Showing 171001 words to 174000 words out of 177624 words

Chapter 58 - SHU'UMIN NAMIJI completed Hausa novel

18 Jul 2024

37570

haɗe  da cewa "Ina tayaka murna, matarka ta haihu, kasamu baby girl"   wani irin sanyin daɗi yaji acikin ƙirjinsa, baisan lokacin dayayi sujja don nuna godiyarsa ga Allah ba. 

Ana kaita ɗakin hutu, wata nurse tace yashigo ya karɓi babynsa,    lokacin daya sanya hannayensa ya amshi babyn, wani irin kukane ya ƙwace  masa, alokacin da idanunsa suka sauƙa akan kyakkyawar fuskarta kuwa,  bugun zuciyarsa ne ya ƙaru, saboda  kokaɗan  yarinyar bata kama da mahaifiyarta,  durƙushewa yayi aƙasa, riƙe da yarinyar tasa yana kuka, hakan kuwa sosai yabawa likitotin mamaki.

Bakomaine yasa sa yake kuka haka ba,  face tsananin danasani na rayuwar da yayi abaya da yake.   yakasance mazinaci, mashayin giya.  "Yanzu idan ƴarsa mafi soyuwa agaresa, tataso taji labarin abun da ya aikata a baya,  wani irin kunya zaiji? mezaice da'ita idan ta tambayesa, meyasa yazamo haka?" tambayar da yayiwa kansa kenan, amma kuma baida amsa, baida kuma me amsa masa.

Rungumeta ya sakeyi tsam,  acikin ƙirjinsa, ahankali yace.

"Kindawo gareni Zahrah, Allah yadawomin dake, Inasonki Inasonki, inamiki so na musamman Allah ya albarkaceki ƴata!!!" kiss ya manna mata akan goshinta, kana yazuba mata idanu,  bazaiyi mamakin kamannin daya gani akan fuskar ƴartasa ba, saboda yasan ba aja da ikon Allah, kuma hakan ma wata rahamace da Allah yayi masa,  Allah ya hanasa Zahrah alokacin dayaso, yanzu yakuma basa Zahrah alokacin dayaso,   hancinta bakinta duka kalan nasa ne, amma kuma idanunta tamkar idanun Zahrah aka ciro aka sanya mata, kallon farko da yarinyar tayi masa, saida yaji tsikar jikinsa ya tashi, saboda gani yayi tamkar Zahrah ce dakanta agabansa.  yana rungume da yarinyar ya ƙarasa gaban Afrah dake kwance akan gado tana kallonsu,  ranƙwafowa yayi ya manna mata kiss akan goshinta, hanu yasa yashafi kumatunta, haɗe da cewa "Nagode ƙwarai Afrah, Allah ya miki albarka, bazan manta da wannan ƙoƙarin da kikamin ba, Inasonki"

Karo na farko kenan arayuwarta da taji kalmar nan tafito daga bakinsa akanta,  "Inasonki" ta maimaita kalmar abakinta cike da mamakinsa.
Kansa yajinjina mata haɗe da sakin murmushi. 

"Ki kwanta ki huta, nasan kinsha wahala sosai" yafaɗi haka yana shafa kanta.
Lumshe idanunta kawai tayi saiga hawaye nabin kan fuskarta. Hanu ta miƙa masa ya bata yarinyar,   ba iya mamaki ba hadda tsoro saida ya bayyana akan fuskar Afrah, sakamakon ganin fuskar yarinyar ɗago kanta tayi ta kalleshi da sauri.

Kamar yasan me take tunani,  murmushi yayi mata haɗe da ɗaura hanunsa akan kafaɗanta.   "Kada kidamu, Allah ne yayi ikonsa, Allah ne yadubeni yayimini rahama,  sannan kuma ko da ace kowa zaiyi mamakin kamannin yarinyar ni bazanyi ba, saboda wacce take kama da ita, jinin jikinane, sannan kuma Allah yana da ikon yin komai"

Ajiyar zuciya kawai Afrah ta sauƙe haɗe da kafe yarinyar nata da ido, tabbas da badan taji ƙauna irinta uwa da ƴa akan yarinyarba, to tabbas da tace ba itace ta haifi yarinyar ba, Zahrah ce, shine aka sanja mata, aka ɗauki nata aka kaita wani gun, itakuma aka kawo mata wannar, a matsayin ƴarta. Rungume ƴar tata tayi, tanajin ƙaunarta aranta.
***

Suna komawa gida Zaid yayiwa Afrah kyautar zuƙeƙiyar mota, tare da kuɗi Naira Million 3 duk na murnan ta haifa masa baby ne,  washe gari kuwa suka tarkato suka dawo Nigeria, abisa takurawan Mom ɗinsa. amma da anyi suna yace  zasu koma.  Aranan da aka haifa masa Zahrah aranan ya mallaka mata babban kamfaninsa na ƙera takalma, dake Italy, aranan kuma akasanjawa kamfanin suna zuwa sunan yarinyar, saɓanin da dayake sunan Zaid.

Tunda aka haifi Zahrah Zaid baibari kowa ya ɗauketa ba, inbanda uwarta, nan ma nono kaɗai take bata,  idan yaɗauketa yashiga ɗakinsa da ita, kulle ƙofar yake da key gudun kada wani ya damesa, komai na duniya shiyake mata, wani irin so da ƙaunar yarinyar yake ji, wanda baitaɓa jin irin saba, akullum kallon Zahrah kawai yakeyiwa yarinyar. Irin soyayyar dayake yiwa yarinyar shike tsorita kowa.

Ranan suna kamar yanda ya alƙawartawa kansa cewa idan ya haifi ƴa mace sunan Zahrah zaisawa yarinyar,  hakance takasance domin kuwa sunan nata yasaka, wato FATIMA ZAHRAH, koda Afrah taji sunan da ƴartata taci sai kawai tayi murmushi,  ko kaɗan batayi fushi da faruwar hakan ba, saboda tasan albarkacin Zahrah itama zata samu soyayya ta musamman daga wajen Zaid ɗin, haka kuma albarkacin Zahrah ƴarta itama zata samu gagarumar soyayya daga wajen ubanta.

Nairori sunyi kuka a wannan rana,  sosai Zaid yayi ɓarin kuɗi tundaga randa aka haifeta kawo yau dayake suna, dukiya kawai yake ɓararwa, tun abun nabawa Mom ɗinsa da Afrah mamaki, har suka daina mamaki,  saboda zuwa yanzu sunsan soyayyar da Zaid keyiwa ƴarsa Zahrah ta wuce gaban kwatance,  harta bacci akan ƙirjinsa takeyi.

(Sai haƙuri idan kunga typing error,  Yau banyi editing ba, wai ina kukene masoyan Zaid, kwata kwata naga alama bakwa farinciki, ace matar Zaid ɗinku nada ciki, amma ku kasa nuna farincikinku, ashe soyayyar takuma, batakai zuci ba, haka team Doctor ma, kuma ashe soyayyar taku ta bogece, tunda anmasa haihuwa ko barka bakuje ba.....)



   *✅OTE ME ON WATTPAD*
           @fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

      *SHU'UMIN NAMIJI !!*

   
    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To Brother KHABIER*

 
*🌈Kainuwa Writers Association*

       
              *WATTPAD*
        @fatymasardauna

*Godiya ta Musamman Agareku HASSAN ATK and HUSSAINI 80k haƙiƙa kuɗin kun cancanci babban yabo, ako da yaushe akullum kuma ina yaba ƙoƙarinku, Allah Yabiya muku baƙatunku na alkhairi. Dani da sauran marubuta muna godiya sosai agareku*

     

*NOTE*     *Nasan daga fara book ɗinnan kawo yanzu na ɓata ran wasunku da yawa, amma inaso kusan cewa sam bahaka naso ba, wannan labarin me suna SHU'UMIN NAMIJI ƙirƙiransa nayi da kaina, ba wani ko wata bane suka bani labari ko shawaran nayi,  sannan kuma inaso yawancinmu  musan cewa yarda da ƙaddara yana daga cikin imani,  balallaine kasamu abunda kakeso alokacin da kake soba, haka kuma balallaine akullum kazamo me nasara ba, haƙiƙa Nasara wani babban jigone da kowa keson samu acikin rayuwarsa, haka kuma rashin nasara ma wani jigo ne da ke sawa mutum ke gane kuskurensa awasu lokutan, idan da'ace komai muka nema zamu samu, to tabbas da ayanzu dayawanmu munshagala da bautar ALLAH  Hakan kuma sam ba dai dai bane, arayuwa akwai abu biyu NASARA da kuma FAƊUWA, balallaine kazamo me sa'a ba ako da yaushe,  dayawanku suna jin haushin abun da nayi, na hanawa Zaid auren Zahrah,  inaso ku fahimceni,  banhana Zaid auren Zahrah da gangan ba, ko wai don son zuciyata ba, a'a, inaso kufahimci cewa rashin Zahrah acikin rayuwarsa shine mafarin shiriyarsa, koda a gaskene ba wai a novels ba, idan kanemi abu baka samuba, kada kazargi wani abu, kada kuma kaga kamar ALLAH Baya sonka ne,  ko kaɗan bahaka abun yake ba, bai zama lallai abun da kakeso yazamanto alkhairi agareka ba,   haka kuma wani lokaci Allah Yakan jinkirta baka abun da kakeso koda kuwa abun alkhairi ne a gareka,  kada kayi fushi domin hakan ma wata JARABAWA ce agareka, ALLAH'n daya haliccemu yafi kowa sonmu, shi ke bamu, shi kuma ke hanamu, kada ki/ka sa damuwa acikin zuciyarka, wai don waninka yasamu kai baka samu ba, kaima watarana zaka samu Insha Allah, sannan kowa aduniya baya wuce rabonsa, haka Idan ALLAH Maɗaukakin Sarki ya tsara abu, to babu wanda ya isa ya sauya,  natsinci kainane kawai da fara typing ɗin wannan labarin batare da nayi tunanin komai ba, hakanan nafara rubutashi, cikin ikon Allah kuma yabani sa'a, kuka karɓeshi hanu bibbiyu, haƙiƙa labarin nan nice nake rubutasa, amma kuma bani ke da ikon abun da zai faru acikinsa ba ALLAH  Ne,  komai da ɗan Adam zaiyi acikin duniyarnan bashi keda ikon yinsaba ALLAH Ne kawai ke bashi dama, to haka ALLAH  Yatsara cewa Zahrah ba matar Zaid bace,  babu kuma wanda ya isa ya bawa Zaid ita sai ALLAH.....  Kuyi haƙuri masoyana  ina rubuta muku labarinne aduk  yanda yazo kaina,  nasan dayawa kunji ba daɗi, saboda bakwason Doctor, sai dai kuma babu yanda nidaku zamuyi dole sai haƙuri, wasu har yanzu suna ran cewa, Zahrah zata koma ga Zaid, sai dai ina mai baku haƙuri domin awannan labarin Zaid ba zai taɓa auren Zahrah ba, haka ƙaddaransa take, kuma duk musulmi yanada kyau ya yarda da ƙaddaransa walau mai kyau ko marar kyau.*

         *CHAPTER 117*

Two years Later!

Acikin shekaru biyunnan da suka wuce abubuwa da yawa sun faru, ciki kuwa hadda haihuwan Husnah, da kuma ƙarin girman da akayiwa Doctor Sadeeq a wajen aiki, Zahrah kuwa tazama lecturer acikin jami'ar da tayi karatu. Abubuwa dayawa sun faru acikin waƴannan shekarun.

Tsaye take agaban wani babban table tana haɗa wasu takardu dake gabanta, ajikinta sanye take da Abaya gown, maroon colour, wanda jikinsa yaji adon duwatsu da kuma flowers masu kyau,  yayinda  Abaya Vail ɗin dake yafe saman kanta, ya sauƙo har zuwa ƙirjinta,   babu wani kwalliya akan fuskarta, lipstick ne kawai sai kuma kwallin data sanya acikin ɗara ɗaran idanunta,   sosai taƙara kyau, cika da kuma wayewa, duk da cewa a ƴan shekaru biyun da suka wuce itaɗin ba baya bace wajen kyau, amma ayanzu komai nata yaƙara ninkuwa akan nada, yanzu tana amsa sunanta na cikakkiyar mace.  Kallonta ta maida kan agogon dake ɗaure akan tsintsiyar hanunta.   "4:30 pm" ta faɗa tana ɗan waro idanunta, da sauri tacigaba da tattare takardun, wasu tasa acikin jakarta, wasu kuwa ta sanyasu acikin wata drawer dake cikin office ɗin. Wayarta da jakarta ta ɗauka, kana ta nufi hanyar fita daga office ɗin.

Motarta ƙiran  Corolla LE  tashiga haɗe da bata wuta, ta fice acikin jami'an..    Bata wani jima sosaiba ta isa sabon gidansu wanda suka koma babu jimawa.

Da sallama ɗauke abakinta ta kutsa kanta cikin falon, babu kowa afalon, sai TV Plasma ɗinsu dake ta aiki shikaɗai.  Direct wani ɗaki dake cikin falon ta nufa,  tsayawa tayi ajikin ƙofar ɗakin tana sakin murmushi, idanunta nakan wani yaro da shekarunsa na duniya bazasu wuce uku ba, ya nata  ƙiriniyansa  shi kaɗai, yaron kyakkyawane sosai, gashin kansa kuwa kamar na larabawa.  Cikin sanɗa tashiga takawa harta ƙarasa wajen dayake zaune, murya a hankali tace.
"Babyy!"    Jin muryar mahaifiyarsa acikin kunnuwansa yasashi juyowa da sauri, yana ganinta, ya tafi ya faɗa jikinta, yana dariya, itama dariyan tayi haɗe da manna masa kiss akan bakinsa, cike da kulawa haɗi da ƙaunarsa.  

"Aunty Sannu da dawowa" cewar Haulat me yi mata rainon yaron, idan zata aiki.

"Yauwa Haulat sannu da gida" Zahrah ta amsa mata fuska a sake.

Ɗaukan yaronnata tayi suka fice daga ɗakin, direct sama ta haura inda anan bedroom ɗinta yake.

Aje yaron nata tayi akan gado haɗe da durƙusawa agabansa, chocolate irin marar zaƙi sosai ɗinnan ta ciro ajakarta, kana ta ɓare ta basa a hanunsa, da murna Asad ya karɓi Chocolate ɗin,  matso da fuskarsa yayi daf da tata, kiss yayi mata akan kumatunta haɗe da cewa "Thank you Mummy!" yayi maganar ne cikin muryarsa dake ɗauke da tsananin yarinta.

Murmushi tayi kana taɗanja kumatunsa, miƙewa tayi ta wuce cikin bathroom acan ta cire kayan jikinta haɗe da sakarwa kanta shower. 

Koda ta fito sama sama ta shafa mai domin yanayin garin ana ɗan busa zafi,    wani dogon skin tight  baƙi ta sanya, wanda yayi matuƙar bayyana surar jikinta, bama kamar hips ɗinta da suka sake cika,  wata riga mai  net tasanya, irin fitted ɗinnan, sosai rigan tayi mata kyau,  ƙirjinta ne kawai yazamana a rufe, amma gaba ɗaya jikinta daga cikinta zuwa bayanta a bayyane suke, haka tsarin rigar yake.

Da Body Spray ɗinta me daɗin ƙamshi ta feshi jikinta,   dogon gashinta dayasha kitson kalaba, ta kama ta ɗaureshi da  ribbon,  direct gaban ɗan madaidaicin fridge ɗin dake ɗakin ta nufa,  buɗewa tayi ta ɗauko goran Yoghurt, buɗe murfin goran  tayi tasoma sha ahankali.

Shigowarsa ɗakin kenan, amma kuma kokaɗan bataji motsin buɗe ƙofarsa ba,   yana sanye da riga da wando na Suit navy blue colour masu kyaun gaske,  tabbas ya sauya daga kamanninsa nada, yaƙara haske da kyau, ga lallausan sajensa da ya kwanta luf akan fuskarsa,  yazama wani na musamman dashi, me tafiya da hankalin ƴan mata, yaƙara zama Handsome, dagani kai kasan kuɗi sun zauna masa..

Dariyan Asad da taji ne yasata waigowa ta kalli yaron, atunaninta ko ɓarna yakeyi mata, gani tayi idanunsa nakan ƙofar shigowa ɗakin, saboda haka itama ta maida idanunta wajen, da taga Asad ɗin na kallo.
Idanunsu ne suka sarƙe a cikin na juna, wani irin murmushine ya ƙwace mata, haɗe da lumshe idanunta, ta kuma buɗesu alokaci guda, shima murmushin yayi mata, kana ya buɗe duka hannayensa, alaman ta taho garesa,    babu musu ta ƙarasa garesa, haɗe da faɗawa cikin jikinsa, atare suka rungume juna, tare da sauƙe ajiyar zuciya.

Hanunsa yasanya yashiga shafa bayanta, haɗe da soma hura mata iskan bakinsa, cikin kunnenta. Luf tayi acikin ƙirjinsa, tana mai jin daɗin abun da yakeyi mata, idan har tanajin iskan bakinsa acikin kunnenta, sosai take samun nutsuwa acikin ruhinta.

Sun kusan mintuna 10 a haka kafun tace dashi cikin sanyin murya.    "Sannu da dawowa!"
Bai amsa mata ba, saima hannayensa daya ɗaura a gefe da gefen cikinta, yashiga shafawa a hankali,  shiru tayi aƙirjinsa tana sauƙe numfashi.  Ɗayan hanunsa yasanya ya ɗago haɓarta, suka jefa idanunsu acikin na juna, wani irin kasalane ya dirar mata alokaci guda, sakamakon tozali da kyawawan idanunsa da tayi.  lumshe nata idanun tayi, tana sauƙe numfashi a hankali, matso da tasa fuskar yayi gaf da tata, harsuna iya jiyo hucin numfashin juna,  bakinsa ya buɗe haɗe da kamo lip ɗinta na ƙasa, yasoma sucking a hankali,  tsikar jikinta ne, ya shiga tashi, take wani shauƙi yasoma ratsa ta,  kusan mintuna 6 yana sucking lip ɗinta, kafun ya tsagaita yashiga maida numfashi.  Ganin haka yasanya ta sanya hanunta akan wuyansa, haɗe da sanya bakinta acikin nasa, ta laluɓo harshensa, tasoma masa shan sweet,   yanda take sucking ɗinsa tausassun laɓɓanta na kai komo cikin bakinsa shine abun da ya ƙara hautsina tunaninsa,  tsananin sha'awarta ne yasake ninkuwa acikin zuciya da jikinsa.  Hannayensa yasanya yana ƙoƙarin buɗe gaban rigarta. Kukan Asad ne ya katsesu daga duniyar da suke ƙoƙarin faɗawa, gaba ɗaya su sunma manta da cewa yana ɗakin. shikuwa Asad chocolate ɗinsane yafaɗi ƙasa, shiyasa sa fashewa da kuka.

Da sauri Zahrah ta ƙarasa garesa haɗe da ɗaukan chocolate ɗin  ta danƙamasa a hanunsa, dawo da kallonta tayi ga Doctor dake tsaye idanunsa sunyi ja. Murmushi tasakar masa, tare da takawa ta ƙarasa garesa, hanunsa ta kama ta zaunar dashi akan gado, kayan jikinsa tashiga rage mai, saida ya rage dagashi dai dogon wandon suit ɗin dake jikinsa.    Bathroom tashiga ta haɗa masa ruwan wanka.  saida taga shigansa wankan kafun ta ɗauki Asad suka fice daga cikin ɗakin, wajen Haulat tamaida Asad, itakuma ta wuce kitchine. Milk Shake tahaɗa masa, haɗe da ɗaukan wani tray na tangaran me kyau ta yayyanka kayan marmarin aciki.   ɗaukan ɗan madaidaicin tray ɗin tayi, tare da cup ɗin da milk shake ɗin ke ciki, ta nufi ɗakinta.

Harya fito a wankan yana zaune akan gado, dagashi sai long jeans ajikinsa,  tanashigowa cikin ɗakin, ya kafeta da tsumammun idanunsa,  ɗan madaidaicin stool ta jawo ta ɗaura kayan hanunta akai, zama tayi akusa dashi. Da kanta tasoma bashi fruit ɗin abaki.  Yanacin fruit ɗin amma gaba ɗaya hankalinsa na ga breast ɗinta da suka bayyana kansu ta saman rigar dake jikinta.  Sarai ta kula da cewa hankalinsa naga breast ɗinta, hakan yasa da gangan ta kuma saɓule wuyar rigan don yagani da kyau.  Tana kammala bashi fruit ɗin, aka soma ƙiran sallan Magriba,  alwala yayi haɗe da ɗaura brown ɗin jallabiya akan wandon dake jikinsa yafita zuwa masallaci, itama alwalan tayi, ta gabatar da sallah, bata tashi akan sallayan ba har saida tayi sallan isha.   Wanka takuma yi, yanzu kam wata fitinanniyar sleeping gown ta sanya wacce iyakarta guiwa,  turarenta da tasan yana tafiya da imaninsa tashafa, haɗe da ɗaukan wani wanda ƙamshinsa ke haifar da kasala, tashafa aƙasan breast ɗinta dama duk wani lungu da saƙo na jikinta. 

Tana tsaye agaban dressing mirror ɗin yashigo cikin ɗakin, dawowarsa daga masallaci kenan.

Lumshe idanunsa yayi haɗe da buɗewa,  idan yabiyewa Zahrah zata zautar dashi ne kawai, gaba ɗaya yawani zama soko akanta, kullum ƙara kyau da cika take, sannan kuma duk kwanan duniya ƙara fito da wani sabon salo take, wanda take rikitasa da su,  ga tarin soyayyarta dake ƙara wanzuwa acikin jini da jikinsa, shikansa baisan wani irin so yakeyi mata ba, amma yayi amanna da cewa, bayan Zahrah babu wata,  ita kaɗaice bata da tamka, ita ta musammance acikin matan duniya. baisan wata mace ba aduniyarsa bayan ita, amma kuma yanaji ajikinsa cewa, yayi dace, yakuma samu gamdakatar wanda bayajin akwai wata wacce zata kama ƙafarta.

Ƙarasowa yayi gaban mirror ɗin ya rungumeta ta baya haɗe da kwantar da kansa abayanta, yana sauƙe ajiyar zuciya, iya ƙamshin dake fita ajikinta ma kaɗai, ya isa yasanya masa feeling, ina kuma ga ya taɓa lallausan fatar jikinta.

Hanu tasanya ta shafi gefen fuskarsa, haɗe da ɗan zame jikinta daga nasa.  Hijab ɗin dake aje kan gado ta ɗauka, haɗe da zurawa ajikinta.

"Hubby Nasan Babyna yayi bacci, banaje na dubasa" tafaɗi haka tana me nufar hanyar fita daga ɗakin.
Bai iya ce mata komaiba harta fice.

Tanazuwa ɗakin Asad ɗinkuwa tasamu yayi bacci akan lallausan gadonsa,  yayinda Haulat mai kula dashi itama tuni tayi bacci, zama tayi ta tofeshi da addu'a, haɗe da gyara masa kwanciyansa. Rage musu hasken wutan ɗakin tayi kana ta yi ficewarta.

Tana shiga tasamesa tsaye dagashi sai towel ɗaure a ƙugunsa, yayinda jikinsa ke ɗauke da danshin ruwa, da'alama ruwa ya watsa wa jikinsa.    Cire hijab ɗin jikin nata tayi, ta nufo inda yake,   atare suka sakarwa juna murmushi,    jawota yayi haɗe da mannata da ƙirjinsa,  hanunsa yasanya acikin gashin kanta, murya asanyaye yace.
"Nayi kewarki dear, muna gida ɗaya amma yau two days kenan banji ɗumin jikin ki ba!"  yaƙare maganar yana me cusa kansa acikin wuyanta.    Lokacin da sajensa ya taɓa fatar wuyanta, saida taji wani yarrrrrr ajikinta,  hanunsa yakai kan cikinta, ya warware igiyan da tazamo mahaɗin rigar dake jikinta, aikuwa take rigar ta buɗe ta gaba, hannayensa duka yasa ya juyo da ita suka zamana suna fuskantar juna.   

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login