Showing 105001 words to 108000 words out of 177624 words
lissafi da kuma hautsina mata ƙwaƙwalwa ba kamar idan tatuna da yanda yasanya harshensa akan kumatunta yanashan hawayenta, yana me kuma yi mata wani irin kallo wanda yakasa ɓacewa daga cikin idanunta,,, batasan me Zaid yakeso a tattare da'ita ba, wataƙila rayuwarta yakeso, wataƙila kuma hauka yakeso yaga tayi, baisan yatakeji idan ta gansa ba, baisan metakeji agame dashi aduk sanda taɗaura idanuwanta akansa ba, sake gyara kwanciyarta tayi, tabbas tana da buƙatar samun wani wanda zata faɗawa gaba ɗaya damuwarta, tana da buƙatar wanda zai kwantar mata da hankali yakuma samamata nutsuwa, tana kuma buƙatar wanda zai fayyace mata abun dake cikin zuciyarta, koda hakan zaisanya tasamu sauƙi da salama,, haka dai Zahrah tayi bacci zuciyarta cike da tarin tambayoyi.....
Zaid ne kwance akan wata haɗɗɗiyar kujera mai kama da gado, wanda take aje cikin wani irin katafaren falo wanda aka ƙawatasa da kayan ƙyale ƙyale dakuma more rayuwa. Murmushine ɗauke akan fuskarsa, yayinda kyawawan idanunsa suke a lumshe, wani irin shauƙi me tsanani yakeji a tattare dashi, a iya ganinta da yayi jiyake tamkar anyaye masa gaba ɗaya damuwarsa ne, idanunsa yasake lumshewa haɗe da sake shaƙan daddaɗan ƙamshin da yakeyi masa yawo acikin hanci, ƙamshin da tun ɗazu yakasa barin hancinsa, "wani irin daddaɗan ƙamshine haka Zahrah'nsa keyi?" ya tambayi kansa,, tabbas zai so ace iyanzu Zahrah na kusa dashi, dakuwa kwana zaiyi manne da'ita yana shaƙan wannan daddaɗan ƙamshin nata, sannu ahankali wani irin muguwar kasala ke dirar masa, yayinda wani irin sha'awarta me tsanani ya kawo masa ziyara,, a hankali yasanya harshensa ya lashi laɓɓansa haɗe da sanya hanu yashafi ƙwantaccen beard ɗin sa wanda koda yaushe yake ƙara ƙawata masa fuskarsa,, a hanakali ya ware manyan idanunsa wanda suka soma sauya launi daga farare zuwa kalan bacci, wanda idan ka kallesu dole zasu sauƙar maka da kasala... Laptop ɗin dake kusa dashi ya ɗauka, haɗe da buɗewa, take hoton kyakkyawar fuskarta ya bayyana akan screen na laptop ɗin,, murmushi yayi haɗi da sanya hanu yashafi kan screen ɗin laptop ɗin..
"Inasonki Zahrah!"
ya faɗi haka cikin wata irin murya me ɗauke da matsanancin shauƙi. Take yaji yana matuƙar sha'awan kallon vedion dayayi mata ɗazu batare da tasani ba, lokacin fitowarta daga gidan Hajiya Shuwa. Wayarsa da vedion ke ciki ya ɗauka haɗe da kunnawa, kallon vedion yakeyi yana murmushi, amma kuma kwata kwata saƙonnin da suke shigowa ta Email ɗinsa sun hanasa sakat.. Kai tsaye fita daga ɓangaren vedion yayi ya kutsa cikin Email ɗin nasa, saƙonnin abokanan business ɗinsa ne, sama sama yakaranta saƙonnin, haryana shirin fita daga cikin Email ɗin sai kuma idanunsa suka sauƙa akan saƙon Jasheer wanda yaturo masa,, hakanan yaji gabansa yaɗan faɗi saboda yasan duk saƙon da zaizo daga Jasheer to akan Zahrah ne,, buɗe saƙon yayi haɗe da ƙurawa hoton da Jasheer yaturo masa idanu.. Wani irin abu ne yaji ya taso yatokare masa maƙoshi, yayinda idanunsa suka kaɗa sukai jajur dasu, take gashin jikinsa suka mimmiƙe, wani irin juyawa yaji kansa nayi masa,, shin dagaske katin ɗaurin auren Zahrah idanuwansa suke gane masa ko kuwa? sake waro manya manyan idanuwan nasa yayi aikuwa ba ƙarya idanun nasa keyi masa ba, sunan Zahrah ne rantaɓe ajikin katin dakuma sunan Dr.Sadeeq,, wani irin ƙara Zaid yayi haɗe da yin cilli da wayartasa, take ta bugi bango takuma faɗowa ƙasa lokaci ɗaya ta tarwatse.. Cikin matsanancin ɓacin rai jikin Zaid yasoma rawa take yaji wani irin matsancin zafi a dai dai saitin zuciyarsa, lokaci ɗaya wani irin tari ya tasomai, take yasoma tari babu ƙaƙƙautawa, sai ga jini na fita ta bakinsa abun mamaki, abun da bai taɓa gani ba arayuwarsa,, da ƙyar yasamu tarin ya tsagaita, amma kuma duk da haka ƙirjinsa bai daina yi masa ƙuna ba, yayinda zuciyarsa keyi masa zafi har cikin cikinsa kuwa yakejin zafin,, a hankali ya jingina bayansa da jikin bango, haɗe da rumtse jajayen idanunsa, numfashi yashiga fitarwa a hankali, daga ni kai kasan yana matuƙar jin ciwo,, cikin yanayi na wahaltuwa haka ya daddafa zuwa cikin ɗakinsa, ƙaramin drower'n dake gefen gadonsa ya jawo haɗe da ciro magungunansa, tsabar ɗacin da yakeji a maƙoshin sa da ƙyar ma ya iya haɗiye magungunan... Kwanciya yayi akan gado haɗi da rumtse idanunsa, baisan ina zai tsoma rayuwarsa ba, baisan tayaya zai fara jure rashin Zahrah akusa dashi ba... Kamar dai yanda Zaid yaga rana haka yaga dare, koda kuwa na minti guda ne baiji wani salama ko sanyi acikin zuciyarsa ba, haka ya share awanni masu yawa cikin ciwo,, sai da yayi sallan Asuba ƙafun wani irin bacci me nauyi ya sace sa batare daya shiryawa hakan ba......
*****
Zahrah kuwa yau da wani irin irin matsanancin ciwon kai ta tashi, gaba ɗaya idanunta sunyi luhu luhu dasu, da gani kai kasan cewa kuka tasha ta ƙoshi.
Yau ya kasance aurenta da Dr.Sadeeq saura kwanaki shida kenan tana ƙirgawa kuma acikin kwanakin nan ne zasu fara gudanar da shirye shiryen da suka tsara,, gaba ɗaya ji takeyi bata marmarin auren, sannan kuma ji takeyi komai yafice mata arai, bawai kuma don batason Dr.Sadeeq ɗin ba, tun shekaran jiya Dr.Sadeeq yakawo mata ɗinkunanta da kuma kayan da zata sanya a kamu da wajen diner, amma kuma ko duba kayan batayi ba balle taga ma ko sunyi mata ko basuyi mata ba, batasan meyake damunta ba, amma tabbas tasan akwai wani baƙon al'amari dayake ta kusanto rayuwarta aduk kwanan duniya. Yau hakanan tatashi taji ko gyaran jikin ma batason zuwa, amma kuma dazaran tace bazata jeba tasan Inna zata sanyata agaba da yawan tambayoyi, don haka ma gwamma kawai ta je ɗin zaifiye mata... Sauri sauri haka ta shirya tafito, saboda tasan cewa yanzu haka Samad na ƙofar gida yana jiranta... ai kuwa tana fitowa taga motar Dr.Sadeeq fake a ƙofar gidan nasu, murmushi kawai tayi haɗe da ƙarasawa wajen motar... "Allah sarki Samad yana da haƙurin jira, da Dr.Sadeeq ne da yanzun ya ƙirata a waya" tafaɗi haka a zuciyarta dai dai sanda taƙaraso gaf da motar, buɗe murfin motar tayi tashiga bakinta ɗauke da sallama, "Kayi haƙuri Samad nabarka kana ta jira" tafaɗi haka tana me ƙoƙarin rufe murfin motar, batare da takalli Inda Samad ɗin ke zaune ba.
Tana rufe murfin motar tadawo da kallonta wajen zaman driver fuskarta ɗauke da murmushi,, a maimakon taga Samad saitaga Dr.Sadeeq, mamakine ya bayyana akan fuskarta alokaci guda, sake ware idanu tayi tana kallonsa, da'alama dai ganinsa yabata mamaki sosai...
Murmushinsa me kyau yayi mata haɗe da kafeta da idanunsa wanda suke sauƙar mata da wani irin yanayi na kasala ajikinta.. Itama murmushin tayi masa haɗe da shagwaɓe fuska....
"Ni dai nayi fushi!" tafaɗi haka a shagwaɓe...
"Tuba nake"
Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana me kama kunnuwansa da duka hannayensa.. alaman ban haƙuri.
"Ni dai naƙi wayon" tafaɗi haka tana me kaɗa idanunta.. Murmushi yayimata haɗe da kamo duka hannayenta yasanya acikin nasa hanun, lumshe idanunsa yayi alokaci guda haɗe da buɗewa
"Nayi kewarki sosai Zahrah na!" yafaɗi haka cikin wata murya me sanyi.
Ɗan guntun murmushi tayi haɗe da soma ƙoƙarin janye hanunta daga cikin nasa hanun, amma kuma bata samu daman hakan ba. "Meyasa jiya kika ƙi ɗaga wayana?" yatambayeta cike da kulawa bayan yagama karantar yanayin da take ciki. Sai alokacin ne ma Zahrah ta tuno da cewa jiya taga missed calls ɗinsa, sanann kuma bata bi bayaba,, ƙaƙalo murmushi tayi haɗe da cewa " Kayi haƙuri nayi bacci ne alokacin"
Kansa ya jinjina badon wai ya gamsu da abun da ta faɗa ba,, ta da motar yayi suka hau kan titi. Saida sukayi nisa a tafiyar kafun yadawo da kallonsa gareta, sosai tayimasa kyau komai nata ya canja, sai dai kuma kallo ɗaya yayimawa fuskarta yafuskanci cewa tayi kuka, dafari yaso tambayarta meke damunta, amma kuma sai kawai ya share,,, sama sama yake janta da hira harsuka iso gidan Hajiya Shuwa... Yana ganin shigewarta cikin gidan ya sauƙe ajiyar zuciya ƴaɗe da kifa kansa akan steering motar, "meke damun Zahrah ne?" ya yiwa kansa tambayar a bayyane, amma sai dai kuma bayida amsar da zai bawa kansa.... A jiyar zuciya yakuma sauƙewa akaro na barkatai, zuciyarsa cike da tunani kala kala yaja motarsa yabar ƙofar gidan....... Ɓangaren Zahrah kuwa kwana biyun nan wasu irin magunguna masu ƙarfin gaske Hajiya Shuwa take bata tanasha, hakan kuwa shike taimakawa wajen hautsina mata tunaninta, wani irin abu takeji acikin jikinta wanda kai tsaye za'a iya ƙiransa da suna sha'awa, ko da yaushe yanzu Zahrah cikin jin feelings take, hattakai ta kawo yanzu alwala ma baya daɗewa ajikinta yake karyewa saboda sosai sperm ke fita ajikinta, duk kuma ɗaya daga cikin aikin magungunan ƙarin ni'iman da Hajiya Shuwa ke bata ne, lallai ita kanta tasan cewa Hajiya Shuwa tayi mata babban haɗi me matuƙar kyau...... (su Doctor za'asha nice😜🙈)
Tunda bacci ya ɗaukeshi da asuba bashi yafarka ba sai ƙarfe 9:30 am, da wani irin zazzafan zazzaɓi yatashi, wanda ya zamana ko ɗaga kansa ba ya'iyawa hatta numfashima da ƙyar yake iya fitarwa. Yana a wannan halin ne yaji anturo ƙofar ɗakin nasa, bai iya ɗago kansa ya dubi ko waye ba amma kuma duk da haka ya gane waye ne yashigo cikin ɗakin... Dasauri Alhj Ma'aruf yaƙaraso garesa...
"Lafiya Zaid meke damunka?" Alhaji Ma'aruf yafaɗi haka yana me kai hanunsa jikin Zaid, da sauri yajanye hanunsa daga jikin Zaid ɗin domin kuwa jiyayi jikin Zaid ɗin yaɗau zafi rau kamar wuta. "Subahanallah, bana ƙira Doctor yanzu" Dad yafaɗi haka yana me ƙoƙarin ciro wayarsa daga cikin aljihu,, bugu biyu Dr.Bilal yaɗauki wayar, cike da damuwa Dad yace yanason ganinsa jikin Zaid ne yatashi. take Dr.Bilal yace gashinan zuwa..
Zama Dad yayi jigum agefen gadon Zaid ɗin, gaba ɗaya yarasa mekeyi masa daɗi, sosai matuƙa cutar Zaid ke damunsa, yana matuƙar ƙaunar Zaid sam bayaso wani abu ya samesa, musamman ma yanzu da Dr.Bilal yashaida masa cewa Zaid ɗin yana ɗauke da ciwon zuciya me tsanani... Mintuna kaɗan Dr.Bilal yaƙaraso gidan, babu wani ɓata lokaci kuwa yashiga yiwa Zaid wasu ƴan gwaje gwaje, drip yaɗaura masa bayan yayi masa wasu allurai guda biyu wanda zasu taimaka wajen kawar da zazzaɓi da kuma ciwon da kansa keyi masa uwa uba kuma su sanyasa bacci, saboda idan yana a cikin hayyacinsa bazai taɓa barin zuciyarsa ta huta ba, yin hakan kuma shike ƙara sawa ciwon yayi tsanani... Bayan sun fito compound ɗin gidan ne Dr.Bilal yagyara tsayuwarsa haɗe da duban Alhaji ma'aruf,, bayani yashiga yimawa Alhaji Ma'aruf ɗin sosai agame da ciwon Zaid ɗin. Bayan sun kammala maganan ne Alhj Ma'aruf yakoma wajen Zaid da tuni wani baccin wahala yasake ɗaukansa......
*****
Rana bata ƙarya, ranar yau takasance laraba kuma yautake kamun Amarya, tun da safe gidan su Zahrah yake acike ƴan uwan Inna sun tattaro ƙwansu da ƙwarƙwatansu sun garzayo, don haka tuni gida yaɗauki hargowa da hayaniyan mutane yayinda amarya kuwa tunsafe take ƙunshe a ɗaki acewarta cikinta ne keyi mata ciwo,, Husnah da Suhaima ne suka taimaka wajen ɗebe mata kewa ta hanyar zama da'ita.....
Ƙarfe uku na yammaci kenan amma tuni gidansu Zahrah ya ɗinke da mutane, ciki kuwa hadda ƴan matan school ɗinsu wanda Husnah ce ta gayyacesu, domin ita dai Zahrah bata da wasu ƙawaye Husnah ce kaɗai ƙawarta... Kowacce ka kalla acikin ƴan matan nan tasha kyau cikin kayan anko ɗinta. Husnah ce tsaye akan Zahrah tana ta faman ɓaɓatu akan cewa Zahrah'n ta tashi su tafi shagon meckup domin tuni Dr.Sadeeq yaturo freinds ɗinsa waƴanda zasu kaisu shagon yin meckup ɗin suna ma jiransu aƙofar gida,, ita dai Zahrah yau jitayi gaba ɗaya bakinta ya mutu sambatajin wani kuzari ajikinta. Kayan da zata sanya da duk wani abun da zatayi amfani dashi, Husnah ta ɗaukar mata haɗe da kama hanunta suka fice daga cikin gidan. Wasu haɗaɗɗun motoci suka shiga kai tsaye aka wuce dasu wani shahararren shagon meckup....
Kwalliya sosai shahararriyar meyin meckup ɗinnan ta tsantsarawa Zahrah akan fuskarta lokaci ɗaya saiga Zahrah ta sauya kamanni asalin kyawunta yasake bayyana tamkar wata balarabiya ita kanta Zahrah saida tayi mamakin ganin kanta, tabbas dabadan tasan ita ɗin ceba, to da sai tace sanja mata fuska akayi, kowa yaga kwalliyanta saiyayi santi saboda tasha kyau iya kyau.. Wani doguwar rigan leshi me kyau da tsada ta sanya ajikinta, take kyakkyawar surar jikinta ya bayyana kansa acikin kayan, sosai ɗinkin yayi kyau yakuma amshi jikinta, zama tayi aka tsantsara mata haɗaɗɗen ɗaurin ɗankwali akanta, yayinda aka nannaɗe mata dogon gashinta atsakiyar kanta, ita dai tsayawa tayi kamar wata statue tana mamakin irin baiwar kyawun da Allah yayi mata, daga riganta har zuwa kan takalminta dakuma ɗan karamin fos ɗin dake rike ahanunta kalarsu yakasance light peach ne, yayinda stones ɗin kayanta suka kasance farare, lokacin da su Husnah sukayi tozali da Zahrah ihu dakuma shewa suka sanya haɗe da tsantsar mamakin irin kyawun da Zahrah tayi, kowa dai yasan Zahrah kyakkyawace amma kuma basuyi tunanin kyawunnata har ya kai hakaba, lallai duk namijin daya samu Zahrah amatsayin mata yayi babban gamdakatar. Take su Husnah suka shiga ɗaukarta hotuna da kuma vedios suna watsawa a instagram dakuma whatsapp, suna cikin buga selfie abokan ango suka ƙaraso don ɗaukar ƙawayen amarya,, duka ƴan matan kowacce da motar da tashiga, yayinda aka bar Zahrah da Husnah sukaɗai saboda Ango yace shi dakansa zaizo yaɗauki amaryarsa... Ƙawaye basu jima da tafiya ba wayar Husnah tasoma ƙara,, murmushi tayi haɗe da kallon Zahrah adai dai lokacin da taɗaga wayar takara akan kunenta, "To ranka shi daɗe gamunan fitowa" abun da Husnah tafaɗa kenan haɗe da miƙewa tsaye hannuwan Zahrah takamo haɗe da miƙar da'ita tsaye..
"Angonki yaƙaraso yace nafito masa dake" murmushi kawai Zahrah tasakar mawa Husnah kana ta sunkuyar da kanta ƙasa.. A hankali Zahrah ke takawa yayinda rigar jikinta kejan ƙasa, babu abun dake tashi ajikinta sai daddaɗan ƙamshin turare,, gaskiya Zahrah tayi kyau sosai ayau ɗin..
Ware idanu Dr.Sadeeq dake zaune acikin motarsa yayi yana me kallon Zahrah, shima yasha ado cikin wata farar gezina me matuƙar kyau da tsada yayi kyau sosai da sosai, kwarjininsa yasake fitowa fili..... Har Husnah ta buɗe murfin motar ta tura Zahrah ciki bai rufe bakinsa ba haka kuma bai ɗauke idanunsa daga kallon da yakeyi wa Zahrah ba, lallai ne godiya ta tabbata ga ALLAH (S.W.A) daya tsara wannan kyakkyawar halitta, kullum kuma koda yaushe yana kallon kyawun Zahrah amma kuma yau saiyake ganin kyawun nata yafi na koyaushe ƙawatuwa.. A hankali ya sauƙe wata irin ajiyar zuciya haɗe da lumshe idanunsa,,, Zahrah kuwa tunda tashiga cikin motar ta sunkuyar da kanta ƙasa tana me wasa da yatsun hanunta,, Motar Habeeb dake bayan ta su Zahrah Husnah tashiga,,, atare motocin suka tashi tafiya sukeyi ahanakali akan titin...
"Zahrah!" Dr.Sadeeq yaƙira sunanta cikin wata irin murya me sanyi dakuma sauƙar da nutsuwa. Kasa amsa masa Zahrah tayi, hakanan taji wani irin nauyinsa ya lulluɓeta.
"Kinyi matuƙar kyau sosai, sai yanzu nasakejin cewa nayi babban sa'a dana sameki, inasonki sosai Zahrah na, ina fata watarana nima kisoni tamkar yanda nake sonki!"
Sai alokacin Zahrah ta ɗago kanta, haɗe da sakar masa ƙawataccen murmushi, jiyayi gaba ɗaya ta kashesa da salon murmushin nata, a hankali ya matso daf da'ita haɗe da kamo hannayenta duka biyu ya riƙesu gam acikin nasa, wani irin soyayyartane yaji yana ƙara shiga jikinsa, jiyakeyi tamkar ya jawota jikinsa ya rungumeta kozai sake samun nutsuwa acikin zuciyarsa.... Harsuka iso katafaren hall ɗin daya cika maƙil da jama'a zuwan amarya da ango kawai ake jira, amma Dr.Sadeeq bai ɗauke idanunsa akan abar ƙaunarsa ba, wani abun daya ƙara rikitar da Zahrah takasa cewa dashi komai shine yanayin yanda yake mata magana da wata irin murya me sanyi... Motarsu na'isowa wajen taron, mc yasoma shela cewa ga ango da amarya sun ƙaraso, take guri yasake ɗaukan shewa yayinda kowa yazura idanun ganin ango da amarya, waƴanda suka zo wajen dan gulma suka sake miƙa wuya musamman ma familyn Dr.Sadeeq wanda anriga da angama gayamusu cewa amaryan ƴar matsiyata ne saboda haka suka baza idanuwan ganin ta don kashewa idanuwansu ƙwarƙwata.... Habeeb ne ya buɗewa Dr.Sadeeq ƙofar motar yafito, yayinda shikuma Dr.Sadeeq da kansa yazagayo ya buɗe mawa Zahrah nata ƙofar,,, cikin nutsuwa ta zuro ƙafafunta waje, kafun daga bisani tafito daga cikin motar, hanunta ɗaya Dr.Sadeeq yakama suka soma taku cike da nutsuwa,, wajene yaɗauki shewa masu murna nayi masu baƙinciki ma sunayi, haka masu ɗaukar amarya da ango hoto da vedio's ma duk sunayi,, gaba ɗaya family'n Dr.Sadeeq ƙamewa sukayi ƙam ganin kyawun amarya ya tsoratasu sosai, saboda basu taɓa tunanin haka zasuga amaryan ba, sunyi tunanin zasu ganta wata almajira da'ita amma kuma sai suka ga saɓanin tunaninsu, lallai ba'abanza ba Dr.Sadeeq ya liƙe akan cewa shi dole sai'ita, takai takuma cancanci ayi mata fiye da haka ma... Har amarya da ango suka ƙarasa mazauninsu mutane basu daina yimusu vedio's ba, haka kuma idanu bai ɗauke daga kan suba.........
*(Bazan'iya cigaba da typing ɗinnan ba, saboda banaso ayi bandani domin nima yau zantaka rawa sosai💃💃💃💃 idan kamu ya kammala zan cigaba da typing😜🤣 Team Zaidu muna tare iya wuya😘, Team Dr.Sadeeq kuna cikin ƙalbina asahun farko ma kuwa🤗)*
*12/January/2020*
*Follow me on Whatsapp and Wattpad*
*Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*Editing is not allowed📵*
*CHAPTER 86 to 87*
Sunkuyar dakai ƙasa Zahrah tayi gaba ɗaya ita kunyar mutanen dake tare a wajen takeyi, tunda take bata taɓa shiga irin wannan taron ba, sai gashi yau akanta ma akeyin taron, ba abun dake damunta kamar yanda idan taɗaga idanunta take ganin idanuwan mutane akanta kowa ita yake kallo da waƴanda suka santa haddama waƴanda basu santa ba,, matso da kansa yayi kusa da'ita haɗe da kawo bakinsa wajen kunnenta "Anan ma kunya zaki nuna?" ƙasa ƙasa yayi maganar. satan kallonsa tayi haɗe da ɗan sakin murmushi amma kuma batace dashi komai ba, haka