Showing 177001 words to 177624 words out of 177624 words
akayi mata har guda uku, ga kayan ciye ciye dana shaye shaye, tsananin farinciki da ƙaunarsa ne suka mamaye zuciyarta, juyawa garesa tayi ta rungumesa, haɗe da cusa kanta acikin ƙirjinsa tana shaƙan daddaɗan ƙamshin jikinsa.
"Thank you so much my lovely husband!!!" tafaɗa cikin sanyi yayinda ƙaunarsa ke ƙara ratsa zuciyarta.
"Babu godiya atsakaninmu My Wife kina da babban matsayi a wajena, keta musamnan ce, inasonki da duka zuciyata!" Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana ƙara matseta acikin ƙirjinsa.
Kwantar dakanta tasakeyi ajikinsa cike da ƙaunarsa, haƙiƙa tasamu duk wani abu da takeso, farinciki, soyayya, da kuma zaman lafiya, sosai Doctor ke bata kulawa, bayason ɓacin ranta ko kaɗan, yana ƙaunarta har acikin jininsa, itama kuma tana ƙaunar mijinnata sosai, ayanzu yafiye mata kowa da komai, yabata farinciki haka kuma yabawa iyayenta, yamantar dasu komai na ɓacin rai da talauci, ya wadatasu da komai na rayuwa, bata da wani TAURARO sama da shi, shiɗin na musamman ne arayuwarta, koda sau ɗayane bata taɓa yin danasanin kasantuwarsa amatsayin mijinta ba, ko da kowa aduniya zai juya mata baya, tasan banda Mijinta Haskenta Abun Alfaharinta. Rayuwarta tayi mata daɗi akoda yaushe saidai tace ALHAMDULILLAH..
***
Yana tsaye agaban dressing mirror yayinda little Zahrah ke tsaye agefensa, tana shan chocolate, Afrah ce tashigo cikin ɗakin hanunta ɗauke da kofin coffee wanda take haɗamasa kullum daren duniya.
Miƙo masa kofin coffee ɗin tayi, ya amsa yana murmushi, aje kofin yayi haɗe dasanya hanu ya jawota jikinsa ya rungumeta, bakinsa ya kai dai dai saitin kunnenta, ahankali yace "Inasonki ƴar lukutar matata!"
Dariya Afrah tasanya haɗe da cewa "Nima inasonka ɗan lukutin mijina"
Murmushi kawai yayi haɗe da sanya hanu yashafi kumatunta.
"Nima inasonka Papa na!!" little Zahrah dake tsaye a gefensu tafaɗi haka da ƙarfi.
"SON SO nake miki farincikina, idan babuke acikin rayuwata, to babu wani haske dazan sake gani, Allah yarayamin ke na aurar dake ga miji na gari!!" yafaɗi haka yana dariya, acikin zuciyarsa kuwa, har yau tsananin danasanin yanda halayansa suka kasance a baya yake, yayi danasani sosai, har gobe kuma akan danasani yake, bazai kuma taɓa daina Istigfari ba har ƙarshen rayuwarsa.
Duk da Little Zahrah bata fahimci me maganganunsa ke nufi ba, amma tasan cewa mace da namiji suna aure, domin wancan satin daya wuce ma sunje auren ƙanwar momynta.
Dagudu taƙaraso ta rungumeshi, ƙasa ƙasa tace "Nidai ko zanyi aure bakowa zan auraba sai Friend, aishima yanasona ko Papa?"
Durƙusawa yayi agabanta cike da soyayyarta yace "Yanasonki mana, ai aduniya babu wani wanda zaiƙi me wannan kyakkyawar fuskar, ke ɗin ta musammance My Soul!"
Daɗine yakama Zahrah, sake rungume mahaifinnata tayi, aranta tana ƙara ƙaunar papan nata, domin adunia tasan bayan shi babu wani wanda zaiyi mata irin wannan soyayyar dayakeyi mata a yanzu......
*** *** ***
Duka ahali biyun rayuwarsu ta miƙa komai suna yinshine cikin farinciki da jin daɗi, akowacce rana ta duniya ƙara ƙaunar junansu suke, saidai muce MASHA ALLAH.
*Alhamdulillah anan nakawo ƙarshen labarin SHU'UMIN NAMIJI ina fatan zakuyi aiki da abun dayake dai dai aciki, inda nayi kuskure kuma Allah Ubangiji yayafemin, nagode sosai da sosai masoyana, haƙiƙa kunbani haɗin kai nakuma ji daɗin haka Allah Yabar Ƙauna, waƴanda na ɓatawa rai don Allah kuyi haƙuri, balaifina bane, haka labarin yake, haka kuma ƙaddaran ZAID da ZAHRAH yake, babu wanda ya isa sauya ƙaddaransa.
*Ku ci gaba da bibiyana Insha ALLAH Zakujini da labarai kala kala wanda ina da tabbacin zasuyi muku daɗi, Ina muku SON ƘAUNA!!! Insha ALLAH Ina zuwa muku da wani sabon labarin wanda zai ɗare ma Shu'umin Namiji, ina kuma da tabbacin cewa zaku ji daɗinsa sosai.*
*✔️OTE ME ON WATTPAD*
@fatymasardauna
*8/March/2020*
*Taku Ako da Yaushe*
fatymasardauna