Showing 21001 words to 24000 words out of 163158 words

Chapter 8 - KAUNA DA SO COMPLETE Hausa Novel

M SHAKUR   

04 Sep 2025

4720

mahaukaci, ahankali tace  Evercare Hospital anatse yace  me suka mata a hospital ? Kallonsa tayi wai yadauka ita Dr ce yake mata magana haka, da yar mitsilan voice tace  it s my brothers hospital, he s a Doctor, his name is Dr Muhammad Chidi, he was trying to wake her up bata tashi ba before I see cancer card in her bag da drugs nata and went to tell him, he told me good job and he did something she wakes up tace she doesn t want anything, Ya Chidi did not do anything to Mami and she got better yadade yana kallonta tunda tafara magana kaman mai reading wani abu kafin anutse yace  thank you! Sai kawai yajuya tabisa da kallo jin yace mata thank you, motan taga yashiga yayi reverse back sai yawuce yashiga layin da mugun gudu tabi motan da kallo har lokacin gabanta na fadi sannan ta kunna motan jin ya kunnu kawai taja bata damu da damage dayama motar ba ai ta gidansu ce.

Budemai gate akayi ya shiga gidan da gudu wani wawan parking yayi yafito yayi cikin gidan, bude kofan flat nasu yayi, falo ne mai bala in kyau ga gefe daya hospital bed ne dayake a gyare, ga wheel chair ga cart da drugs da abubuwa da dama na hospital ke kai, ga wata nurse dake sanye da uniform tana ganinsa tace  welcome Dr ko kallonta baiyiba direct yawuce wani daki dake nan kasa yabude kofan kai tsaye Mami yagani harta chanza kaya ta kwanta Imam na rufamata bargo duk juyowa sukayi suka kallesa sai yataho wajen gadon muryansa yanuna bacinrai sosai yace  mesa ka barta ta fita Imam? Why didn t you call me? Imam zaiyi magana Mami tace  baruwan Maheer shima baisan nafita ba, ni nahana ma aikatan su kiraka I wanted naje nai lalli kallonta yayi idanunsa sunyi wani iri yace  we could ve called mai lalle har nan gida Mami, what if something happened to you shiru Mami tayi tana kallonsa saitai murmushi takalli Imam tace  Maheer ka gayama yayanka Aliyu I can t escape death, ko da ban fita daga gidan nan ba, nagaji da zama waje daya, I m not happy, da ragowan karfi na akan mene bazan fita ba saidai komi azo amini agida eh, nagaji, ku barni naji dadin rayuwana ko yayane kafin mutuwan tazo duk ita muke jira duk kuhuta dasauri Imam yaduka yace  Mami, Mami why are you talking like this? Cikeda fada Mami tace  why won t I talk like this? Kaima nadawo gidan nan yarinyar data taimakeni baka mata godiya ba sai cimata mutunci kana mata tijara daban daban kake agabana sabida kaga bani da karfin fada dakai sai yanda kukai dani dakai da yayanka, me kuke nufi dani? Ku kyaleni naje nakama haya nayi zamana mana, baku bani kwanciyan hankali, bata farin cikina kuke ba, kulleni kawai kuke adaki kullum Maheer zaiyi magana Mami tace  duk ku tashi kufitan mini daga daki, kufita I don t want to talk to any one acikin ku juyawa ahankali Babban yayi yafita, shima Maheer yatashi yafita Mami tai shiru saitakai hannu ta goge fuskanta, she knows mesa suke all this abubuwan nan but tagaji bataso, ko mutuwa zata risketa tafiso mutuwan ya risketa tana cikin farin ciki da annashuwa, yes tafita tafadi ta suma and sai me? Farin cikin tafita taga jama a taga mutane ta shaki fresh air outweighs sumewan datayi da sauransu, and she also met a beautiful young girl Amrah.

Imam na fitowa yaga yayan nasa yawuce staircase yayi sama, Ya Haidar akwai bakan zuciya, yadan jima tsaye a wajen saiya kalli kofar dakin Mami sai ya kadakai yawuce benen yayi sama direct yayi dakin dake karshe chan lungu a saman, knocking yayi yana tsaye kusan 5secinds sannan daga ciki yace  come in bude kofan yayi yashiga ciki yana tsaye yabama kofan baya yana cire kayan jikinsa anatse Imam yace  can we talk Ya Aliyu ? Labcoat din ya yazare ya ijiye kan gado yace  uhm hmm ma ana yana jinsa, ahankali Imam yace  please kadan rangwanta wasu abubuwan akan Mami, if you look at it since tana stage din da there s really nothing we can do why don t we let her have her way eh Ya Haidar? But right now she feel caged, she feels suffocated, please Yaya let her be kaji, tadinga fita anytime takes& &  wani kallo daya juyo yama Imam yasa yakasa karasa maganan, cikin kakkausan murya yace  do you think tana fita fainting everywhere dataje is good for her? Do you think sabida she has just few more days or weeks or months to live who knows na barta taita yanda takeso tana decreasing quality na life dinta? Do you think i should just give up on her? Do you have any idea the way i spend day and night making research for any miracle that can cure Mami looking for trials here and there ? Lumshe idanunsa yayi kadan trying so hard to control temper nashi sannan yabude su yace  kome Mami takeso i mean komenene she knows me, I will provide it for her ko a bangon duniya ne I can go and bring it to her reach, but tadinga fita I will never let that happen, she was lucky today Imam what if she fainted while driving on a her way? Yayi shiru yace  sabida she s dying I should just let her die? I can t, I can t and this conversation ends here please yana maganan yawuce yashiga bayi, Imam yadade tsaye awajen all maganan da Ya Haidar yayi is true sabida ance zaka mutu doesn t mean abarka kayi acting reckless ka kashe kanka, banda hakaba it bothers Ya Haidar ciwon Mami sama da kowa, ahankali yajuya yafita yabar dakin he will talk to Mami dake fushi anjima when she is calm.

=ث?KAUNA DA SO=ث?



'


EPISODE 1?? 1??
Wanka yayi yafito daure da towel, shiryawa yayi cikin wani simple 3quater ash color da white vneck t-shirt sai uban kamshi yake, yafito sanye da slippers yakaraso falon daidai nurse na fitowa daga dakin takallesa tace  she refuse to take her drugs Dr Imam dake zaune a dinning kallon nurse din yayi jin abinda tace, anatse Haidar yakalli agogon dakin yace  it s almost time you can leave, I m not going anywhere dasauri Nurse din tace  thank you Dr tawuce wajen kujera tadauki wani leda ta warware abayanta tasaka tasaba handbag tafice while shikuma yawuce kitchen, da kansa Imam yataso yabiyosa yace  mezaka dafa mana Dr Yaya Aliyu Haidar ? Wani kallo Haidar yamai baiyi magana ba, Imam yayi dariya yazo ya tsaya kusada shi, kadakai kawai Haidar yayi yabude freezer yana ciro chicken Imam ya karba yawuce wajen tap yana wankewa, yaciro frozen peppers yasa a food processor yayi chopping nasu, cikin 40min yahada chicken soup sannan yayi smoothie na apples da cucumber, yabude wani powder magani na magnesium da Calcium yazuba ciki yasa komi a tray yadauka yafice daga kitchen din, Imam kuma yazuba nasa soup din yafito yawuce yayi zamansa a dinning.

Gently yabude kofan dakin Mami da sallama abakinsa yar karama, Mami na kwance kan gado tana ganinsa tadauke kai, maida kofan yayi yarufe yataho dakin yazo wajen gadon ya ijiye abincin a kan carpet yadawo bakin gadon yazauna yayi shiru yana kallonta kafin ahankali yakama kafafunta yadaura kan cinyansa ya matsa calmly da wannan muryan mai bala in dadi ta lallashin iyaye yace  Hajiya Mami shiru Mami tamai, ahankali cikeda lallashi yace  I am sorry Hajiya Mami, dan Allah kidena fushi dani yayi maganan yayi shiru yana kallonta, yakai kusan minti daya ahaka yana kallonta sai Mami tajuyo takallesa sai kawai ta taso ta zauna kusadashi tace  I felt dizzy na sume and so what? A gida ma yanamin haka naga ko, inaso nai kunshi tanuna hannayenta da akamata kunshi dayayi kyau sosai da kafafu tace  bazan iya fita ba? Aliyu mutuwan nan ko munaso ko bamu so saitazo then why should I restrict my self from living? Ka barni lemme make the few days I have left memorable, sanda ciwon zata kankama ma ko ance naje nan da chan bazan iyaba eh& .. dan shiru tayi sabida yanda taga yana kallonta idanunsa sun kada sunyi jaaa, saikuma taji zuciyanta yamata rauni, ya mugun bata tausayi, danma namiji ne, is not easy kaga mahaifiyarka right in front of you kuma kasan bazata dade a duniya ba, yanda yaga jikinta yayi sanyi tama daina fadan sai yaji komi ya tsaya masa, ataushashe yace  me da me kikeso Hajiya Mami? Yanda kirjinta yamata sanyi na rashin kuzari yasa tama kasa magana, matsa kafanta yayi yayi murmushi yace  tell me kallonsa tayi tai murmushi tace  inaso nadan dinga fita koda bazanyi nisa ba, kaman zuwa su chefane, da sauransu inaso nadinga zuwa gyadamata kai yayi yace  okay zan dinga kaiki dasauri tace  aikin ka fa ? Ahankali yace  my work can wait anytime kike bukatan wani abu Hajiya Mami, yanzu sauko kici abinci abincin ta kalla saita kallesa tace  nagaji da cin irin wayan nan abinci Haidar, kubani dambu, fate, burabusko, farfesu, da abubuwa masu zaki sunake so shiru yayi duk yana kallonta saiya gyadamata kai yace  okay let s finish eating this i will get pen ki lissafa ko me kikeso i will get them tommorow, you haven t eaten anything, come Hajiya Mami yayi maganan yana kamata batai musu ba ta sauko carpet din ta zauna daidai ana bude kofan Imam ne yaci gayu yace  bari naje gida Mami tace  ka gaidamin da Maman Samha murmushi yayi yace  okay makesure kin cinye tasss, idan kinason wani abu call me zan taho miki dashi anjima gyadamai kai tayi tace  banda gudu a mota karban smoothie tayi tanasha, ahankali Haidar yace  what happened today Mami? Dan kallonsa tayi kafin tabasa labarin from beginning to the end tace  nadade banga yarinya mai shigarai kaman itaba, she s very very caring Aliyu baice komi yadinga bata abincin tanaci she ate small yabata magungunan ta tasha na dare dan magrib yayi sannan yakamata yakaita bayi tai alwala yafito yasata a dadduma yabata hijabi lokacin an tada salla a masallaci bayinta yakoma yayi alwala sannan yafito yaje sama yasa jallabiya yana zuba kamshi yafito yawuce mosque.

Saida akai isha i yadawo yashigo gidan, dakin Mami yabude itama mikewanta dagakan sallaya kenan tamasa murmushi tace  bari na watsa ruwa gyadamata kai yayi tabude bayi ahankali ta shiga shikuma yawuce wardrobe nata very comfortable abubuwa suke saya mata, rigan bacci yaciro mata doguwa har kasa pink mai bala in taushi ya ijiye akan gado, skin dinta use to become so flecky so sheerbutter take shafawa ya ijiyemata dawani simple body spray dawasu safuna dawani man zafi saiya wuce yazauna kan wani kujera dake gaban study desk dake dakin yana facing bango, fitowa Mami tayi daure da towel idanunta akansa saita dauke tazo bakin gadon ta zauna tai amfani da karamin towel ta goge jikinta tadauki man ta shafa tadauki rigan tasaka ta zare towel ta ijiye gefenta sannan tazauna tadanyi gyaran murya, juyowa yayi yataso towel din yafara dauka ya maida bayi saiya dawo yaduka agabanta kafanta yadauka yasaka kan cinyarsa ya shafaman da kyau kafin yashafa man zafi yasa mata safa duk Mami na kallonsa, yasake daukan dayan kafan yamata haka saiya gutsuro kadan yazo ya shafa a lips dinta sai kallonsa take Haidar baida magana, baida hayaniya, amman yanada zurfin ciki sosai, banbancinsa da Imam kenan shi yanada magana da yanzu yacika dakin da hayaniya. Maida kayan shafa yayi yadawo ya gyara pillows din ya kwantar da ita yaja bargo ya rufamata yana rage remote na AC while Mami tahada hannu tana yan addu a zama yayi abakin gadon yana kallonta, ahankali Mami takai hannunta takama nasa, kallonta yayi hakan yasa calmly Mami tace  taho jawosa tayi sai kawai tadaura kansa saman cikinta zai tashi dasauri tace  I m fine ba abinda kemin ciwo ka kwanta Aliyu ijiyan zuciya ya sauke ya kwantar da kansa cikin nata, anatse Mami ta shafa kansa tai shiru kaman mai tunani kafin chan tace  you ve dedicated your whole life to me, baka fita da frinds, baka zuwa shakatawa na samari irinka, baka zuwa buga su kwallo ko golf kaman su Imamu, you don t do anything for yourself sai ni, amman natashi natasaka agaba da fitina, inata masifa kaman bana ganin abubuwan dakake tauye kanka akaina ko, I m so inconsiderate zaiyi magana tace  shiii I don t want you to talk shiru yayi saitadan jinkirto ta yanda zataga kansa da kyau akan cikinta shima yana ahaka ya kalleta all she sees is dan yaronta data haifa 35yrs ago, lumshe idanu tayi tabude cikin wani sanyin murya tace  I don t think without you I would have survived all this years Aliyu, seeing how you ve worked so hard everyday for me wants me to live more for you, banso natafi na barka, thank you Aliyu, Allah maka albarka maida idanunsa yayi ya lumshe da sauri he hates when Mami tafara irin maganganun nan, har gwara ma tanamai masifa da fada ma da wannan emotional abubuwan, yayi shiru kawai ahaka, baitaba nunama Mami weakness nasaba bazatasa yakuma fara yauba, seeing him weak will be wat will kill her first kafinma ciwon, dago kansa kawai yayi yana bude idanuwansa yakama hannunta yakai bakinsa yayi kissing yace  enough of the talk, you had a busy day yau, now sleep ijiyan zuciya ta sauke saitai murmushi ganin karfin halinsa da jarumtarsa cikin yar kankanuwan murya tace  gobe zakaga Amrah don t be rude like your brother Maheer kaji ? Gyadamata kai kawai yayi saitai murmushi ta kwanta yasake gyaramata rufa ta lumshe idanu nan da nan bacci ya kwasheta yadade zaune awajen yana kallonta, juyawa tayi cikin bacci hulanta ya salube babu gashi akanta sai wasu yan kwarorin gashi farare Chemo ya cinye gashin tass, yadade yana kallonta ahaka kafin yatashi ya gyaramata hulan yasa mata da kyau, yaja drawer gefen gadon yaciro stethoscope yamakala a kunnenta yakai ya daura a kirjinta yayi shiru sannan ya cire ya ijiye yamata addu a da kansa saiya mike yajuya yafita daga dakin yarufe kofan ahankali without making a sound ya kalli agogon bango is 9:30 tunda har yakai war haka bai dawo ba bazai kwana nan ba yau, kofa yawuce ya rufe dudda sunada ma aikata he don t trust aikinsu, immune system na mamansa is low, baison anything dazai sa tadauki wasu germs ko bacteria hakan yasa kawai yashiga kara gyara falon da dinning dan nanne wajen zamanta da gadonta na mara lafiya, yayi mopping ko ina ya goge ko ina da duk inda hannunta zai iya tabawa da abubuwan dake kashe germs har tv kana ganin yanda yake aiki kasan yanada zafin jini, wuraren 10:30 yagama yatafi sama dakinsa yashiga direct yafada bayi sai wanka.

Yafito daure da towel yana tafiya abubbude zai wuce wajen wardrobe yaji wayansa na kara juyowa yayi yakalli wayan saiya bude wardrobe nasa yadauki kayan dazai saka yadawo yazo yazauna abakin gadon yakalli screen na wayan Dr B aka rubuta a screen din, saida wayan ya katse yayi dialing number yakai kunnensa ringing daya aka daga muryan mace ne daga bangaren cikin more like fada da masifa tace  how many miss calls kaga na maka Haidar? Shiru yayi baice komiba sabida yanda tamai maganan da fada, kaman tagane meyake nufi tadan sassauta murya tace  how many miss calls kaga namaka fisabilillahi? I ve called you more than 30times, you left the hospital without letting me know, inata kiranka tun kafin magrib har zuwa yanzu baka dagawa and ina tambayanka kamin banza wani irin miskilanci ne wannan ?.
=ث?KAUNA DA SO=ث?



'

EPISODE 1?? 2??
Strictly da muryansa dake fita da kyar yace  they was an emergency at home I had to rush back home, I left my phone in my room while I ve been with Mami all this while sosai kirjinta ke tafarfasa when will this old winch die tasami kan Haidar dinta all to her self? Taki mutuwa? Yaro baida sukuni sabida ita, baida lokacin soyayya akan mene, mata kawai tazama annoba arayuwan danta ga yaronta haddden guy ga mahaukacin ilimi gasa dan baiwa, da kyar ta sassauta muryanta tace  how is she?  Asleep yafadi kai tsaye da yar karaman murya, dan sassauta muryanta tayi tace  I ve missed us Haidar, I ve missed you, I can t remember the last time muka zauna and had a good conversation tare tun muna UK, you barely look at me ko a hospital, you are either with patients ko busy making research ko kana gida tareda Mami, in all this do you even know what I m going through? Dan shiru yayi he felt a little bit bad cus yasan how much Habiba ke sonsa, Beeba really loves him, ahankali yace  I thought kin bini siyama Mami drugs a mall the other day dasauri tace  ko kallo na isheka ne, ba dadan mun hadu a hanya bama ai bazan ganka ba shiru yayi feeling bad ahankali yace  I will check my schedules for next week, I will see you murmushi tayi sosai tace  thank you, I love you Dr AH anatse yace  me too he s always serious idan da sabo ta saba da halinsa zatai magana yace 

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login