Showing 66001 words to 69000 words out of 177624 words

Chapter 23 - SHU'UMIN NAMIJI completed Hausa novel

18 Jul 2024

37536

ne!" Dr yafaɗi hakan cike da son ganar da Yayarta sa, cewa ba bu wani aibu agame da aurensa da Zahrah.

Gaba ɗaya duk iya abun da yasani agame da Zahrah, bai ɓoye mata ba, sai da  yasanar mata, atunaninsa hakan zai sanya Aunty Raliya ta ƙaunaci Zahrah, amma me sai gani yayi tana taɓe baki haɗe da kawar da kanta gefe alamar ma ta'inda maganar tasa  take shiga tanan take fita.

Yana idar da zancen ta dubeshi haɗe da ɓata fuska tace "Kagama?  kai a tunaninka zaka bani wata hujja dazata sanya naga dacewar aurenka da'ita ne, hmm  niba yarinya bace Sadeeq, yakuma zama dole kasanja tunani, kakuma manta da maganar wata wai ita Zahrah, idan kuma kafison kafuskanci ɓacin rai daga wajen Hajiya, to kaci gaba da zama akan bakan ka harmaganan takai ga kunnen Hajiya!!" tanakaiwa nan a zancenta ta miƙe fuuu tawuce cikin ɗakinta tabarshi zaune.

Hannayensa yasanya duka biyu ya tallafi kansa,  lallai akwai babban ƙalubale a gareshi,  agun Aunty Raliya ma kaɗai ga'irin ɓacin ran daya fuskanta, inaga Hajiyarsa kuma.?

Miƙewa yayi daga zaunen da yake tamkar wanda ƙwai ya fashewa a jiki haka yake tafiya, gaba ɗaya ƙwaƙwalwarsa tasake dagulewa, yazone don yasamu mafita amma sai gashi abubuwa sun sake dagulewa.

Da ƙyar yake iya tuƙa motar tasa. Haka yanufi gida cikin rashin kuzari, sai dai fa haryanzu bai saduda da maganar Auren Zahrah ba, yanaji ajikinsa cewa Zahrah zata zamo matarsa Insha Allah.

Gagarumin meeting su ZAID suka gudanar mai zafi, a babban hotel ɗin nan wato SHERATON, sosai aka samu riba dakuma ƙarin buɗi a ɗaya daga cikin  company'n nasa da suke Nigeria, hakan yasa yaƙarawa gaba ɗaƴa ma'akatansa albashi.

Sunjima suna meeting ɗin dan haka amatuƙar gajiye suka fito dukansu, lokacin har dare yasoma rufawa.    Kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa, yayi yaga karfe 6 daidai na yammaci, ɗan ƙaramin tsuka yayi haɗe da soma yunƙurin cire rigan suit ɗin jikinsa wada yaɗaura akan kayan dake jikinsa, 
saboda gajiyan da yayi bai iya tuƙi da kansa ba, sai  driver'nsa yaƙira yayi driving ɗinsa.

Gyara kwanciyansa yayi ajikin kujeran motar haɗe da lumshe idanunsa, wani irin sarawa kansa keyi masa,  daga wani ɓangare na zuciyarsa kuwa sosai meeting ɗinnan ya ɓata masa rai, domin kuwa ya hanasa ƙarasawa ga ZAHRAH'nsa,  wacce saboda itane ma gaba ki ɗaya yadawo ƙasar, yayi missing din Zahrah sosai,  yayi missing kyakkyawan murmushinta haɗi da kyawawan idanunta, yayi missing kallon kyawawan laɓɓanta masu daɗin tsotso. Gaskiya dole  ya killace Zahrah tayanda zata zama nasa shi kaɗai.

Suna isa gida kai tsaye ɓangarensa ya wuce, a gajiye yashiga bathroom yayi wanka,  koda yafito a wankan, direct masallaci ya wuce donyin sallan magriba. Sai da yajira aka yi sallan isha tare dashi a masallaci, kafun  ya siɗaɗo yadawo ɗaki ya kwanta, yau ko abar ƙaunar tasa wato wine baisha ba bacci ɓarawo yayi gaba dashi.

Zahrah ce kwance akan katifarta sai juyi take ta kasa bacci, gaba ɗaya kanta ya kulle zuciyarta cike take da tarin tunanuka kala kala. "Anya banyi sauri kokuma gangancin yarda da kuma amincewa da soyayyar Dr da nayi ba?" zuciyarta ta tambayeta.
Zumbur haka ta miƙe zaune, haɗe da soma girgiza kanta
" A'a banyi kuskure ba, tabbas bayan shi babu wani maiso da nuna tausayi gareni!" tabawa kanta amsa a bayyane.

Wayartace takawo haske alamar shigowar ƙira, kasancewar ta sanya wayar a silent hakan yasanya wayar batayi ƙaraba.

"Doctor" shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayar.

"Shima baiyi bacci ba kenan" tafaɗi hakan a bayyane.

Saida wayar ta kusa katsewa kafun Zahrah ta ɗaga ƙiran haɗe da kara wayan akan kunnenta.

"My princess bakiyi bacci ba kenan?" Dr Sadeeq yatambayeta cikin muryarsa mai ɗauke da damuwa.

"Um, kaifa me yahanaka bacci" Zahrah itama  tatambayeshi.

"So da ƙauna dakuma tunaninki susuka hanani bacci! kefa mai yahanaki bacci?" yatambaya cike da son jin amsar da zata fito daga bakinta, "Allah yasa itama tunani na ne ya hanata bacci" yafaɗi hakan a zuciyarsa.

Kunyane yaɗan kamata amma sai ta basar haɗe da sauƙe ajiyar zuciya "A'a nikam karatu nake, shiyasanya banyi bacci ba, amma yanzuma zanyi baccin." tafaɗi hakan a taƙaice.

Ko kaɗan baiji daɗin amsar da ta basa ba, amma yasan cewa wataran dole zatayi tunaninsa kamar yanda shima yake nata tunanin.

"Naji daɗi sosai da kika amince dani Zahrah na! hakan yasa na ƙara jin sonki sosai da sosai a cikin zuciyata!!"  cikin shauƙin so yafaɗi maganar.

"Umm banji mai ka faɗa ba!" Zahrah tafaɗi hakan cikin wani irin salo wanda batasan ma tayi shi ba, duk da kuwa cewa taji mai yace, iskancine kawai irin nata.

Lumshe idanunsa yayi da suka soma sauya kala, sosai yanayin yanda tayi maganar ya sauƙar masa da kasala.

"Bacci kika farane Zahrah na?" yatambayeta cike da kulawa, domin kuwa shi anasa zaton dagaske batajisa ba.

"Um!" Zahrah ta basa amsa a taƙaice cikin ƙasa ƙasa da murya, domin kuwa tanaso yayarda cewa baccin takeji, saboda har yanzu, bata gama amanna dacewa sonsa take ba, kuma koda za'a kasheta tasan cewa ba sonsa take ba, kawai dai ta tsinci kantane da amince masa, amma batun soyayya kam babu shi.

"To kiyi bacci mai daɗi kinji My princess, inasonki sosai, ki kulamin da kanki, banson koda ɗigon wani a bune ya raɓe ki!"  Dr ya faɗi haka cikin shauƙin SO (Sisters kujisafa su likita ashe an iya kalaman love, lol.)

"Uhumm sai da safe." Zahrah tafaɗa a taƙaice bayan ta zare wayar daga kunnenta.
  "Gaskiya abune mai matuƙar wahala koyawa zuciya So'n  abun da bata so, ya Allah kataimakeni, haƙiƙa banajin tsanarsa haka kuma banajin soyayyarsa a zuciyata, sannan kuma inaji ajikina cewa zan'iya rayuwa dashi, to me hakan ke nufi, ba so bane kuma ba ƙi bane to menene?" tatambayi kanta a bayya ne, saidai kuma bata da amsar da zata bawa kanta.

Komawa tayi ta kwanta bayan ta kashe wayarta ta gaba ɗaya.

Cike da saƙe saƙe bacci yayi awungaba da ita.

Ɓangaren Dr Sadeeq ma, sai da yajima yana saƙawa da kuncewa, ba abun da yake ɗaure masa kai, kamar yanda ya kasa fahimtar cewa Zahrah, na son sane ko bata sonsa. da ƙyar dai shima bacci ya'iya ɗaukarsa.

Washe Gari.
  
Yau tun saven thirty suke da lecture, dan haka da wuri tasoma shirya kanta, sosai tayi kyau cikin shigar jar abaya haɗe da jan hijab ɗin dake jikinta,   hand bag ɗinta ta rayata a bisa kafaɗanta. Kana tafice zuwa tsakar gida.  Zama tayi akan taburma haɗe da jawo farantin ƙosai da kuma kofin kunun da Inna ta aje mata tasoma sha.  Baffa ne yafito daga cikin ɗakin sa yanaganin Zahrah yace
"Yauwa  kinfito ko, tun ɗazu kuwa likita yake jiranki a waje" 

"Eh Baffa nafito" tabashi amsa cike da mamakin jin cewa wai Dr yajima da zuwa, yanama jiranta a waje, amma kuma bai ƙira ta a waya yasanar mata ba.

Aƙagauce taci abincin kasancewar har bakwai tayi.

Tana fitowa yasakar mata kyakkyawan murmushi, itama murmushin ta sakarmasa bayan tagama ƙaremawa kwalliyarsa ta yau kallo.

"Kinyi kyau my princess!" yafaɗa cike da nishaɗi, domin kuwa sosai tayi masa kyau, jan kayan da tasa ya karɓi kalan fatarta.

"Kaima haka" tabashi amsa a taƙaice.

Murmushi yakumayi haɗe da buɗe mata murfin motar nuni yayi mata da hanunsa alamar tashiga, wani murmushi mai tsayawa a zuciya tayi masa haɗe da shigewa cikin motar tayi mawa kanta mazauni.

Tafe suke suna hira cike da nishaɗi, wanda gaba ɗaya yawan hiran Dr ne maiyi mata shi.
A haka har suka iso cikin makarantar, ƙoƙarin buɗe murfin motar ta soma yi.

"Ya haka? baki sallameni ba fa, kike ƙoƙarin  tafiya" Dr Sadeeq yafaɗi hakan cikin sigar zolaya.

Murmushi Zahrah tayi masa haɗe da yin fari da'idanunta "Bangane ba" tafaɗi haka cikin salo.

Lumshe idanunsa yayi haɗe da sanya hanu yashafi  sajensa,  "Inanufin bakice kina sona ba"

Dariya haɗe da kunyane suka kama Zahrah sai kawai ta buɗe murfin motar tayi ficewarta, domin kuwa bazata iya masa abun da yakeso ba.

Saida yaga shigewarta cikin hall kafun yaɗauke idanunsa daga kanta,  yanason mace mai kunya gashi Zahrah takasance me kunya. Cike da tarin tunaninta yabar cikin makarantar.

Ita da Husnah suna fitowa a lecture sukayi mawa kansu ma zauni a inda suka saba zama ko da yaushe.

Cike da tsananin farinciki Husnah tace "Naji daɗi ƙwarai Zahrah da kika amincewa Dr, wallahi gayen ya haɗu da yawa ƙawata,  tabbas idan kika auresa kin more don nasan za kisha madaran soyayya!"

Hararan wasa Zahrah ta wurgamawa Husnah, cike da son basar da zancen tashiga shafa cikin ta " Nifa yunwa nakeji" tafaɗa tana mai turo baki gaba.

"Kada dai kice zakimin sakalci, domin niba Doctor bane" Husnah tafaɗa cikin tsokana. dukan wasa Zahrah takai mawa Husnah, da sauri Husnah ta kauce.
Cafeteria  suka nufa acan suka cika cikinsu, daganan suka sake shiga cikin wani lecture'n.

Jikin   wata bishiya dake kusa da ƙofar fita daga makarantar  yayi parking motar sa,  gyara zama yayi haɗe da duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa.  Kallonsa ya mayar zuwa bakin tangamemen gate ɗin makarantar tasu,  hakanan yakejin ba zai iya fuskantar ta gaba da gaba ba.

Amatuƙar gajiye su Zahrah suka fito a lecture.  Tare suke tafe ita da Husnah, domin yau zataimawa Husnah rakiya ne zuwa  super market.   kai tsaye suka nufi ƙofar fita daga makarantar  kasancewa driver'n gidansu Husnah najiransu a waje.

Wani irin faɗuwar gaba taji, ya risketa adai dai lokacin da ta fito daga cikin makarantar.

Daga ɓanagaren Zaid kuwa zuciyarsa ne tashiga dukan uku uku, alokacin da'idanunsa suka sauƙa akan Zahrah,  hanu yasa ya murje idanunsa domin tabbatarwa da kansa cewa ita ɗince kokuwa gizo idanunsa suke masa.
Tabbas itaɗince Zahrah'n sane, har yanzu tananan da kyawunta, dakuma surarta mai ɗaukar hankalin duk wani lafiyayyen ɗa Namiji. 

"ZAHRAH!" yaƙira sunanta a bayyane, duk da kuwa yasan cewa bazata ji sa ba.  dai dai lokacin daya soma yunƙurin buɗe murfin motarsa don yaƙarasa gareta, dai dai lokacin itakuma ta shige cikin mota tare da Husnah.

*13/December/2019*

   
  *Voted, Comment, and Share please.... Follow me on Wattpad @fatymasardauna
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

               *SHU'UMIN NAMIJI !!*

      *Written By*
*Phatymasardauna*

*Dedicated to My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

             *WATTPAD*
        @fatymasardauna
         ___________________

*Editing is not allowed📵*

   *CHAPTER 57 to 58*

Cikin Hanzari ya buɗe murfin motar tasa ya fito, sai dai baikai ga ƙarasawa garesu ba, motar su ta gangara kan titi haɗe da ɗaukar hanya.

Hannayensa duka biyu yasanya ya kama ƙugunsa, haɗe  da furzar da iskan numfashi ta bakinsa, sam baiso haka ba, amma babu yanda ya'iya dole binsu zaiyi.

Kallonsa yamaida ga sauran cincirindon ɗaliban da suke tsaye a bakin gate ɗin makarantar.

Gani yayi gaba ɗaya sun saki baki da hanci suna kallonsa, sai kace wanda suka ga baƙon halitta, bama kamar ƴan matan dake tsaye a wajen.
Tsuka mai sauti yayi haɗe da komawa cikin motarsa, da gudun gaske ya cilla motar tasa kan titi, haɗe da rufa mawa motar su Zahrah baya.

"Yadai, naga lokaci ɗaya duk kinyi wata iri dake?" Husnah tatambayi Zahrah wacce tazama  silently  lokaci ɗaya.

A jiyar zuciya ta sauƙe haɗe da maida kallonta ga Husnah " Faɗuwar gaba nakeji Husnah, ban kuma san dalilin hakan ba" Zahrah ta faɗi haka cikin  damuwa.

"To fa, Allah dai ya tsare, amma ki yawanta addu'a, domin hakanne zaisa koma mene ne yazo da sauƙi"  inji cewar Husnah.

"Insha Allah!" Zahrah tafaɗi hakan tana mai kwantar da kanta a jikin kujeran motar, tanajin Husnah tace da Driver'n ya karkata akalar motar, ta sanja shawara  shoprite kawai zasuje,  bamusu kuwa ya sanja hanya zuwa Shoprite ɗin. Itadai Zahrah batace dasu komai ba.

Basu wani jima suna tafiya ba, suka iso tangamemen Shoprite ɗin.   "Muje ko" Husnah tace da Zahrah tana mai ƙoƙarin buɗe murfin motar.

Cikin sanyin jiki Zahrah, tafito daga cikin motar  suka nufi cikin shoprite ɗin. 

Basket biyu Husnah ta ɗauka nata ɗaya na Zahrah ma ɗaya, acewarta Zahrah ta zaɓi duk wani abun da take so, sam bahaka Zahrah tasoba amma babu yanda ta'iya, domin kuwa Husnah kafiya gareta, idan tace kayi abu tofa wai dole sai kayi.

Kayan shafa suka soma ɗauka, kafun suka garzaya zuwa kan su jaka da takalma ƴan yayi,  basu tsaya anan ba hadda kayan ciye ciye sai da suka ɗauka.

Cike da gajiyawa  Zahrah ke tura Basket ɗin da kayanta ke ciki, ita mamaki ma take yanda Husnah tasa suka jidi kaya mai yawa har haka,  amma idan tayi la'akari da irin gata da kuma kuɗin da mahaifin Husnah ke dashi, to sai tagama ba wani abun mamaki bane, kuma kuɗin kayan bazai mawa Husnah wahalar biya ba, domin kuwa anshagwaɓata sosai agida.

Daki daki aka lissafa kayan nasu, inda Zahrah ta ɗauki kayan dubu ishirin Husnah kuwa na dubu ishirin da biyar ta eba,  ƙoƙarin miƙa wa Cashier  ATM card ɗin dake hanunta Husnah ta soma  yi.  Amma sai  Cashier'n  yayi murmushi haɗe  da cewa
"Ai Hajiya ba'a buƙatar kuɗin ku, domin kuwa an riga da an biya muku, tunkafun ku kammala sayayyan, sannan wanda yabiya muku yace idan ma kuna da buƙatar ƙari, to kukoma ku ƙara, duk shi zai biya kuɗin"

Cike da mamaki Zahrah da Husnah suka shiga  kallon  juna.

"Anbiyamana fa kace Cashier? shin ka kosan me kake cewa?" Husnah tatambayeshi cike da mamaki.

"Ƙwarai kuwa nasan me nake cewa,  kudai ku ɗau kayanku kawai kuje, sannan ku gode mawa Allah, don shi yaje fo muku tsuntsu daga sama gasashshe "  Cashier'n nan  yafaɗi haka yana mai washe baki, kasan cewar shima anbarmasa kyautan ragowan canjin su.

Mamakine ya lulluɓe su Zahrah domin su a iyaka sanin su basu da wani wanda zai biya musu kuɗin siyayyan da sukayi, domin kuwa basu zo da kowa ba banda driver, inakuwa driver zaisamu maƙudan kuɗaɗe irin haka har ya biya musu kuɗin siyayya alhali shima yana fama da kansa.

"Kozaka iya faɗamana wanda ya biya mana kuɗin ?" Husnah ta tambaya.

"A gaskia bansan saba, sai dai da duk kan alamu irin larabawan nan ne da suke zuwa Nigeria lokaci zuwa lokaci" Cashier ɗin nan yafaɗa musu haka, domin shi a yanda yafahimta, da dukkan alamu wanda.yabiya musu kuɗin baiyi zubi da ƴan nan gida Nigeria ba, duk da kuwa cewa muma muna da kyawawan maza amma kuma kyawun wani ya ɗare na wani.

Idanu Zahrah da Husnah suka zaro atare, sakamakon jin abun da Cashier yace.

"Balarabe fa kace?" Husnah ta sake tambaya cike da mamaki.

"Eh Balarabe, kece Zahrah ko?"  Cashier'n nan ya tambaya  yana mai nuna Zahrah da hanunsa.

"Ya'akayi kasan sunana  ?" Zahrah ta tambayesa cike da mamaki.

Murmushi kawai yayi haɗe  da miƙa mata wata farar takarda.
"Ungo yace inbaki"

Cikin tsoro Zahrah ta karɓi takardan da Cashier ke miƙo mata,  haɗe da buɗewa.

_"Kiɗauki duk wani abun da kikeso MY ZAHRAH! ban damuba koda duka Shoprite ɗin zaki ce kinaso, zan iya mallaka miki kome kikeso a duniyar nan,  ko da kuwa dukiyata zata ƙare"_  abun da aka rubuta a jikin takardan kenan.
Wani irin bugawa Zahrah taji ƙirjinta yayi,  "To waye?" tatambayi kanta a fili.

"Yadai me aka rubuta acikin takarda'n?" Husnah ta tambayi Zahrah cike da zaƙuwa.

Bata takarda'n Zahrah tayi domin batasan me zatace da'ita ba.

Husnah tana gama karanta takarda'n tasaki murmushi haɗe da kallon Cashier'n nan daya zura musu idanu... "Mungode sosai, idan ka haɗu da wanda yabiyamana kuɗin, ka isar mana da saƙon godiya" daga haka ta kama hanun Zahrah suka fice daga cikin Shoprite ɗin, bayan sun ɗau ledodin siyayyarsu.

"Saida sukazo bakin mota kafun Husnah ta saki hanun Zahrah,  still fuskarta ɗauke da murmushi tace "Mekika fahimta game da wannan takardan, da kuma biya mana kuɗin sayayya da akayi?"

Cikin ɗaurewar kai Zahrah tace "Ni ban fahimci komai ba, sai ma tsananin mamaki da nake, taya haka zata kasance, anya kuwa ba wata maƙarƙashiyan ake shirin ƙulla mana ba Husnah?"

Dariya sosai Husnah ta kwashe dashi,   domin kuwa maganar Zahrah takai a dara.

"Maƙarƙashiyan soyayya ba,  babu wani aljanu, kawai dai inaga wani ne yaganki kuma ya yaba, shine kawai"  Husnah tafaɗa tana mai danne dariyanta.

"Bangane ba me kike nufi?" Zahrah ta tambaya cike da ruɗu, domin ita kwata kwata ma bata fahimci inda kalaman Husnah suka dosa ba.

"Kada ki damu zaki gane mushiga mota"
Jiki a sanyaye Zahrah tabuɗe murfin motar tashiga, a gidan baya sukai mawa kansu masauƙi ita da Husnah..
Suna shiga driver yayi mawa motar key suka ɗauki hanyar Suleja unguwar su Zahrah.
(yauwa kuyi haƙuri jiya nayi mistake sunan unguwar su Zahrah ba Maraba bane, sunan unguwarsu Zahrah Suleja ne, kainane ya ɗau charge shiyasa)

Yanaganin tafiyarsu yasaki ƙawataccen murmushinsa,  "Haryanzu tananan da halinta na tsoro, yayi imani Zahrah bazata taɓa sanjawa ba"
" komai naki yana burgeni Zahrah, inason komai naki!" Zaid dake cikin motarsa yafaɗi haka cike da shauƙi.

"Nifa gaba ɗaya kaina ya kulle, kimin bayani mana Husnah, me takardan nan take nufi ne?" Zahrah tafaɗi haka cikin zaƙuwa.

"Ki kwantar da hankalinki ƙawata, kawai dai bazai wuce irin mutanen nan masu alkhairi bane suka aikata hakan, wayasani ma ko Dr Sadeeq ne" Husnah tafaɗi hakan tana mai kallon Zahrah.

"Mene? kinanufin wai Doctor ne zaiyi haka? gaskiya banjin cewa shi ne, domin idan da shi ne, dole zai bayyana kansa na gansa,  kodai ke akeso amawa wannan hidiman akayi mistake aka ambaceni" Zahrah tafaɗi haka cikin kokonto. 

Dariya Husnah takuma sawa, haɗe da dafa  kafaɗan Zahrah..

"Wai lafiyanki kuwa Zahrah? kinga yanda kika firgice lokaci ɗaya sai kace wacce ta aikata aikin rashin gaskiya, to ni  miye ma  abun damuwa ne don wani yabiyamana kuɗin sayayya?  kinga bafa mu muka sa sa ba, ko ma waye shi yasanya kansa, kishare kawai ƙawata" Husnah taƙare maganar ta ta bayan ta  ɓare sweet ta jefa acikin bakinta.

"Hmmm" kawai Zahrah ta'iya cewa, haɗe da mai da kanta jikin kujera,  itakam gaba ɗaya kanta ya kulle, taya za'ace bakasan mutum ba, amma kuma ya biyamaka kuɗin siyayyan da kayi, irin haka ne mutum sai yaje ya jefa kansa a matsala.

Tafiya suke amma Zahrah ta kasa cewa komai, sai ma Husnah ce keta ƙoƙarin janta da hira, amma jefi jefi take amsa mata, domin kuwa wannan faɗuwar gaban da takeji har yanzu baidaina ba.

A haka har suka iso ƙofar gidan su Zahrah'n... Har cikin gida Husnah tayimawa Zahrah rakiya, kana ta fito tashiga mota suka tafi.

Zama tayi akan katifarta haɗe da zubawa kayan siyayya da sukayi ido, sam zuciyarta bata kwanta da wanda yabiya musu kuɗin kayan ba,  zuwa yanzu ya kamata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login