Showing 78001 words to 81000 words out of 163158 words

Chapter 27 - KAUNA DA SO COMPLETE Hausa Novel

M SHAKUR   

04 Sep 2025

4770

mata dasauri Beeba ta ijiye wayanta tace  wowww My Haidar thank you so much all this for me tashiga bude ledan tana kallon abubuwan ciki tana murmushi sosai, daidai ana kiran salla, Aliyu yace  I have to go an fara kiran salla, take care of yourself Allah kara sauki gyadamai kai tayi ranta fesss dudda bawai taso yatafi da wuri haka bane tace  toh love you Haidar ahankali yace  me too yana tada mota tasauka tarufomai kofa yayi kwana abinsa yatafi, sosai yake sauri cus yanaso yaje gida yama Mami dinner anguwansu yakai yasauka yashiga masallaci yayi salla yafito yakaraso wajen gidan yayi horn aka budemai yashiga daidai yanajin ringin waya daba tasaba dasauri yakalli gefensa wayan Beeba yagani wow ya akayi tabar wayanta a motansa, bai damu dayama kalli wanda ke kira ba yakarasa yayi parking daidai wayan na sake ringing yakai hannu yadauki wayan yaga Mama ke kira, kin dauka yayi harya katse saida kiran yakara shigowa sannan yadauka yakai kunne yayi shiru, muryan Beeba yaji tace  Alhamdulillah Haidar a motanka nabar wayana ? Ahankali yace  yesss dasauri tace  okay zan ma Abdul kwatance yazo yakarban mini ahankali yace  okay I just got home zanba gateman ya karba wajensa dasauri tace  toh toh, thank u Dr zare wayan yayi daga kunnensa ya katse daidai WhatsApp message na saukowa daga sunan dayaga tai saving da Best Cousin tace  ai wlh naso ta mutu sabida kuyi aurenku ba damuwa mayyar mata, taki mutuwa kaman tana jira a busa kaho yadade yana kallon sakon kawai saiya mika hannu ya ijiye wayan ya yunkura zai sauka saikuma yasake daukan wayan yadanna screen din, tanada password alphanumeric pattern password ne, yadade yana kallon screen din kaman mai tunani kawai saiyayi typing Hydar kawai wayan yabude abin ma saida yasa yabama kansa tsoro yanda yayi guessing sunansa ne a password dinta, kawai saiya danna watsapp dinta ya shiga tanada chats da different mutane ga sunayen maza dayawa but hakanan ba sune matsalan sa ba direct Best Cousin yaje gabansa na bugawa, yawanci voice note ne chats nasu, hannunsa ne ya danna voice note na Best Cousin din yaji dariya takeyi kaman mahaukaciya tace  wlh natayaki murya Beeba da auren nan amman wlh naso itane tasha drip dinnan ta mutu ba inyamura ba, mesa ma baki mata alluran direct a jikinta tana bacci ba ?
Daidainan voice din yakare gaban Aliyu kawai yashiga bugawa saiya danne next voice wanda yake na Beeba tace  ke rufamin asiri ai rannan danaje gidan yana nan, kaninsa na nan shima, sai inyamuran yarinyar na nan itama, kinsan waye Aliyu kuwa he is very smart wlh zai gano I did somthing gabansa faduwa yake none stop cus kwata kwata brain dinsa baitaba kawo masa Beeba ba this thing that happened, wait how did she get that injection ko shi as Dr baida accesss to that lethal abu? How did she gets it? Komawa yayi yana sauraron hiransu na baya baya wanda yawanci cousin din nata tambaya take har yanzu Mami bata mutu ba, sai kuma inda Beeba da kanta take bata labarin Inyamura yarinyar ce kaman fa karbi drip din ba Mami ba, rannan harda kukan bakin ciki sAbida Mami is still alive, rawa jikin Aliyu yashigayi ya ijiye wayan da sauri yana dafe kansa Innalillahi wa Innailaihi raji un Beeba! Like Beeba? Me Mami tamata? Rannan datazo gidansu was the first ever time ita da Mamin sa suka hadu to me Mamin sa ta taba mata datake so ta kashemai mahaifiyar? Innalillahi wa innailaihi Raji un how could human be so cruel no wonder Mami tace batason yarinya zuciyanta bai natsu da ita ba, Mami baiwar Allah jitayi ajikinta Beeba is not a good person, okay so take ta kashe Mami sabida suyi aure da gaggawa runtse idanu yake ayanda yakeji kaman yaganta shima zai iya kasheta cus da ace Mami aka sama abin nan wlh halan kafin sukai asibiti ma Mami tarasu amman bakomi and he will make this promise ko da Beeba ce the last woman on earth bazai taba hada jini da ita ba balle aurenta saidai yakoma ga ubangijin sa ba aure da kyar yafito daga motan yadauki wayan yawuce wajen gateman yabasa da kyar yace  za a zo a karba yajuyo ahankali yadawo ciki yabude kofan flat nasu ya shiga babu kowa a falo kansa sarawa kawai yake, imagine ya dakatar da Chef da Nurse suspecting them not knowing Beeba ce ta aikata abin, and she s the least person dayayi expecting cus bawai tawani San Mamin sa bane, zama yayi akan kujera ransa a mugun bace yake saisa ma baiso Mami tagansa yadafa kansa ya lumshe idanu ko 15min ba ayi ba bacci ya daukesa mai nauyi sosai.

EPISODE 4?? 7??




Fitowa daga daki Mami tayi cus tasan taji alamun an shigo bataga mutum ba Aliyu tagani zaune kan ku??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????jera yayi bacci awahale dasauri tazo wajen tazauna tana kallonsa takai hannu ta taba kansa taji dumi hakan yasa ahankali tace  Aliyuuu bude idanunsa yayi dan baida nauyin bacci sosai ganin Mami sai kawai ya kwanto yadaura kansa kan cinyanta murya chan kasa yace  Mamiiii  na am Aliyu meke damunka? Baice komiba yayi shiru yana lumshe idanu kawai yakoma bacci.
**



Tana kwance adakinta kaman marainiya Daddy yashigo kallonsa Ziora tayi batace komiba, Daddy yayi murmushi yazo bakin gadon yazauna tareda dagota yace  I come with good news but it s between us banson Mommyn ki tasani kallon Daddy kawai Ziora take, Daddy yayi murmushi yace  tommorow in the morning Aliyu father is coming to this house so that we will discuss marriage naku with Aliyu dawani sauri Ziora ta tashi tace  Daddy are you saying the truth? Daddy yace  wlh wani irin mikewa Ziora tayi sai kawai tahau rawa tace  Daddy I m very happy, Daddy that means i am getting married tomorrow ? Daddy yace  I don t know yet Ziora tazo dasauri tazauna kan cinyan Daddy tana shafamai gemu yace  Daddy please I want to marry Yaya Aliyu tommorow Daddy yace  shiiii, stop talking my friend, tommorow is Saturday you know your Mommy use to go to Church both tommorow and next so they will come here when she s in church so just keep your mouth shut, your step Mom will dress you up tommorow so that u will greet your inlaws now sleep dasauri tasauka daga jikinsa tahau gado tahau bacci bawasa ta runtse idanunta tana murmushi sosai tana ganin Aliyu tana numfashi sama sama Daddy yana kallonta there s nothing dayake so aduniyan sama da farin cikin Ziora he watched her har bacci yayi awon gaba da ita.

Washegari
Around 8:00 nasafe Mommy ta shirya tsaf abinta zuwa church sai 2 ko 4 ma zata dawo, while Obinna da Chidi sun tafi airport dauko Only Brother Daddy kaninsa he uwa daya uba daya but shi har yanzu he s a Christian, Ziora wani irin farin ciki take, Daddy yakadata wajen step Mom dinta dan ashiryata.
Kannin Daddy na kama da Daddy sosai sai ga Yayan Barrister Alhaji Sani wanda yazama Abokin Daddy sosai, sai best friend din Daddy Abokin kasuwancin sa shima Igbo ne Amaraka duk suka shirya cikin Igbo attire na gani na fada wanda kana gani kasan an barar da kudi.

Da asuba Abba yama Imam text kan ya shirya zasu fita wajajen 10, Imam yamai reply da toh. Wajajen 10:30 suka iso Imam sai kallon gidan yake baisan inane ba, aka bude musu gate suka shiga compound, Daddy na tsaye sun fito tarbansu, tareda brother sa dasuke kira Igwe, da Amaraka da Alhaji Sani, Chidi da Obinna duk suna compound Daddy din tsaye, Daddy na rike da wannan sandar Odogwu dinnan, Imam sai kallonsu yake cus yaga kamansu sosai da Ziora gabansa kawai na fadi non stop.


Motar convoy ce sai jeep guda uku, budema Abba akayi yasauko yana sanye da Babban riga Imam ma ya sauko Daddy na kallonsa yaganesa cus waye baisan minister Abuja ba, daman Aliyu dan Minister ne? Banda haka sun taba Business da dadewa tun kafin yazama minister Abba yabude baki yace  Chuku! Daddy yace  Alaji dasauri Daddy yawuce while Abba shima na tahowa suna ganin juna suka wani kashe suna dariya irin na manya tawagan Abba duk suka fiffito ana gaidasawa Daddy yace  muje muje suka shiga cikin flat din Barrister da komi yake kal kal yana kamshin turaren wuta, Ziora dake dakin Step Mom nata tana bata atampa tan sakawa tace  Step Mommy my father Inlaw is here ohh today is my wedding day it s happening dariya sosai Barrister tayi tace  today is not your wedding Madam Dasauri Ziora ta make mata kafada tace  Uhm un today is my wedding day nidai Step Mommy tace  abeg banni naje nai serving baki dasauri Ziora tace  I want to go too baki Barisster tarike tace  innalillahi ke waya kiraki, idan ba a kiraki ba you are not allowed to go outside karki fito okay kaman zatai kuka ta gyadamata kai.

EPISODE 4?? 8??







Wadata ko ina akayi da abinci, gaban Imam sai bugawa yake none stop, cus taking a closer look at Chidi da Obinna da Daddy he knows suna gidansu Ziora dan ga kama nan dasukayi, what are they doing here? Wani meeting na election stuff yakawo Abba gidan nan?
Kannin Daddy yamike cikeda mutuminci yace  welcome everyone cikin harshen turenci yace  a al adan mu anything dazai hada iyayen yaro da yarinya waje daya means we are forming alliance nasu that means aurensu zamu hada, zamu bada labarin yaranmu wanda iyaye Uba ke fada so Ogenechuku over to you murmushi Daddy yayi yace  2005 aka haifi Ziora March 27th, I remember lokacin shekara daya dana koma musulmi kennan, I use to say anytime na haifi Baby girl zan bata suna Amrah cus lokacin danaje aikin Hajji a wajajen Rauda naga wata Mother dake gudu tana neman diyarta tana ihu Amrah, Amrah and yarinyar from no where just hugged me so I promise myself idan Allah yabani baby girl Amrah zan samata Daddy yayi shiru kaman yana tunani yace  I have 10 children Amrah is my only girl, anan Abuja aka haifeta anan ta girma bata taba zuwa kauye ba gaskiya, tagama secondry school she just started university tana 100 level accounting, a bangaren Islamiyya tanada izifi biyar akai hadda takeyi ta iya hadis, tauheed da little Arabic, my daughter as per yarinyar data taso cikin maza is stubborn kowa yayi dariya a falon, Daddy yace  but she s very very kind, she s so soft hearted, she s free and she s a very sweet young lady, I know tashiga family naku zataga alot of cultural shock duba da she s Igbo but I hope you will hold her hand and walk her through this new path with love not with bitterness Abba yace  in sha Allah, in sha Allah Imam na kallon kowa jin kaman maganan aure ake amman still bai gane ba brain dinsa kaman baya functioning, Daddy ya kalli Abba yace  who is your son ? Dasauri Imam yakalli Abba deep down hoping yaji labarinsa za a bayar, Abba yayi murmushi cus he loves culture yace  Aliyu shine yarona na farko my first son! Sosai gaban Imam yafadi, Aliyu? Meya hada Aliyu da Ziora? Bashi ke son Ziora ba? Abba yace  shi tun yana dan kankani baida surutu baida hayaniya ba irin wannan ba yanuna Imam dake gefensa, yace  bantaba sanin Aliyu ma can become a Dr ba a irin yanda baida surutu but I guess ciwon mahaifiyarsa motivated him, yayi secondary school nasa anan he finished at 14yrs yatafi university Havard yafara medicine he finished school very early yadaura masters yagama yayi PHD all kafin age of 35yrs he s an Oncologist Abba yayi shiru saikuma yace  he s very calm baida magana da sometimes zaka dauka bakin hali ne but ka fahimce sa zaka gane haka yake, for Aliyu his mother is his life, baya wasa da ita, he s kind too, baida wani mugun hali that I know of, saisa mukazo nemamai auren yarku, muma we hope zaku nunama danmu culture naku with love for things to move smoothly Daddy yace  in sha Allah idan kun shirya I will love muyi auren musulunci yanzu then we let our children fix date for celebrating wedding nasu bakaramin dadi Abba yaji ba yace  sure sure Alhamdulillah, Bismillah muyi yanda zuciyan Imam ke bugawa kasa daurewa yayi yamike yana daga wayansa kaman an kirasa yace  Abba ina zuwa ana kirana Abba yace  bazaka tsaya a daura auren yayanka dakai ba dasauri yace  it s important yanzun nan zan dawo yawuce yafita da sauri har jiri jiri yake gani Chidi yabisa da kallo, imam yayi gate nasu yafita dasauri sai kawai yasa gudu kaman mahaukaci kirjinsa namasa kaman zai kama da wuta, daman ya iya gudu aiko haka yake gudun har zuwa bak1n junction na unguwan yatare machine daya gani yahau baimayi magana ba sai hawaye yanakai bayan hannu yana gogewa he felt betrayed, how can Aliyu da Mami zasu yaudaresa haka after everything dayamusu? Shi Aliyu ke bari yayi babysitting uwarsa harya dawo daga aiki but babu wanda yagaya masa cikinsu zai auri Ziora.



Daura aure akayi tsakanin Aliyu da Amrah akan sadaki naira miliyan biyar Baban Aliyu yabiya cash guards nasa na video ana hamdala ana shafa fathiha, su Chidi da Obinna duk suka shafa, Daddy yace  bari afito maka da yarka Abba yace  kwarai kuwa yakamata

Tashi yayi yawuce ciki yabude kofa tsayawa yayi Daddy yana kallon Ziora da Barrister ta shirya cikin wani sabon lafaya dinta pink tasaka normal black bodyhug aciki Ziora tai wani irin kyau kaman ba itaba tana murmushi sosai tana kallon Daddy, Daddy yace  Barrister are you sure this is my Baby or you change her ? Dasauri Ziora tace  Daddy is me Barrister tai dariya Daddy yaje wajen saiya mata peck a goshi yace  you re now a married woman Dr Aliyu s wife, muje ki gaida your husband s parent dawani sauri Ziora tasaki hannun Daddy zatai gaba Barrister takamata dasauri tace  Amrah keee wannan zumudi haka, bari na lullubeki har kai, banda rawan jiki Barrister ta yafamata mayafin itama ta dauki nata tasaka ita da Daddy suka kama hannun Ziora suka fito da ita duk ana video Abba yamike yana gyara Babban Riga yace  Masha Allah Masha Allah, Amrah wani irin yaye lullubin Ziora tayi daga kanta kawai tayi hugging Abba ba zato ba tsammani tace  yesss, yessss, my new Daddy good morning sauke kai kasa Barrister tayi cikeda kunya shi kansa Daddy saida yaji wani irin kunya.

EPISODE 4?? 9??




Abba saida ya lura da yanda parents na Amrah felt disappointed da abinda tayi hakan yasa as a wise elder mai hikima yadan tapping bayan Ziora yace  My daughter how are you? Fitowa Ziora tayi daga jikinsa tasa hannunta takama hannun Abba dasauri cikin tsananin farin ciki tarike tana murmushi sosai tana kallonsa ganin Baban Yaya Aliyu for the first time tace  I am very fine thank you My new Daddy tana kallon fuskan Abba sosai kaman zata hadiyesa da fararen idanunta ganin yanda Aliyu yayi kama da Abba, Barrister ce tai karfin hali tace  baki gaida sauran iyayenki ba dasauri taleko still bata sakin hannun Abba ba tace  good morning everyone I m Amrah Mrs Aliyu Daddy dai ganin zata iyayin wani abin kunya yasa yace  toh bi Maman ki kutafi daki Ya Chidi jiyake kaman ya kwadeta sabida takaici, sakin hannun Abba Ziora tayi tace  My New Daddy take care of yourself okay, see you later gyadamata kai Abba yayi yace  you too take care Allah miki albarka Amrah tabi step Mom tana kwashe daurin lapayan sama fararen kafafunta suka bayyana dan ji take kaman zata fadi bata saka kalan kayan ba duk ana ganin fararen kafafunta Chidi kawai yakada kai yana cizan lips.
Wajajen 12:30 akai sallama aka gaggaisa suka tafi.
*

Gabaki daya yau Aliyu da zazzabi yatashi idanunsa sundan taso sun kumbura sabida tsananin bacin rai dayake ciki na abinda Beeba tayi, dama he s off today so kawai yama asibitin text he s going for leave sabida zai fara treatment din Mami sannan yama Chef da Nurse message duk sudawo yana tura abin kawai ya kashe wayansa yatashi yafada bayi da ruwan zafi yayi wanka yafito ya shirya yasaka faran jallabiya yasa hula yatafi masallaci kansa ciwo yake, yadade a mosque sai wajajen 7:30 yadawo kamshi dayaji a kitchen yasa yatafi kitchen din dasauri Mami yagani tana girki hakan yasa yayi wajen dasauri yace  Mami why are you cooking barshi na karasa wani kallo Mami tamai tace  lafiyata kalau zan iya wuce kaje falo ka zauna ka jirani naji bazan iyaba zan sanar dakai kazo, wani magani zakasha wannan dakake zazzabi ahankali yace  zan huta yau bazani aiki ba Mami tace  okay to tafi kasa fita yayi saiyaja kujera yazauna gaban island na kitchen din yana kallon Mami tana girki, harta gama tuwon shinkafa tayi da miyan taushe tayi kunu sannan tahadamai shayi dayaji kayan kanshi tace  yau bazaka sha coffee ba yana hanaka samin ishashen bacci, zo tayani daukan flask din mukai dinning tasowa yayi yadauka yakai dinning ya ijiye saida yatayata kwashe komi sannan suka fito tare taja kujera tace  zoka zauna tahowa yayi yazauna tadauki plate ta warware tuwo daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login