Showing 174001 words to 177000 words out of 177624 words
kallon juna suka shigayi cike da shauƙi, hanunta ta ɗaura akan chest ɗinsa tana shafawa a hankali, lumshe idanunsa yayi haɗe da laluɓar fuskarta ya haɗe bakinsu waje ɗaya. A hankali suke sucking lips ɗin junansu, suna fidda wani irin numfashi mai sauti, cike da nutsuwa ya zame gaba ɗaya rigar jikinta, tayi ƙasa, hannayensa yaɗaura abayanta yashiga shafawa yana yawo dasu ahankali har ya gangaro zuwa kan ƙirjinta, still bakinsu na haɗe dana juna suna bawa kansu hot kiss. Saida sautin numfashinsu dukansu ya sauya, alokacin da hanunsa suka shiga yawo akan breast ɗinta, cire bakinsa yayi acikin nata kana ya gangaro da bakinnasa zuwa wuyanta, tsotseta yake son ransa, yana fidda wani irin numfashi dake nuna yana cikin tsananin mayen sha'awa dakuma sonta. ƙafafunsu ne suka soma gazawa wajen ɗaukarsu, tana acikin ƙirjinsa suka nufi kan bed. Maƙalewa tayi ajikinsa, ahankali take goga masa breast ɗinta akan chest ɗinsa, hakan kuwa sosai ya ruɗasa, tana kwance aƙasansa yayinda shikuma ya yi mata rumfa da faffaɗan ƙirjinsa, sukansu basusan awacce duniya suke ba, gaba ɗaya sun zauce, alokacin daya gama ratsa cikin jikinta, sai da wasu hawaye masu ɗumin gaske suka gangaro daga cikin idanunta, sam hawayen bana baƙinciki ko damuwa bane, wannan hawayen sukan fitane alokacin daya dace, lokacin da mutum yakasance baya acikin duniyarsa, irin wannan hawayen sukan fitane, alokacin da mutum wanda ke acikin tsananin magagin sha'awa da kuma so yasamu abun dayakeso a lokacin daya kusa zautuwa, wannan hawayen na musamman ne, wannan hawayen sukan fitane alokacin da mutum yasamu cikar muradinsa.
Yanayin da suka samu kansu aciki, yakasance me daɗi agaresu, gaba ɗaya daren sun ƙare shi ne cikin soyayya, yayinda Zahrah keta zuba masa shagwaɓa shikuma ya dage sai lallaɓata yake, koda sau ɗayane bayason abun dazai ɓata ranta. Gaba ɗaya yagama shagwaɓata, yamai da ita saikace wata ƴar 7 year. Yanzuma shagwaɓan tagama zuba masa, tana kwance luf acikin ƙirjinsa, yayinda shikuma ya kafeta da idanunsa, dake ɗauke da mayen sonta. Kissing ɗinta yayi akan goshinta, haɗe da maida duka hannayensa cikin ƙirjinta, har yau jinta yake kamar sabuwar budurwa, koda yaushe ƙara shiga zuciyarsa take, sannan babu wani abu na jikinta daya sauya daga mai kyau zuwa marar kyau, breast ɗinta har yau sunanan a yanda suke babu wani abu daya samesu, hakan nema yasa ako da yaushe yake nanuƙe mata, ya murzata son ransa, atunaninsa bacci take saboda haka yayi ƙasa da kansa zuwa ƙirjinta, wani numfashi ta sauƙe alokacin da taji hucin numfashinsa, na sauƙa akan ƙirjinta ahankali, dama baccinta baiyi nisa ba, duka hannayenta ta cusa acikin gashin kansa, tana yamutsawa slowly, ahaka har bacci ya ɗaukesu dukansu..
(Nima bacci nakeji, kuyi haƙuri typing ɗin dare nayi, yanzu nagama kuma dare yayi sosai, saboda haka da safe idan Allah Yakaimu zan sake muku shi. Please kubani Vote sosai a wannan page ɗin, Inason wannan page ɗin, da wanda zanyi gaba sufi kowanni page na baya yawan vote, next page na Zaidun mune.)
*✅OTE ME ON WATTPAD*
@fatymasardauna
#Love
#Romance
# SON SO @ my wattpadians.
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*Godiya ta musamman agareka NAZEEFI YAREEMA (N YAREEMA) wannan fejin gaba ɗayansa kyautane agareka*
*Godiya mai tarin yawa ga duk wani ko wata, dake mini forwading novels ɗina, haƙiƙa kuna ƙaramin ƙarfin guiwa, kuma inajin daɗin hakan sosai, Allah Yabarmu tare*
*Bazan taɓa mantawa dakuba my lovely fans, haƙiƙa kuma kuntaka rawar gani sosai wajen sambaɗomini comment, ina alfahari daku aduk inda kuke masoyana, Allah yabar ƙauna maitarin yawa a tsakaninmu Ameen*
*Da bazarku nake taka rawa my Wattpadians, SON SO tare da SON ƘAUNA nakeyi muku, Inasonku irin sosai ɗinnan*
*CHAPTER 118*
*(END! END!! END!!!)*
Rayuwa tana tafiya ne da gudu gudu batare da wani mai rai ya ankara da hakan ba, akullum kwanan dunia shekarunmu ƙara ƙarewa suke, sannan ƙara girma muke, sake kusantar mutuwa muke. Daga kwana ɗaya anzarce kwanaki daga kwanaki anwuce satuttuka daga satuttuka anwuce watanni daga watanni anɗarawa shekaru. Haka yake ako da yaushe, acikin waƴannan kwanaki da shekarun kuma abubuwa ne masu yawa suke faruwa suke kuma shuɗewa, wani yasamu cigaba wani kuwa yasamu naƙasu, wani ransa yayi baƙi wani kuwa ransa yayi fari ƙal. To hakance takasance acikin labarin ZAID da ZAHRAH, shekaru sunja rayuwa ta haɓaka, shekaru sama da biyar kenan yanzu, har lau kuma rayuwa suke cike da farinciki....
"MY SOUL! MY SOUL!! MY SOUL!!!" muryarsa daketa kwaɗa ƙiran sunan MY SOUL ta ƙaraɗe ilahirin farfajiyan gidan, tundaga cikin katafaren falonsa, keta kwaɗa ƙiran har ya kawo compound ɗin gidan.
Sanye yake da wando track suit sai kuma wata farar t-shirt ƙafarsa sanye suke cikin wani takalmi mai igiyoyi. Tsayawa yayi haɗe da sanya hannayensa akan ƙugunsa yana fesar da numfashi, yayinda yaketa baza idanunsa, ko zai hango wacce yake nema. Babu wani abu daya sauya ajikinsa, sai ma kyau da hasken fata daya ƙara, ga wani haɗaɗɗen ƙasumba daya daɗa ƙawata kyakkyawar fuskarsa, lallai shiɗin namiji ne cikekke, wanda zai ɗauki hankalin duk wata mace data gansa, ya haɗu sosai da sosai, duk da cewa shekarunsa sun ƙaru akan nada, amma duk da haka yana nan ayanda yake, kyawunsa da kwarjininsa suna nan, haryanzu shiɗin mutum ne mai tsananin son gayu, sam bayason ƙazanta, komai nasa me ajine. ZAID kenan namijin dayazamo abun kwatance acikin sauran mazaje, namijin daya iya jure dakon soyayya me tsananin zafi, namijin daya zamanto sadauki, akan soyayya.
Sake gyara tsayuwarsa yayi, haɗe da ƙara furta ƙiran sunan
"MY SOUL"
Da gudun gaske wata kyakkyar yarinya wacce bazata wuce 6 year ba ta ƙaraso tsalle ɗaya tayi ta haye bayanshi, lumshe idanunsa yayi, alokacin dayaji an ɗale kan bayansa, yasan babu wani ko wata da zaiyi masa wannan aikin idan ba MY SOUL ɗinsa ba. Hanunsa yasanya ya jawota daga bayansa, zamewa yayi akan guiwowinsa haɗe da ɗaura duka hannayensa akan kafaɗunta.
"Maƙoshina saura kaɗan yafashe My Soul duk kuma akanki ne, kinaji inata ƙiranki shine kikaƙi ki amsa ko?" tamkar wani ƙaramin yaro shagwaɓaɓɓe haka ya faɗi maganar.
Dariya fara kyakkyawan yarinyar da yanayin fuskarsu ke shige da tata tayi, haɗe da sanya hanunta akan dogon hancinsa.
"I'am Sorry My Papa luv, ina cikin garden ne, kuma na amsa amma bakaji ba" yarinyar tafaɗa tana ɗan juya idanunta.
Murmushinsa mai kyau yayi mata haɗe da jawota jikinsa ya rungume.
"Bazaki daina juya idanunki idan kina magana ba ko?" yatambayeta yana me shafa bayanta ahankali.
"Papa luv banice fa nakeyin hakan da gangan ba, nima banasanin najuya idanuna idan ina magana!" tafaɗi haka a shagwaɓe hartana ɗan buga ƙafafunta a ƙasa.
Lumshe idanunsa kawai yayi yana maijin ƙarin ƙaunar ƴartasa na ratsa jini da tsokan sa, sosai yanayinta ke kama dana Zahrah babba, haka kuma ɗabi'ar Zahrah ne wani lokaci idan tana magana takan juya idanunta, to itama wannan haka ta keyi, sau da dama idan tana abu, kallon real Zahrah kawai yakeyi mata, domin kuwa yanzu da ta ƙara girma kamanninta da Zahrah sai ya sa ke fitowa, baisan wani irin soyayya yakeyiwa ZAHRAH ƴarsa ba, gaba ɗaya soyayyan da yayiwa Zahrah itace ta dawo kan yarinyar, wani irin so yake yi mata da baida misali, jinsonta yake ako ina na jikinsa, Zahrah ƴarsa itace rayuwarsa, itace Hasken sa, itace madubinsa, wacce idan ya duba ransa keyin sanyi, samunta yafiye masa komai aduniya, samunta wani alkhairi da ginshiƙi ne acikin rayuwarsa, domin kuwa tunda yasameta, arzikinsa suka yalwata akan nada, shikansa ayanzu baisan iya adadin dukiyarsa ba, itakanta yarinyar kamfanoni masu tarin yawa ya buɗe mata, sosai yake samun alkhairi adalilinta.
"Papa Luv!" yarinyar ta ƙirasa murya a sanyaye.
Buɗe idanunsa yayi ahankali haɗe da sauƙesu akan babyn ta sa "Na'am My Soul" ya amsa mata.
Ya mutse fuska tayi haɗe da cewa "Yunwa nakeji Papa Luv banyi breakfast ba"
Waro kyawawan idanunsa yayi haɗe da miƙewa tsaye ya sungumeta suka nufi inda zai sadasu da babban falon gidan.
Tana tsaye agaban dining area tana nunawa hause girl yanda zata shirya musu dining ɗin, tasha adonta cikin wani jan lace me kyau da burgewa, taƙara cika ta zama babbar mace, dagani kai kasan tana murza naira son ranta, domin wani haske ta ƙara tayi fat da ita. Shigowarsu cikin falon suna dariya yasanya ta maida hankalinsu gareta, batasan wannan wace irin soyayya bace ke tsakanin Zahrah da Babanta Zaid, soyyace irin ta bugawa a jarida.
Tana tsaye tana kallonsu suka ƙaraso dining area'n kujera yaja ya zauna akai kana ya ɗaura Zahrah akan kujeran dake gefensa na dama, dama kuma haka suke zama koda yaushe.
Murmushi Afrah tayi haɗe da cewa "Nashiga ɗakinka banganka ba ae, sainayi tunanin kana wajen yin gym, ashe ma kuna tare da Zahrah"
Murmushi kawai yayi haɗe da sanya hanu ya shafi kan Zahrah, baitankawa Afrah ba saima duban Zahrah da yayi cike da so yace "Me zan zuba miki?"
"Duk abunda zakaci Babana nima shi zanci!" Zahrah tafaɗi haka tana kashe masa idanunta ɗaya.
Dariya suka sanya atare haɗe da bata hanunsa suka tafa, abinci yasoma zuba musu da kansa, acikin plate ɗaya, dama kuma a yanzu baya taɓa cin abinci saida Zahrah, zaiƙi ci da kowa amma zaici da ita, kujera Afrah taja ta zauna itama, haɗe da soma yin serving ɗin kanta, don ta lura babu wani wanda yake ta ita, daga Zaid ɗin har Zahrah, su dama kansu kawai suka sani.
Shida kansa yaciyar da ƴartasa, itama haka ta dinga basa abincin abaki har ya ƙoshi, sama sama suke hira da Afrah, nan ma itace take jansu da hira, amma daba haka ba bazasu kulata ba, ita har mamakinsu ma take, Zahrah sam bata damu da ita ba, kamar ba itace ta haifeta ba, zancenta baya wuce mahaifinta dakuma Momyn Friend ɗinta, wanda suke makaranta ɗaya dashi.
Tana gama goge bakinta da tissue ta kalli Papa Luv ɗinnata ashagwaɓe tace. "Please Papa luv yau muje shan ice cream mana!"
"My Soul yau inada aiki, mubari sai gobe mana, kinga fa next week zamu koma U.S.A, akwai abubuwan danakeso nayi kuma kafun mu koma" yafaɗi haka bayan ya aje kofin tea ɗin dake riƙe ahanunsa.
Sake shagwaɓewa tare da narke fuskarta tayi, ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba haɗe da cewa
"Ae Dan Allah Nace Papa Luv, inaso naje ne!"
"Shikenan zo muje na shiryaki" yafaɗi haka yana mai miƙo mata hanunsa.
Tsalle ta doka haɗe da faɗawa jikinsa ta rungumesa, cike da farinciki ta kai masa sunbata akan ƙuncinsa.
"Thank You Papa Luv"
Ɗagata yayi caɗak akan kafaɗunsa haɗe da sanya hanu ya kwashe wayoyinsa dake kan table, direct suka wuce ɓangarensa.
Kai kawai Afrah ta girgiza haɗe da cigaba da cin abincinta, sam abunsu baya damunta, tasaba da hakan, koda yaushe haka suke, kamar tip da taya basa rabuwa.
Shida kansa yayi mata wanka yashiryata cikin wasu riga da wando na jeans masu matuƙar kyaun gaske, naɗe mata dogon gashinta yayi a tsakiyar kanta, da wani babban ribbon, lokaci ɗaya kyawunta da tsananin kamaninta da Zahrah suka sake bayyana, shima wanka yayi kana ya shirya kansa, cikin wasu riga da wando masu kyaun gaske, sosai yayi kyau sai tashin ƙamshi yake, Little Zahrah dakanta saida tayaba kyawun da Papa Luv ɗinta yayi.
Yana riƙe da hanunta suka fito harzuwa falo, kallonsa ya maida ga Afrah wacce ta mato akan kallonsa.
"My Wife bazaki zo kirakamu bane?" ya tambaya.
Murmushi kawai tayi haɗe da lumshe idanunta, akasalance tace "Kuje kawai Dear nikam inanan, amma ku tahomin da nawa ice cream ɗin"
Hanu Zahrah ta ɗaga mata alaman bye bye kana suka fice daga cikin falon.
Barinta yayi awajen sayan kayan maƙulashe irinsu chocolate da sauransu shikuma ya nufi wajen turaruka. Tana tsaye ta ƙurawa wani babban ledan chocolate dake can sama idanu, so take ta ɗaukoshi ta sanya acikin kayanta amma kuma wane ita, ya ɗarawa tsayinta, jitayi anrufe mata idanu a hankali, a iya saninta mutum ɗayane keyi mata hakan, saboda haka yanzuma tasan cewa shiɗinne, dariyan farinciki tasaka haɗe da cewa "ASAD!"
Dariya yayi haɗe da sake mata fuska ta juyo zuwa garesa, kyakkyawan yarone wanda bazai wuce 7to8 year ba, yarone fari tas dashi tamkar ajinsin larabawa yafito, tsallen murna Zahrah tasanya haɗe da rungumesa, shima rungumeta yayi cike da jin daɗin ganin ƙawartasa wacce rabonsa da ita yau tsawon sati uku kenan, tun da aka basu hutun makaranta rabonsa da ita..
Cike da ɗokin ganinsa Zahrah tace. "Laaa Asad dama zanganka anan? kaida waye kukazo? nidai nida Papa Luv ɗina mukazo, aibansan zamu sameka anan ba da munzo tunda wuri"
Hanu yasanya ya ɗan murɗe bakinta cikin halayyarsu ta yara yace "Baki gajiyawa da Surutu Soul ina Papan naki?" yaƙare maganar yana me baza idanunsa.
"Asad me kakeyi anan, bacemin kayi chocolate zaka ɗauka kazo ba?"
Daga Asad har Zahrah atare suka juya suna kallon mai maganar. Kyakkyawar mace wacce ta amsa sunanta mace mai aji da kamala, sanye take da abaya gown black colour ta yane jikinta da mayafin abayar, komai nata na burgewa ne, kallo ɗaya zaka mata, kakuma son sakewa domin ba irin ƙananan matannan bane, duk da cewa bata da wani jiki, haka kuma bata wani sanja ba, har yanzu tana nan da kyawunta mai fusgar hankali.
"Itace Mamanka?" little Zahrah tafaɗi haka ƙasa ƙasa tana kallon Asad.
Kai Asad ya kaɗa mata alamar "Eh"
Da gudunta ta ƙarasa wajen Momyn Asad ta rungumeta, cikin surutunta daya zame mata sabo tace.
"Oyoyo Mom Asad, dama inataso mu haɗu dake, amma bakya zuwa school ɗinmu, Dad ɗin Asad ne kawai yake zuwa, ni da Asad abokaine sosai, kuma dan Allah kudawo U.S.A kunji, muma kunga can zamu koma" tunda little Zahrah tafara zuba bata tsagaitaba sai yanzu.
Hakanan Zahrah taji yarinyar ta burgeta, durƙusawa tayi agaban yarinyar haɗe da sanya hanu ta shafa fuskarta, hakanan taji bugun zuciyarta ya ƙaru, "Idanunta ne ke mata gizo kokuwa dagaske kamanninta take hangowa akan fuskar yarinyar?" tambayar da tayiwa kanta kenan, cike da son sanin amsa.
Murmushin da Little Zahrah tayiwa Mom Asad ne yayi sanadiyar kusan rugujewar zuciyarta. "ZAID" tafurta sunan acikin maƙoshinta da kuma kan laɓɓanta, sai dai kuma amon sauti baifito ba.
"My Soul"
Taji wata murya dabazata taɓa mantawa da ita ba tafaɗa.
Dagudu Little Zahrah takamo hanun Papa Luv ɗinta dake tsaye.
"Yauwa Papa zokaga Momyn Friend ɗina Asad, wacce nafaɗamaka tana da kirki, tana bawa Asad abun daɗi, shikuma yana bani."
Idanunsa ya sauƙe akan bayan wata mace dake durƙushe a ƙasa tabasa baya, cigaba da jansa little Zahrah tayi harzuwa inda Mom Asad ke durƙushe amma bata ɗago fuskarta ba.
"Momyn Asad, ga Papa Luv ɗina nima, tare dashi mukazo" little Zahrah tafaɗa cike da kauɗi.
Ahankali ta ɗago manya manyan idanunta ta ta kalli mutumin da Zahrah ke cewa shine Papa Luv ɗinta.
Atare bugun zuciyarsu suka tsananta, take wani irin abu ya tsarga jiki da jijiyoyinsu.
Da ƙyar ta'iya daure zuciyarta ta ƙaƙalo murmushi.
Shima murmushin yayi haɗe da sunkuyar da kansa ƙasa.
Hanun Asad ta kama jiki asaɓule ta juya daniyar barin wajen.
"Asad" taji muryar Zaid yaƙira sunan yaron.
Tsayawa sukayi cak amma ita bata juyo garesa ba, takowa yayi har inda suke ya durƙusa haɗe da kamo hanun Asad.
"My dear ya hutu?" yatambayi Asad.
"Lapiya" Asad yabashi amsa yana murmushi.
Kallonta yayi haɗe da cewa "Dama Asad ɗanki ne?"
Kanta kawai ta jinjina masa alamar "Eh" gaba ɗaya ta ƙosa subar wajen shikuma yakama Asad ya riƙe ƙam.
Murmushin dake ƙarawa fuskarsa kyau yayi haɗe da cewa "Fine boy, natayaki murnan samun wannan kyakkyawan yaron, amma kuma saidai inajin tsoron abunda zai faru anan gaba, Asad abokin Zahrah na ne, idan nan gaba yasan nayiwa mahaifiyarsa laifi mai girma yakike tunanin zai ɗauki abun?"
Kanta ta girgiza masa haɗe da ɗanyin murmushi. "Kada kace haka Zaid, abu idan ya wuce yana da kyau amantasa, afuskanci gaba, banafatan Asad yasan abun da ka aikata agareni" ɗan numfasawa tayi tare da kama hanun Asad. "Sauri nake zanwuce gida" kallonta ta mayar ga Little Zahrah da ta ƙura mata idanu tun ɗazu, murmushi Zahrah tayi mata, haɗe da shafa kanta, sosai taji son yarinyar acikin ranta.
"Allah ya albarkaci rayuwarki Rabin raina" Tana faɗan haka taja hanun Asad suka bar wajen.
Saida ta ɓacewa ganinsa kafun yasaki wani murmushi haɗe da cusa duka hannayensa acikin aljihun wandon jeans ɗin dake jikinsa. Little Zahrah ce tataho zuwa garesa haɗe da maƙalewa acikin jikinsa, murya asanyaye tace "Papa dama kasan Mommyn Friend ne?"
Murmushi yakumayi akaro na sau babu adadi, hanunta yakama suma suka bar wajen, batare daya bata amsar tambayar da tayi masa ba.
Tunda suka shiga mota batace da yaronnata ƙalaba, shima baitanka mata ba, domin dama shi hakanan yake ba mutum ne mai son yawan magana ba, yana da miskilanci wani lokaci. Ganin da yayi cewa kamar Momyn nasa na cikin damuwa ne yasanyashi gyara zama haɗe da cewa.
"Momy wani laifi ne Papan Friend yayi miki? naji kamar yace wai bayaso muji ko mu sanine oho"
Harara ta watsa masa, hakan yasashi yin gum da bakinsa, shidama gulmace ke cinsa, da yasani ma da baitambaya ba.
Tana isa gida tasamu Husnah da Areefa matar Asad, sunzo suna jiranta, sam basu sanar da ita zuwansu ba, batayi mamakin ganinsuba kamar yanda tayi mamakin ganin yanda aka sauya mata tsarin falonta, aka mamaye gaba ɗaya falon da decorations masu kyaun gaske, tsayawa tayi tana ƙarewa falon nata kallo.
"Happy Birth Day to you my dear Wife!!!"
muryar Dr.Sadeeq ta karaɗe ilahirin kunnuwanta, kallonta ta maida inda taji muryartasa na fitowa.
Fitowarsa daga ɗaki kenan yasha ado cikin riga da wando na jeans masu matuƙar kyau. Murmushi tasakar masa, gaba ɗaya ita tamanta da cewa yaune birth day ɗinta.
Hanunta yakama suka nufi wani ɗan keɓeɓɓen waje dake cikin falon, sosai aka ƙawata wajen da decoration's mai kyau, kusan suman tsaye tayi alokacin dataga irin hidiman da mijinnata ya shirya mata, manya manyan cake masu kyau da tsada yasa