Showing 51001 words to 54000 words out of 177624 words

Chapter 18 - SHU'UMIN NAMIJI completed Hausa novel

18 Jul 2024

37545

rayuwarki"  zuciyarta ta faɗa mata hakan cike da ƙarfafa mata guiwa, "Amma tayaya hakan zai kasance, bayan banda wani ginshiƙi dazai taimakamin ?" Zahrah tatambayi kanta,  sake gyara zamanta tayi haɗe da ɗaukar wayarta, kai tsaye tashiga wajen dazai sadata da apps ɗin wayar,  Word Charm shine game ɗin daya ɗauki hankalinta, duk cikin apps ɗin dake wayar, dama tanason game ɗin, don haka kaitsaye tashiga tasomayi, take taji kewa da kaɗaicin da take ji sun soma ragewa, a wannan rana dai  Zahrah batayi wani dogon tunani  da takura kanta ba, dazaran taji ta takura zata ɗauki wayarta tasoma buga game,  idan ta gaji  da buga game ɗin kuwa, sai ta shiga Instagram shima sosai yake rage mata kewa (nima haka, lol)..

Tayi kyau sosai cikin blue rover gown ɗin dake jikinta,  wata baƙar lufaya ta sanya a jikinta wanda yataimaka wajen ƙarawa shigar tata kyau da armashi,  batayi wani kwalliya akan fuskarta ba, ta dai shafa man leɓe dakuma kwalli, amma duk da haka tayi kyau, dama mai kyau ko baiyi kwalliya ba kyawunsa baya ɓuya.

Kasancewar yau baza su jima a makaranta ba, yasanya bata ɗauki jakaba, sai wasu ƴan littatafai da ta ɗauka a hanunta, sai kuma wayarta,      koda ta fito tsakar gidan zaune a bakin  murhu ta iske Inna tana tuyan ƙosai, wanda Baffa yace ayi na karyawa.

"Inna ni zanwuce makaranta" Zahrah ta faɗa tana mai ƙoƙarin gyara zaman lufayan dake jikinta.

"Bazaki tsaya ki karyaba Zahrah"
Baffa dake fitowa daga cikin ɗakinsa ya faɗa.

Ɗan guntun murmushi Zahrah tayi haɗe da shafa cikinta "Banajin yunwa sosai Baffa, kuma ina tsoro kada na makara!"

"Eh kina da gaskiya, kinga kuwa tun ɗazu likita, yazo yana jiranki, bayanda banyi da shi ba akan yashigo, amma sam yaƙiya, don haka gwamma ki hanzarta, a dawo lafiya "  Baffa yaƙare maganar yana mai yunƙurin komawa cikin ɗakinsa.

"Ameen Baffa nagode!" Zahrah tafaɗa cike da farinciki, domin kuwa karo na farko kenan a rayuwarta da taga tsananin kulawan Baffa a kanta.

Tana fitowa yasakar mata kyakkyawan murmushinsa,  ga mamakinsa sai yaga itama ta sakar masa murmushi, wanda yayi matuƙar taɓa masa zuciya, domin kuwa bakaɗan ba tayi kyau, da tana murmushin.

"Saiyanzu ki ka ga daman fitowa? kinshanyani kamar kin aje dutse" Doctor yafaɗi maganar yana mai turo baki gaba, tamkar ƙaramin yaro.

Dariya sosai Zahrah ta shiga yi, domin yanayin yanda yayi maganar yazama dole wanda ya gani ya dara,   hangame baki Dr yayi yana kallon yanda take dariyan, abun da bai taɓa gani ba kenan, tun haɗuwar su da'ita, bai taɓa ganinta tana dariya ba sai yau, ashe ma duk kyawunta da yake gani, bai ga komai ba, domin da tana dariyan tafi  masa kyau.

Hanunta tasanya ta toshe bakinta, haɗe da tsagaita dariyan da takeyi, kallonsa tayi haɗe da cewa "Bakaga yanda kazama yaro ba dakana maganan nan, tamkar ɗan shekara takwas!"

Murmushi yayi haɗe da jefamata hararan wasa, cikin yanayin da yayi magana ɗazu yakuma cewa "Shine kikemin dariya ko? sai na faɗaki da mamana!"  ai kamar yaƙara mata fower'n da riyan nata ne,  nan take taci gaba da dariyanta, hadda ɗan guntun ƙwalla a idanunta,  wani irin sanyi da nishaɗi yaji yana huda zuciyarsa, tabbas bashida wani buri da yawuce yaga Zahrah tana cikin farinciki Alhmdlh, yau gashi ta sanadiyarsa tana dariya dakuma nishaɗi,

"Kayi haƙuri, bazan sake shanyaka ba, amma gaskia ka iya shagwaɓa da yawa!" Zahrah tafaɗa dai dai lokacin da tayi mawa kanta mazauni acikin motar, haryanzu dariyane kwance akan fuskarta.

"Wato dai yau mugunta kike ji dashi, dariya hadda hawaye!" Doctor yafaɗa cikin nishaɗi.

"Bahaka bane, kai ɗinne dai kawai kabani dariya!" itama ta basa amsa cikin nishaɗi.

"Dagaske kike, saboda ni kike wannan nishaɗin? " Dr ya tambayeta cike da zaƙuwa, duk da kuwa cewa yasan sabo da shiɗinne take nishaɗin.

"Eh mana, saboda kaine, kasan kaban dariya sosai, kuma nasan bama ni kaɗaiba, duk wacce takalleka a irin wannan yanayin dole zatayi dariya"

Ajiyar zuciya Dr ya sauƙe haɗe da murza key ɗin motar, suka ɗau hanyar da zata sadasu da titi.  

"Idan kina dariya kinfi ko yaushe kyau ƴan mata na!" Dr yafaɗa cikin muryar nutsuwa.

Saurin maida kallonta garesa tayi, jin abun da yafaɗa tayi kamar wani almara,  sai kuma taga yanayinsa tamkar bashine yayi maganar ba.

Yi tayi itama kamar bataji mai yace ba, mai da kallonta tayi ga titi, tana mai kallon yanda ababen hawa suke gudanar da hada hadansu.

"Maiyasa ki ka ƙi cin abinci? ko kinfiso ki zauna da yunwa ne?" Doctor ya jefo mata tambayar da batayi zato ba.

Kallo ɗaya ta yi masa ta kau da kanta gefe, "Banjin yunwa ne, sannan kuma banaso na yi latti"
tafaɗi maganar a taƙaice.

Baice da'ita komaiba, saima buɗe ɗan ƙaramin drowern dake jikin motar yayi, wani haɗaɗɗen cake dake cikin wani ɗan ƙaramin kwali ya ciro, haɗe da ɗaura mata akan cinyarta,  " Kici, kuma banson musu" yanayin yanda yayi maganar zai tabbatar ma da cewa, ba wasa yake ba.

"Nagode, amma zanci idan muka fito a lecture" itama ta faɗa kai tsaye.

"Yanzu nakeso kici, umarnine bawai shawara ba"  yakuma faɗi maganar  cikin yanayi mai nuni da cewa da gaske yake maganar.

Batason yi masa musu, domin koba komai yayi mata halacci a cikin rayuwarta,  a hankali take gutsuran cake ɗin tana kaiwa bakinta, duk da cewa cake ɗin yayi mata daɗi. 
Duk abun da takeyi yana lure da'ita, yanayin yanda take tauna abincin shiyafi komai burgesa.

Saida taci cake ɗin fiye da rabi, kafun ta dawo da kallonta garesa, "Naƙoshi" tafaɗa tana mai yatsine fuska.

"Dole sai kin cinye, domin kuwa ni idan nabawa mutum abuna, bai isa yacemin ya ƙoshi ba, dole sai yacinye koda kuwa ya ƙoshin"

Ɗan guntun murmushi tayi haɗe da cewa "Dagaske nake naƙoshi, amma da alama dole kakeson min"

"Dolen dole ma kuwa" yafaɗa dai dai lokacin da yagama parking motar tasa, domin kuwa harsun kawo cikin makarantar tasu, hanu ta ɗaura akan murfin motar da niyar buɗewa ta fita, tuni ya dannawa ƙofofin luck,  saurin kallonsa tayi domin bata fahimci hakan da yayi me  yake nufi ba.

"Babu inda zakije, matuƙar baki cinye cake ɗin nan ba" yafaɗi hakan yana me jingina bayansa a jikin kujeran da yake kai.

Ƙwaɓe fuska Zahrah tayi cikin sigar lallashi, tace "Kayi haƙuri, naƙoshi, idan naci da yawa, bazan iya karatu yanda ya kamata ba!"

"Um,Um, naƙi wayon, saura kaɗanne fa please kicinye shi mana Zahrah!" Doctor Sadeeq yaƙare maganar cikin lallashi.

"Um, Um, na ƙoshi, gaskiya idan naci zai cutar dani, zanyi ƙatuwa da yawa, ni kuma banaso nayi ƙatuwa!" cikin zallan shagwaɓa Zahrah tayi maganan.

Dariya sosai Dr Sadeeq ya sanya, domin kuwa maganar Zahrah ta bashi dariya, wai ita bataso tayi ƙatuwa hmm.

"To ai yaune kawai, kuma kinga bazakiyi ƙatuwa ba, nima banso kiyi ƙatuwa da yawa, amma inaso kiyi ƙatuwa kaɗan!" yanayin yanda yayi maganar  kaɗai ya isa sanyawa mutum mutuwar jiki.

Batace dashi  komaiba, domin bata fahimci inda maganar tasa ta dosa ba, ɗaukan ragowan cake ɗin tayi, tashiga turawa acikin bakinta, tamkar wacce aka bawa guba. 
Dariya Doctor Sadeeq yashiga yi mata ƙasa ƙasa, domin kuwa yanda takecin cake ɗin, dagani kasan dole a kayi mata bawai a son ranta bane. tana cinyewa ya miƙomata goran ruwa, ai kuwa ba musu ta karɓa ta shiga sha, domin dama duk cake ɗin ya shaƙeta.

Cikin yanayi na shagwaɓa da ɓata fuska tace " Na cinye yanzu zan iya tafiya!" 

Dariya Dr yayi haɗe da cire luck ɗin da yasanyawa ƙofofin motar "Zaki iya tafiya, amma kikula da kanki sosai, sannan idan kun fito a lecture wani zai kawo miki saƙo daga nine ki amsa"

"Wani saƙo?" Zahrah ta tambaya cike da ɗaurewar kai.

"Zakiyi latti,kiyi sauri kije" Dr yafaɗi hakan don kawar da tambayar da tayi masa.
Bata sake cewa komai ba tabuɗe murfin motar tafice, yauma dai sai da yaga shiganta cikin hall ɗin kafun yatada motarsa yabar cikin makarantar, direct shima asibiti ya nufa, domin yau yanada aiki sosai.

Sosai yau ta gane Lecture ɗin da akayi musu, saɓanin sauran ranakun da suka wuce wanda ba komai take fahimta daga cikin abun da ake koyar musu ba.

Fitowarsu kenan daga lecture, tafe suke su biyu, yayinda Husnah keta mita, wai jimawan da sukayi suna lecture, yasanya tanemi gaba ɗaya abincin cikinta ta rasa.

Dariya Zahrah tayi haɗe da cewa "Nikuwa kinga ɗigo na yunwa banaji, domin kuwa yau ɗure, a kamin dan dole na"

"ɗure kuma bestie? Amma badai Inna da Baffa bane sukaimiki ɗuren bako?"

"Doctor Sadeeq ne!" Zahrah tafaɗa a taƙaice.

"Doctor Sadeeq kuma? lallai kuwa Doctor yayi babban ƙoƙari, shiyasa na ganki yau kina cikin farinciki"  Husnah tafaɗa tana mai ƙoƙarin gimtse dariyar  da take ƙoƙarin taso ma ta, domin ita kam ta hango wani babban al'amari dangane da Doctor dakuma Zahrah.

"Maikike nufi?" Zahrah ta tambayi Husnah cikin tsare gida.

Husnah batakai ga bata amsa ba, wani mutumi  ya ƙaraso garesu, hanunsa ɗauke da wata leda, sallama yayi musu suka amsa masa.

Kaitsaye ya miƙomawa Zahrah ledar dake hanunsa, haɗe da cewa "Gashi inji oga"

Take maganar da Dr yafaɗa mata ɗazu a cikin mota, cewar wani zai kawo mata saƙo, ya faɗo mata, cikin sanyin jiki ta amshi ledan, haɗe da ce masa ta gode.

"Saurin karɓe ledan Husnah tayi daga hanun Zahrah, haɗe da cewa "Allah yasa abun daɗi ne, domin yawuna haryafara tsinkewa, kinsanni ba baya bace wajen kwaɗayi"

"Wow special gift!!" Husnah tafaɗa sanda idanunta suka gane mata abun da ke cikin ledar,

"Amma ba haka naso ba, ƙawata naso ace wani abun ci ne kinga da sai na morewa bakina!" Husnah ta ƙare maganar tana mai ɓata fuska.

Dariya Zahrah tayi haɗe da sanya hannayenta ta dafa kafaɗun Husnah,  cike da nishaɗi tace " Allah ƙawata, ki rage kwaɗayi, yanzu idan abun ci ne, yazuba mana wani abu a ciki, mukazo mukaci, ya cutar da mu,kuma fa? kinga kwaɗayi ya jawo mana kenan,kuma bai mana rana ba"

"Dan Allah malama sakeni,  nayarda da Dr nasan babu abun da zai ɓamu wanda zai cutar da mu, kedai kawai mugunta ne irin naki, bayan kinsan inajin yunwa, muje cafeteria muci abinci please!" Husnah tafaɗa tana mai daɗa kwaɓe fuska.

"Yi haƙuri ƙawata bani nakar zomonba, muje sai kici abincin ko" Zahrah tafaɗa cike da kulawa.

"Ungo kayan shafanki, domin kuwa cigaba da  riƙesu ma,  ƙaramin yunwa zaiyi" Husnah ta ƙare maganar tana mai miƙomawa Zahrah ledar dake hanunta.

Dariya kawai Zahrah tayi haɗe da amsar kayan, sarai tasan Husnah bata da haƙurin yunwa ko kaɗan.

Ice cream kawai Zahrah tasha, yayinda Husnah kuwa ta cika cikinta da shinkafa.    Yau darasi biyu garesu kacal,  don haka suna fitowa kowa ya yi ƙoƙarin kama gabansa.

Waige waige tashiga yi ko zata hangosa, amma babu alamar komai irin motarsa,  wayarta ce ta soma ƙara alamar shigowar ƙira,    Number ne ke yawo a kan screen ɗin wayar babu suna, dama kuma batayi tunanin Numbern zai fito da suna ba, domin batayi saving numbern kowa ba, wama ta sani da zatayi saving number'nsa.

Har saida wayar ta kusa katsayewa kafun Zahrah ta ɗaga ƙiran,   "Zahrah! na gaji, da yawa, aiki yamin yawa, please ga nan driver na, zaizo ya ɗaukeki ya kaiki gida, kiyi haƙuri kinji ƙanwata!!" Dr Sadeeq ya faɗi haka cikin kwantar da murya, da gajin yanda muryansa take fita slow kasan cewa a matuƙar gajiye yake.

A jiyar zuciya Zahrah ta sauƙe haɗe da cewa "Shikenan kahuta lafiya"

"Yauwa Ƴan mata na, ki kulamin da kanki" ƙit ya kashe wayar, ba tare da ya tsaya ya saurari mai zata ce ba.

Murmushi kawai Zahrah tayi haɗe da girgiza kanta, "Hmm wai itace  ƴan mata, itakam yanzu ai ta wuce a ƙirata ƴan mata saidai sauran Zaid" tafaɗi hakan a zuciyarta, take kuma taji idanunta sun kawo ruwa.  Dai dai lokacin motar Dr Sadeeq ta ƙaraso inda take tsaye,   kasan cewar yayi mata bayanin cewa driver'n sane zaizo ɗaukarta, dan haka batayi wani jinkiri ba, ta buɗe murfin motar tashiga, ko kallon inda driver'n yake batayi ba,     "ZAHRAH!" muryan Dr Sadeeq ya daki dodon kunnuwanta, saurin maida kallonta inda taji muryan tayi, ai kuwa shiɗinne kwance a jikin kujeran gidan baya, idanunsa ɗaya ya kashe mata haɗe da ɗage giransa ɗaya sama, "Surprise!" yafaɗa fuskarsa ɗauke da murmushi.

Murmushi itama tayi masa, haɗe dayin ƙasa da kanta,  domin yanayin yanda yayi mata maganan, yasanya taji jikinta yayi sanyi. 

"Dawo nan muzauna, ki bar driver yayi aikinshi"

Ɓata fuska Zahrah tayi haɗe da turo baki gaba, cike da shagwaɓa tace "Ni dai kabarni na zauna anan ɗin ma yayi!"

"Nace ki dawo nan muzauna ko!" yafaɗi hakan babu alamar wasa akan fuskarsa.

Cike da sakalci Zahrah ta dawo gidan baya inda yake zaune,  ko kallonsa batayi ba saima langwaɓewa da tayi a jikin kujera.    Har sukayi nisa a tafiyan babu wanda yace da ɗan uwansa ƙala,    cikin  shagwaɓa tace "Bakace min aiki yamaka yawa ba, amma mai yasa kazo?" 

"Saboda ya cancanta nazo, ina da burin baki kyakkyawan kulawa a ko da yaushe, ko bakiyi farinciki da hakan ba?"

"Nayi farinciki sosai!" Zahrah tafaɗa kai tsaye, domin kuwa sam batason irin kallon da yake yawan yi mata a wasu lokutan.

Baisake ce da ita komai ba, shima sai ma komawa da yayi ya jingina bayansa da jikin kujeran motar.

A haka har suka iso ƙofar gidan su Zahrah'n,   kallo ɗaya tayi masa haɗe da buɗe murfin motar tayi ficewarta, yana ganin shigewarta gida, yace driver ya ta da motar suje.

Bayan Sati Biyu....

Wani irin shaƙuwa ne mai ƙarfi yashiga tsakanin Doctor Sadeeq da Zahrah, kullum shi ke kaita mkaranta shi kuma ke ɗauko ta, sosai yake bata kulawa, baya son duk wani abu da zai ɓata ranta, ko ya sanya taji ba daɗi, ɓangaren Zahrah ma, sosai take kiyayewa dashi, tana iya ƙoƙari wajen ganin bata musa masa idan ya umarceta da tayi abu, ko kaɗan batajin wani abu a dangane dashi, tana dai yi masa biyayya tana kuma ganin girmansa, domin kamar yanda yace ta ɗaukesa, a matsayin ɗan uwa, to a matsayin ɗan uwan ta ɗaukesa, domin kallon yaya take masa,  sannan kuma sosai wayarta take ɗe be mata kewa,  yakanyi ƙoƙari wajen ganin ya ƙirata a waya, a kowani dare, sai dai hiran tasu bata tsayi suke sallama da juna,  sosai rayuwarta tasamu canji, bakamar da ba, duk da cewa abune mawuyaci manta abun da ya faru da'ita, amma takanyi ƙoƙari ƙwarai wajen ganin ta gusar da duk wani damuwarta.

Tsaye yake a gaban tangamemen dressing mirror ɗin dake kafe a jikin bangon ɗakin nasa, yayi kyau sosai cikin riga da wandon shadda dake jikinsa, ba abun da jikinsa keyi banda tashin ƙamshi,  hannayensa duka yazura a cikin aljihun wandon shaddan dake jikinsa,    tabbas a kwai wani al'amari mai girma dake cikin zuciyarsa, haƙiƙa kuma akwai abun da yakeso ya furta,amma tayaya, baisan da wani manufa zata ɗauki zancen ba, baisan wani amsa zaiji daga bakinta ba, wannan shiya hanasa furta mata tsadaddan kalman dayake ta ɓoyewa tsawon lokuta,  bayajin zai samu abun da yakeso daga gareta, bakuma yajin zai samu amincewarta, ya tabbatarwa kansa cewa, a yanzu lallashi take buƙata fiye da komai, sannan kuma bata buƙatar wata magana wanda zata zamo sanadiyar rugujewar ɗan farincikin da ta soma samu,   sai zuciyar sa ta ƙarfafa masa guiwa, saikuma gangar jikinsa tayi sanyi laƙwas. 

"Ba'asan jarumin Namiji da tsoro ba!" wata zuciyarsa ta furta masa hakan.

Ƙwarai ya yarda da cewa shi ɗin jarumi ne, amma kuma gurin da yake da muradin isar da saƙonnasa wajene mai rauni,  dole zai fuskanci ƙalubale guda biyu, rashin nasara, ko kuma, yin nasara,   wayarsa ya ɗauka ya sanya a cikin aljihunsa, kai tsaye ya fice daga cikin  ɗakin nasa, yana shiga cikin motarsa ya bata wuta, kai tsaye unguwar su Zahrah ya nufa, sosai ya yarda da shawaran da zuciyarsa ta basa, lallai yazama dole ya bayyana mata sirrin dake kwance cikin zuciyarsa,  sai dai yasan balallai ta aminta da ƙuɗirinsa ba,  amma zai jarraba ya gani.

A ƙofar gidansu yayi parking motarsa, haɗe da ciro wayarsa, ya danna wa Number'n Zahrah  ƙira, sai dai harzuwa lokacin zuciyarsa fat fat haka take bugawa. tana ɗaga wayar yace "Ina ƙofar gidanku, dan Allah kizo ki sameni" banji mai tace masa ba, sai gani nayi ya mai da wayar tasa cikin aljihunsa, haɗe da sauke nannauyar ajiyar zuciya....

(Tofa readers, mai kuke ganin Doctor Sadeeq zai faɗawa Zahrah, da haryakejin tsoron faɗa mata, sbd baisan daya zata ɗauki maganar ba,  to zadai muji kome nene a next page insha Allah!   Ko ina Baba Zaidu kuma 🤷‍♀)

         *3/December/2019*

*Voted,Comment, and Share please..... Follow me on Whatsapp and Wattpad @fatymasardauna



🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

               *SHU'UMIN NAMIJI !!*

         *Written By*
   *Phatymasardauna*

*Dedicated To My Brother Khabier*

*🌈Kainuwa Writers Association*

{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

       
          *WATTPAD*
   @fatymasardauna

*Editing is not allowed📵*

(😂Yasin bansan haka Baba Zaidu yake da masoya ba sai kwana biyu da bana taɓo sa, ashe dai masoyan Zaid sunfi maƙiyansa yawa,  kusha kurumin ku mutanen Zaidu yau zan taɓo muku chapter'n shi, su Munubia nasan anyi missing 🤣)

   
     *Chapter 46 to 47*

Tana aje wayan ta ɗauko wani rover hijab ɗinta ta sanya a jikinta,    koda tafito daga cikin ɗakin nata, zaune ta iske Baffa da Inna, a tsakar gida, domin dai dama dare yasoma rufawa,  cike da ladabi tace " Baffa Doctor Sadeeq yana ƙirana a waje"

Gyara zama Baffa yayi haɗe da cewa " to naji ƙaran tsayuwar mota ai, ashe dai likitane yazo, to adawo lafiya" 

Muguwar harara Inna ta jefamawa Zahrah, cike da masifa tace "Wato ni banza bankai matsayin da zaki tambayeni ba ko? wato Baffanki kaɗai kika gani a wajen?"  

Cikin sanyin murya Zahrah tace "Kiyi haƙuri Inna, naga shi ya kamata na sanarmawa hakanne, tunda ya na nan!"

"Wuce kije ƙiran da yake miki kinji Zahrah'u, barta Salame yau masifa take ji dashi" Baffa yaƙare maganar yana mai wurgamawa Inna harara.
Bata kuma sauraran abun da Inna zatace ba tasakai tayi ficewarta daga cikin gidan..

Duk da cewa babu wadataccen haske a wajen, amma tana iya hango kyawun da kayan jikinsa sukai masa,  "gaskiya Dr kyakkyawane shima" tafaɗi hakan a cikin zuciyarta.

Da sallama ɗauke a bakinta ta ƙaraso

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login