Showing 120001 words to 123000 words out of 219361 words

Chapter 41 - AJIYA A DUHU COMPLETE HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

5201

.
Ya faWa cikin daka tsawa. Dan shima abinda Nuratun tayi a asibiti har yanzu haushin bai bar ransa ba. Dakatawa Nuratu tai daga shirin sha?e Huznah. Sai dai cikin wani irin ihu da hargowa ta ce,  Yaya Fawzan wai har wannan tsinanniyar ce zatace tana son Yaya AA. Son shi take amma tazo ta raSu da jikina inata bata shawarar yanda zata sameshi. Ni wannan ?ar iskar zata maida bahuwa. Na rantse da ALLAH yau saina haWa miki jini da majina ta yanda bazaki taSa sake sha'awar yima kowa ?wacen saurayi ba dan ........ ta ?arasa da ashariya mai girman gaske tana sake zaburowa kan Huznah.
? ? ? ? ?? Cikin ?an?anin lokaci rikici ya har?ume a tsakaninsu da hayaniyar ta saka su Mamy fitowa. Hakama Oum sai gata da Abah harda masu aiki duk sun yo waje. Itama Nibras da Saheeba haka. Wani irin jan faratunnan ?arin da Nuratu tayi a hannunta tai a saman fuskar Huznah,tun daga wajen kunnenta har zuwa bakinta. ?ara Huznah ta saki na azaba tana mai dafe fuskarta da duka hannuwan biyu jikinta na rawa. Aiko cikin tashin hankali Mamy da Oum sukai kan Huznah Win, ita kuma Saheeba ta ri?e Nuratu. Mugun ciwo Nuratu taima Huznah , dan yanda kasan tsagar yarbawa irin na farkon ?arnin nan haka suka kasance har sanda huWu na yatsunta. Jini tuni ya ji?e wajen abinka da farar fata jiki kuma babu wahala.
? ? ?? Ai Fawzan baima san ya kwashe fuskar Nuratu da mari ba. Yana ?o?arin sake kai mata wani Abah ya ri?e hannunsa yana mai girgiza masa kai. Kuka Huznah take sosai na azaba, hakama Nuratu kukan marin da Fawzan ya mata take yi. Sai dai bakinta bai mutu ba sai sake jadadadama Huznah take idan bata fita a sabgar AA ba ALLAH sai dai ta kasheta. AA nata ne ita kaWai. Yanda taketa surutai yasa kowa ya fahimci akan AA suke faWan, dan in ka cire Mamy da su Abdul-hakeem sai ita Saheeba babu wanda yasan ala?ar Huznah da zuwa gidan ma.?
? ? ? ?? Dole Abdull da Yaseerah da jikinta duk ke faman rawa suka kama Huznah zuwa mota domin kaita asibiti. Ita kuma Saheeba taja Nuratu sashenta. Nibras da bayanin Nuratu ya sata jin wani irin ?ai?ayin ba?in ciki a zuciya fuuuu ta wuce nasu sashen itama. Sai Mamy da Oum da Abah da Fawzan kawai aka bari. Cikin Sacin rai Fawzan ya ce,  Wannan yarinyar sam bata dace da Ajwaad ba wlhy Abah. A haka kuke son aura masa ita tana abu kamar ?ar daba. Daga zuwan yarinya taji mata wannan mugun ciwon a fuska. Haka dama Wazun a asibiti tayi akan Lilly, tana wani tambayar wai ba itace tasan labarinta ba, uwar mi ta sani to? Mi aka gaya matan akan su Shahidahn .
? ? ? ? Cike da mamaki Abah ya ce,  Wace Lilly da Shahidah? .
? ? ?  Lilly dai daka sani Manaal da Shahidah na Kano .
? Wani irin girgiza zuciyar Mamy tayi, haka Oum ma sai da ta Wan rumtse ido. Yayinda Abah ya furta,  Fawzan kasan mi kake faWa kuwa? Da gaske kake yi? .
? ??  Wlhy Abah da gaske nake yi. Itama an kwantar da ita a asibitin ne shine suka shigo duba Auta .
?? Wani irin lumshe idanu Abah yayi zuciyarsa na masa nauyi a cikin ?irji........
'?









('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

?an NIGER 1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=؞?AJIYA A DUHU....=؞?_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



______________

........A Sangaren Maanal kuwa bayan fitar Shahidah text ta turama RK dan tana son su ?arasa maganar da suka fara. Ko minti biyu ba'a cikaba kuwa da tura sa?on sai ga kiransa ya shigo. Kamar bazata Wauka ba ta dai daure ta Waga Win tare da saka hans free kawai. Sallama tai masa da sassanyar muryarta da a yau rauninta ya sake fita fili. Shima sai ya amsa mata da tashi sassanyar muryar. Tare da faWin,  Gani a compound Win ku .
? ?? Sosai mamaki ya kama Maanal, harta kasa Soyewa sai da ta furta,  Wasa kake amma? .
? ?? Murmushi yayi mai sautin da har taji,  Da gaske nake my queen, dama ina gidan kusan minti goma kenan bana son takura miki ne kawai, harma ina shirin juyawa sai kuma ga sa?onki .
? ? ? Ajiyar zuciya Maanal ta sauke, zuciyarta na sake ?arfafata akan RK Win. Tabbas bata bu?atar yin rayuwar aure da kowa. Hasalima bata da burin yin auren kwata-kwata. Amma tasan iyayenta da ?an uwanta bazasu bari ba. Sai kuma Ajwaad, dole ne ta tabbatar masa da abinda yake ganin bazata iya ba. Zatai auren a cikin zuri'arsa kodan tabbatar masa da wannan Maanal Win ta yanzu tafa banbanta da wadda ya sani a baya. Mi?ewa kawai tayi ta Wan gyara hijjab Winta na salla da har yanzu bata cire ba, sai Wan turare data ?arama jikinta ta fita. Babu kowa a falon dan su Barrah na tare da Abbansu basu dawo gidan ba. Kitchen ta shiga ta Wauka ruwa a tray da glass cup. A karo na farko ta nufi falon ba?i sannan ta fita compound inda RK yake. Iso tai masa zuwa falon ba?in, hakan sai ya sake bashi mamaki sai dai baice komai ba ya bita.
? ? ? ? ? Koda suka shiga ita ta zuba masa ruwa da kanta sannan ta zauna. A karan farko da yaji ya kasa daurewa ya furta,  Gaba Waya sai mamaki kike bani. Gani nake kamar bake ba .
? ? ? Guntun murmushi kawai Maanal tai masa. Sai kuma ta kallesa.  Idan kiWa ya canja itama rawar canjawa take yi ai. Ina son ka san yanzu muna akan gaSar serious ne .
? ? ? ?  Hakane. Nima hakan nafi so mu kasance Win Maanal. Na kuma ji daWi da godema ALLAH daya kawo mu wannan gaSar Win.
? ? ? A hankali ta haWiye ?an kwallar data ciko idanunta.  ?azun mun fara magana sai dai bamu ?arasa ba, shiyya nace kazo yanzu dan in sha ALLAHU kamar yanda na sanar maka gobe zan wuce Kaduna. batare da jiran amsarsa ba ta mi?a masa diary Win data shigo da shi a cikin wata kyakkyawar bag. Amsa yay yana ciro sa daga jakan, sai kuma ya Wan jujjuya shi a cikin hannunsa sannan ya Wago ya kalleta. Itama shi take kallo, dan haka ta janye nata idanun.
? ? ?  Na yarda da kai fiye da yanda kake zato. Badan komai ba sai dan wasu dalilai. Sannan kai Win koba komai jinin Oum ne. Wadda nake kallo uwa nagartacciya bayan mahaifiyata. Kaje da wannan zaka samu dukkan tarihin rayuwata data shuWe a ciki, dan in har akwai abinda na rage ban rubuta ba to zai kasance ?alilan ne, ko kuma baida muhimmanci. Bayan ka gama karantawa zaka iya sake tun-tuSar Oum dan sake samun gamsuwa. Daga nan sai ka yanke dukkan hukuncin daya dace koyaya ne zan amshe shi. Dan ALLAH in har baka gama karanta shi har ?arshe ba kada ka kirani a waya, kada kazo kaduna. daga haka ta mi?e tsaye, shi dai kallonta kawai yace yama rasa abin cewa.
? ? ??  Dare ya farayi sai da safe
A karo na farko ya Wan ja numfashi ya fesar, sai kuma ya jinjina mata nasa kan yana mi?ewar shima. Haka suka fito a tare kamar wasu kurame. Dai-dai nan motar Abdull ke shigowa gidan. Duk tsayawa sukai suna kallon motar har wanda ke ciki suka gama fitowa. Da mamaki RK ya furta,  Abdul-hakeem . Sai kuma ya juya yana kallon Maanal. Itama shi Win ta kalla, tare da faWin,  Ka sanshi ne? .
? ? ? ? ? Kafin ya bata amsa Yaseerah ta fito da Huznah, fuska duk facin bandage musamman Sarinta na dama. Nufarsu RK yayi, dan haka badan taso ba itama tabi bayansa. Duk da Abdull yayi mamakin ganin RK a gidan sai ya danne, sai da suka gaisa RK yake tambayar abinda ke faruwa idonsa akan Huznah. Bayani Abdull yay masa a ta?aice. Kamar RK Win zai yi magana sai kuma ya fasa ya juya yana kallon Maanal.
? ? ??  Inaga ni bara naje, ki musu iso ciki ko? .
?? Kai kawai Maanal ta jinjina masa, sai kuma tai masa ALLAH ya kiyaye hanya tai gaba abinta batare da tace ma su Yaseerah komai ba.. Suma komai basu ce Win ba suka bita kawai, yayinda Abdull yake ta satan kallon Maanal Win. A ransa yana raya aji da nutsuwar yarinyar, gata ?ya?y?yawa da wani skin nata mai Waukar hankali da yay ?aranci ga matan wannan zamanin da suka maida kansu fararen dole da bleaching.....

? ? ? ? Gaba Waya Shahidah kasa cewa komai tai da bayanin Abdull Win. Dan Yaseerah taso su Soye amma Abdull ya kware zance ga mijin Shahidah abinsa, dan shi dai namiji ne babu ruwansa. Godiya sukai musu, suma suka mi?e suna musu sallama dan dare ya fara. Dama ita Maanal bama ta tsaya a falon ba ganin kallon ?urullar da Abdull Win ke mata a kaikaice duk da kuwa hijjab ne a jikinta har ?asa. Ko bayan wucewarsu da Huznah ta shigo Wakin Maanal bata kulata ba, tanata ma haWa ?an abubuwan da zata wuce da su Kaduna ne kawai. Itama Huznah Win bata kulata ba tai kiran mamanta a waya. Basu wani jimaba sukai sallama dan ta sanar mata ne kawai zata dawo Kaduna gobe....

? ?? _______________&

?? A Kaduna kam kamar yanda Daddy ya faWa sunje Kebbi garin Giro asalin tushen su Maanal. Sai dai an samu saSani tsakaninsu da manyan da ya kamata su gana da su. Dan kuwa an tabbatar musu kakarta da babanta da baffanta sunje Kaduna, wani kuma babban Senator ne ya aiko aka Waukesu a mota wai zasuje wajen Asiya daya tabbatar musu yasan a inda take.
? ?? Rasama abin faWa Daddy yay, Dan ya rasa yanda zai fassara zancen musamman akan batun senator da suka ce. Haka dole suka baro garin gwiwa a sage. Basu iso gida ba sai dare, zuwa lokacin kuma kowa yay barci, sai dai hakan bai hanashi zuwa ya sami Ammie a sashensa ba tana jiransa. A kallo Waya da yay mata ya fahimci hankalinta a matu?ar tashe yake kuma.......

___________&

? ? ?? Washe gari Shahidah, Maanal, Huznah da yara suka tashi da shirin wucewa Kaduna. Dan yaran ma babansu yaje school Winsu ya daidaita komai. Jirgin ?asa zasu bi, dan haka Uncle Sadeeq Win da kansa ya kaisu train station bayan sallar zuhur. Basuyi ko mintuna goma ba suka wuce. Koda suka iso Kaduna Amaal ce tazo Waukarsu. Dan ita kaWai tasan da zuwan nasu sai Hajiya Basariyya. Itama saboda Huzna ne ta sani Win.

? ? A dai-dai sashen Ammie Amaal tayi parking motarta. Bata ko gama kashewa ba Huznah tai ficewarta daga motar. Da kallo duk suka bita, sai kuma Amaal ta taSe baki da faWin,  Wawuya kawai . Babu dai wanda yace komai tsakanin Maanal da Shahidah. Sai ma ficewa da sukai daga motar suma. Itama Maanal bata jira su ba tai sashen Ammie da sauri, dan kewarta take sosai, burinta kawai ta ganta a jikin Ammien. Da sallama ta buWe ?ofar, sai kuma ta Wan tsaya turus tana kallon yarinyar dake ?o?arin buWe ?ofar itama alamar zata fito. Yarinyar Maanal ta zubama ido. Dan sam bata santa ba. Itama dai yarinyar kallonta take yi. Sai kuma ta nuna ?ofar dake da takalma kusan ?afa goma tana faWin,  Ki shigo mutanen gidan suna ciki. Muma ba?i ne yau muka zo .
? ? ? ?? Kamar Maanal zatai magana sai kuma ta jinjina kai kawai tayi gaba, a ranta tana maimaita zancen yarinyar da daga gani zatai Wan karen surutu. Sallama ta sake yi bayan yarinyar ta matsa ta bata hanya, batare da jiran amsa ba kawai ta shiga Wauke da handbag nata tana faWin,  Ammie, Hameed, Waleed wai duk kuna in...... .
Turus ta haWiye sauran maganar sakamakon saukar idanunta akan Ammie dake zaune kanta a sunkuye kamar ma tana kuka. Da sauri ta saki bag Win hannunta ta nufeta, a gabanta ta dur?usa tare da ri?o hannunta tana mai le?a fuskarta.  Ammie miya sameki kamar kina kuk....? .
? ?? Nan ma ta kasa ?arasawa ganin fa da gaske kukan Amma keyi. Amma sai Ammie Win ta sakar mata murmushi da sake jim?e hannunta cikin nata tana ?o?arin sharce hawayen da Wayan hannun. Ina tuni Manaal da zuciyarta ta tsarga tai wata irin juyawa tana kallon wanda ke cikin falon. Nene ta fara kalla. Sai Daddy, sai wani dattijo daya sata Wan sakin baki, tana kai dubanta ga wanda ke a gefensa ta mi?e zambar, jikinta har wani tsuma yake ta nuna tsohuwar dake a gefen mutumin da ta zuba mata idanu. Sai dai kuma ta kasa ma magana lips Winta ne kawai ke Wan karkarwa. A hankali Ammie ta ri?o hannun nata cikin tsawatarwa ta ce,  Manaal minene haka kike yi. Ki zauna ki gaishe su .
? ? ??  Ammie never!! .
? Ta faWa wani irin kuka dake zuwa maka batare daka shirya ba na kufce mata. Hannunta dake cikin na Ammie ta warce ganin mutumin ya yun?ura ya mi?e da alama wajenta zai nufo. Tuni tai ?ofar dake cikin falon da gudu abinta tana sakin wani irin kuka mai ban tausayi da taSa zuciya. Duk kallo suka bita da shi. Yayinda mutumin ya furzar da zazzafar iskar bakinsa ma?oshinsa na wani irin kaikawo a wuyansa da sauri-sauri alamar shiga tsananin damuwa. Tsohuwar nan ya kalla, itama kallonsa take cike da damuwa. Kanta ta Wan girgiza masa. Sai ya sake furzar da huci mai kauri yana komawa ya zauna a inda ya tashi saboda maganar da tsohon nan yay masa.
? ? ?? Nene ce ta katse shirun nasu da faWin,  Kuyi ha?uri mu bata lokaci zata huce. Kunga ana saka ran sai ma gobe in ALLAH ya kaimu zata iya tazo gata ma tazo yau babu zat....... Sauran maganar ta ma?ale sakamakon shigowar Shahidah da Amaal dake dariya Barrah da Haneeff biye da su... Sororo Amaal da Shahidah sukai suma cikin wani yanayi, sai Shahidah ce tai ?arfin halin juyawa ta Wan kalla Ammie. Ganin kan Ammie a gefe ita bama kallon ta inda suke take ba ya sakata maida kallonta ga Amal da itama ta Wago. Sai kuma duk suka maida kan suka du?ar ?asa fuskokinsu na sake bayyanar da fushinsu. Nene ce tai ?arfin halin musu sannu da zuwa. Sai kuma ta nuna musu wajen zama na kujerun dake kusa da su.
? ?? Wani irin tsuma jikin Babu dake tsaye kamar ma wanda ya daskare yake, gashi ya zubama Amal da Shahidah idanu kawai...
? ? ?  Shahidah bakuga ba?i bane? .
? Nene ta faWa cikin son katse musu yanayin. Kallonta duk sukayi, da ido tai musu nuni da mahaifin nasu. Wani irin taunar lips Amal tayi, sai kuma tai yun?urin barin wajen tana hawaye. Ganin haka yasa itama Shahidah yun?urawa zata bar wajen da sassarfa, amma sai carab Babu ya ri?o hannunta. Cak ta tsaya hawayen da take ri?ewa na rige-rigen zubowa.
? ??  Shahidah .
? ? Ya kirata cikin tsananin taushin murya da sanyi. Hawayenta ta share tare da juyowa cikin dakiya ta kallesa.?Hannun nata ya saki, dan duk da ba kallon raini ta masa ba ko wula?anci har tsakkiyar ransa yaji nauyi da tasirin kallon. Batace masa komai ba itama tabar wajen tabi ?ar uwarta data shige Wakin Ammie. Duk abinda ke faruwa a idon kowa ne harda Daddy dake a falon, hatta Ammie datai uwar watsi da su tana kallonsu ne ta gefe ido......

? ? Tsohon nan ne yayi murmushi, da faWin,  Masha ALLAHU girman Wan mutum ba wuya. Shekara bakwai da wasu watanni kawai da bamu gansu ba sai duk suka canja mana kamar ba su ba .
? ?? Murmushi Nene ta sake yi mai faWi,  A sosai su Maanal duk sun canja musamman ma Maanal Win. Dan wannan gaba Waya ba waccan Maanal Win da kowa ya sani bace ba. Sai dai muyi fatan kuma yanzu ALLAH ya kawo miji na gari .
? ?? A tare suka amsa da Amin. A hankali Ammie ta mi?e tana faWin tana zuwa. Babu wanda ya dakatar da ita ta nufi Wakin da Maanal Win ta shiga, dan tafi tsoron yanayinta fiye da na Amaal da Shahidah. Gashi taga su Wakinta suka shiga, ita kuma Maanal nasu ta shiga.....

? ??? Fitowar ta daga bayi dai-dai da shigowar Ammie Wakin. Juyawa tai da sauri zata koma cikin bayin Ammie ta dakatar da ita.
? ? ?  Maanal! .
? Cak ta tsaya sai dai bata juyo ba. Sai ma hawaye dake rige-rigen zubowa daga idanunta wanda dama su takeyi tunda ta shiga wankan. Cikin Wacin murya da fitar sautin kuka ta ce,  Ammie waya kawosu garemu? Mi sukazo yi mana? Mi suke bu?ata kuma yanzu a garemu. Ko anan Win ma sun zo su koremu ne? Sun zo su sake tozartamu a idanun mutanen arzi?inmu na nan ne suma? Ko sunzo su sake shegantamu su aibanta ki..... kuka yaci ?arfinta ta kasa cigaba da maganar. Hannu Ammie takai ta share hawayen da suka wanke mata fuska itama. Tare da matsowa kusa da ita, hannunta ta ri?o tare da juyo da ita suna fuskantar juna...........
'?







('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

?an NIGER 1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=؞?AJIYA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login