Showing 135001 words to 138000 words out of 163158 words

Chapter 46 - KAUNA DA SO COMPLETE Hausa Novel

M SHAKUR   

04 Sep 2025

4748

yayi murmushi kawai cus ya lura ba a shiga tsakanin ma aurata yace  In sha Allah we will do this together and we will get through this together gyadamai kai Aliyu yayi sai alokacin yakai shayin bakinsa ya kurbi kadan.
**





Bayan Abba yaga tafiyan Aliyu kirjinsa bugawa yashiga yi sai kawai yawuce mota yasa akaisa gida direct suna shiga ya sauko daga mota yawuce ciki dasauri yabude kofan falo Mama ce kadai zaune tai crossing legs tana kallon tv tana shan fruitss ganin Alhaji yasa tace  Alhaji kadaw& & .  Ina Maheer? Abba yatambaya da zafin rai Mama tace  mekuma yafaru yayi wani abunne? Wani kallo da Abba yamata yasa tace  Allah baka hakuri yana sama dakinsa, nakira maka shi ne ?Wuceta kawai Abba yayi batare daya bata amsaba yayi sama, Mama tabisa da kallon ranta fess daga gani mai apkuwa tariga ta apku, dakin Imam Abba yabude yashiga yana kallon Imam dake kwance kan gadon jikinsa duka ba karfi yamutu sosai yana ganin Abba ya yunkuro ahankali yatashi yazauna yace  ina wuni Abba maida kofan Abba yayi yarufe yataho cikin dakin ya tsaya gaban Imam yana kallonsa anatse yace  Maheer! Ahankali Imam yace  na am Abba cikin kakkausan murya yace  kai ka aikama da mahaifin Amrah letter cewa Aliyu yasaki Amrah? Dasauri Imam ya kalli Abba cus wlh baisan anyi hakaba dan lokacin baya hayyacinsa, girgixama Abba kai yayi yace  a a Abba yadade yana kallonsa saikuma yace  Imam koda wasa na gano dasa hannunka aciki inamai tabbatar maka bazan yafe maka ba saisa nazo dakaina nake maka wannan tambayan cus kafadi gaskiya da bakinka zan yafe maka amman nan gaba nazo nasan gaskiya duk wanda keda hannu ciki badan yafe masa ba Imam na kallon Abba baice komi ba, Abba ya tsaresa da idanu saiya kadakai yafita yawuce dakinsa, Mama data labe dan lungun flowers dake wajen tafito tana murmushi ranta fari kal tawuce ta tafi kitchen ta shiga store dan bawa Beeba update, Beeba na daga wayan Mama tace  kaman fa iyayen yarinyar sun tafi da yarsu ayanda naga fuskan Abba ba lpy cike da farin ciki Beeba tace  kadan suka gani Mama tace  mahaifiyar tasa fa Beeba? Sonake ta sheka? Beeba tace  don t worry I have plans for her itama, bari na kira Farida nabata labari saida safe ta katse wayan dan tana cikin tsananin farin ciki.
**


Daga Mommy har Daddy kallon yanda Ziora ke kuka suke duke akasa, babu wani wanda ya iya cemata tai shiru kota yakuri, jikin Daddy yayi sanyi he feels terrible, like a bad person, someone that s inconsiderate, to worsen everything for him was the fact dayaji cewa Aliyu is even on admission ya sume, sosai yaji badadi, yaji kaman bai kyautaba, Mommy ta lura da the way Daddy was feeling low sai kawai tamike ta taho wajen Ziora takama kafadanta tace  tashi muje daki jikinta zafi, Mommy takalli Daddy tace  call another Dr for her Nwuke, she s running temperature Mommy tarike Ziora tace  bia, bia, taho taho bamata iya tafiya tsabagen tashin hankali, Yaya Aliyu dataji is on admission really shakes her, Mommy tajata, ahankali take takawa Mommy na lurada ita, ahaka sukahau staircase sunkai kusan 5min kafin su shanye staircase din Mommy tawuce da ita dakinta tazaunar da ita kan gado sai kawai tawuce bayi tahada ruwan zafi sosai abayi tafito cikeda fada tace  idan bakimin shiru anan ba saina tattakaki stupid girl, when you were shouting up and down you wanted to marry didn t you know what you should do, or how you should behave a aure? Buckle up cus you are just starting the journey, ba soyaya akeci a aure kullum ba akwai alot of challenges, kimin shiru nace kona bubbugeki hadiye kukan Ziora tayi Mommy takamata tacire mata kaya tai bayi da ita, kai ashe Aliyu lallabata yake, the way Mommy tagasata she thought mutuwa zatayi dan saida ta raina kanta, tagasu har saida taji gabanta kaman ba nataba, Mommy tabarta abayin tafito, lallabawa Ziora tayi tai wankan tsarki da Aliyu yace tadingayi dazu da safe, koda Mommy tadawo tagama towel tabata takamota suka fito Mommy tashafa mata mai tasa mata wata yar gown daya tsaya a knee tace  I will bring food for you now lallabawa tayi tasaka hijab datazo dashi tahau kan dadduma tai la asar magrib da isha i duk cikin 3min sannan tadaga hannu sama tana kuka tace  Ya Allah please make my Yaya Aliyu well, I don t want him to be sick, I love him very, very much wallahi, I know he s a good person I will never fight him again shigowa dakin Mommy tayi da tea da wani miyan yarensu ta ijiye takamota da kanta take bata abincin abaki tanaci da kyar tasha tea saiga Daddy da wani Dr magunguna yabata da allura aka mata sannan aka samu tai bacci Daddy yatafi dakinsa, Mommy tazauna tabuga tagumi tai shiru tana kallon Ziora tunani daban daban aranta especially yanzu dataga yariga yayi deflowering yarinyarta, ijiyan zuciya ta sauke tai shiru, taja bargo tarufa mata tamike takashe wutan dakin tabude kofa tafita daga dakin tawuce nata dakin batare dataje na Daddy ba, tafada bayi tai wanka tafito tai shirin kwanciya ta kwanta takashe wuta tayi tayi bacci yazo bacci yaki zuwa, sai tunani take, tadamu sosai, yarta is married batason auren yakare tundadai anyi sannan har an sadu, tai shiru ta tashi zaune ta kunna bedside lamp tadauki bible nata tafara addu a, she wants her daughter to be very very happy, tunda taga yarta na son yaron and Chidi ya yaba da halin yaron cus Chidi da wuya yaso mutum yasa kawai taji she wants the marriage to work, yes she supports Ziora tadan zauna agida she will use the period to teach her everything about marriage da yanda suke kama zuciyan miji ayaren su, ijiye bible din tayi around 4:30 na asuba tawuce tashiga bayi tayo wanka tai brush tafito wuraren 5, sauka kasa tayi tashiga kitchen girki tashiga yi na gani na fada, wuraren 6 tagama tsaf tai arranging komi a wani hadadden basket mai bala in kyau sauran ta ijiye a dinning tahayo sama tabude kofan dakin, Ziora tashiga ta dubata she s still sleeping bata running temperature.
Mommy tawuce tafita tashiga dakinta tasake wanka saita fito ta shirya cikin wata bubu na adire mai bala in kyau tasaka wig dinta na gashi mai kyau daya tsayamata a kafada, tasa a kunne da sarka da agogo looking very fine ta fesa turare sannan tafito tasauka kasa tawuce tadauki basket din da car key tafito compound tabude motanta tasa basket din abaya tabude gaba tashiga taja motan.
**


Wuraren 5 Aliyu ya farka yaga Chidi na aiki da system, tashi Aliyu yayi yazauna yaga an cire masa drip din yakare and he feels so good and light, Chidi da idanunsa kekan system yace  there s toothpaste and new brush a bathroom ka dauro alwala mutafi mosque ahankali Aliyu yasauka baisan wani treatment Chidi yamai ba but he feels better dudda deep down he s still hurt but ciwon dayake yi yaragu sosai bayin yawuce yashiga yadade tsaye gaban madubin wlh wlh tunanin Amrah yake yana wani irin feeling dinta aransa amman yadaure ya kauda tunanin yayi brush, yayi komi yafito yasami Chidi shima yamike suka fito tare har zuwa mosque sukai nafila kafin suyi jam i, azkar Aliyu ya tsaya yayi sannan suka fito suka shigo hospital din zuwa dakin Mami direct bude kofa Chidi yayi nurse na ciki har lokacin tana ganin Dr Chidi ta tashi tana gaidasu Chidi yashigo yana duba Mami komi lpy lau yakalli Aliyu yay murmushi yace  bari naje nafara rubuta discharge papers gyadamai kai Aliyu yayi yazo yazauna yana kallon Mami dake bacci peacefully Chidi yabude kofa yafita yana turama Obinna message da wayansa kan yasa security yatura masa footage na jiya da yamma lokacin da aka kawomai da delivery, Obinna yamai watsapp da toh.


Wuraren 6 Mami tashiga bude idanunta ahankali Aliyu yana zauna yana kallonta harta karasa bude idanunta tasss tadaura kansa hannunta Aliyu yadauka yarike yasakin mata murmushi mai taushi Mami ta tsaresa da idanu sosai babu wani karfi ajikinta har lokacin amman ahankali tace  meke damunka? Bakada lpy ne? Sabida yarame mata A idanu sosai, murmushi yayi yana gyara muryansa yace  lafiyana kalau Mami idanunki ne, ya jikinki? Meke miki ciwo yanzu ahankali tace  bakomi, ina kabar Amrah da sassafe haka? Dan faduwa gabansa yayi amman saiya daure yace  nabarsu da Chef suna hada miki abincin kari, tashi muje kiyi brush ki chanza kaya yau zamu koma gida an sallamemu yayi maganan yana tashi yadago gadon Mami tai zaman zaune, yana kokarin dukawa dan yakawo mata slippers Mami takama hannunsa dasauri Aliyu ya kalleta Mami ta tsaresa da idanu saita jawosa ahankali tace  zauna nan tanunamai gefenta agadon, ahankali Aliyu ya zauna hannunta Mami takai kan fuskansa tace  you look sick tell me the truth meke damunka ? Kabar da hannunta yayi yace  Mami baki da lafiya I m worried taso muje yakamata yatadota ahankali take tashi, standard wheelchair na dakin yakawo yadaurata akai yakaita bayi yabata brush yana hada ruwan wanka before yabarta tai wankan saida yasa towel ya gasatama kafafu da hannayenta kafin yafito ya barta Mami nadaga zaune tazare gown din tai wanka tai alwala bakaramin dadin jikinta taji ba tace  shigo Aliyu kofa Aliyu yabude yashigo dawani simple gown haka na bacci a hannunsa yada karamin towel yashare mata fuska da hannuwa da kafafu sannan yasamata rigan awuya yajuya baya Mami takarasa sawa sannan yafito da ita tuni harya gyara gadon hijab yabata yasata agadon tana daga zaune tai sallolij dake kanta.


Parking Mommy tayi a asibitin tadaga wayanta takira Chidi ringing daya yadaga yasa wayan a kunnensa anatse tace  come outside hospital naku ina waje dan shiru Chidi yayi sai yace  okay ya katse wayan yafito saida Mommy taga futowansa sannan tabude motan tafito Chidi yataho wajen yana kallonta, bayan motan tabudemai tace  carry that big basket for me basket din yakalla saikuma ya kalleta yace  Mommy kinada patient in this hospital ne wakika zo gani this early morning? Wani kallo Mommy tamai tace  Wai kodai I m at the wrong hospital ne ba anan akai admitting my Inlaw ba ? Zaro idanu Chidi yayi yana kallon Mommy data harareshi tace  I m not that wicked da kukan nan naka bazai tabamin zuciya ba tayi gaba abinta Chidi yadauko basket din yarufe motan dasauri yabiyota yana murmushi and she dress respectfully that kind wajen musulmai zataje, inama Mommy ta musulunta da burinsa yagama cika na duniya, cikin asibitin suka shiga har zuwa dakin da Mami take Chidi yasa hannu yayi knocking kofar tareda bude kofan ahankali daidai Aliyu na zarema Mami hijabi duk suka juyo, wani irin kunyane yakama Aliyu hada ido dayayi da Mommy Ziora tareda Dr Moh yadauke kansa kasa dasauri, Mami tai wani cikakken murmushi na manya ganin Mommy namata murmushi tana tahowa wajen gadon tace  sannu da zuwa sannu da zuwa Mommy tana karasawa tazauna bakin gadon tana kallon Mami sai kawai tai hugging Mami without saying a word tana shafa bayanta Mami tayi kayataccen murmushi Aliyu yadan kallesu Chidi ya ijiye basket din ahankali yana kallonsu yana murmushi, sun dade ahaka Mommy tasaketa cike da girmamawa tace  ya karfin jiki? Mami tace  we thank God, and Alhamdulillah for your brave Excellent son Dr Muhammada he s an angel Mommy na rike da hannunta tace  the lord is your strength, In sha Allah kin rabu dashi har abada, I woke up very early namiki breakfast dasauri Mami tace  serve me please dan I m very hungry anatse Aliyu yazo wajen yadan duka yace  good morning Ma kallonsa Mommy tayi tace  call me Mommy daga yau am I clear ? Gyadamata kai Aliyu yayi, Mommy tace  duk kuzo kuzauna anan including you Chidi, I ve made food for everyone duk saikunci, Ifeanyi sit here tanunama Aliyu kujeran dake gaban gadon dake kusa da ita Aliyu yadauka ahankali, bude kula Mommy tayi lafiyayen rice and stew da pepper soup tayi sai kamshi yake, sai tai shayi normal cus Chidi na so, Mami tafara zubamawa tabata Mami ta karba tace  Allah amfana tasake zubawa takalli Chidi dake zaune akan couch tace  ga naka zuwa yayi ya amsa, saita shiga zuba another one da manya manyan nama daga Mami har Chidi satan kallonta suke tasa spoon saita shiga juyawa ta debo a spoon takalli Aliyu like her son tace  open your mouth lemme feed you Ifeanyi, you look so skinny you don t eat cus you are busy taking care of you mom, oya budemin baki wani kalan kunya Aliyu yaji cus he s not use to this type of abubuwa like this while yare ba ruwansu, sosai Mami tai murmushi tana kallon Mommy dataga ta chanza unlike the last time Chidi was feeling very proud of his Mom tunda har tafara son Aliyu wlh Aliyu zaiga gata, cus Mommy saita so Aliyu sama da yanda takeson Ziora shine first Son Aliyu nata, Mommy tadebo rice din zuwa bakin Aliyu tace  zaka bude baki kona maka dure? Akunyace Aliyu yabude bakinsa Mommy tai murmushi sosai tasamai abincin tana shafa gefen fuskansa cikeda wani irin tausayi dakuma kaunar Aliyu.

EPISODE 9?? 0??



Abincin was so tasty Masha Allah, yayi dadi sosai, anatse Aliyu yakeci yakasa kallon kwayan idanun Mommy data tsaresa da idanu duk kunya yakeji he s not use to this kind of thing ya hadiye, Mommy takara debo abincin tace  good Ifeanyi I want you to be eating like this takai bakinsa ya karba Mami sai murmushi take, bata taba sanin zata farka taga abin farin ciki hakaba, koba komi she s very happy cewa mahaifiyar Amrah tai accepting auren nan dakuma yaronta and she s making effort ta nuna hakan, saitaji tanaso tac1 abincin sosai danta nunama Mommy duk daya suke, taci abincin sosai especially ruwan pepper soup din, kusan rabin abincin Aliyu yaci yadan sauke kai kasa yace  I m okay Mommy, thank you Mommy tace  Inlaw haka yake bayason abinci ? Mami tace  haka nake fama da Aliyu ai yaci naki ma sosai, cikin shida Amrah bansan wazai dingama wani fada ba duk basuson abinci murmushi Mommy tayi saita shiga cin abincin da Aliyu yarage with the same spoon abin ya burge Mami, tass ta cinye tadauki bottle water tabude taba Aliyu tace  sha karba yayi yasha zai ijiye sauran ta karba tasha sannan Chidi yatashi shima yagama yace  toh Masha Allah nakoshi let s start going Dr let s pack up ko Aliyu ya gyadamai kai suka tashi bawani kaya bane daman amma sukai arranging komi Mommy na tayasu arranging suka fita da komi sukakai mota, sannan Dr yakawo wheelchair Mami tace  banni na taka da kafafuna kamata Mommy tayi suka fito tare suka shiga bayan motan, Aliyu yashiga gaba shikuma Chidi yaja motan Mommy shikadai duk suka tafi gida Mommy da Mami ba hira, Mommy na yabawa da yanda Mami kejin English.

Mami tace  Wlh I can t wait to see Amrah na tasan tacika tai fam sabida ban bari an kawota asibiti wajena ba banso taita kukan nan yau zansha rigima murmushi Mommy tayi cikeda hikima tace  a gidan mu ta kwana jiya da yamma tazo sabida Aliyu yasamu ya kwana asibiti tareda ke ijiyan zuciya Aliyu ya sauke jin abinda Mommy tace, dasauri Mami ta kalli Mommy, Mommy tace  malaria ne an mata allura harna fito bata tashina zuwa anjima I m sure zata dawo Dasauri Mami tace  yauwaaa haka nakeso har gida sukakai dayake Aliyu yama nurse messege basaitazo asibiti ba suna zuwa gida Nurse da Chef duk suna nan suka fito suka tarbi Mami da Mommy takama suka shiga ciki while shi da Chidi na kwasan kaya suka wuce ciki.
**

Ahankali Ziora ke bude idanunta kadan cikin bacci tadan lumshe idanu kadan tabudesu tana kallon filon dake gabanta dataga Yaya Aliyu ya daura kansa akanta yana kallonta wani kissing nata, wani yirrrrr jikinta yayi tadan lashe bakinta kadan feeling bakinsa awajen sosai yana tsotsan nata tadaga hannunta tadaura saman boobs dinta dataji nipples din sun tashi sosai tana imagining bakinsa kan nipples dinta daidai Daddy na knocking kofan yana kiran sunanta Amrah tareda kunna wutan daki tarrr tabude idanunta batare data amsa Daddy ba takalli gefenta ba Yaya Aliyu saitama kasa motsi ganin kaman she s still sleeping sai Daddy ya kashe wutan dakin back yajuya yafita daga dakin baiso ya tadata cus yasan batada lpy.
Ziora takara bin gefenta na kallo dasauri cus she knows taga Aliyu awajen wani abu taji ya tsaya mata a wuya gawani kalan wutan son Aliyu datakeji and she also regret saying she don t want the marriage again and she don t like him again abun na cinta, hawaye ta goge tamike daga gadon she feels so good sosai tana takawa ahankali tawuce bayi da kanta tahada ruwan zafi ta shiga ciki tai wanka tadauro alwala tafito tazo tai salla tafara addu a sosai bana wasaba kan Aliyu sannan tawani kwanta akasa yanda taga Ya Chidi yasa tana mugun tsoron zuwa hospital din tasan zai cimata mutunci bana wasaba kuma Yaya Aliyu might not say anything sabida yariga tace batason aurensa sai akwai ta zauna awajen har apptie na abinci bataji kwata kwata.

Around 10 wayan Chidi yahau kara yaciro wayan Obinna ne hakan yasa yadaga wayan Obinna yace  I ve

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login