Showing 81001 words to 84000 words out of 163158 words

Chapter 28 - KAUNA DA SO COMPLETE Hausa Novel

M SHAKUR   

04 Sep 2025

4766

ledan tasamai tasamai miya da namomi da man shanu takawo gabansa magana zaiyi tace  ka cinye tasss sannan tazubamai shayi takawo gabansa ta ijiyemai kafin ita tasama kanta da kumu tazauna tafara ci tadan kalli yanda yakeci ahankali anatse tace  meke damunka Aliyu? Dasauri Aliyu yakalli Mami jin tambayan datamai zaiyi magana akai knocking tareda bude kofa Chef ne Mami tace  ahh oyoyoo Chef shigowa tayi tana murmushi tace  good morning Ma how have you been? Good morning Sir gyadamata kai Aliyu yayi yana mikewa yadauki cup na tea nasa yace  bari naje na kwanta Mami sai chan anjima zamu hospital din yawuce sama abinsa yana shiga dakinsa yarage kayan jikinsa yaja drawer yajefa wayan nasa daya kashe, he just needs good sleep he will be fine yakalli agogo yasan by 10 Abba zaije gidansu yarinyar chan mai rawan kai sai kawai ya kwanta yaja bargo yana lumshe idanu sai bacci.

Mami na zaune kan dadduma a falo tanajan charbi wayanta yahau ringing dake kan center table, hannunta tamika tadauka Baban Aliyu tagani a screen din hakan yasa tadan dakata kafin ta danna takai kunnenta ahankali tace  Assalamu Alaykum shiru Abba yayi saiya lumshe idanunsa yabude su asanyaye yace  congratulations to us Asiya an daura auren yaron mu harmun baro gidan ma muna hanya yanzu haka dasauri Mami tace  Alhamdulillah Alhamdulillah, bantaba tunanin yau za a daura auren ba Abba yace  konima haka amman cewa sukayi su haka akeyi a al adan su wai yanzu yarage su yaran su fadi rannan dasukeso ayi taro, nasan Mahaifinta da dadewa tun yana dan kasuwa anatse Mami tace  Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah Abba yace  inata kiransa number sa akashe Mami tace  yadan kwanta ne kansa namasa ciwo nace yahuta ahankali Abba yace  natura miki video komi ta watsapp shima na tura masa, idan kin bani izini zanso nazo gidan sabida mu zauna muyi discussing ya bikin da tarewanta zai kasance ahankali Mami tace  zanyi magana da Aliyu kome yace zai sanar dakai Abba ya gyadamata kai yace  toh yayi shiru batare daya katseba ahankali Mami tace  tom sai anjima Abba yace  sai arabama makota sweet Mami tai murmushi batace komiba ta katse wayan tashiga watsapp da sauri ta kunna data nan taga messege from Baban Aliyu video ne guda biyar dasauri tashiga downloading tana kwalama Nurse da Chef kira.  Kuzo an daurama Aliyu aure da diyata Amrah Mami was extremely happy suka fito duk atare suka kalli video sanda aka fito da Amrah ta rungume Daddy zokaga dariya da Nurse da Chef keyi Mami tai murmushi she promised zata koya mata komi game da al adun bahaushe dakuma alkunya.

Daki Mami tawuce tashiga tafito da ATM card nata tabama Chef tace  Huwala jeki sayomin sweet dayawa masu kyau da tsada pin dina is 3451 Chef na murmushi tace  angama latest mother Inlaw in town tafita bata wani jimawa tadawo Mami tace su bata plate tadebi sweet dayawa da kanta tawuce tahau bene tana tafiya ahankali har sama dakin Aliyu tabude.


EPISODE 5?? 0??





Akan dadduma Mami Aliyu daya tashi har yayi wanka yana sanye da dark blue shadda datamai kyau sosai dakin sai kamshi yake tashi ga sanyin AC, yana zaune yana tasbihi da yatsu yana shafa kansa, yana ganin Mami yamike Mami kawai taja hannunsa zuwa bakin gadonta tace  zonan ta zaunar dashi tana basa plate na sweet din a hannu tadauki daya tabude tace  budemin bakinka bai motsi da baki ba Mami takama habansa tarike ta turamai sweet abaki tace  Alhamdulillah Babanka yakirani ya daura maka aure da Amrah dasauri Aliyu ya kalli Mami yana dakatawa da lasan sweet na bakinsa dayakeyi Mami na farin ciki sosai tace  an daura muku aure Aliyu yanzu Amrah matarka ce Halak malak dasauri yace  but Mami why? Daga zuwa tambaya ? Dasauri Mami tamai dakuwa tace  mai garinku Aliyu, I m happy da aka daura an daura muku aure ne sabida Allah ya kaddara yau za a daura muku auren ayaune Amrah zata zama matarka ko kana wajen ko baka wajen did u see wat I tell you nagaya maka Amrah matarka ce saida ma tashigo rayuwana, none of us yayi tunanin yau za a daura aurenku kai kana nan kana bacci ni inachan ina abin gabana but an daura maka aure Aliyu so Alhamdulillah Mami tazauna tana kallonsa ganin fuskansa yanuna he s not happy at all tawani hugging nasa ta side tace  kasan menakeso yanzu inaso ayi bikin kutare cikin one week hade fuska yayi yakalli Mami kaman zaiyi kuka yace  Mami I m not yet ready to start living together with that girl dawa zanji please dake ko da ita da kanta ke rawa? Besides za a fara trail naki we are going to hospital today once Dr Moh calls Sosai Mami ke hararan sa tace  eh muje zan mai magana inhar abinda zai dauki sama da sati daya ko biyu ne abari saina gama bikin yarona sai afara trail din, Aliyu I m so happy kayi aure, yanzu ci, sha, sutura, kulawa da komi na Amrah yakoma kanka, ka kare hakk1nda da kyau kar Allah ya hukuntaka lemme even go and call my baby, ka kunna wayanka ka shiga watsapp Abban ka yatura maka video daurin auren da komi anjima kaje ka gaishesa kamasa godiya

Mami tana maganan ta tashi tafita Aliyu yabita da kallo ganin yanda she s so happy harda yar wake takeyi kaman ba Mami ba, wallahi he s not happy at all da auren nan all lisaafjn sa yau akaje tambaya su kara bada rana da zasu koma asa rana maybe one month ko two month, amman first day na zuwa gidan yarinya kawai Anba yaje ya dauro masa yarinya, that girl that is senseless da batasan komiba he s not happy duk ransa yakara bac1 daman gana rannan dayake fama dashi.
**

Mai machine bai dire Imam a ko ina ba sai gidansu sauka yayi ya kwaso iban kudin dake pocket nasa yabasa kawai yashiga gida idanunsa sunyi jazur yayi flat nasu da gudu gudu yabude kofa kaman mahaukaci Mommy na zaune tareda mai zuwa mata gyaran kuma a palour taga Imam yashigo azuciye idanunsa sunyi jazur ko kallonta baiyiba ba sallama yayi stairs da gudu tace  Maheer Maheer, Imam, Imam lafiya ? Tamike tana kallonsa amman harya kai sama mai gyaran kumban ta kalla tace  ina zuwa please jirani ba lafiya bantaba ganin Imam hakaba bene tayi tawuce sama direct zuwa dakin Imam din tabude kofan dakinsa ahankali tanajin sheshekan sama sama ga dakin duhu faduwa gabanta yayi yamaida kofan tarufe ta kunna wuta Imam dake zaune abakin gado yajuyo da idanunsa jazur yace  leave me alone Mama, leave my room Mama da hankalinta yatashi sosai cus kap yaran babansu babu happy child like Imam baya fushi he s always full of life ga fara a ga wasa ga barkwanci seeing him like this ya tsananin tada mata da hankali tazo wajen gadon taja kujera ta zauna tana facing nasa tace  Imam what happened to you? Bayan hannu yasa yana g?e fuskansa bayama magana sai ijiyan zuciya dayakeyi, Mama takama hannunsa ahankali tace  Maheer nine fa, mahaifiyarka Akwai abinda bazaka iya gayamin a duniya ba, mwya faru Maheer, menene my Imam ? Kallon Mama yayi da jajayen idanunsa abun is eating him up wayanda yadauka sune suna sonshi and consider them family betrayed him, saikawai ya sauka daga gadon yazube akasa yana daura kansa saman cinyan Mama hawaye masu zafi suna fitowa Mama tace  Imam talk to me ko menene I m sure baifi karfin Allah ba and I m still alive tell me dago kansa tayi ta goge mai fuska tasss tace  gayamin ahankali yace  Mama nine mutum na farko dana fara haduwa da yarinyar nan sunanta Amrah amman Igbo ce Mama ta tsaresa da idanu tana kallonsa tadai daure karta hanasa magana yace  akwai wata rana muna Golf club tareda Nabeel rannan ne first time Dana hadu da ita, something happened ta Mami ta suma a saloon dasauri Mama tace  wace Mami? Ahankali yace  Maman Aliyu da kyar Mama tai controlling kanta tai shiru Imam yace  tadawo da Mami gida still dani tahadu har mukai magana dayasa Mami tagane nasan yarinyar nan daga wani waje, Mama all this while ko kallo yarinyar nan bata ishi Ya Aliyu ba, ko yarinyar tazo gidan cus itada Mami na shiri sosai dani kadai take hira har naman sauketa a makarantan su, Mama k?ll?m ina gidan nan fa, ko ranan nan bata da koy ninakai Mami asibiti ta duba yarinyar, yau Abba yamin text na shirya zai rakasa wani waje muna zuwa naga gidansu yarinyar ne wai yaje nemawa Aliyu aurenta anama daura auren nabar wajen Mama kuma Aliyu nada budurwarsa likita fa Dr Beeba, nikeson Amrah, I ve been wanting to tell her amman rashin lafiyan nan datayi dakuma match dana buga made me got so busy I even gave her ticket I was planning tazo rannan zan fadamata amman sai bata zo ba Mama do you know wat is paining me? Mama ta girgixamai kai, Imam yace  yanda dagashi har Mami suka boyemin komi wlh wlh bantaba ganin Aliyu yama yarinyar magana ba ma, sannan Mami bata taba gayamin Aliyu na son Amrah ko wani abu ba, danaga Aliyu gidan nan I was asking him Meyazo yi yaki kulani that means dukansu sunsan inason yarinyar shine suka biyemin especially Mami datasha ganin wasana da yarinyar har ina sata kuka, Mama why will they do all this to me bayan everything dana musu? I do everything for Mami, o take care of her, I baby sit her amman nizasuma haka su boyema wat is going on ? Budan bak1n Mama tace  Allah yakara

Dudda harga Allah tasan cewa bazata taba bar1n danta ya auri wata kabila ba indai ba bahaushiya bace but taji dadi sosai, tace  sanda nace cemaka karabu da mutanen nan kajini? Gani kake kishi ne na tsani uwar Aliyu ne kawai amman gashinan sun gwadamaka halinsu, duk zaman dakayi kana musu boyi boyi duk rannan duniya kana gidansu amman suka maka wayau suka aure budurwan ka yarinyar dakkaeso sukai hakan without coughing anything out sAbida karma kasan meke faduwa good for you, kai kasan waye bil adama kuwa yanda Mama ke maganan kaman Imam ya hadiye zuciya yamutu sai goge kwalla yake Mama tace  munafikin miskulun yaga kanason yarinya yabi ta kasa ya aureta mutanen nan makirai ne goge idanunsa Imam yayi yamike kawai abinsa mikewa yayi yana huci yace  Wlh wlh bazan yardaba nina fara sanin Amrah kuma nina fara sonta Mama cikeda son tunzurasa tace  to ya zakayi? Mezakayi aure anyi an gama? Amrah tazama matar Aliyu? An riga an cuceka an aure maka yarinyar dakakeso my dear kwanta kai bacci ka lallashi kanka tommorow is another day ai yanzu ka kiyayesu before Aliyu ya kwace maka har club din ball dinka cikin zafinrai yace  wlh wlh Mama bazan taba yafewa Mami and Aliyu ba and I will make them pay dearly for this thing dasuka min you will see yana maganan yajuya yafice.

EPISODE 5?? 1??





Dakin Barrister tashigo ta tarar da Ziora na tsaye tana kiciniyar kwance daurin lafayan da ta mata na kugu takasa budewa amman harta cire rigan ko bra babu ajikinta ba kunya Barrister tamaida kofa tarufe tace  wai bazaki dena tsirara haka kiyi tumbur ba bakisan you are married ba yanzu? Kwata kwata bata maganan take ba tace  Step Mom I can t open this help me please hannu step Mom tasa ta kwance mata abin tadauki yar half gown nata tabata tana dauke kai tace  ungo nidai sa kaya kije falo Babanki na kiranki dasauri tazura rigan tafito tayo falo da saurinta zaune taga Daddy a falo da Chidi da Obinna duk suka kalleta Daddy yace  zo nan Princess dasauri tawuce wajen Daddy zata zauna kan cinyansa as usual Daddy yace  no you re a married woman now all this things kidena kinji dasauri tace  okay Daddy tazauna gefen Daddy tana kallonsa Daddy yace  I don t want any of you to tell your Mother about what happened dakaina zan sanar da ita anjima da daddare and explain everything to her, no matter wat your mother is your mother and I will want her to bless your marriage Ziora ta gyadamata kai, Daddy yace  when you want to greet your inlaw in Hausa land you don t hug them, you bend and greet them, kinajina? Gyadama Daddy kai tayi tace  yes Daddy Daddy zaiyi magana tace  Daddy me I don t even want the celebration the one we did today is enough for me since I don t have any friends the ones I had kunce baku sonsu, I will pack all my clothes today and you and my brothers will take me to my husband house please kowa kallonta yake Daddy yace  okay but I will have to discuss that with your husband first Ziora tawani washe baki tamike tace  okay lemme go to my room and call my Mami tamike bata jira amsansu ba ta fece da gudu Chidi ya dafe kai Obinna ya kwashe da dariya Daddy yamike kawai yabita, Obinna ya matso kusada Chidi yakawo bakinsa saitin kunnensa yace  if I m that Dr ko, I swear I will show her wat marriage is da kanta zata fara kuka batason auren again duk rawan kan nan zata bari Chidi yamai wani kallo kawai yatashi yace  natafi hospital yawuce yafita yanama Aliyu text  congratulations Brother I will be at the hospital any moment from now


Shigowa Aliyu yayi gidan bayan yaje yayi la asar yakalli Mami data riga ta shirya cikin hijabinta sky blue tasaka lace tayi kyau sosai abinta yace  let s go Mami gaba yayi Mami tabiyosa abaya da Nurse dinta itada Nurse suka shiga baya while Aliyu yashiga gaba yajasu sabida Mami na baya ahankali Aliyu ke tafiya da motan Mami is extremely happy today sai tunanin Ziora take dasauri ta kallo nurse tace  laaaa kiga na mance da wayana agida kuma nasan abu mai wuya ne Amrah na bazata kirani ba Nurse tace  ai zamata kira Aliyu sarai yana jinsu yayi kaman baijiba har sukakai asibitin su Chidi yayi parking suka sauko suka shiga har sama office din Dr Chidi Aliyu yayi knocking Chidi da kansa yafito yazo yace  Mom welcome Ma yayi maganan yana bama Aliyu hannu suka gaisa duk suka shiga ciki suka zazzauna Chidi yabude fridge yabasu ruwa Mami tace  ahh lallai har ruwa ake badawa kowa yayi dariya kafin ma afara magana Mami tace  Muhammad nasan koda Aliyu zaimin rufa rufa kai bazakamin ba saisa nataho da nurse dina sabida takaramin bayani da kyau da kyau cus inada tambayoyi danakeso ka amsamin cutan nan nice mai ita ajiki ba wata ba murmushi Chidi yayi yace  what are your question Mom ? Ahankali Mami tace  ka gayamin gaskiya wannan maganin ko treatment nema zance dazaku daurani akai zai daukeni kwanaki naw? Sati nawa ko wata nawa kafin agama nasami lafiya kona gangara cus Allah ne mai kowa da komi?
Kallonta Aliyu yayi Mami taki kallonsa, Chidi zai kalli Aliyu Mami tace  ni zaka kalla Muhammad ba Aliyu ba trust me I am stronger than him murmushi Muhammad yayi yace  gaskiya Mami I can t for sure say ga kwanakin da treatment din zai dauka, depend on yanda jikinki ya karbi abin depend on immune system naki, zai iya daukan weeks, months, days or even year komi na hannun Allah Mami ta jinjina kai tace  okay tambaya ta tabiyu nafara karban treatment din ya zan dingaji ajikina, nayi trails da dama tun a UK wasu azaban da wahalan danake sha yamafi na ciwo na tell me wat should I expect? Ijiyan zuciya Chidi yasauke yace  akwai zazzabi that s fever, rashin karfi da kuzari, amai ko gudawa, rashin apatite, jiri da sauransu, it can go as far as kizo ki kasa komi ba da kanki saidai adinga miki Mami tai shiru kaman mai lissafi saita kalli Aliyu tace  Aliyu inaso kaje ka sami mahaifin Amrah ayi walimab da za ayi na tarbi diyata and welcome her to my home kafin na fara this treatment na rasa karfin welcoming Amrah ja idanun Aliyu yayi yabude baki zaiyi magana Mami tadagamai hannu alamun yamata shiru takalli Chidi dake kallonta tace  I want to stand on my feet and welcome my daughter home da lafiyata ina cikin hayyacina na tabbatar yes d ana na tare da matarsa kafin na fara treatment din, hakan will guarantee me koda na rasu in the process na treatment din banda regret sabida nasan Aliyu ne nada mata that will look after him, idan kuma na rayu naji sauki zanga jikokina na rainesu dan haka Dr kabani 1week I will come back for my treatment Mami tamike tace  muje nurse Nurse tamike tatie hannun Mami suka fita Aliyu na zaune kawai this is biggest butinsa he took leave for this but Mami is just about aure aure aure saikace yagayamata auren soyayya ne ko son yarinyar yake, Chidi yayi small smile yace  Mothers will always be mothers Aliyu Ijiyan zuciya Aliyu yasauke yayi wani gajeren smile daya tsaya a lips nasa yace  I will love to

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login