Showing 60001 words to 63000 words out of 219361 words

Chapter 21 - AJIYA A DUHU COMPLETE HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

5145

dan har ?arfe Wayan rana. Jin ana kiran sallar zuhur daga masallacin cikin companyn ya sata sauke ajiyar zuciya da ajiye kayan aikin nata ta mi?ar da hannunta da ya Wan sage da ambaton sunan ALLAH.
? ? ? Mi?ewa tai zuwa window Win office Win ta le?a batare data ma kowa magana ba, dan daga wajen ana hango masallacin. Hango ma'aikata tayi nata fita zuwa ?atuwar harabar companyn. Ganin mazansu da matansu ne yasa ta fahimci masallacin harda mata kenan. Dan wasu ma na ?o?arin shigane yayinda wasu suka kasance rukuni-rukini suna hirarsu. Sai wasu dake alwala ta can ?arshen katangar inda aka tanada domin hakan. Huci taWan furzar daga bakinta tare da barin wajen, dai-dai suma su Yaqub na mi?ewa. Sauran fita sukai gulma fal bakinsu, yayinda shi kuma Yaqub yazo inda take.
Shine ya sanar mata tazo suje salla. Kanta kawai ta jinjina masa ta baro wajen ALLAH ya sota ta taho da hijjab kasancewar yau ma shigar Abaya ce a jikinta ?irar Dubai ruwan ?asa. Hijjab Win ta buWe ta saka bayan ta zame hularta da Wan kwalin abayar data naWo a kanta ta ajiye saboda hijjabin ya rufe mata gashinta sosai. Hankalinta kwance kuma kanta tsaye ta fito a office Win daga ita sai wayarta kawai a hannu. Kusan duk an fice ma, dan wajen yayi tsitt, dan haka a gaggauce ta nufi elevator jin za'a tada sallar kasancewar su suna a 4th floor ne. Bata gama dai-daita tsaiwarta ba kawai taji shigowar mutum babu ko sallama. Dan haka ta Wago manyan idanunta domin ganin wane sallamemmen ne haka........
'?


('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

?an NIGER 1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
=?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=؞?AJIYA A DUHU....=؞?_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



.......Saurin janye idanun nata tai ?irjinta na wani masifar dokawa. Sai dai ta wani dake a zahiri yayinda fuskarta ke sake komawa ciWin-ciWin fiye da yanda tashi take. Boss ne da kansa ba wani ba. Wato AA Darma, da alama shima ya makara fita sallar ne, dan illahirin fuskarsa da hannayensa da ?afarsa dake sanye da slippers daya saka dan ba takalman da yazo dasu a ?afarsa bane cover shoes sai nason ruwa suke yi. Elevator na tsayawa itace tai saurin fara ficewa dan harga ALLAH jinta take kamar an matse a cikin rami tsabar yanda ya cika ko'ina da kwarjininsa. Da kallo ya Wan bita, sai kuma miya tuna oho yay saurin janye idanunsa shima yana fita daga elevator Win.
? ? ? ? Dukansu basu samu raka'ar farko ba. Koda aka idar da sallar mafi yawan ma'aikatan sun wuce kitchen ne kai tsaye, dan ana musu abincin rana a wajen harma dana safe. A manyan dai ba kowa ne ke nufar kitchen Win ba sai wanda yaso hakan kasancewar suna da damar sakawa a kawo musu har office. Manaal ma daba gama sanin tsarin tai ba duk da an bata komai a rubuce tun a ranar interview karantawa ne batai ba office ta koma. Hankalinta a rarrabe sai dai tana iya ?o?arin ta na ganin ta saita kanta ta buWe lunch box Winta ta fidda abincinta ta hau ci tana cigaba da sarrafa computer Winta domin maida aikin zanen da tayi a ciki. A haka a shiririce ta gama shigar da komai kafin ta naWesa a flash drive ta ajiye. Koda an bu?acesa a wajen meeting da shi zatai amfani. Knocking ?ofar akayi, batare da ta canja daga yanda take ba ta bada iznin shigowa dan ita kaWaice har yanzu su Yaqub babu wanda ya dawo. Wata budurwa ce da bazasu wuce sa'anni ba. Sanye take da skirt da riga na atamfa sai Wan mayafi data yana. Cikin girmamawa ta gaishe da Maanal Win. Amsa mata tai da kulawa. Hakan sai ya saka yarinyar farin ciki dan yanzu ake gulmar Maanal Win a ?asa cewar dagani zatayi girman kai, sai kuma ita tazo taga ba hakan ba yanzu.
? ? ?  Sunana Mabaruka Rabi'u. Ina Waya daga cikin Sales and Marketing Department. HOD ne yace a sanar miki ana bu?atarki a ?asa idan babu damuwa .
? ?? Cikin Wan sakewar fuska da ba murmushi take ba Maanal ta ce,  Okay sister Mabaruka ba damuwa gani nan tafe .
? ?? Murmushi Maburaka ta mata tare da sake Wan rissinawar girmamawa ta furta,  Na barki lafiya . Daga haka ta fice a office Win. Ajiyar numfashi Maanal ta Wan sauke, sai kuma ta shiga tattara tarkacen kayan da taci abinci ta maidasu a lunch box Win. Ruwa tasha ta Wan gyara fuskarta sannan ta mi?e ta fice a nutsenta daga ita sai wayarta a hannu. A First floor ta samu kusan dukkan ?ananun ma'aikatan harda waWanda ba nan Winne mazauninsu ba. Sai dai da'alama duk an tattarasu anan Winne dan har su Yaqub ma suna a wajen ashe. Duk da cika mata idon da sukai haka ta dake ta gaishe da HOD dake ta faman sakar mata murmushi. Yana Waya daga cikin wanda sukai mata interview. Amsa mata yay da kulawa, kafin ya juya ga ma'aikatan yay sallama. Duk amsawar sukayi duk da kuwa ba dukane musulmai ba a wajen. ?an juyowa yay tare da nuna musu Maanal cikin harshen turanci ta ce.  Wannan itace sabuwar _Watch Designer_ Win Mawaad Company da aka sake ?aro mana in sha ALLAHU, zatai muku introducing kanta .
? ? ? Tafi suka shiga yi gaba Wayansu. Hakan yasa Maanal Wan sakin murmushi tana binsu da kallo, sai da suka lafa sannan ta gyara tsaiwarta cike da nitsuwa ta furta, Sunana Maanal Habeeb Giro. Junior Watch Designer kamar yanda aikina HOD ya faWa. Ina fatan zan samu haWin kai da yarda daga gareku baki Waya .
? ??  In sha ALLAHU!! .
Suka faWa cikin haWa baki. Murmushi ta sakar musu a karo na biyu mai matu?ar taushi. Sai kuma ta haWe hannayenta waje guda ta sake furta,  Ina mika godiya a gareku da fatan alkairi baki Waya. ALLAH ya bamu ?warin gwiwar sauke hakkin dake kayinmu baki Waya .
? ? Nan ma sun amsa mata da amin. Daga haka HOD ya Wan ?ara mata bayani akansu. Kafin ya sallamesu kowa ya koma kan nasa aikin. Ita kuma suka nufi elevator tare da shi. Sai faman zuba mata surutu yake ita dai batace komai ba sai Wan murmushi da take masa na karar haWuwar farko. Conference room suka nufa kai tsaye daga nan. In da ta sami dukkanin shugabannin da alama su ake jira ma a wajen. Wajen zama duk suka nema, a dai-dai kuma lokacin CEO ya shigo AS Winsa biye da shi. Duk mi?ewa sukai alamar girmamawa, sai da ya zauna AS Winsa ya ajiye masa kayan hannunsa gabansa sannan ya Wan Wago ya dubesu. Zaunen suka kai suma a nutse, daga haka room Win yay Wan shiru na kusan mintuna uku kafin ya ajiye tab Win hannunsa da yake sarrafawa yay gyaran murya yana kallonsu cike da dakewa da nutsuwarsa. Suma sake nutsuwar sukai da maida hankalinsu garesa. Banda Maanal da tun kallon farko data masa a sanda yake shigowa ta Wauke kanta bata sake ba. Gaba Waya jinta take a takure a wajen dan su biyu ne kawai mata. Sallama yay musu kafin ya sauke dubansa ga tab Win gabansa ya fara magana acan ?asan ma?oshi.  Wannan taro ne daya haWa Sangarori guda biyu, wato na shugabanni da kuma ?ir?ira da zane na wannan company. Wato Executive Team da kuma Design and development. Kafin kai tsaye mu fara abinda ya kawo mu akwai sabuwar staff data shigo cikinmu zai ?yautu ta gabatar da kanta anan .
? ? ?? Ji Maanal tai kamar ta kai masa naushi dan haushi, amma sai ta dake ta?i koda motsi sai da CTO dake gefenta yay mata magana ?asa-?asa.  Sistet Maanal .
? ? ? ?? Komai batace ba ta mi?e cike da kamewa ta furta,  Sunana Maanal Habeeb Umar Giro. Junior Watch Designer in sha ALLAHU .
? ?? Sunyi welcoming nata baki Waya tare da mata fatan alkairi. Bayan ta koma ta zauna ya cigaba da faWin, makasudin shi wannan zaman akan sabon project namu ne in sha ALLAHU. Wasu sun san da shi wasu basu sani ba saboda rashin samun zaman meeting da ba'aiba a wancan satin gaba Waya. Akwai Companyn da zamu fitar ma sabon agogo, sun kuma bamu zaSi kafin mu sake zama dasu. Dan haka Design and development ko kuna da wani sabon design da zaku gabatar mana mu duba? .
? ?? Bayan Maanal akwai Watch Designers Directors har uku a wajen, sai dai dukansu kowanne nada iya limit Win aikinsa ta yanda baya shiga aikin wani. Hakan yasa Waya daga cikinsu Wagowa ya Wan dubi Boss Win.  E to Sir bamu san ko yaya tsarin project Win zai kasance ba. Sai musan a cikinmu wazai bada sample
? ? Kansa ya Wan gyaWa, sai kuma ya kai dubansa ga Sales and Marketing Manager. Da sauri ya mi?e dan yasan minene ma'anar kallon. Bayani yay a ta?aice, Dan haka sai duk suka maida hankalinsu ga Director Steven. Kansa ta gyaWa shima tare da maida kallonsa ga Maanal, suma sauran duk sai suka koma kallonta. Yanda suke kallon natane ya bata mamaki, kafin ta nema ?arin bayani Director Steven ya ce,  Wannan aikinki ne Sister Maanal. Idan kinada wani sample na zane a ?asa company na bu?atar gani, idan kuma babu zaki iya neman lamanin samarwa .
? ? Gaba Waya sai Maanal taji ma kamar zata daburce. Amma ta shiga ambaton ALLAH tare da aro jarumta. Cikin ?ar dakiyar da nutsuwar data azama kanta ta dole ta bata ta jinjina ma Director kanta. Sai kuma ta Wan kallesu itama ta fara bayani.  Zan iya gabatar da wanda ke a hannuna Win idan basuyi ba sai na sake wasu sabbi .
? ? ?? Cikin gamsu duk suka gyaWa mata kai, kafin boss ya gama shan ?amshinsa batare daya kalleta ba ya furta,  Zaki iya nunawa .
? ? Bata tanka ba, sai dai ta mi?e hannunta Wauke da flash drive data naWe zanen Wazun da tayi. Amsa Director Steven yayi a matsayinsa na shugaban sashenta, ya nufi ?aton television dake kusan bango guda a room Win yay connecting, atake Wan tambarin data saka na farko mai Wauke da zanen agogo mai ?yau da zanen fuskarta a tsakkiya ya bayyana. Remote Win Director Steven ya mi?a mata, dole ta fito daga inda take tsaye ta koma gaban tvn. A nutsenta ta fara danna hoto na biyu ya fito, agogone mai ?yau da tsari matu?a duk da kasancewar a zane yake. A take duk suka shiga ambaton,  Woow!! Woow!! a hankali. Shi dai boss kaimai baice ba, amma fa ya zubama hoton idanu yanda ya kamata, bayani tayi cikakke akan agogon da tsarinsa da nauyinsa. Sai kuma ta koma nuna sassan jikinsa da sunayen data basu da yanda yakama ace ingancinsu ya kasance. Da ?arshe tai bayanin yanda agogon zai iya bu?atar ingantaccen aiki kafin fitar da shi. Tafa mata suka shigayi tamkar conference room Win zai buga shima. Dan har ga ALLAH tayi matu?ar gama birgesu, tayi dukkan bayanin da har sauran Sangarorin zasu iya yi. Ashekaru kaf Winsu babu wanda bai bata fin shekara goma zuwa ashirin ba, dan itace ?arshen ?an?anta da ?arancin shekaru a cikin nasu, hatta da Wayar macen zata iya girmar Shahidah ma balle ita. Taji daWin yanda suka yaba mata duk da shi mai gayya da aikin baice komai ba dai. Sai da duk suka lafa itama ta dawo ta zauna a nata mazauni kafin yay ?ar gyaran murya.
? ? ??  Zamuyi nazari akan wannan Win, amma WD Maanal zata iya samar mana da wasu samples kamar uku bayan wannan daga nan zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu. Sai ku haWasu a sake tattaunawa .
? ?? Duk sun gamsu da hakan. Dan haka ba'a wani sake jan zancen ba taron ya watse. Shine ya fara ficewa a room Win AS Winsa biye da shi. Duk mi?ewa suma sukai hankalinsu akan Maanal suna sake jinjinama ?o?arin ta da ?arfafata. Itako sai wani Wan karen daWi take ji kamar ta ciji uwawunta. Ta ?ara ta fita a wajen ta kira Ammie ta bata labari, kai har RK sai yasha labari yau....

? ?? Koda Maanal ta koma office zaman wasu sabbin samples na zanen ta fara dan babu wasa batare data kula kowa ba. Garama Yaqub ya mata sannu da zuwa. Tayi nisa a aikin nata akai mudu knocking ?ofa. Batare data Wago ba ita dai taji sauran na magana da shi. Saurayine kamar su Yaqub da zai iya girmarta ita kam a shekaru, amma kasancewarsu oganninsa cike da girmamawa ya gaishesu. Sai kuma ya maida hankalinsa kan Maanal. Hakanne ya sata Wagowa ta Wan kallesa. Duk da tayi mamaki sai ta danne, ta amsa masa da kai. Bai damuba ya cigaba da faWin,  Sister Maanal kinada visitor .
? ??  Visitor? .
? Ta maimaita da mamaki. Sake tabbatar mata da hakan yay ta ha hanyar jinjina kansa. Ta Wan yi shiru kamar mai nazari tana wasa da pencil akan lips Winta sai kuma ta ce,  Okay ina zuwa .
? ? ? Da girmamawa ya amsa mata da,  Ai kamar Wan gida yake. Bari na masa iso . Bai jira amsarta ba ya juya ya fita. Ba'a rufa mintuna biyar ba aka sake knocking ?ofar. Zamanta ta gyara da veil Winta, yayinda hankalin su Zaharadeen duk yana akan mai shigowar. Yana buWe ?ofar ?amshin turarensa na rige-rigen fara iso mata a hanci, hakan yasa ta Wan Wago idanu ta kallesa. Murmushi ya sakar mata yana jingina da ?ofar tare da harWe ?afafunsa da hannayensa a ?irji. Sai kuma ya laluba aljihunsa ya ciro wayarsa ?irar kamfanin Samsung mai ?yawu da tsada ya shiga mata hotuna. Hararsa ta Wan yi tana mai girgiza kanta ta maida ga abinda take yi. Sai da ya gama dan kansa kafin ya kai du?e ya Wauki abinda ya ajiye a ?asa yana ?arasa shigowa da faWin,  Oh oh my queen Kinga kuwa yanda kujerar nan tai matu?ar dacewa da ke. Kin gama cika Watch Designer Maanal Winki Tawajena. Dan haka ina tayaki murnar shiga sabon Office. Amin afuwa dana kasance a late, tun safe naso nayi hakan uziri yasa ban zauna ba na koma asibiti. Naso tahowa da rana hakan bai yiwu ba kuma dai .
? ? ? Ita dai kallonsa kawai take yana tsiyaya surutunsa kamar yanda sauran ma ke kallonsa suna murmushi. Hannu ya shiga basu, suna amsa da sauri da kuma girmamawa dan sun san yana da wani babban matsayi da kima a companyn. Dai da ya gama gaisawa da su ya maido hankalinsa kanta yana fiddo cake mai ?yau daga cikin kwalinsa. Sai kuma ya tsitstsira abu a kansa kamar wata mai shirin hure birthday cake ya kunna masa wuta. ?auka yay ya zagaya ta inda take ya ajiye a gabanta sosai bayan ya tattare kayan zanen dake a gabanta ya Wauke su gefe........
'?



('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

?an NIGER 1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=؞?AJIYA A DUHU....=؞?_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



......... Bismillanku . Ya faWa idonsa akansu Zaharadeen. Sai kuma ya koma ga ?ofa yana faWin,  Kuma ku shigo .
Mamakine ya kamata ganin ma'aikatansu kusan su goma sun shigo harda AS Win Boss. Gaishesu sukai saboda kusan dukansu suna a sama da su. Da kai kawai ta iya amsa musu ita dai saboda al'ajabin RK. Daga haka ta juyo tana masa wani kallon. Ganin yanda ta zuba masa manyan idanun nata masu rikitashi ya wani langaSe kansa da marairaice fuska yana Wan du?owa gab da ita ta yanda ita kaWaice zata iya jinsa a maganar da zaiyi.  Please ki daina min irin kallon nan kina rikita min lissafi na ne .
? ?? Harara ta Wan sakar masa tare da janye idanun gaba Waya. Babu yanda ta iya da fitinar RK dole ta hure kamar yanda yake bu?ata, dan ya tabbatar mata idan batayi hakan ba babu inda zaije yau. Ganin yaja kujera ya zauna ga mutane ya cika musu office da su ya sata hurewar kawai dan kaWan kenan daga aikinsa ya zauna Win. Cake ne dai duk yanda yayi taci ta gutsira ta bashi a baki ?i tayi, sai ma tai kicin-kicin da fuska ta yanda dole ya ha?ura dan baya son yaga ta haWe masa ?ya?y?yawar fuskar nan tata damuwa yake shiga. Haka dole da kansa ya gutsira yaci ya mi?ama wanda ya gayyato da su Yaqub dake a office Win kowa ya yanka yasa a baki. Daga hakan nutsuwa yay sosai yay mata addu'oin fatan alkairi da nasara a wannan aikin, ita harma hakan yaso bata mamaki, yayinda sauran ke amsawa da amin.
? ? Bayan ficewar kowa ya wani zabga tagumi yana kallonta. Itako ta sake maida hankalinta ne a aikinta. Sai da taji kallon nasa na neman cutar da ita ta Wago ta kallesa tare da sakar masa ?ar harara, sai kuma tai masa nuni da su Yaqub da ido. Murmushi ya saki mai ?ayatarwa da gyara zamansa. Ita kuma ta maida kanta yay ?o?arin dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta.
? ??  Maanal .
? Har tsakkiyar kanta taji yanda ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login