Showing 39001 words to 42000 words out of 163158 words

Chapter 14 - KAUNA DA SO COMPLETE Hausa Novel

M SHAKUR   

04 Sep 2025

4739

ganin fuskanta sosai sabida gyalen data jawo gaba yasa da sauri ta sauka daga jikin Mami takoma gefenta takai hannunta takama na Mami tarike, tarage muryanta chan kasa kaman mara lafiya tace  good morning Yaya Imam, Good morning Yaya Aliyu tadan turo baki sannan takalli matan tace  good morning saikuma takalli Mami murya kasa kasa kaman munafuka baruwanta da zuciya daya tace  who is she Mami? Mami tace  she s Yaya Habiba, greet her properly dasauri Ziora ta kalleta tace  good morning Yaya Habiba mikewa Aliyu yayi dasauri Ziora ta kallesa, wani mugun kallo yamata batasan sanda tashiga jikin Mami da gudu ba tai lamooo, Mami tabata rai tace  wai me hakane Aliyu, ina dalili? Jan gyalenta Beeba tayi baya dan taga ma wace yarinyar ce haka daga shigowanta attention yakoma kanta ana cikin mahimmin magana, kallo daya tama Ziora tagane yarinyar from mall that day, faduwa gabanta yayi, meya hada yan gidan nan da arniyan kabilan yarinyar nan eh? Car key Aliyu yadauka yayi kofa kawai yafice abinsa, Imam yadan saci kallon Ziora datai lakur gefen Mami yace  Mami nafita jogging Mami tace  adawo lpy yana ficewa Beeba ta sauke gyalenta baya ahankali tamike tadauki jakan super market din tace  Mami gashi bayawa dasauri Mami tace  ahhh nan fa daya ina dalili zaki kashe kudi yara daku eh Habiba Beeba tai murmushi tace  Mami dan Allah ki amsa Mami tace  tom Allah amfana Allah kuma yayi albarka gyadama Mami kai tayi tace  Mami meza a daura miki for lunch or akwai wani abu dazan tayaki yi ? Murmushi Mami tayi Ziora tawani kwanto jikinta tana kallon fuskan Beeba sosai dan ita ta iya kallon mutane tana tuna rashin mutuncin data mata rannan a mall suna tare da Ya Aliyu, Mami tace  wlh babu aikin komi agidan nan, bakinga Chef ba yanzu haka nasan ta daura ma abincin rana, yi kari abinki, idanma kinason wani abu kisa amiki Mami tayi maganan tana kallon Ziora datai lamo ajikinta kaman yar yarinya tace  Amreery anyi breakfast kuwa ? Abincin plate na Beeba ta nuna tace  Mami I want to eat that thing, my step mom use to make it for my Dady, I use to eat it with my Dady at home murmushi Mami tayi tace  muje nasamiki dakaina dasauri tamike tacire takalminta takama hannun Mami tabita suka shiga kitchen Beeba tabita da kallo kanta ya gama kullewa, nurse din Mami itama tana kitchen tunda akai baki ta shiga wajen dan sun soma xama kawaye ma da Chef din Mami.


Bugawa kirjin Beeba yasoma yi, tashiga bin ko ina da kallo a dakin taga drip na Mami dake cikin cart na drugs nata dakenan falo meaning duk randa taji zazzabi su drips dinne za a dauko amakala mata, all she needs is ta matsa wajen and just inject alluran in drip din before anybody gets out, the moment akama Mami fixing the drip sunanta gawa acikin likafani yanda zuciyanta ke bugawa zaka dauka fada ake awajen, ta kalli kitchen sannan tabi falon duka da kallo tana kallon sama babu CCTV camera, mikewa tayi rike da handbag dinta da syringe nata ke ciki tayi wajen cart na magungunan Mami, tai maza ta duka tana zaro syringe na alluran daga jakanta, tadauki drip guda tana waige waige tana juyo hayaniyansu a kitchen sama sama, jikinta rawa kawai yake tahau kiciniyan soka alluran ta saman bakin drip din& ..

EPISODE 2?? 0??




Dawani irin sauri Beeba ta juye daidai ana bude kofan kitchen din, Ziora tafara fitowa rike da plate mai kyau a hannunta dake dauke da waina biyu da miya da nama dayawa, Mami biyeda ita abaya, awani irin rude Beeba tajaye syringe din ta wurga jakanta tana kakkallon drip tana juyawa, Mami ta tsareta da idanu hakama Ziora dudda bawai ta santa bane though ai kaman matan wannan mutumin ne ko, but hakan baisa tai mamakin ganinta wajen magungunan Mami ba, dan murmushi Beeba tayi tajuyo tana kallon Mami kafin ta duka ta maida drip din ta ijiye da kyau ta yanda bazai zuba ba tace  Mami inadan dube duben medication dinki ne
Tadawo ta zauna tana ijiye jakanta a gefenta while Mami tasa hannu tajama Ziora kujera dake rikeda plate tace  maza sit here kici abinci Amrah zama tayi tana ijiye plate din agabanta har lokacin babu mayafi akanta, tadauki spoon zataci dashi Mami tace  ba mun wanke hannu a kitchen ba ci da hannu gutsuran masan tayi dan karami takai baki tanaci takalli Mami dasauri tace  Mami is yummy Mami tace  eh amman banji kinyi Bismilalah kafin kifara cin abincin ba dasauri tace  bismillah abu Beeba taji azuciyanta Mami is just after this arniyan, ga sirikanta tazo amman hankalinta nakan wannan, daukan tray tayi tafara cin nata ahankali, daya Ziora taci taji she s okay zata tashi Mami tace  ina zaki? Murya chan kasa tace  Mami I m okayyyy dan hararanta Mami tayi tace  bani plate dinnan zauna kiga Mami ta karbi plate din tasa wankanken hannunta ta gutsuro masan tasa miyan tace  haaa budemin bakin, yarinya batacin abinci saisa kaman ahureki kifadi, open your mouth bakinta Ziora tabude ahankali Mami tasamata abincin aciki wani dadi taji batasan sanda tai smiling ba saitaji abincin yafi dadi a hannun Mami, Mami takara gutsuro na biyu tace  oya open your mouth bude bakinta tayi daidai ana bude kofan dakin Aliyu ya shigo da sallama ciki ciki Mami na sama Ziora abinci abaki, kallo daya yama wajen yadauke kai dasauri Mami dake ba Ziora abinci abinta tace  kadawo Dr Aliyu? Gyadamata kai yayi yace  eh Beeba tai murmushi sosai tana kallonsa yashigo falon yasami waje yazauna yadaura kafa daya kan daya yana taba wayansa Beeba sai kallonsa take hakanan she s feeling kaman yakosa ta tafi kuma ita bazata bar gidan nan yanzu ba.

Mami tace  good girl saura nama girgizama Mami kai tayi tace  Mami I m okay ai anci nama see my stomach is too full now Mami tace  naji muje, ki wanke hannu you will explain to me why you don t like school kullum gudowa kike ashagwabe ta gyadama Mami kai sukaje kitchen, hannu ta wanke Mami ma ta wanke suka fito Mami ta kalli Beeba dakecin nata masan ga Aliyu zaune a gefe daya yahade fuska tace  bari na shiga ciki nadan kwanta dasauri Beeba tace  toh Mami na, ina nan ai ba yanzu zan tafi ba ta wutsiyan idanu Mami taga Aliyu ya kalleta almaun baison zaman tai murmushi tace  toh ba matsala you can join us kema kika gama gyadama Mami kai tayi Mamita juya ta kalli Ziora tace  let s go kama hannun Mami Ziora tayi suka shiga dakinta.

Zama Mami tayi akan gado Ziora ma dasauri tazauna kan gadon tace  Mami kanta Mami tashafa cikeda so tace  as a Muslim bakisan babu kyau mace na yawo tsiraicinta na nunawa ba? Annabi Muhammad SAW yace ita mace ko ina a jikinta al aura ne illa wajhaha wa kaffaiha fuska da tafukan hannu sune ba al aura ba, I understand you, I know these are your kind of clothes, but riga haka kaman rigan yar tsana is meant for staying indoors bakifita dashi ba, sannan ba mayafi, ga gashinki ana gani, idan na kaiki na siyamiki kaya za a miki fada a gida ko? Gyadama Mami kai tayi ahankali alamun eh tace  yes Mommy will collect them, these are the type of clothes I have, sai Daddy use to buy me abaya but is not the type I see on Hausa girls body a school namu, my own abaya is different, My step Mom use to buy me normal Hausa abayas, atampa and lace but Mommy collect all of them she understands the girl sosai hakan yasa Mami tace  okay what about school? Mesa baki zama a school eh? Kinaso nai fada dake ? Girgixama Mami kai tayi ahankali tace  I don t like the school, I want Daddy to take me to US, I want to school there cikeda hikima Mami tace  to bakisan saikin nunamai zaki natsu kiyi karatu yaga kinada good result anan sannan zai kaiki US dinba, kidinga zuwa school kinji gyadama Mami kai tayi tace  but Mami I m afraid of su Mira, I don t want her to beat me, she almost beat me that day is Yaya Imam that saved me Mami tai shiru tana kallonta nan da nan tashiga ba Mami labarin rannan, from yanayin Ziora kasan batajin magana but irin yaran nanne da rashin jinma bawai iyasa sukayi ba koya sukayi a wajen wasu kuma bata iya fada ba, and yarinyar na tsoron yaran especially Mira, anatse Mami tace  kije makaranta abinki amman ba ruwanki dasu karma ki shiga harkansu duk randa she mistakenly touch you saina aika Imam yacimata mutunci and you will tell your Dad sabida ayi reportikg nata to school authority but karki karajin tsofonta she can t do you anything okay .

=ث?KAUNA DA SO=ث?


'
EPISODE 2?? 1??

Gyadama Mami kai tayi, Mami tace  let s read Qur an then saimuyi magana kan yanda akeyin salla da kyau, anatse kuma cus gaida Allah yana bukatan ka natsu akuma tsanake sake gyadama Mami kai tayi, Mami tadauki Qur ani tabata tace  budemin suran da kike da Malamin ki dasauri Ziora takarba tabude Juma a taba Mami tace  this Surah Mami calmly Mami tace  Masha Allah Suratul Juma a, karanta naji karban Al Qur anin Ziora tayi back to her hand, ta tashi zaune ta gyara zama da sauri, da zuciya daya tafara karatu kuma with all her voice, bawai she s shouting bane or screaming but tasaki duka muryanta and she s so audible exactly yanda take karanta ma Ustaz nata idan yazo gida.
Tunda suka shiga daki Aliyu na zaune inda yake a falon baice kalaba, while Beeba nacin masa abinta kadan kadan just to pin down awajen, tadauki ruwa a glass cup tanasha kaman daga sama duk sukaji muryan Ziora daga dakin Mami, batada wani special kira a at all but her voice is more of English sef, sannan kanajin karatun kasan yar koyoce.
 Auzubilllahi mina shedani rajimmmm tawanija mmmm din yafi akirga, Mami sai kallonta take yanda take karatun her face da kanta duka suna moving like kaman all this yan yaran aji dayan islamiyya dinnan, but she s so damn precious and cute, tace  Bismillahi Rahmani Raheeeeemmmmmm saitakara bude murya and she s so confident tace  Yusabbihu lilaahi maaaaaaaaa tawani ja maaaa din ba iyaka Mami na kallonta, tace  maaaaa fis samaawaati wa maa fil ardil Malikil Quddoosil  Azeezil Hakeemmmmmmmmmmm Beeba dake falo tana shan ruwa dariya ne yakamata da batasan sanda ta kware sosai ba, Aliyu ya kalleta fuskansa a hade.
Ziora tacigaba.  Huwal lazeeeeeeeeeeeeee takara ja kaman ba gobe tana bude hanci cus da gaskiya and with all her will take karatun baiwar Allah, tace  ba asa fimmmmm instead of  ba asa fil tace  ummiynaaaa instead of  ummiyyeena Rasoolam min hum yatloooooooooo takaraja saitawani sauke ijiyan zuciya danta gaji, Beeba ta daura hannu akan bakinta dariya ba kakkautawa tana tare bakinta sabida kar Mami taji, Ziora tace  yatlooooooo  alaihim aayaatihee wa yuzakkeehim wa yu al& & .yullll& .yul& .. takasa fadi sai fama take tanasa yatsanta akan Qur anin tanabi, ahankali Mami tace  yu allimuhumul Kitaaba wal Hikmata wa in kaanoo min qablu lafee dalaalim mubeen dasauri Ziora tace  mubeeeeeen tanabin Mami tana murmushi sosai.

For the first time Aliyu tunda tazo gidan yamata magana ganin kalan dariyan datake tana taushe baki yace  and what s the laugh for? Tana dariya tana pointing dakin Mami tace  wace kalan dakikiyace yarinyar nan Dr? Hakanan Aliyu baisan mesa ba but har ransa yaji kalman dakikiyan yamai badadi ko kadan, ya tsareta da idanu kawai baya kyaftawa, Beeba tace  I mean common little Idris na gidanmu 4yrs old can read Qur ani much more than this girl, yarinya sai kace a jahiliya perio& &   stand up and leave! Aliyu yafadi da kakkausan murya dayasa takallesa da gudu danta kara gasgatar da abinda yace mata, fuskansa ba Rahama yace  I wont say it again, and this should be the first and last time you will talk ill of any guest na Mami zafi zuciyanta yayi tana kallonsa wai Aliyun nan da me yake takama? Kodan sabida yaga Babansa shine Minister Abuja? Batacemai komiba tamike rike da tray tawuce kitchen takai ta ijiye tafito yana zaune awajen fuskansa ba wasa, tadauki gyalenta ta yafa tadauki jakan tarike tawuce tai wajen kofan dakin Mamin tai knocking tareda sallama tace  Assalamu Alaykum Mami Mami dake biyama Ziora karatun Al Qur ani karasa kai ayan tayi har karshe sannan ta dakata ta amsa sallaman tace  Bismillah, shigo Habiba mikewa Ziora tayi tace  Mami I want to water my mouth is dry Mami tace  okay nima kawomin mara sanyi Beeba na shigowa dakin Ziora nabin gefenta tafito taja kofan tana dan tsalle kanta ba komi har lokacin tai hanyar kitchen abinta ta shiga takalli Nurse tace  Anty Nurse and Anty Chef Mami wants water that is not cold, me I want cold one tawani juya idanu that looks funny duk sukahau mata dariya, Chef tace  this Mami friend is so adorable Nurse tace  ashe dai bani kadai nake ganinta haka ba Chef tadauki bottle water mara sanyi tabata, Ziora takarba da mai sanyi ma tajuyo tana fitowa daga kitchen din zata fara tsalle karaf ta hada idanu da Aliyu daya mata wani irin kallo da saida hanjin cikinta yakada tarasa dalili, baice kalaba da hannu yamata pointing gyalenta data bari kan kujeran data zauna itada Mami datazo dazu, gabanta na faduwa dum dum dum ta taho sumsumsum har zuwa wajen kujeran taso hannu tadauka, zata wuce akufule kaman zai maketa yace  cover that ugly hair dan kallonsa tayi adan tsorace, yana kallonta still, wani kalan shakkansa take ganin baida imani, saita gyadamai kai ta ijiye goran ruwan guda biyu akan kujera sannan ta daura gyalen akanta, zata dauki ruwan da hannunsa yamata pointing shoes nata yace  in this house we don t enter with shoes sake gyadamai kai tayi jikinta har rawa rawa yake tajuya wajen canvas nata dake gaban kujeran tai bending takai hannu zata dauka riganta ya zazzago down da mahaukacin sauri Aliyu yadauke kansa, Ziora tamike tajuya tawuce wajen kofa tabude ta ijiye takalmin ta anan entrance na shigowa sannan tadawo zata kara wucewa yanuna jakanta yace  is the bag for me? Dasauri ta kallesa suna hada ido tadauke idanunta dasauri gabanta na fadi wai wannan yaron Mamin baida mutunci ko kadan ga bakar magana, juyawa tayi takai hannu zata dauki jakanta strictly yace  we are not dirty people in this house! Dasauri tajuyo ta kallesa, mugun kallo yamata for the first time yamata hausa yace  mai katon goshi kawai daidai Beeba na fitowa daga dakin maganan karaf a kunnenta dasauri ta kalli Aliyun da kyau, saita kalli Ziora data dauki jakanta ta rataya tazo tana daukan bottle water yarinyar ma looks scared, sannan tasake kallon Aliyu, Aliyu taji just now yayi magana yacema yarinyar nan mai katon goshi kawai? Daman Aliyu na magana haka har yana cracking jokes yana barkwanci, yataba gayamata da dadewa yanason yaga mutum mai goshi, bugawa kirjinta yashiga yi sai kallon Ziora dake tahowa abinta takeyi tabi gefenta tashiga daki ta maida kofan tarufe.

Beeba ta kallesa tace  I m going Dr mikewa yayi baice mata komiba sai yayi gaba tabisa abaya suka fice.
Ziora na shiga dakin taga Mami tajawo wani drawer ga leda a hannunta da abubuwa a ledan, atampa sabuwa Mami taciro tasaka a ledan da turaruka ke ciki tace  tayani kaima Habiba colleague na yayanki this Amrah karba Ziora tayi tanadan dukawa alamun respect yanda yaran yare keyi, tajuyo tafito tabude kofan tafita, bazata iyasa takalminta canvas ba, hakan yasa kawai tazura kafafunta cikin hadadden palm sandal na Hermes brown dake gaban dakin, kafanta yayi yar chukul fara kal a ciki da fararen nails nata gyararru masu kyau cus tanada very cute feet, tajuya tafara tafiya, Aliyu na tsaye wajen motan yana facing Beeba ita Beeba na jingene da motan tana facing nashi ta hango Ziora na zuwa da leda a hannunta niki niki, Aliyu dayake yabama flat din baya bai luraba, kawai jitake ta tsani yarinyar hakan yasa da gangan takai hannunta takama hannun Aliyu tarike gam, yawani kalleta cus why will she hold his hand agidansu Mami tagansu ahaka fa? Yanajin nauyin mahaifiyarsa fa, daidai Ziora na zuwa wajen ta tsaya gefen Aliyu very close to him ita baruwanta, Beeba tana wani kashe murya tace  I will miss you My Liuu .

=ث?KAUNA DA SO=ث?


'
EPISODE 2?? 2??

Hannun dasuka rike Ziora dake tsaye dab da Aliyu ta kalla harda wani kara lekawa taga nawa akafi rikewa kaman munafuka baruwanta, Aliyu ya kalleta da sauri yana fizge hannunsa daga hannun Beeba cikin kakkausan murya yace  Ke! Dasauri Ziora tadago kanta takalleshi, tawani buga kafanta akasa dasuka zazzago gaban takalmin sosai ashagwabe kaman zatai kuka tace  Mami said I should give Yaya Habiba this and you re shouting at me again yana kallonta ba wasa a fuskanta yace  and are you giving her

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login