Showing 45001 words to 48000 words out of 177624 words
yanason komai nata, idan tana kuka tanayimasa kyau sosai, haka ma idan ta kwaɓe fuska bakaɗan ba take kyau, gaskia tana da abubuwan burgewa da yawa, da tunaninta yasamu ya kammala cin abincin duk da cewa baiwani ci mai yawa ba, saida yafita ya ɗanƴi exercise kafun ya dawo ya kwanta, domin a matsayinsa na likita yasan illan dake cikin kwanciya daga cin abinci..
Washe gari
Alhamdulillahi tatashi da ƙarfi a jikinta, sai dai ɗan abun da baza a rasa ba, tun tashinta da haushinsa ta tashi, domin jiya tanaji tana gani haka ya yaudareta yayi mata allura, bayan yagama kashe mata jiki da ƙwayoyin da ya bata, don haka bakinnan a ɗane yake ita adole tana fushi da likita.
Kasancewar yau Asabar babu aiki, yasanya bai tashiba harsai 9 na safe, wanka yayi yashirya cikin kaya masu kyau haɗe da baɗe jikinsa da daddaɗan turare, motarsa yanufa direct bayan yafito daga ɓangaren Hajiyarsa, JABI LAKE yanufa inda yayiwa Zahrah siyayya sosai.
(hmm readers kunaga zaƙewar doctor batayi yawa ba kuwa 🤔)
Yaukam har zauren cikin gidan yashiga anan yatsaya yasoma kwaɗa sallama, Cike da zumuɗi Inna dake zaune a tsakar gida tasoma amsa sallaman nasa, domin tasan bazai shigo hanu rabbana ba, sauran kayan maƙulashen da yasa yawa Zahrah jiyama ita tacinyesu.
"Iso mana likita, ai dakazo kawai ka iso, bawani nuƙu nuƙu nanma fa gidan kune !!" Inna tafaɗa fuska a sake,
Ɗan murmushi kawai Dr Sadeeq yayi haɗe da ƙarasa shigowa cikin gidan, akan tabarma ya zauna kamar koda yaushe,
Yana zama Zahrah tafito daga cikin banɗaki, daga ita sai ɗaurin zani a ƙirji sai kuma ƴar ƙaramar lufaya dake jikinta, kallo ɗaya zaka mata kasan cewa daga wanka take, saurin ɗauke idanunsa yayi daga gareta, yayinda ita kuma tayi saurin sunkuyar da kanta ƙasa, sam bata zaci ganinsa ba awannan lokacin. Sumi sumi haka ta raɓa tashige cikin ɗakinta.
Bayan sungama gaisawa da Inna ne ya yayi shiru haɗe da sunkuyar da kansa ƙasa, sarai Inna tasancewa wajen Zahrah'n yazo don haka kai tsaye tace masa yashiga yasamu Zahrah'n aciki.
Shikam harga Allah bayason shiga ɗakinta, domin kaɗaituwar mace da namiji a waje ɗaya hatsarine, amma ya ya'iya tunda yalura cewa iyayen riƙonnata ƙaramin tunani garesu.
Tsaye take atsakiyar ɗakin, saka rigarta kenan ko zip ɗin rigarma bata gama jaba, jin sallamansa yasa tayi saurin dawo da kallonta bakin ƙofar, harta fara zaton ko kunnenta ne yaji hakan ba sallamarsa bane, sai kuma taga yashigo cikin ɗakin, da sauri ta matsa jikin bango ta manne bayanta, domin gaba ɗaya bayanta a waje yake,
"Uh sorry nashigo kinasa kaya ko" Dr Sadeeq yafaɗa yana mai kallonta.
Harara ta gallamasa haɗe da turo bakinta gaba, dagani kasan fushi take.
Dariya yasanya harsai da fararen haƙwaransa suka bayyana,
"Fushi kikeyi dani ko?, to ai balaifina bane, dolece tasa nayi miki alluran don ki samu sauƙi, yanzuma kuma wasu alluran nazo nayi miki" yafaɗa yana gimtse dariyarsa.
Kuka Zahrah tasanya haɗe da sake matsewa ajikin bango,
"Dan Allah kada kamin, banason allura kataimakeni!" tafaɗa cikin muryar kuka da tsoro.
"Shiiii kada kitaramana jama'a madam, ni ba allura zanmiki ba wasa nake miki " Dr yafaɗa yana mai ɗaura yatsansa ɗaya akan laɓɓansa alamar tayi shiru.
"Ni bazansake yarda dakai ba, ai jiyama cewa kayi ba allura zakaminba, amma kuma shine kabani wani abu nasha kamin, ni bazan sake yarda dakai ba!" Zahrah tafaɗa tana matsar ƙwalla daga idanunta.
"Hahhh to ya'isa haka yanzu kam dagaske ba allura zanmiki ba, juyo na jamiki zip ɗin kinji ƴar ƙaramar ƙanwata !" Dr Sadeeq yafaɗa cikin tsokana,
"Dan Allah kafita banaso, zanzo na sameka, domin ni ba wani namiji da zai sake taɓamin jiki ehe !" Zahrah ta faɗa cike da shagwaɓa.
Wani irin zubawa tsikar jikinsa yayi, domin yanayin yanda tayi maganar kaɗai ya isa sanya jarumin namiji faɗawa cikin wani yanayi,
(Hahhhh likita bokan turai, to Zaid ma yafaɗa a wani hali, balle kai da bakasan salon mace ba 😂)
(Manage yau baida yawa sosai bacci nakeji kuma dama banda enough charge, wata acikin ku tataimaka ta tsammin charge pls 😥.)
*25/November/2019*
*Voted, Comment, and Share please. Follow me on Wattpad @fatymasardauna*
*1:58 pm*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
phatymasardauna
*Dedicated To My Lovely Brother Khabier*
*🌈Kainuwa Writers Association*
*{United we stand & succeed; our ambition is to entertain and motivate the mind of readers}*
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*Editing is not allowed📵*
*( My Lovely, My Sweetness, My Happiness, My Best Friend ever, inasonki sosai da sosai ƙawata rabin raina, wannan page ɗin gabaki ɗayansa kyautane a gareki HAUWA Kulun MAJADAN 😂, JIDDATUL HUSSARY kiji daɗinki ki mo re ƙawata takaina HOUWER )*
*Chapter 40 to 41*
Nannauyar ajiyar zuciya Doctor ya sauƙe, haɗe da zura hannayensa a cikin aljihun wandon sa, "Shikenan to tunda kince haka, na baki two minute kacal kisameni a waje, idan kuwa bakifitoba zan dawo na sake iskeki, kuma wlh sai na danneki na jamiki zip ɗin da ƙarfin tsiya" dagajin yanda yayi maganar kasan cewa tsokana ce kawai.
Kai kawai ta iya jinjina masa alamar cewa taji zata fito ɗin,
Ɗan gun tun murmushi Dr yayi haɗe da sakai yafice daga cikin ɗakin.
Yana fita ta sauƙe nannauyar a jiyar zuciya, haɗe da sanya hanunta a bayanta, taƙarasa jan zip ɗin rigarta, zunbuleliyar hijabinta ta zura akan rigar haɗe da ficewa daga ɗakin, saboda tasan idan bata je bama tabbas zai biyota.
Zaune ta iskesa a cikin rumfar dake barandar gidan nasu, can gefe dashi ta zauna haɗe da kawar da kanta gefe domin kuwa ta lura gaba ɗaya idanuna akanta suke,
"Banason wasa matso kusa kisha maganinki !" yafaɗa babu alamar wasa akan fuskarsa.
Ɗan ƙaramin bakinta tacunno gaba haɗe da sake ɓata fuska, Allah ya sani ta tsani magani sosai da sosai, batama so ayi mata ko da zancen magani ne.
Batare da ya sake ce da ita komaiba yashiga ɓallo ƙwayan maganin daga jikin tablet ɗinsu, yana sawa a hanunsa, har sai da yagama ɓare iya wanda zatasha a yau ɗin, miƙo mata maganin yayi haɗe da bata goran ruwa,
Fuska a daƙune haka ta karɓi magananin saida ta rumtse idanunta sosai kafun ta iya haɗiye maganin, gashi dama irin magani mai ɗacin nan ne,
"Kishirya next week zaki koma makaranta " Dr Sadeeq ya faɗa yana mai latsa wayar da dake riƙe a hanunsa, bakuma alamar wasa akan fuskarsa.
Saurin dawo da kallonta garesa tayi, haɗe da girgiza kanta, "A gaskia ni bazan sake komawa makaranta ba !" Zahrah tafaɗa cikin ɓata rai,
"Maiyasa ? " Dr Sadeeq ya tambaya kai tsaye.
"Saboda babu amfanin hakan, ana karatune don a inganta rayuwa, to nikuma tawa rayuwar tajima da rugujewa, mai yasa zanɓata lokacina wajen gyara abun da bashi da kyau, bakuma zai gyaruba, na haƙura da komai zanjira mutuwata kawai !" Zahrah taƙare maganar cikin yanayi mai nuni da cewa zuciyarta tagamayin rauni,
" Idan ginin gida ya ruguje, ƙoƙari ake a sake gyarasa, akuma sabuntasa har yafi nada ɗin daya ruguje kyau, da kuma ƙawatuwa, shin kinsan maiyasa ake yin hakan? " Dr Sadeeq ya tambayeta bayan yamai da gaba ɗaya nutsuwarsa gareta.
"A'a" tafaɗa a taƙaice.
"Saboda yanada matuƙar amfani gamasu shi, sannan kuma yana da kyau idan karasa dama ta farko, kasake neman wata damar, domin sau dayawa anasamun nasara ne a gaba, bawai a farko farko ba, idan kika ci gaba da kashewa kanki ƙargin guiwa, to zuciyarki zata zama mai tsananin rauni, babu amfani idan kikace bazaki inganta rayuwarki ba, amma inaso kisanar dani fa'idan yin hakan, nuna kin yarda da ƙaddara yana ɗaya daga cikin mantawa da komai, idan kika zauna a gida, bazaki taɓa samun cigaba ba, nasan abun da Zaid yayi miki har yau yana cikin zuciyarki, kuma inada tabbacin cewa idan kinsamu wadataccen ilimi nan gaba, zaki iya yaƙi da azzalumai irin su Zaid, please Zahrah kada kicemin a'a, nayi hakanne saboda samamiki sauƙi, da kuma cireki a kaɗaici !" Dr Sadeeq yaƙare maganar cikin muryan tausasawa, dason ƙara mata ƙarfin guiwa.
Hawayen da suka shiga ambaliya akan fuskarta ta sanya hanu ta share
" Yar zuwa yau banajin akwai wani sauran farinciki daya ragemin a gaba, da wani ido mutanen duniya zasu kalleni? wasu zasu ɗauka cewa ni nakai kaina garesa, wasu zasumin dariya wasu ko zasumin Allah ya daɗa, babu wani namiji da zai tunkareni da sunan soyayya, rayuwata a yanzu tana gudana ne tamkar ruwan shayin da aka sa ma sa lipton amma ba asanya sugar da madara acikin saba, dan Allah kada ka matsa akan cewa lallai saina koma....."
"Ya'isa haka Zahrah, banason yawan gardama, shin bazakiyi ƙoƙari ki inganta rayuwarki ba? haƙiƙa Zaid yacutar dake, amma hakan bawai yana nufi ya ƙarar da rayuwarki bane baki ɗaya, matan da akamawa fyaɗe suna da yawa a duniyarnan, amma kuma hakan bai sa sun tauyewa kansu wani nau'i na jin daɗin rayuwarsu ba, ke mai yasa bazaki yi haka ba ? inaso ki manta da komai, kuma daga yau ɗinnan nagama maganata, next week zaki koma school insha Allah, tun yanzu saiki fara shiri !" Dr yafaɗa fuskarsa babu alamar wasa.
Aikuwa yanayin yanda taga fuskar tasa a ɗaure tamau yasa takasa ce dashi komai, hakanan yake mata kwarjini a cikin idanunta.
Miƙewa yayi tsaye, haɗe da cewa "Kibiyoni waje inason muyi wata magana"
Saurin kallonsa tayi, domin ita rabonta da fita waje tun randa mummunar ƙaddaranta ya rusketa, wanda kuma da bazata taɓa mantawa ba.
Jiki a saluɓe haka ta rufa masa baya, suna zuwa bakin motarsa taja ta tsaya, haɗe da sake tamke fuska.
Murfin ƙofar mai zaman banza ya buɗe haɗe da fiddo wata ƙatuwar leda,
" Idan har kika kumamin musu to tabbas zamu ɓata dake, sannan kuma wlh allurai shida zan danneki na miki da ƙarfin tsiya bandamu ba koda ma sun karye a cikin jikinki, ke kikaso!" Dr Sadeeq yafaɗa cikin tsare gida, yayinda yake miƙo mata zungureriyar ledan dake hanunsa.
"Dan Allah kayi haƙuri kada kamin allura, amma a gaskia ni baxan iya karɓan komai daga gareka ba, ni bazan sake karɓan abun kowa ba, domin kuwa da haka Zaid yasamu ya cuci rayuwata yasamin babban tabo mai wahalar gogewa!" Zahrah tayi maganar cike da tsoro da kuma ƙunan zuciya.
"Alluran dai kikeso kenan, shikenan bana ɗaukosu dama nazo dasu kusan guda goma" Dr Sadeeq yafaɗa yana mai niyar sake buɗe murfin motar.
A tamanin Zahrah ta ruga zuwa gida,
Dariya sosai Dr Sadeeq yashigayi, sosai yarintar Zahrah yake burgesa, haƙiƙa Zahrah yarinyace, domin kuwa kallo ɗaya zakai mata ka fuskanci cewa tsananin yarinta na damun ta sosai, akan allura gaba ɗaya ta ruɗa kanta.
Baiyi yunƙurin komawa cikin gidan ba, sai neman wani yaro yayi yabasa ledan yace ya kai cikin gidan, shikuwa key yayi mawa motarsa yayi tafiyarsa.
Zahrah kuwa tana shiga cikin gidan kaitsaye ɗakinta tawuce haɗe da banko ƙofar ta rufeta gam, faɗawa tayi kan katifarta tana mai sauƙe a jiyar zuciya, ko da taji ƙaran tashin motar Dr Sadeeq ɗin, wani sanyi taji a cikin zuciyarta, haka kawai yazo ya zurkuɗa mata wannnan maka makan alluran nasa, ai wlh bata saɓuwa.....
*New York City*
Kwance yake akan makeken gadon sa, daga shi sai ɗan wani 3 guater jeans, yayin da ya ware ƙafafunsa, duk da cewa akan gado yake, amma saboda tsabar iskanci irin na Zayd sanye yake da takalma (toms) aƙafarsa, yayinda hanunsa ke riƙe da wata zungureriyar kwalbar giya, gefensa kuwa wata kyakkyawar baturiya ce kwance tsirara bako ɗigon abun rufa tsiraici a jikinta, daganinta kasan irin cikakkun ƴan iskan nanne, gaba ɗaya ta tsare Zaid da idanunta, sai wani lasan baki takeyi tamkar tsohuwar mayya, bakomai yasa hakan ba, face yanda gaba ɗaya ta gama kwaɗaituwa da Zaid ɗin, amma kuma yaƙi amincewa ya kusanceta, gaba ɗaya wani irin muguwar sha'awarsa takeji, duk kuwa yanda ta nu namasa zallan karuwancinta a fili, yaƙi kusantar ta, saima sake je fata cikin kogin sha'awa da yayi,
Zaid kuwa da gangan yaƙi kusantarta, domin yanzu tsagwaran iskanci yake ji dashi, sai ya ɗauko mace yagama ƙwaƙuleta, yabarta batare da yayi sex da'ita ba, wayarsace tasoma ƙara alamar shigowar ƙira, har ƙiran ya katse Zayd bai ko kalli inda wayar take ba balle yasan wake ƙiransa,,
Cike da salo irin na ƴan bariki wanda ta yarda cewa idan hartayi masa zai kusanceta, ta sake matsowa daf dashi, a hankali ta zura hanunta acikin 3 guater jeans ɗinsa, haɗe da soma shafa kan mararsa a hankali, yayinda ɗaƴan hanunta ke kan faffaɗan ƙirjinsa tana shafawa slowly, ta yadda zaiji abun har tsakiyar kansa, cike da ƙwarewa tashiga murza ....
A hankali yaɗago idanunsa da suka soma sauya launi ya sauƙesu akan baturiyar, ai kuwa yayi kyakkyawan gani, domin kuwa fuskar Zahrah yagani ta bayyana akan ta baturiyar, bakomai yasa hakan ba face giyar da yasha da tasoma yi masa aiki, da ƙarfin gaske yajawo baturiyar jikinsa, haɗe da matseta ƙam a ƙirjinsa, take jikinsa yasoma ɓari,lokaci ɗaya yashiga bata kyakkyawan romance wanda yasanyata tafara nishin daɗi.
Gaba ɗaya baturiyar nan tadawo masa Zahrah acikin idanuwansa, baisan sai yaushene matsanancin sha'awar da yakemawa Zahrah zata sake saba, a kullum a ko wani daƙiƙa sha'awar Zahrah sake ninkuwa masa takeyi acikin zuciyarsa,
Hmmm duk jaraba irin ta wannan baturiya yau fa sai dai ta haƙura, domin kuwa Zaid tun kan abunnasa yagama shiga jikinta, yayi saurin tureta gefe, wani irin masifaffen ɓacin raine yazo masa, ƙarya ne yasani ba Zahrahn sa bace wannan, sharrin giyane kawai, idan har giya zata iya sanyawa yaga fuskar wata a matsayin Zahrah, to bata isa sawa ɗanɗanon wata yakasance tamkar na Zahrah'nsa ba, Zahrah da ban take komai nata na dabanne, cikinta a cike yake, bakamar sauran matan dayake mu'amala dasu ba, wanda su gaba ɗayansu a wage suke daga ciki har waje, ita kuwa Zahrah daga ciki har waje a haɗe take, bakomai yasanyashi ture baturiyar nan gefe ba face jinsa da yayi ya faɗa zuruf tamkar anzura ƙwallo a raga, bathroom ya wuce kaitsaye yasakarmawa kansa shower.
Itakuwa mayyar baturiyar dolenta ta maida ɗan fingilan rigarta ta fice daga cikin ɗakin, cikin matsanancin sha'awa, Zayd ya jangwalo mata bala'i.
Zayd kuwa a daddafe yayi wanka, domin kuwa wani irin ciwo marar sa ke yi, koda yafito a wankan a daddafe yasha tea da lamon tsami, kwanciya yayi lamo yana mai sauƙe numfashi akai akai, lallai yazame masa dole yakoma Nigeria kodan Zahrah ma, yazame masa dole yakomawa Zahrah domin kuwa bazai zauna sha'awarta ta kashe shi ba, amma ya ɗau alƙawarin cewa wannan karon bazai mata da ƙarfi ba, lallaɓata zaiyi tabasa kanta cikin sauƙi, da wannan tunanin bacci yayi awungaba dashi,
(Hmmm ayi bacci lafiya Zaidun Munubiya,lol).
Nigeria.
Yaune ranar da Dr ya shaidawa Zahrah cewa zata koma makaranta.
Don haka tun tashinta, tatashi tanajinta wani iri, gaba ɗaya ji take gabanta na faɗuwa, hakanan take tsarge, gani take tamkar kowa yasan maiyafaru da'ita, a daddafe tayi wanka, wata simple gown tasanya ajikinta, wanda bata da ado ko kaɗan, wata ƙatuwar lufaya ta zura wanda tsawonsa ya wuce guiwarta. Jin maganarsa a tsakar gidan, yasa taji ƙirjinta ya ɗan buga kaɗan, cikin rashin kuzari tafito daga cikin ɗakin.
Kamar yanda yayi mata kyau, haka shima yaga tayi masa kyau, duk da cewa babu ɗigon kwalliya akan fuskarta.
"Muje ko!" Yafaɗa a taƙaice, saurin ja da baya tayi haɗe da girgiza kanta, domin kuwa ko karen hauka ne ya cijeta, bazata yarda ta shiga motarsa ita kaɗai ba.
"Muje Baffa na jiranmu a waje" Dr Sadeeq yafaɗa domin yaga alamar a tsorace take,
Ajiyar zuciya mai ƙarfi ta sauƙe haɗe da bin bayansa, domin kuwa tuni yariga da yayi gaba.
(Please two days zakuna haƙuri dani domin typing ɗin ba ya yawa, ina busy ne sosai, dan Allah kada kuyi ƙorafi, insha Allah next page zanmuku da yawa)
*27/November/2019*
*Voted, Comment, and Share please...follow me on wattpad @fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Lovely Brother Khabier*
*🌈Kainuwa Writers Association*
*{United we stand & succeed; our ambition is to entertain and motivate the mind of readers}*
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*Editing is not allowed📵*
*Chapter 42 to 43*
Suna fita kuwa ta iske Baffa yayi ɗare ɗare agaban motar Dr Sadeeq sai washe haƙora yake kai kace anmasa kyautar ƴan kuɗaɗe ne.
Dakansa ya buɗe mata murfin motar ɓangaren gidan baya, cikin sanyin jiki ta shiga cikin motar, kaitsaye yashige ɓangaren driver haɗe da mawa motar key...
Tunda suka ɗau hanyar makarantar tasu Baffa ke faman zuba kamar wani kurna, yayinda Doctor Sadeeq ke amsa masa jefi jefi, domin hankalinsa gaba ɗaya yana ga Zahrah, wacce ke zaune tayi jigum a gidan baya, akai akai yake satan kallonta tacikin madubi..
A haka dai harsuka iso cikin makarantar tasu, dai dai bakin ƙofar hall ɗin da zasu gudanar da lecture yau, ya yi parking motar tasa, domin dama already ansanar dashi cewa yau a wannan hall ɗin zasu gudanar da lecture.
A hankali ta buɗe murfin motar ta fito kafaɗarta ɗauke da jakar makarantar ta, cikin takunta mai ɗauke da nutsuwa ta nufi cikin hall ɗin kai tsaye, ko wai gensu batayi ba, tanashiga hall ɗin kallo yadawo kanta, take taji wani irin muguwar faɗuwar gaba haɗe da karyewar zuciya, gani take tamkar kowa yana ganin abun da yafaru da ita rubuce akan goshinta.
Karab idanunta suka sauƙa akan Husnah wacce take faman aikin haɗa wasu takardu dake gabanta. wani irin sanyi taji zuciyarta tayi sakamakon ganin husnah, domin kaf makarantar bata mu'amala da kowa bayan husnah, da matuƙar farinciki Husnah ta rungume Zahrah, domin koda wasa batayi tunanin ganinta ba.
"Kamar mafarki nakeyi gaskia naji daɗi sosai ƙawata!" Husnah tafaɗa cike da tarin farinciki.
Zama sukayi a tare dai dai lokacin Sir Bature yashigo cikin hall ɗin, tsit haka ajin ya ɗauka ana ta sauraran lecture ɗin dayake yi musu, a zahirin gaskia tanajin abun da yake cewa, amma kwata kwata bata fahimtarsa, awa biyu suka ɗauka chur suna lecture, kafun daga bisani yafita daga ajin, gyara zama Husnah tayi haɗe da mai da kallonta ga Zahrah cike da kulawa tace " Yanzu ina likitan yake ?"
Ajiyar zuciya Zahrah ta sauƙe haɗe da cewa " Ba maganar Doctor bace damuwata Husnah, babban damuwata shine gani nake tamkar abun da Zaid yamin yana rubuce a gaban goshina, Husnah gani nake tamkar kowa yasan abun dake damuna !" Zahrah taƙare maganar cikin raunin zuciya.
" Kada kice haka