Showing 42001 words to 45000 words out of 177624 words
a sake kai tsaye yanufeshi, "Yauwa likita ka'iso saikuyi maganar acikin gida ko, kasan mutumiyar taka sai a hankali" Baffa yafaɗa still washe da baki, like namesake ɗina (fatiwasha lol), ba musu Dr Sadeeq yarufa masa baya suka shiga cikin gidan.
Yauma dai a tsakar gidan yazauna duk da cewa babu yawancin haske a tsakar gidan amma akwai hasken farin wata.
"Wai Zahrah bazaki tashi kije bane, nacemiki gashi yashigo har cikin gida, dan Allah Zahrah kada ki watsamana ƙasa a ido, kidubi girman mutumcin dayayi miki sanda kike ciwon hauka kitashi kije " Inna tafaɗa cikin lallami.
"Ciwon Hauka kuma Inna?" Zahrah ta tambaya cike da mamaki domin dai ita a saninta batayi wani ciwon hauka ba,
"Ƙwarai kuwa kedai tashi kije kawai" Inna ta faɗa still cikin lallami, bawai don tasoba haka tasanya hijab haɗe da ficewa daga cikin ɗakin.
Tun fitowarta a cikin ɗakinnata ya kafeta da idanunsa, har taƙaraso can gefe dashi ta zauna, haɗe da takurewa waje ɗaya tana matsan ƙwalla,
"Saiyaushe zaki daina kuka ne?" Dr Sadeeq yatambaya cikin tattausar murya,
Shiru tayi bata amsa masa ba domin jin kalamansa take tamkar zuban narkakken dalma acikin kunnuwanta,
"Matsowa yayi gaf da ita, har tana iya jiyo ƙamshin turarensa, babu wani tsoro kokuma ɗar ya sanya hannayensa akan kumatunta yashiga share ma ta hawaye, sosai jikinta yaɗauki rawa domin tayi matuƙar tsorata da hakan,
"Banason kukanki Zahrah, nasani dole kina buƙatar ayi miki uzuri, kinajin ciwo da damuwa a cikin ranki, kuma kinada buƙatar kyakkyawan kulawa, kidaina min kallon wani bare kokuma na daban, kiyi mini kallon ɗan uwanki, wanda zaki iya gayawa damuwarki, inaso kifaɗamin duka damuwarki kinji ƙanwata, nasan zakiji sanyi idan kika faɗi ko kaɗanne daga cikin damuwarki !!" Dr Sadeeq yayi maganar cikin lallashi dakuma tausasawa,
Kuka takuma sanyawa mai sauti, domin kuwa tabbas abun daya faɗa ɗin hakanne, tana buƙatar mai kulawa da'ita, tana buƙatar ɗan uwa mai ɗaukar damuwarta, saurin ɗago da kanta tayi ta kallesa, sakamakon jin hannayensa da tayi akan nata,
Kai ya jinjina mata batare da yace da ita komaiba, yana kallonta tayi kuka harta ƙoshi, a hankali take sauƙe ajiyar zuciya, kofin ruwan dake gefensa ya ɗauka, haɗe da kawai bakinta, babu musu taɓuɗe baki ta soma sha, domin kuwa yanda zuciyarta ta bushe tana buƙatar ruwan,, saida tasha fiye da rabi kafun ta tsagaita da shan ruwan, sosai taji zuciyarta tasoma dawowa daidai nutsuwarta kuma yasoma sauƙa,,
"Yaushe zaki koma makaranta ?" Yajefomata tambayar kansa tsaye, kallon mamaki tabisa dashi, domin kuwa ko a wasan mafarki bata sake kawo sake zuwa makaranta acikin zuciyarta ba, itakam ai duk wani farinciki yawuce mata,
"Kada ki yarda da abun da zuciyarki takecewa, ba'akanki aka faraba, haƙiƙa abune mai ciwo amma idan kika daure zuciyarki, zaki iyayin rayuwar farinciki kamar kowa" Dr Sadeeq yafaɗa cike da son ƙarafafa mata guiwa,
"Kada kayi ƙoƙarin yaudarana domin kuwa sam banda wani sauran farinciki, yaruguzamin duk wani burina, to yanzu inaso kasanar dani shin menene amfanin karatuna bayan zuciyata cike take da ƙunci? kuma miye amfanin farincikina bayan rayuwata ke waye take da duhu ?, zanfaɗama damuwata domin nayarda dakai, inajin ciwo mai zafi a zuciyata bankuma san ranan warkewarsa ba, shin maiyasa zaka ce nayi farinciki bayan kasan cewa bazantaɓa samuba ?"
Ɗan gajeren murmushi yayi haɗe da matse hannayenta gam acikin nasa, "Saboda inada yaƙinin baki farinciki mai ɗorewa, amma saikin daina sakanki a damuwa "
Wani irin kallo tawatsa masa wanda yake nuni da cewa tana buƙatar ƙarin haske akan maganganun nasa.
"Zahrah ke yarinyace mai ɗauke da tarin ƙuruciya, kinaga yadace kibar rayuwarki tatafi a haka ?"
Dr Sadeeq yatambaya yana mai kafeta da idanu.
"Haka Allah yatsaramin, BAZAN BUTULCE BA, yadda da ƙaddara yana da kyau, NAYARDA DA ƘADDARA TA, saidai kuma bazan mantaba har abada, babu mai aurena, babu kuma mai tallafawa rayuwata, zanƙare rayuwata acikin ƙunci, idan har kaɗaukeni ƴar uwa kamar yadda kafaɗa, to inaso ka yi tunani shin wacce ta tsinci kanta acikin mummunar ƙaddara irin tawa akwai sauran farinciki da yarage mata?, ni yarinyace haryanzu bangama sanin rayuwaba, amma tabbas nasan mai kyau dakuma marar kyau, saboda haka rayuwata a gurɓace take, yariga daya ruguzata, bakuma zata taɓa kafuwa ta tsaya da ƙafafunta ba har abada, BANI DA ZAƁI likita amma akwai Allah ya isarmin komai!!" gaba ɗaya hawaye yagama wanke mata fuska, wannan karan ba iya zuciyarta bace tayi rauni hadda tashi zuciyar, lallai ƙaddaran Zahrah mummuna ce, amma kuma yazama dole yatsaya yakawar mata da duk wani duhu dake rayuwarta shi mai iya dawo mata da farincikin tane idan harzata amince, amma yasani Zahrah ta yanke ƙauna gaduk wani ɗa namiji,
"Likita ga abinci ko" Inna takatsemusu tunanin da sukeyi su dukansu.
Inna tana aje abincin tajuya tashige cikin ɗaki, kallonsa yamaida kan ɗan ƙaramin bakinta dake bushe, sannan yakuma maida kallonsa kan idanunta, a matsayinsa na mutum mai karantar yanayin ɗan adam, take yakaranci halin da take ciki, bayajin yunwa ko kaɗan domin saida yaci abinci kafun yafito, amma saboda dalili ɗaya yasa yajawo kwanon abincin gabansa, shinkaface ƴar gida jalof, ko mai batajiba ballantana albasa, amma haka ya share, yakai loman abincin cikin bakinsa, taunawar farko yaci karo da dutse amma haka dolensa ya basar (readers likitafa yagamu da girkin manya Inna, lol🤣).
"Zo muci" yafaɗa a taƙaice,
Saurin kallonsa tayi haɗe da girgiza kanta, domin ita yanzu abinci baya gabanta, damuwarta ma abincine a wajenta,,
Babu alamar wasa akan fuskarsa kaitsaye yanufi bakinta da hanunsa wanda yake ɗauke da ƙwayoyin shinkafa domin da hanu yakecin abincin,,
Saƙare haka tayi tanakallonsa domin wannan shine karo na farko a rayuwarta da wani ɗa Namiji ba muharraminta ba ya taɓa yunƙurin bata abinci a baki,
Kai tagirgiza masa alamar bataso haɗe da kawar da kanta gefe,
"Kinaso muyi faɗa kenan, kuma hakan nanufin baki ɗaukeni ɗan uwaba, nasan wunin yau bakisa komai a cikin kiba, sbd haka banason gardama, idan kuwa kikace bahaka ba, to akwai alluran da na taho da'ita, yanzu sainasa Baffa da Inna su riƙemin ke na yi miki har guda uku!! " yaƙare maganar in a serious tone, aikuwa ya faɗar mata da gaba domin kuwa tsoron alluran da takeyi haryazarce tunanin mutane, "Haaaa" Dr Sadeeq yafaɗa still yana kusanta hanunsa ga bakinta, tamkar dai za abawa ƙaramin yaro abinci.
"Basaikabani ba zan iya ci!" Zahrah tafaɗa cikin raunanniyar muryarta,
"To ci ingani" Shima yafaɗa yana mai turo mata kwanon abincin gabanta, ahankali ta sa hanu ta tsakuri abincin, tamkar wacce akace ta tsakuro garwashin wuta da hanunta, daƙyar ta iya buɗe baki ta kai loman abincin bakinta, murmushi yayi haɗe da sanya hanunsa acikin kwanon abincin yasoma ci, duk da cewa ba daɗin abincin yakejiba, adole Zahrah take kai loman abincin bakinta bayanda ta'iyane kawai,,
Lomanta huɗu ta soma kwarara amai a wajen tamkar zata amayar da ƴaƴan hanjinta, miƙewa tayi daga tsugunen da take domin tasoma ɓata jikinta da amai, aikuwa wani irin jiri ne ya ɗe beta take ta faɗa kan Dr Sadeeq dashima yake yunƙurin tashi tsaye,, gaba ɗaya yatarota tafaɗa cikin ƙirjinsa, yayinda aman dake jikinta ya gogu ajikin kayansa,,
Da sauri su Inna da Baffa suka ƙaraso wajen domin tundaga ɗaki sukejin ƙaran amannata, "Lafiya likita maiyasameta kuma ?" duka suka tambaya cikin ƙosawa, da'alama dai sungaji da lamuranta.
" Bakomai inaga olsa (ulcer) ce kawai ke damunta " Dr Sadeeq yafaɗa yana mai ƙoƙarin shimfiɗeta a akan tabarman da suke zaune,
Saidai gaba ɗaya ba ƙarfi a jikinta, saboda haka duk ta narkemasa a cikin jiki, yayinda shikuwa zuciyarsa ke tsananta bugawa, addu'a yake a zuciyarsa Allah yasa ba abun da yake zargi bane ke damun Zahrah idan kuwa abun da yake zargine tabbas babban tashin hankali na gaba...
(Wani tashin hankali munbanu readers 😲, Allah yasadai bacikine da ita ba, da Zaidu ya yi aiki mai tsada 🤣 )
*Breakfast na baku kuji daɗinku*
*23/November/2019*
*Voted, Comment, and Share please....follow me on Wattpad @fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Lovely Brother Khabier*
*🌈Kainuwa Writers Association*
{United we stand & succeed; our ambition is to entertain and motivate the mind of readers}
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*Editing is not allowed📵*
*Chapter 38 to 39*
A hankali Doctor ya kwantar da ita, cikin sanyin jiki yanufi motarsa don ɗauko jakarsa ta aiki, domin dama daga office yake yabiyo tagidannasu,, Allah yasa ba abun dayake hasashe bane yake shirin faruwa, lallaiko idan har ya zamana Zahrah ciki ne da ita, to fa shikansama yashiga tashin hankali, bawai ita kawai ba, domin yasan ɗan guntun tsarin daya shirya rugujewa zaiyi, to ina kuma ga Zahrah wacce bata gama warkewa daga ciwon dake jikinta ba, kuma ace taƙara faɗawa cikin azabar wani ciwon, tabbas yasan tashin hankalin da zata shiga sai ya take wanda tashiga a baya,, jiki a saluɓe haka Dortor Sadeeq yadawo cikin gidan, zuwa lokacin har Inna ta ɗauketa takaita cikin ɗaki.
Tana kwance akan ƴar katifarta, sai faman sauƙe numfashi take a hankali, dagani kasan aman da tayi ya galabaitar da'ita sosai, zama yayi gaf da'ita, haɗe da kama hanunta, lokaci guda yaji jikinta yaɗau zafi sosai, kayan aikinsa dake cikin jakarsa ya ciro ya fara yi mata ƴan gwaje gwaje,
Wata irin ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya Dr Sadeeq ya sauƙe sakamakon gano abun dake damun Zahrah da yayi, duk da cewa baiyi mata gwajin ciki ba, amma a iya ɗan bincikensa da yayi ya gano cewa bata ɗauke da ciki, ulcer ce kawai tayi mata mummunan kamu, sakamakon yunwa daya samu mazauni acikin cikinta.
Kallonsa yamaida kan Baffa haɗe da cewa " Bawani babban damuwa bane ulcer ce, yanzu zanje na ɗauko wasu allurai a asibiti sainazo nayi mata, insha Allah komai zaiyi dai dai"
"To likita Allah yayi albarka muna godiya sosai !" Baffa yayi maganar cike da yabawa ƙoƙarin Dr Sadeeq.
Miƙewa Dr Sadeeq yayi haɗe da sakai yafice daga cikin ɗakin, yana fita su Inna ma suka mara masa baya.
Kwanciya tayi lamo tamkar wacce ruwa ya ƙare mawa a jiki, gaba ɗaya jinta takeyi bata da kuzari, gawani irin zafi da ƙuna da ƙirjinta keyi mata,,
Koda Dr Sadeeq ya ɗauko magunguna da Alluran da yakamata ace yayi mata, sai da ya biya ta wani katafaren wajen sai da kayan marmari yasaya mata dangin su apple da su inabi hadda abarba, bai tsaya anan ba hadda fresh milk saida yabiya ya saya, gudu yashiga sharawa akan titi, burinsa ɗaya shine yaje yabata taimako mai kyau, sosai yakejin tausayinta, saboda ta cancanci a tausaya mata, daga wani ɓangare na zuciyarsa kuwa idan yatuno da cewa ba ciki bane da'ita, sai yaji wani irin sanyi da nishaɗi na ratsa zuciyarsa, wanda ya alaƙanta hakan da cewa bayason tasamu ciki saboda zata sake shiga wani hali marar daɗi. (kuji shifa😏 wai hakane reaɗers?)
Mintuna ƙalilan ya iso ƙofar gidannasu.
Koda yanemi Inna da tayi masa iso zuwa ɗakin Zahrah'n, cewa tayi yashiga kai tsaye ai anzama ɗaya su yanzu ɗan uwa suka ɗaukeshi (hmm)
Yanda ya barta haka yataradda ita sai dai yanzu idanunta a lumshe suke, "Zahrah!!" yaƙira sunanta dai dai lokacin da yake ƙarasawa kusa da'ita.
A hankali ta buɗe idanunta tasauƙesu a kansa, ɗan guntun murmushi yayi mata, wanda yasanya gabanta mugun faɗuwa, domin kuwa murmushin nasa yatuna mata da murmushin Oga Babba (ZAIDU manyan maza, lol), take taji wani irin abu ya toshe mata maƙoshi, yayinda zuciyarta tayi ƙunci.
Aje ƙatuwar ledan dake hanunsa yayi, haɗe da zama akan katifarta ta, "Tashi ki zauna" yafaɗa yana mai kafeta da ido, kai kawai ta girgiza masa alamar bazata iya tashi ba, ajiyar zuciya ya sauƙe, haɗe da kamo hannayenta duka biyu ya ɗagota zaune, duk da cewa yana matuƙar jin shock idan yataɓa jikinta, amma babu yanda zaiyi dole hakan shine mafita.
Ledar daya shigo da'ita ya buɗe, haɗe da ɗauko apple guda ɗaya ya miƙa mata, kallonsa kawai tayi haɗe da kau da kanta gefe,
"Magani bazaiyi aiki a jikinki yadda ya kamata ba, harsai kinci abinci, idan kuwa kikasha magani bakici abinci ba zai wahalar dake sosai, dan Allah banason gardama Zahrah, nasan kuma kema kina buƙatar abinci, don haka ki karɓi apple ɗinnan kici, ciwon ulcer bazai taɓa sake kiba matuƙar kina zama da yunwa!!" yaƙare maganar cikin lallashi.
Ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba haɗe da ɓata fuska, sam batason cin wani abu daga garesa, amma yana ƙoƙarin tursasata dole, kuma yayi gaskia dayace tana buƙatar abinci, tabbas ita kanta tasan tana buƙatar abinci.
"Yauwa Zahrah nasan dama keɗin maijin magana ce, karɓa kici ko!" yaƙare maganar yana mai marairaice fuska, haɗe da kusanto da apple ɗin dai dai saitin bakinta.
Hanu tasa ta karɓi apple ɗin, a hankali take gutsuran apple ɗin kamar mai gutsuran magani, duk da kuwa cewa taji test ɗinshi a cikin bakinta,, tana cinye apple ɗin ya miƙo mata goran fresh milk mai sanyi.
"Ungo wannan ma ko kaɗanne kisha, nasan zai taimaka kuma idan kika sha bazanmiki allura ba!"
Saurin kallonsa tayi, don tabbatar da abun da ya faɗa, aikuwa idan dai har bazai yi mata allura ba idan tasha, to lallai zatayi ƙoƙari tasha ɗin,
"Ka tabbata bazakamin alluraba idan nasha?" tafaɗi maganar a sangarce, cikin kuma yanayi na marar lafiya,
"Bazan miki allura ba Zahrah, idan dai harkika sha, kuma koda zan miki ma kaɗan zanmiki kuma bamai zafi ba!" yaƙare maganar yana murmushi.
Take tasake turɓune fuska haɗe da turo baki.
"Nifa wasa nake miki bawata allura dazan miki !" Dr Sadeeq yafaɗa yana dariya ƙasa ƙasa.
Karɓan goran fresh milk ɗin dake hanunsa tayi, haɗe da kafa kanta tasoma sha, tun asalinta ita mai son madara ce, haka kuma fresh milk yana ɗaya daga cikin abubuwan da takeso, sabo da haka sosai tasha har saida taji cikinta yacika, take kuma ɗan kuzari yasoma dawo mata, miƙo masa goran tayi alamar taƙoshi,
"Kishanye duka" yafaɗa a taƙaice,
"A'a naƙoshi" itama tabasa amsa ataƙaice,
"Okay to mai kikeson ci yanzu kuma?" yatambaya yana mai tsareta da idanu.
"Babu" ta basa amsa a taƙaice,
Kansa kawai yajinjina haɗe da ɗauko drugs ɗin daya taho mata dasu yasoma ɓarewa yana bata, sai ta rufe ido haɗe da ƙanƙame jiki sannan take iya sha, shiko dariyama take basa, bai taɓa ganin mai tsoron allura da magani kamarta ba.
Yana gama bata maganin yace ta kwanta, batayi ƙoƙarin musa masa ba, ta kwanta domin kuwa kafun yace mata kwantan, idanunta harsun fara rufewa,, "Zahrah!" yaƙira sunanta, shiru babu amsa kuma bata ko motsaba sai idanunta da suke buɗewa suna rufewa a hankali, da'alama dai yabata wani magani ne mai matuƙar kashe kuzarin jiki.
Dariya yayi ƙasa ƙasa haɗe da cewa "Yarinta da daɗi"
zuƙa zuƙan alluran daya taho dasu guda biyu, yaciro acikin ledan haɗe da haɗa komai da komai wanda ya kamata,
Riƙe alluran yayi a hanunsa haɗe da mai da kallonsa ga Zahrah wacce take kwance lamo, a hankali yasanya hanunsa ajikinta haɗe da juyata, saida ya rumtse idanunsa shima kafun ya'iya yi soka mata alluran, yana gamawa ya juyata ɗaya gefen ma yayi mata, sosai taji zafin alluran amma bata da bakin magana, sai dai hawaye da suka soma gangara daga cikin idanunta.
"kiyi haƙuri Zahrah ƴan mata, dolece tasa namiki alluran, inaso naga kinsamu lafiya ne!" Dr Sadeeq yafaɗi maganar cikin tausasa murya, bayan yashare mata ƙwallan dake sauƙa a gefen fuskarta, miƙewa yayi tsaye haɗe da sakai yafice daga cikin ɗakin, bayan yatattara kayan aikinsa.
Bai taradda Inna a tsakar gida ba sai Baffa, don haka a gurguje yayi masa sallama, yatafi sbd dare yasoma rabawa.
Ɓangaren Zahrah kuwa tun kafun Dr Sadeeq yafita bacci yayi awon gaba da'ita, domin daga magungunan har alluran da yayi mata suna saka bacci.
A hankali yake tuƙin motar tasa, fuskarsa cike take da annuri, Situation ɗin Zahrah kawai yake tunawa, sosai komai nata yake burgesa, musamman ma tsoronta, hakanan yakejin kansa cikin nishaɗi idan yana tare da'ita, baikumasan dalilin faruwar hakanba.
Koda ya yi parking motarsa kai tsaye ɓangaren mahaifiyarsa ya nufa, domin yau ko gaisawa basuyi ba ya fice daga gidan,
Koda yashiga falonnata bai isketa ba, don haka kaitsaye yanufi bedroom ɗinta domin yanada yaƙinin cewa zai taradda ita acan.
Knocking ƙofar bedroom ɗinnata yashigayi a hankali, jin knocking ɗin ya tsananta ne yasa taba wa mai knocking ɗin umarnin shigowa, domin dama tana da yaƙinin cewa shiɗinne kasancewar taji ƙaran shigowar motarsa cikin gidan.
Zaune ya'isketa akan sallaya, da'alamu idar da sallan nafilanta kenan.
Harƙasa ya durƙusa ya gaidata cike da girmamawa, cikin sakin fuska itama ta amsa masa gaisuwarsa haɗe da cewa " Ina kashigane yau tunsafe ?"
Ƙeyarsa yashiga sosawa a hankali, yayinda fuskarsa ke ɗauke da ɗan murmushi.
" Am Hajiya aikin office ne ya ɓoyeni, dana tashi kuma sai na biya ta gidansu Zahrah domin duba jikinta, to danaje sai nasamu batajin daɗi !" ya faɗi maganar fuskarsa ɗauke da alamar damuwa.
"Gidansu Zahrah kuma Sadeeq ?, to Allah ya sauwaƙa, a kwai a binci, a derny saika ɗebi iya yanda zaka iyaci, domin daganinka bakasa komai a cikin ka ba" Hajiya tafaɗi maganar cike da kulawa,
"To Hajiya zanci insha Allah" yaƙare maganar yana me miƙewa tsaye, sallama yayiwa mahaifiyartasa kafun yasakai yafice daga cikin ɗakin.
Yana fita Hajiya tasaki ƙwafa haɗe da cewa
"Nasan maganinka aure zanyimaka ko da baka shiryaba, natabbatar hakan zai sa ka rage yawan kaiwa dare a waje, kullum kai baka da hutu aiki tamkar engine, duk kuma rashin iyali shiya jawo hakan ".
Yana isa ɗakinsa yasoma rage kayan jikinsa, ɗan ƙaramin towel ya ɗaura haɗe da faɗawa bathroom yasakar mawa kansa shower, cikin zuciyarsa kuwa cunkushe take da tarin tunanuka kala kala, haƙiƙa yasan cewa yana buƙatar mace akusa dashi, domin dai shiba dutsi bane da zai zauna haka ƙiƙam ko da yaushe, dole yana buƙatar wacce zata na taimakawa wajen enjoying life ɗinsa, tun ba yauba yagane cewa yana ɗaya daga cikin maza masu yawan buƙata, amma kuma sosai yake ƙoƙari wajen shan pills wanda zasu sama masa relief, a gurguje yayi wankan yafito, wata brown ɗin jallabiya mai kyau yasanya bayan yatsane ruwan dake jikinsa, kulan abincin daya ɗauko a falon Hajiyarsa yajawo haɗe da buɗewa, jallof ɗin shinkafa ne sai coslow, kaɗan ya tsakura a cikin plate yasoma ci, gaba ɗaya tunanin Zahrah yacika masa zuciya wani irin feeling yakeji a kanta, idan yatunota sai yaji nishaɗi ya sauƙa acikin zuciyarsa,