Showing 120001 words to 123000 words out of 177624 words
acikin drower'n kala kala sai wanda ranka yaso zaka saka, wata jar atamfa taciro wacce taji ɗinkin pencil gown,, tana sanya doguwar rigan yayi mata kyau haɗe dayi mata ɗas ajikinta, daga kan guiwanta harzuwa ƙafarta atsage yake ta bayan rigan, tanason atamfar sosai saboda tana ɗaya daga cikin kayan da Maman Husnah ta bata, Husnah ce kuma takai akayi mata irin wannan ɗinkin duk da kuwa irin tsadar da atamfar take dashi, kallon kanta tayi acikin madubi, murmushi tasakarwa kanta saboda ita kanta ta yaba da yanda rigan tayi mata kyau ajiki, wani ɗan madaidaicin vail me kalan ja ta ɗauka haɗe da rufe jikinta, duk da kuwa cewa kayan yana da ɗan kwali, sai dai bazata iya tafiya daga ita sai wannan rigan agaban Doctor ba saboda sosai hips ɗinta suka bayyana, ga shi breast ɗinta sun bayyana kansu ta saman rigar kasancewar wuyan rigan yana da ɗan faɗi. Da turaruka masu daɗi ta feshe jikinta... A hankali ta buɗe murfin ƙofar ɗakin tafito, ɗan tsayawa tayi tana kallonsa,, kwance yake akan kujera yayinda idanunsa ke a lumshe, yasha adonsa cikin wata bugaggiyar shadda blue colour. Murmushi tayi domin kuwa yayi mata kyau, sosai kuma hasken fatarsa yasake bayyana acikin blue ɗin kayan. A hankali tashiga takawa har zuwa tsakiyar falon, ƙarewa falon kallo tashiga yi, ita dai haryanzu bata gamsu da cewa wai nan ɗin falon ta bane, koda wasa ma bata taɓa tunanin zata shiga cikin daula irin wannan ba,, bata ankara ba saiji tayi anriƙe mata hanu, da dauri ta juyo don batayi zaton idonsa biyu ba,, Murmushi yasakar mata haɗe da cewa,
"yaushe kika tashi?" yayi tambayar kamar bashi yaganta ɗazu ba..
Zama tayi akan kujera haɗe da cewa " banjima da tashi ba"
Tashi yayi daga kan kujeran haɗe da kama hanunta, kaitsaye haɗaɗɗen darny area'n dake cikin falon yanufa da'ita, jawo kujera ɗaya yayi daga cikin kujeru huɗu dasuka ke waye wani babban table, zaunar da'ita yayi haɗe da buɗe wani babban food flask, plate ya ɗauka yazu ba mata soyayyen dankalin turawa'n dake cikin kulan (Chips) wata food flask ɗin yasake jawowa pepper chicken ne dayasha albasa, shima zuba mata yayi haɗe da haɗa tea acikin wani cup, turo mata duka plates ɗin dakuma cup ɗin tea ɗin yayi gabanta,, saurin ɗago kanta tayi ta kallesa, kansa ya jinjina mata alamar koma me take tunani hakane, take ta shagwaɓe fuska haɗe da cewa "Bazan iya cinye duka wannan abincin ba yamin yawa"
"Bakomai kici sosai, nasan kinajin yunwa" yafaɗi haka yana me ƙoƙarin barin wajen.
"Kai kuma fa?" batare da ta shiryawa fitowar tambayarba, saikuma bakinta yayi saurinfurtawa,, tsayawa yayi da tafiyar haɗe da juyowa, murmushi yayi mata haɗe da cewa "Ni bayanzu zanci ba" harya fice daga cikin falon bata ɗauke idanunta daga kansa ba,, ajiyar zuciya ta sauƙe haɗe da ɗaukan fork tasoma cakan chips ɗin tana kaiwa bakinta, dama yunwa takeji sosai,, sosai taci chips ɗin saidai tea ɗin sama sama tasha shi, naman kuwa ko taɓa shi batayi ba, domin ita gaba ɗaya naman kaza baiwani dameta ba, tafison gasashshen naman sa, fiye da na kaza, sai da taji cikinta yayi haniƙan kafun ta kimtsa wajen haɗe da miƙewa takoma cikin falon,, haryanzu dai idanunta basu ƙoshi da ƙarewa falon kallo ba, rayuwa kenan wai yau ita Zahrah ce zaune acikin wannan katafaren gida dasunan gidan aurenta, ita da ko gado bata dashi akan zallan ƴar katifa take kwana sai gata yau ta kwana akan haɗaɗɗen gado harda lallausan bargo da ta rufa dashi,, a hankali ya turo ƙofar falon yashigo, wayarsace riƙe a hanunsa yana latsawa,, gaf da'ita ya zauna har kafaɗunsu suna gogan na juna, hanunsa ya sanya ya shafi ɗa kalallen cikinta, "Wannan ɗan ƙaramin cikin baiƙoshi ba"
Murmushi tayi masa haɗe da waro idanunta "Dan Allah kayi haƙuri wallahi na ƙoshi" tafaɗi haka tana me ɗauke hanunsa daga kan cikinta.. Kallonta yashigayi yana me karantar yanayinta yayinda ita kuma tayi ƙasa da kanta, batason haɗa idanu dashi kwata kwata, "taso muje" yafaɗi haka yana me miƙewa tsaye, babu musu ta miƙe, hanunta ya kama suka nufi wata ƙofa dake cikin falon, key ya sanya ajikin ƙofar ya murɗa, tura ƙofar ɗakin yayi, still hanunta na riƙe acikin nasa hanun suka kutsa cikin falo'n, falone ma dai-dai ci wanda aka kewaye tsakiyansa, da wasu kujeru dark purple masu kyau, yayinda tsakiyar falon kuwa aka cike sa da wani ɗan madaidaicin chanies carpet dark and light purple colour, wasu labulaye masu kyau kalan light purpule su suka ƙawata jikin ƙofa dakuma windown falon, wani ɗan ƙaramin plasma ne maƙale ajikin bangon falon, su kenan iya abun dake cikin falon amma kuma duk da haka falon yayi kyau, kasancewar kalan kujeru da labulayen kalane me ɗaukar hankali, ga kujerun sunsha pillow ƴan ma dai-dai ta gwanin ban sha'awa, yana riƙe da hanunta suka kuma shiga cikin wani ɗaki dake cikin falon,, gadone me kyau irin na zamani da drower'nsa me ɗauke da murafe shida, sai kuma su dressing mirror dakuma abun aje takalma da jaka,, kayan furnitures ɗin bawasu masu tsada bane daga kujerun har gadon bazasu wuce dubu ɗari huɗu ba, amma kuma anyi kayan da kyau da kuma inganci,, kallon sa Zahrah tayi alamar tanason ƙarin bayani,, murmushi yasakar mata haɗe da sa hanu ya shafa kumatunta, yace da'ita
"Kayan ɗakin da Baffa yayi miki ne"
Daɗi da farinciki ne suka cika zuciyar Zahrah take tacigaba da wurga idanunta tana kallon kayan, Allah sarki Baffa ashe haka yayi mata ƙoƙari batasani ba, lallai Baffa yafaranta ranta sosai, bata taɓa tunanin zata samu kaya haka ba, ashe dai Baffa yanasonta yana kuma ƙaunar fitar da'ita kunya, lallai wannan kaya sunfiye mata komai, saboda koba komai zata tsallakewa gorin wasu mutanen, wani irin tausayin Baffan nata ne taji ya sake ɗarsuwa aranta,, duk da cewa shiba mawadaci bane amma yayi ƙoƙari ya wadata ta da kayan ɗaki masu kyau dai dai da me rufin asiri, babu abun da zatace da baffanta sai godiya,, kan gadon taje ta zauna tana murmushin jin daɗi, sai taji tafi ƙaunar ɗakin ma fiye da wanda aka kaita daga farko, duk daɗin kyauta dai baikai ace da kuɗinka kacire ka saya ba.
"Yanaga kin wani zauna madam? taso muje nunamiki kawai nayi, bawai nace anan zaki zauna ba" Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana me miƙa mata hanunsa alamar takama sutafi,,
Shagwaɓe fuska Zahrah tayi haɗe da kwantar dakanta gefe
"Nidai nafison nan please kabarni anan!" taƙare maganar cike da zallan shagwaɓa..
Takowa yayi yazo gaf da'ita haɗe da sanya hanunsa ya ɗago kafaɗunta.
"Nan ɗakin hutawan kine, can kuma ɗakin aurenki ne ɗakin dana zaɓa mana ni dake domin muyi rayuwar auren mu, kodai baki yaba da zaɓin nawa bane? kokuma baki amshi kyautar danayi miki bane?"
Ɗara ɗaran idanunta ta ɗago ta sauƙesu akan nasa idanun, kanta ta girgiza cikin sanyin murya tace " Ba haka nake nufi ba, kuma nayarda da duk inda kazaɓamin zanyi rayuwa aciki, kayi haƙuri idan maganata ta ɓata maka rai ban....."
"Shiiiiii" ya katseta ta hanyar ɗaura hanunsa akan laɓɓanta, jawota jikinsa yayi , haɗe da sanya yatsarsa yashiga zagaye ɗan ƙaramin bakinta,, ƙasa tayi da'idanunta domin kuwa bazata iya jure kallon cikin idanunsa ba, sake matso da fuskarsa yayi daf da tata har numfashinsu na'iya gauraya waje guda, yayinda dogon hancinsa ke gogan nata hancin, atare suka lumshe idanunsu, ahankali laɓɓansa suka sauƙa akan nata laɓɓan, baikai ga soma yin kissing ɗinta ba ƙaran wayarsa ta karaɗe cikin kunnuwansu, da sauri ya sake ta,haɗe da sanya hanu acikin aljihunsa ya ciro wayarsa dake ta faman ƙara, katse ƙiran yayi haɗe da kashe wayar baki ɗayanta ya kuma maidata cikin aljihun rigansa.
Hannayenta dake cikin nasa hanun ya murza haɗe da ɗanyin ƙasa da murya "Kibani aron 1 hour inaso in ɗan fita"
Batasan lokacin da ta ɗago kanta ta kallesa ba, mamaki ya bata wai ta basa aron 1 hour shida ƙafarsa ae bazata ɗaure saba,
Baijirayi abun da zatace ba yakama hanunta suka fice daga cikin ɗakin, direct asalin falonsu suka dawo, matsawa kusa da'ita yayi ya manna mata kiss akan goshinta, haɗe da cewa "Sainadawo" adawo lapia tayi masa cike da kunyar sunbatar da yayi mata agoshinta,, tanajin tashin motarsa ta sauƙe ajiyar zuciya haɗe da zama akan kujera tamaida hankalinta ga tv, a zuciyarta kuwa hamdala take da Allah yasa bai sumbaceta ɗazu ba, itakam matuƙar kunyarsa takeji, sosai yakeyi mata kwarjini acikin idanunta.....
***
*GERMANY*
Tunda suka iso cikin ƙasar suka kuma sauƙa ababban asibitin dake cikin birnin Germany ɗin Zaid bai buɗe idanunsa ba, duk da kuwa irin kulawan da ƙwararrun likitotin asibiti'n suka basa, bawai baya cikin hayyacinsa bane, sarai yana a cikin hayyacinsa, ƙunci da kuma tarin damuwa me tsanani ne suka hanasa buɗe idanunsa, baison ya buɗe idanunsa kunnuwansa su jiye masa labarin cewa anɗaura auren Zahrah, baya buƙatar yin tozali da fuskar kowa acikin duniyar nan idan ba fuskar Zahrah ba,, yagama yarda da hukuncin da zuciyarsa ta yanke masa, lallai kwanciyarsa haka baida wani amfani, yakamata ne yatashi yayi yaƙi don samo soyayyar Zahrah, idan har bai manta da date ɗin daya gani ajikin katin auren ba, to jiya ne ɗaurin aurenta, wasu irin hawaye masu zafin gaske ne suka silalo daga cikin idanunsa haɗe da gangarowa tagefen kumatunsa,, a hankali ya ware idanunsa da suka jima da rikiɗewa suka zama jajur dasu, baya tunanin zaisake samun farinciki acikin rayuwarsa matuƙar yarasa abar ƙaunarsa Zahrah, tashi yayi zaune haɗe da rumtse idanunsa, ƙuna yakeji acikin ƙirjinsa sai dai kuma zafin wannan ƙunan baikai zafin ƙunan da soyayyar Zahrah keyi masa azuciyarsa ba,,, Alhaji Ma'aruf dake tsaye a wajen ɗakin da Zaid ɗin ke kwance, ta cikin makeken glass ɗin daya zamewa ɗakin window ya hango Zaid ya tashi zaune, da sauri yaje ya ƙira Doctor domin kuwa tunda suka zo Zaid ɗin bai motsaba sai yanzu,, ƙa'idansu ne idan zasu duba marar lafiya babu wani me shiga kansu harsai sun ga babu wani matsala sannan zasu bar ƴan uwansa suje kansa,, hakan yasa dole Alhaji Ma'aruf ya dakata daga waje likitan shi kaɗai ya shiga.. Bayan kamar wasu mintuna likitan yafito yabawa Alhaji Ma'aruf daman ganin Zaid ɗin, ae ba'iya Alhaji Ma'aruf kaɗai ba hadda Mum suka rankaya zuwa cikin ɗakin,, har gabansa dukansu suka ƙarasa, hanu Alhaji Ma'aruf ya ɗaura akan kafaɗan Zaid haɗe da cewa "Ya ƙarfin jikin naka?"
Bai amsa musu ba saima kallonsu daya shiga yi kamar wani wawa...
"Ina Zahrah?" shine abun daya iya fitowa daga cikin bakinsa kawai, saboda shine abun dake cikin zuciyarsa..
Kallon Kallo Alhaji Ma'aruf da Mum suka shiga yiwa juna, sukam dai basuda wani amsa da za su bashi domin kuwa sarai labarin Auren Zahrah ya isa ga kunnensu, yanzu haka itaɗin matar wani ce, babu amfanin ɗago zancenta...
Alhaji Ma'aruf ne yayi ta maza haɗe da sauƙe ajiyar zuciya cike da lallashi yakuma dafa kafaɗun ɗan nasa " Yanzu ba lokacin damuwa bane Zaid, bakuma lokacin daza ka sa kanka acikin ƙunci bane, kabar maganan Zahrah, yanzu samun lafiyarka yafi komai a wajen mu, idan kasamu lafiya sai ayi abun daya dace amma maganar Zahrah abarshi" Alhaji Ma'aruf yaƙare maganar cikin kwantar da murya.
Laɓɓansa ya cije haɗe da girgiza kansa
" Bazan taɓa samun nutsuwa da salama ba Dad har sai Zahrah tazamo tawa, Inasonta Dad, so ba irin na wasa ba, samunta ayanzu yafiyemin komai, taɓa kaji Dad, zuciyata takusa bugawa akan soyayyarta, ba irin bugawan da kasani ba Dad, Bugawa zatayi tayanda bazata sake aiki ba har abada kuwa!" Zaid yaƙare maganar yana me ɗaura hanun Dad ɗinsa akan ƙirjinsa dai dai saitin da zuciyarsa take....
"Baka da hankaline Zaid? ka kosan mekake cewa? wani irin mahaukaciyar soyayya ce wannan? anya kuwa Zaid baka zautu akan wannan banzar soyayyarba?" Mum ta tambayesa cikin yanayi na ɓacin rai, sosai abun nasa yanzu yake sosa mata rai..
"Mutuwa zanyi Mum akan Zahrah zan iyayin komai wallahi dagaske ni mahaukacine akan soyayyarta inason...."
"Kanasonta ko, shikenan tunda baka gujewa saɓon Allah saikaci gaba da sonta idan zaka sameta, domin kuwa yanzu ta riga da tayi maka nisa, saboda matar wani ce!" Mum tafaɗi haka ta hanyar katsesa daga maganar dayake...
Tamkar sauƙar guduma aka haka yaji sauƙan maganganun mahaifiyartasa acikin kunnuwansa,, kallonsa yamayar ga Dad ɗinsa,, kai Alhaji Ma'aruf ya jinjina masa alamar kalaman mahaifiyarsa gaskiya ne..
"Zahrah zata dawo gareka idan har Allah ya rubuta cewa itaɗin matarkace, amma yanzu kacireta acikin zuciyarka, saboda ahalin yanzu Zahrah tajima da zama mallakin wani, kasani kuma tunata da kuma cigaba da sonta zai iya jefaka cikin halaka" Dad yafaɗi haka ga ɗannasa cikin tsananin tausayawa...
Dafe ƙirjinsa yayi da sauri haɗe da cije laɓɓansa, da ƙyar ya'iya motsa laɓɓansa aniyarsa yafurta wata kalma, sai kuma labari yasha banban, tarine ya sarƙesa, take jini yasoma fitowa daga cikin bakinsa, ƙoƙarin riƙesa Dad yasomayi amma kuma kafun yakai ga riƙesa tuni yafaɗo daga kan gadon, Mum kuwa tuni tafice aɗakin taje taƙira Doctor's,, kafun Doctors ɗinma suzo tuni Zaid yayi mugun fita acikin hayyacinsa, gaba ɗaya jini ya ɓata gaban rigar dake jikinsa, idanunsa ne suka juye wani irin numfashi yaja me sauti, saikuma komai na jikinsa yasake alokaci guda, daidai lokacin Likitoti suka ƙaraso cikin ɗakin .... Taimakon gaggawa suka shiga bashi don ceto rayuwarsa cikin ikon Allah kuwa suka samu numfashinsa ya dai-dai ta, allurai suka narka masa wanda zasu sanyasa bacci...
Babban likitan dake kula da al'amuran Zaid ɗinne, ya rufe Dad da faɗa akan wai saboda me yasa aka faɗawa Zaid ɗin maganar da zata tada masa da hankali, haƙuri Dad yashiga bawa Doctor ɗin, sharuɗa masu tsauri Doctor ya shumfuɗa musu, akan cewa lallai dole babu wanda zai sake ganawa da Zaid ɗin harsai bayan kwana uku, sannan kuma koda sunkoma gida yazama dole akiyaye shiga damuwa dakuma ɓacin ransa, saboda yanzu zuciyarsa tazama kamar wani ɗanyen ƙwai sai anayi ana lallaɓata, zuwa yanzu abu kaɗan ne zai sanya ta buga, wanda hakan kuwa dai dai yake da rasa rayuwar Zaid ɗin baki ɗaya
***
Bayan awanni 4
Shikaɗai yasan irin raɗaɗi dakuma ciwon dake kwance acikin zuciyarsa, hawayene suke ta fita daga cikin idanunsa suna gangara akan ƙuncinsa,, "Da gaskene Zahrah'n sa tayi aure? me yasa Zahrah zatayi masa haka? Bazai taɓa iya jurwa ba, lallai koda Zahrah tayi aure bazai taɓa daina sonta ba, kuma koda duka mutanen duniya zasu taru akansa bazai sanja ƙudurin dake zuciyarsa na auren Zahrah ba, zaiyi duk wani abu wanda yasan Zahrah zata dawo garesa koda kuwa hakan zaijawo sanadiyar rasa rayuka ne, ZAHRAH kawai yasani kuma itace cikar burinsa"..... (😳 karya kasheni nima🏃♀🏃♀)
*(Gobe Birthday na💃💃 zan baku updated insha Allah💃💃gobe akwai show agidan Doctor 🙊 )*
*21/January/2020*
*Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*Editing is not allowed📵*
*CHAPTER 94 to 95*
*NIGERIA*
Tunda Doctor yafita baisake dawowa cikin gidanba harkuwa Zahrah ta ƙaraci zamanta acikin falon ta koma uwar ɗaka, sai dai kuma yayi mata waya yasanar mata cewa yana gidan Hajiyarsa wani uzuri ne ya riƙesa...
***
Idar da sallan isha ɗinta kenan ta miƙe haɗe da ƙarasawa gaban dressing mirror, lotion ɗinta me ƙamshi ta shafa ajikinta, powder kawai ta shafa akan fuskarta sai kuma man leɓe... Wata rubber pencil gown maroon colour ta sanya ajikinta, rigace irin marar nauyi ɗinnan sannan kuma an cika gabanta da fararen duwatsu wato (stones) wani maroon ɗin mayafi me ɗan kauri ta ɗauka haɗe da kafa ɗaurin ɗan kwalin nan na turban akanta, sosai tayi kyau saikace wata balarabiya, zama tayi akan gado haɗe da jawo wayarta, ajiyar zuciya ta sauƙe, har cikin ranta tana mamaki ƙwarai na rashin dawowan Dr.Sadeeq, tun safe daya fita haryanzu baidawo ba,, tashi tayi ta rage gudun ac'n dake cikin ɗakin, haɗe da ɗaukar wayarta tafice zuwa falo, hankalinta gaba ɗaya ta maida kan tashan MBC Bollywood da suke haska film ɗin nan me suna SANAM TERI KASAM bata taɓa kallon film ɗin ba amma kuma tana da waƙoƙin film ɗin acikin wayarta saboda sosai waƙoƙin sukeyi mata daɗi,, ta shagala a kallon film ɗin har idanunta sunfara kawo ƙwalla saboda tausayi, jitayi ansanya hanu anrufe idanunta , a razane ta ƙwalla ƙara domin kuwa sam bataji motsin shigowan mutum cikin falon ba, da sauri tature wanda yarufe mata idanun gefe haɗe da tashi tsaye,, ganin cewa shine yasanya tashiga sauƙe ajiyar zuciya akai akai,, murmushi yasakamar mata haɗe da cewa
"Matsoraciya"
Zama yayi akan kujera,, itama zama tayi tana me da numfashi sosai yatsorata ta donkuwa bata tsammata cewa shi bane sam ta manta ma da cewa babu mayafi ajikinta... Kafeta da'idanunsa yayi yana me ƙarewa kwalliyartata kallo,, sai alokacin ta ankara da irin kallon dayake jifanta dashi.
"Sannu da dawowa!" tafaɗi haka cikin sassanyar murya.
"Yauwa, kimin afuwa najima da yawa" yafaɗi haka yana me sanya hanunsa ya kama kunnensa alamar yana neman afuwa, murmushi kawai tayi masa haɗe dayin ƙasa dakanta...
Miƙewa tsaye yayi haɗe da cewa "Bari naje nayi wanka, akwai kayan fruit acikin fridge please kiɗan yanka min kafun na fito"
"To" kawai tace dashi haɗe da tashi tanufi wajen fridge ɗin shikuma direct ya wuce ɗaki donyin wanka...
Tana kammala yanka fruit ɗin ta ɗauko wani plate me kyau tarufe yankakken fruit ɗin, kan kujera ta koma ta zauna haɗe da sake maida hankalinta ga tv.. Sanye da tree guater jeans ajikinsa haɗi da wata farar t-shirt ya fito, ƙamshi kawai yake fitarwa, satan kallonsa Zahrah tayi haɗe da ɗan sakin murmushi, bata taɓa ganinsa acikin irin wannan shigar ba amma kuma yayi mata kyau sosai.. Akan lallausan carpet ɗin dake malale tsakiyar falon ya zauna haɗe da tanƙwashe ƙafafunsa, alama yayi mata da hanunsa cewa ta miƙo masa fruit ɗin, ɗaukan plate ɗin tayi taƙarasa gabansa, durƙusawa tayi har ƙasa kana ta aje plate ɗin,, "Miƙomin wancan ledan" yafaɗi haka yana meyi mata nuni da leda wanda shiya shigo dashi sam ita batama lura ba,, cike da nutsuwa taɗauko ledan