
Gaba ɗaya kasa sakewa a cikin makarantar Zahrah tayi a wannan ranan, dole ta tattara yanata yanata ta dawo gida.
Zaune take jigum akan tabarma yayinda hannuwanta ke dafe da ƙuncinta, idan da za'a ce za'a kasheta idan bata faɗi, tunanin me take ba, to tabbas da sai dai a kashetan, amma ita kanta batasan tunanin mai take ba.
Inna da fitowarta kenan daga bayi, hanunta riƙe da buta, kama ƙugu tayi, haɗe da maida kallon ta zuwaga inda Zahrah ke zaune tayi jigum.
"Wai lafiyanki kuwa Zahrah? meke damunki ne? tun safe haka kike sukuku, yanzu kuma kinyi tagumi tamkar wacce akamawa mutuwa, kodai halinki na da, kike son dawowa dashi ne? to wallahi bazan ɗau wannan iskancin ba, tun wuri ma kisani!" Inna taƙare maganar cikin faɗa faɗa.
"Ko ɗaya bahaka bane Inna, narasa taya zan ɓullowa matsala ta ne!" Zahrah tafaɗa cike da sanyin murya.
"Matsala! wace irin matsala kuma?" Inna ta tambaya cike da son jin gulma.
"Inna wai Likita ne yace zai aure ni !" Zahrah tafaɗi hakan cikin sarƙewar murya.
"Likita yace zai aure ki!" Inna ta maimaita maganan cikin ƙaraji haɗe da sanya duka hannayenta biyu ta dafe ƙirjinta.
Kai kawai Zahrah ta'iya gyaɗa mata domin zuwa lokacin har ƙwalla sun soma cika mata ido.
Wani irin guɗa Inna tasa, haɗe da sake kama ƙuƙu, "Lallai kuwa, wannan babban al'amari ne, mai ɗauke da tarin farinciki, Allah yasa dai kin amince masa?" cike da zaƙuwa inna taƙare maganar.
"Bazan iya ba Inna, kuma ma ni yanzu babu batun aure a tsarina,zan zauna kawai naƙare rayuwata cikin ƙaddarata!" Zahrah tafaɗa lokacin da hawayen da suka cika idanunta suka samu daman gangarowa.
Salati Inna ta sanya, haɗe da soma tafa hannaye.
"Amma kedai Zahrah anyi shashar banza, sokuwa marar wayo, ashe dai baki da hankali, yanzu a yanda kike ɗin nan, kin samu ance za'a aure ki a haka, kice wai baki amince ba, lallai yau nasake tabbatar mawa da kaina cewa ke wawuyace, to wlh baki isa ba, baki isa ɓarar mana da alkhairan da zamu samu ba, aure dole ko kina so ko bakya so, wato kinfiso kita zama damu, goɗo goɗo dake ba aure ko, to kisa aranki cewa aurenki da likita ba fashi, dole!"
"Babu wanda zai mata dole!" Muryan Baffa dake shigowa cikin gidan yakaraɗe kunnuwansu.
"Maikake shirin faɗa ne malam, kakosan me ta aikata kuwa, Likita fa yace yanason aurenta amma taƙi?"
"Ƙwarai kuwa duk na saurari zancen ku, magana ta gaskia Salame, baza'ayiwa yarinyar nan dole ba, yanzu lokacin ta ne, yakamata a bar rayuwarta tasha iska hakanan!" Baffa yafaɗi maganar sanda yayi mawa kansa masauƙi akan wani ɗan dakali dake tsakiyar gidan.
"Laaaa shikenan kuma, kakosan abun da kake cewa? kana nufin zuba mata idanu zamuyi, ba mu isa mu sata dole ba? wani shan iska kake ƙoƙarin samawa rayuwarta, sanin kankane cewa babu wani wanda zaizo yace zai jajiɓeta a yanda taken nan, don kawai likita ya rufa mata asiri yace zai aureta, saikayi ƙoƙarin hure mata kunne."
"Tashi ki koma ɗakinki kinji Zahrah, kiyi tunani mai kyau, idan kin yanke hukunci to kisanar dani!" Baffa yafaɗa cike da kulawa.
Cikin rashin ƙarfin jiki haka Zahrah ta koma cikin ɗakinta, yayinda take jiyo bala'in Inna a tsakar gida.
Jingina bayanta tayi da bango, haɗe da lumshe idanunta, saiyanzu take jin cewa bata kyautawa Doctor Sadeeq ba, amma kuma shima baikyautu ace yazo mata da magana mai nauyi kamar wannan ba, ko da wasa bata taɓa kawowa a ranta cewa wani zai sota anan kusa ba, gaba ɗaya ta cire soyayya a tsari da jerin rayuwarta, tabbas sai dai ta yaudari kanta, amma tasan bazata taɓa ƙara son wani ɗa namiji ba a rayuwarta, ta yarda da shawaran da Husnah ta bata, amma kuma abune mawuyaci, tarayyanta da Dr Sadeeq yazama mai ɗorewa, shin dagaske aurenta yakeso yayi koko shima wata manufartasa yakeson cimmawa? tatambayi kanta tambayar da bata da amsa, "Idan bakiyi aure ba, haka zaki dawwama Zahrah?" wata zuciyarta tayi mata wannan tambayar. hawayene suka shiga gudu akan fuskarta, lalllai akwai babban ƙalubale a gabanta.
Zaune yake akan derny table ɗin dake tangamemen falon Hajiyar tasa, plate ɗin abinci ne aje a gabansa, yayinda yake juya spoon ɗin dake cikin abincin dake gaban nasa a hankali, kusan mintuna 10 kenan da kawo masa abincin, amma yakasa koda kai loma ɗaya ne na abincin bakinsa, gaba ɗaya hankali da tunaninsa baya garesa.
Cike da tuhuma Hajiya da tun ɗazu take kallon sa tace
"Wai meke damunka ne Sadeeq? gaba ɗaya yanayinka ya sauya, kowa yaganka yasan cewa kana cikin damuwa? gashi nace kaje gidan su Saleema, amma kayi banza da maganan bakaje ba har yau"
Ajiyar zuciya Doctor Sadeeq ya sauƙe haɗe da maida kallonsa ga mahaifiyar tasa.
"Inada damuwa Hajiya!" yafaɗi hakan cikin sanyin murya.
"Subahanallah! damuwa kuma Sadeeq, damuwar me?" Hajiya ta tambaya cike da kulawa, Allah yasani tana matuƙar son ɗan nata.
"Nasamu wacce nake so ne Hajiya!" Sadeeq yafaɗa cikin ɗar ɗar, don baisan ya Hajiyar tasa zata ɗauki al'amarin ba.
"Kasamu wacce kake so? wani irin magana ne wannan, wato so kakeyi kamai dani ƙaramar mace ko, to wallahi baka isaba, bazai taɓa yiwuwa ba, nariga dana gama magana da iyayen Saleema, har ƙanin mahaifinka yashigo cikin lamarin, saboda haka wannan batun kama dainasa tun kafun ranka yakai ƙololuwa wajen ɓaci, banason shirme!" Hajiya tafaɗi maganar a fusace, haɗe da tashi tabar masa falon.
Tabbas dama yasani ko da Zahrah ta amincewa aurensa, to balalle ne Hajiyarsa ta amince masa ba, amma yasan cewa yanamawa Zahrah so mai tsanani, kuma insha Allah, zai aure ta ya rayu da'ita har zuwa ƙarshen rayuwarsa, domin yaji hakan a jikinsa.
(Tofa readers kunji abun da Hajiyar Dr tace, shi kuma kunji abun da yace, koya zata kaya oho.... Kuyi haƙuri wlh yau ina busy! Shiyasa na muku kaɗan.)
*7/December/2019*
*Voted,Comment, and Share please..... Follow me on Wattpad @fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
*Phatymasardauna*
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
'''{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*Editing is not allowed📵*
*Chapter 50 to 51*
Cikin rashin kuzari yamiƙe haɗe da nufar hanyar barin falon, ko kaɗan babu nutsuwa acikin zuciyarsa, ko sake bi takan abincin nasa baiyi ba, haka yafice daga cikin falon. kaitsaye ɓangarensa yanufa. Shirya kansa yayi cikin riga da wando na suit. kaitsaye asibiti ya wuce domin kuwa akwai wasu patient da zai gani.
Gaba ɗaya tunanin Zahrah ya kulle, hartakai ta kawo ko makaranta taje ma bata da wani aiki saina tunani, ko karatun ma da ake koyar dasu bata fahimta, abubuwane sukai mata yawa, tayi matuƙar danasanin marin da tayi mawa Dr Sadeeq, haƙiƙa idanunta sun rufe, batare da tayi tunanin komai ba ta yanke hukunci, sai dai kuma har yanzu tunaninta daya gushe bai dawo gareta ba, takasa yanke hukunci, haka kuma takasayin tunani mai kyau, saidai tayarda da abu ɗaya. shine Doctor Sadeeq sam basa'an auren ta bane, yafi ƙarfinta. Yau kimanin kwana huɗu kenan da faruwar haka a tsakaninsu, tundaga wannan daren kuwa harzuwa yau, Dr baisake zuwa gareta ba, saidai fa kullum safiya, yana turo drivern sa akan yaɗauketa yakaita makaranta. amma zancen dai ɗayane, bata taɓa yarda tashiga motar, koma sauraran driver'n nasa batayi.
Dariya sosai Mahmud yashiga yi, a lokacin da yagama jin matsalolin abokin nasa, haƙiƙa Sadeeq yabasa dariya, ko da wasa bai taɓa tunanin wai Namiji kamar Sadeeq zaiji tsoron furtawa mace kalmar soyayya ba.
Tsuka Dr Sadeeq yaja haɗe da ɓata fuska cike da takaicin dariyan da Mahmud ɗin ke masa yace
" Bawai nafaɗa maka matsalata bane don kasani a gaba kayita min dariya ba, mafita nake nema Mahmud, gaba ɗaya kaina ya kulle, inasonta banakuma tunanin zan'iya barinta, amma kuma naga alamomin cewa zan rasata a fili!" Dr Sadeeq yafaɗi maganar cikin son abokinnasa ya ƙarfafa masa guiwa.
Ƙoƙari Mahmud yayi wajen tsaida dariyar tasa haɗe da gyara zama
"Yazama dole nayi maka dariya Sadeeq, a matsayinka na likita bokan turai, ka kasa jure zafin soyayya, amma kuma ko kaɗan banga laifinka ba, sai dai kuma, akwai ƙalubale a gabanka!" Mahmud yaƙare maganar yana mai waina pen ɗin dake riƙe a hanunsa.
"Wani irin ƙalubale kenan Mahmud?" Dr Sadeeq yatambaya cike da zaƙuwa, saboda shi mafita kawai yake nema.
"Nasara ko kuma akasinta, sune babban ƙalubalen da zaka fuskanta, amma ina mai maka fatan nasara, duk dacewa banganta ba, amma nasan tahaɗu sosai, saboda nasan abokina ya'iya zaɓe!" Mahmud yafaɗi hakan cike da barkwanci, wanda hakan kuma halinsa ne.
"Bazaka taɓa canjawa ba Mahmud, kai ko da yaushe idan ana magana mai amfani saikayi yanda kayi ka sako wasa a ciki." Dr Sadeeq yafaɗi hakan yana mai shafa suman kansa.
Ƴar ƙaramar dariya Mahmud yayi haɗe da ɗaukan cup ɗin juice ɗin dake gabansa yakai zuwa bakinsa.
"Babu amfanin ƙara tada zancen a gareta Sadeeq, tunda ta nuna maka bata sonka, inaganin kabata lokaci, ko ba komai zatayi tunani mai kyau, amma fa hakan danace bawai yana nufin kada kasake zuwa gareta bane, zaka iya zuwa gareta ako da yaushe, amma kada ka sake ɗago mata da zancen inaga haka zaifi!" Mahmud yafaɗi hakan cike da son ƙarfafamawa abokinsa guiwa.
Ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya Dr Sadeeq ya sauƙe, haɗe da haɗiyar yawu, sai yanzu yasomajin sanyi a cikin zuciyarsa, domin kuwa da gaba ɗaya kansa ne ya kulle.
"Zanyi yanda kace Mahmud, sai dai kuma inajiyewa kaina tsoro, kada a gaba taƙi amsata, sannan kuma yanzu bansan da wani ido zan kalle ta ba!" Dr Sadeeq ya faɗi haka cikin ɗar ɗar.
Dariya Mahmud yakuma kwashewa dashi a karo na biyu, lallai yayarda cewa so mugun abune, domin kuwa shi kaɗai ke sa jarumi kuma gwarzon namiji acikin tsoro dakuma ɗar ɗar.
"Yanaga jikinka gaba ɗaya yaɗau rawa, kada dai kabani kunya, tsoronta kakeji tun yanzu, idan kuma akayi auren yaya kenan?" Mahmud yatambaya cike da shaƙiyanci.
Tsuka kawai Dr Sadeeq yakuma ja, haɗe da miƙewa tsaye, domin idan yabiye ta Mahmud to baƙin ciki sai ya cika masa zuciya, domin kuwa halin Mahmud ne tsokana da yawan barkwanci.
"Gwamma nayi tafiyata zaifi min, kayi dariyanka ka ƙoshi, ai nine nakawo kaina office ɗinka, kana da right ɗin da zaka iyamin komai" Dr Sadeeq yakare maganar yana mai gyara zaman suit ɗin dake jikinsa.
Ko sake sauraran Mahmud dake ta faman dariya baiyi ba, yayi ficewarsa daga office ɗin Mahmud ɗin.
Cikin ɗan kuzarin da yasamu yake tuƙa motar tasa, yanzu kam yagama aminta da shawaran da zuciyarsa ta basa. Kai tsaye gida ya koma, wanka yayi haɗe da shirya kansa cikin wani haɗaɗɗen riga da wando na jeans masu kyaun gaske, sosai kayan sukai masa kyau a jiki, suka kuma fito da asalin kyawu da kwarjininsa, babu abun dake tashi ajikinsa sai daddaɗan ƙamshin turare. Makullin motarsa ya ɗauka haɗe dasakai yafice daga cikin ɗakin.
Zaune take