Showing 210001 words to 213000 words out of 219361 words

Chapter 71 - AJIYA A DUHU COMPLETE HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

5208

haWin Yazeed da Maanal bazai haifar da Wa mai ido ba sam balle farin cikin da ake fata. Alhamdullah ya fahimceta shima dan jiya ya kwana ne yana auna abubuwa a ransa. Gefe kuma ga Ammie taje har Waki tana masa kuka da ro?o da magiya akan yabar batun Maanal da Yazeed Win dan ALLAH ya aura mata koma waye).
? ? ?? Bayan tattaunawa irin ta manya masu ilimin addini da sukaga duniya duniya ta gansu suka yanke rana har ma da sadaki a take. Dan yanda suka bu?aci ayi nan da sati uku zuwa wata guda sam Daddy baiyi musu ba. Duk da zuciyarsa cike take da rauni da tausayin Yazeed. Shi baima san ta yanda zai tunkari Yazeed Win da wannan batu ba. Gefe kuma shi kansa yana takaicin rashin wannan alkairi da yaso haWawa tsakanin jininsa dana Ammie. Wata irin tsanar Hajiya Yaya da Sabuwa yaji ta ?ara faWi a zuciyarsa. Dan wannan karon sun kaishi ma?urar da dole sai ya Wauki mataki a kansu kam......

_________&

? ? ?? A Abuja kam su Oum sun tadda AA cikin matsanancin Sacin rai da damuwa. Dan shima yaga wani kaso na abinda ke yawo a media Win tun jiya. Hankalinsa ya tashi matu?a, tare da tausayin kansa da Maanal. Yata ?o?arin gwada kiranta amma sai ya kasa. Hakama ya gwada kiran Mamy domin ya ro?eta ta cire takunkumin datai masa amma ya kasa. Dan yayi al?awarin koda soyayyar da yake ma Maanal zata kasance ajalinsa bazai taSa bijire ma Mamyn ba balle akai ga tona mata asiri a wajen mutane masu daraja da suke mata kallon girmamawa da mutuntawa. Koba komai ita Win mahaifiya ce, tanada babbar daraja a garesa, darajar da zai iya sadaukar da koma miye akan ta. SaSon UBANGIJI ne kawai Oum da Mamy da Abah zasu sakashi ya bijire musu, dan wannan kam har abada babu biyayya a tsakaninsa da su. Amma bu?ata takai da kai ta rayuwa koda zai cutu zai sadaukar, dan haka ya amincewa kansa ne zai auri Maanal kawai da amincewar Mamy dan itace kawai matsalarsa a yanzu. Hankalin Oum ya tashi, dan ya kafe shi kada a kira masa kowanne likita lafiyarsa ?alau. Lallashin duniya ya?i sauraren kowa, daga ?arshe ma yace shi zai yi tafiya ne zuwa gobe.
? ? ? Ita kanta Mamy yanayin AA Win ya bata tsoro, amma ta zaSi dakewa akan janyewa. Dan a ganinta ai dama sai anji wuya ake jin daWi, dolene tabi kowacce hanya domin dawo da yaranta hannunta. Abah kuwa ransa a Sace yake da AA, taurin kan yaron da kafiyarsa na zafafar ruhinsa. Dan haka ya tattara al'amarin AA Win ya watsar gefe, dan har gobe yana akan bakansa na har fa sai AA ya buWi baki da kansa ya ro?a a nema nasa auren Maanal bayan ita kanta yaje ya bata ha?uri da neman gafarata, ya kuma sanar masu dalilinsa na bijirewa a baya..........
'?


Oh-oh tarna?i kenan




09032345899




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=؞?AJIYA A DUHU....=؞?_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



______________


.........Washe gari kamar yanda AA ya faWa ya bar gidan batare da sanin kowa ba. Yayinda Abah ya samu kira daga baba Sardauna akan batun nemawa Rafeeq aure da sukai jiya a Kaduna. Tare da batun hukuncin da suka yanke akan AA da Najeeb suma. Dan haka a weekend Win da za'a shiga za'ai taron family na gaggawa. Duk da zuciyar Abah ta girgiza matu?a haka ya danne ya amsa da to, yayi kuma ALLAH ya sanya albarka. Baba na yanke kiran ya wani zube a kujera yana ambaton sunan ALLAH. A kuma dai-dai nan Oum ta shigo ta samesa tana hawaye da waya a hannu da alama itama dai ta samu batun kai kuWin Rafeeq Win gidan su Maanal kenan.
? ? ?  Gadanga ka gani ko, kaga abinda naketa son ka fahimta game da al'amarin nan ka?i ko. Ni Rafeeq zaima haka ya zagaye yaje yasa a nema masa auren Maanal? Auren Maanal fa, yarinyar da Ajwaad ke matu?ar so.....
? ?  So?!! ..
Abah ya katseta a fusace yana mata wani irin kallo. Cikin zafin rai ta cigaba da faWin,  So kike magana Fateema? To wane irin so Ajwaad kema Maanal? Lokaci yayi da zaki daina son kanki da yawa saboda soyayyar Wanki ta rufe miki idanu. Shin idan Rafeeq baisa an nema masa auren Maanal ba yaya kuke son yay muku? Ki gaya min shi Ajwaad Win bai san akwai ala?a tsakanin Maanal da Rafeeq bane? Tun a farko miyyasa bai Wauki matakin nuna masa yana sonta ba? Girman kai! Ko tsabar ya rainama mutane wayau ne? Ko kuwa ita Maanal Win bata san ciwon kanta bane? To wlhy bari kiji, kodai ku kama kanku ke da Wanki, kokuma ku haWu da fushina. Kuma wannan ya zama gargaWi na ?arshe da zaki sake zuwa min da wannan zancen. Kuma shima na bashi kwana uku kacal ya sanar da wadda yake so dan cikin weekend za'ai family meeting, idan ba hakaba duk Wadda aka zaSa masa wlhy, wlhy dole ya aura. Na gaji da case Win Ajwaad a gidan nan tunda bai san ciwon kansa ba, shi kaWai bazai cigaba da bani ciwon kan da ?an uwansa dake manya basa bani ba. Ke kuma kina biye masa saboda sonsa ya rufe miki ido.
? ?? Ya tashi fuuu ya fice daga falon ma gaba Waya. Wasu irin hawaye masu raWaWi da zafi ne suka shiga sakkoma Oum da gudu, ga jiri na neman zubar da ita a ?asa. Babu shiri takai zaune. Hayaniya take jiyowa kamar a gidan, jiki na rawa ta mi?e ko ganin gabanta batayi ma da ?yau ta fito tana faman haWa hanya....
? ? ? ??  Naga dai ya fito da jakka har ya saka a mota tun bayan dawowarku sallar asuba. Sai kuma ya sake cirewa ya Wauka yazo ya fita da ?afa. Amma wlhy ban yi tunanin akwai matsala ba duk da na fahimci ransa a Sace yake dan ko gaisuwata ma bai amsa ba.
? ? Wannan furucin kawai Oum ta iya ji daga bakin maigadi sanda ta fito daga haka ta silale a wajen. Sai farkawa tayi ta ganta a gadon asibiti su Fawzan zagaye da ita. Ganin ta buWe idanu duk sukai kanta, Babban Yaya da Fawzan na gefe da gefenta, a kallo Waya zakai musu ka fahimci sunyi kuka, dan idanun ?an maza duk ya kaWe. Hannayenta dake cikin nasu ta ?ara dam?ewa, sai hawaye sharrr, muryarta na rawa ta ce,  Fadeel Ajwaad, da gaske Ajwaad yabar gida? .
? ? ? ? Kai kawai babban yaya ya du?ar, hawaye na ciko masa idanu dan bai san amsar da zai bata ba. Sai ta juya ga Fawzan, shiko bashi da ?arfin zuciya irin tasu, sai hawaye sharrr, ?o?arin cire hannunsa yay daga cikin nata amma ta sake dam?esa.  Fawzan kuka kake kaima. Kodai na rasa Ajwaad ne, dan ALLAH ku gaya min. sai kuma ta shiga yun?urin tashi zaune. Da sauri suka maidata suka kwantar. Abah dake ta ?o?arin danne nashi tashin hankalin ya matso kusa da ita sosai ya zauna, cikin muryar lallashi ya ce,  Fateema ki kwantar da hankalinki dan ALLAH. Ajwaad fa ba ?aramin yaron da kike goyawa bane har yanzu. Karki manta shekara Wai-Wai har talatin ne da shi da Woriya. Duk ma inda yaje zai dawo....
? ?? Kuka Oum ta sake fashewa da shi tana faman girgiza kai.  Dan ALLAH kada kaimin haka Gadanga, ka dawo min da yarona. Kuma kun san Ajwaad nada lalura kada yaje wani waje ya shiga matsala. Wlhy bazan yafe muku ba bazan kuma yafema kaina ba....
? ? ? ? Kallo Waya yay mata ya kauda kansa gefe. Fin minti Waya sannan ya sake kallonta,  Nace ki kwantar da hankalinki, in sha ALLAHU a yau zai dawo gida, dan na saka a binciko min duk ma inda yake ko ?asar nan bai isa bari ba a yanzu dan na saka an dakatar da komai nasa daga aiki, hatta account Winsa .
? ? Wani irin nannauyar ajiyar zuciya Oum ta sauke. Yayinda Mamy da takaici ya cika ta taSe baki a kaikaice. Ita har mamakin ?arfin halin Oum nan take a ranta, mtsoww wai su za'aima pretending. A zahiri kuwa itama matsawa tai kusa da gadon Oum Win ta fara lallashinta....

? ?? __________&

? ? ? ? A Kaduna kuwa bayan wucewar ba?i Daddy ya kira Ammie a waya, dai-dai nan itama Nene ta iso. A tare suka nufi sashen Daddy, inda yake tare da ?a?an Nene uku. Sosai Ammie tayi mamakin taron, amma sai ta danne suka gaisa. Babu wani Soye-Soye ko jan zance babban Wan Nene Yaya Nuhu ya mata bayanin komai. Duk da jin al'amarin kamar daga sama taji sanyi a ranta, har bata san sanda ta saki ajiyar zuciya ba. Sai dai ?asan ranta wani kalar abu mai nauyi take ji. Godiya ta dingama Daddy saboda fahimtarta da yayi ya janye batun Yazeed cikin sau?i haka. Gefe kuma tanama Maanal addu'a da fatan ALLAH yasa Rafeeq ya zama sanadin kwaranyewar damuwarta. Yasa kuma iyakar wahalarta kenan. Sun tattauna sosai game da tsaida bikin sati uku kawai da akayi, dan hatta da sadaki sun ajiye abinsu. Dan haka dai babu zama shiri kawai ya kamata a fara...
? ? ? ? A waya Daddy ya kira Maanal da Shahidah da Amaal suma. Shi da yaran Nene sukai musu bayani. Da ?arfi Maanal ta rumtse idanunta, cikin jarumta ta shiga kokawa da zuciyarta, yayinda take ambaton sunayen ALLAH har ta samu nutsuwar da take bu?ata. Ta kuma tunatar da kanta hakan shine dai-dai, shine kuma zai bata masalaha da kwanciyar hankali a wannan gaSar. Batace komai ba dai a gabansu, hakan kuma na nufin nuna alkunya da kowa yay zato. Sai dai hankalin Shahidah da Amaal harma da Ammie na kanta. Koda suka dawo sashen duk motsinta na a idonsu, amma a mamakinsu bata nuna wani reaction ba sam. Saima a mamakinsu yanda ta Wan warware daga kwanciya ciwon kwana biyun nan da take ciki tayi. Sai duk suka cigaba da mata addu'a a zukatansu, duk da ?asan ransu na jin tausayinta saboda sanin har yanzu tana son Ajwaad. To amma tunda shi bai nuna yanayi ba har yanzu basu da wani dalilin damuwa da son ganin sai ta aureshi ai...
? ? ? Washe gari suka shirya suka koma Abuja, suka bar Nene da Ammie da fara tsara shirin biki. Koda suka iso Abuja ma duk motsin Maanal a idon Shahidah ne, sai dai har suka kwanta bataga wani damuwa a tattare da ita ba. Washe gari kuma safiyar litinin, sukai shirin office yara makaranta suka wuce. Shahidahn da kanta ta ajiye Maanal a kamfani, ita kuma ta wuce nata aikin. Yau kam a kallo Waya su Zaharadeen suka fahimci Maanal Win a Manaal Winta take. Dan tun daga gaisuwa ko Yaqub bata sake kulawa ba ta shiga ayyukanta. Lokacin tashi kuma nayi tana a ?an farko na barin kamfanin. Washe gari ma haka tai musu, bata shiga sabgar kowa da komai, aikinta kawai ke kawota. Ko'a zaman meeting da sukai sau biyu dan kamfani na shirin fitar da agogon data zana ga ?an kasuwa a dakenta take. Sai kuma a meeting Win taji cewar CEO yayi tafiya, dan AS ne yay dukkan zaman a madadinsa. Batabi takan zancen ba balle ta nuna ya dame ta...

? ? ________&

? ? ? AA dai bai koma gida ba. Suna kuma da tabbacin yana a ?asar dan an hanashi fita. Amma an kasa gane inda yake. ALLAH sarki Oum duk ta fita a hayyacinta. Ita kanta Mamyn abin fa ya fara damunta. Sai dai tana ?o?arin ganin ta danne dan a ganinta AA nayin duk wannan abunne dan ta amince ya auri Maanal. Itako tana akan bakanta ko Oum zata mutu Ajwaad bazai auri yarinyar nan ba sai zaSinta. Ga batun meeting na family kwanakin na sake matsowa. Nibras ma ta matu?ar tada hankalinta, duk ta rame bata da aiki sai kuka. Yayinda Babban Yaya da Fawzan suka kasa zaune suka kasa tsaye sunata kai kawon binciko inda AA Win ya Soye kansa batare da sanin Abah ba. Matsalar da aka samu ya rufe duk wayoyinsa ma ta yanda baza'a sameshi ba. Sai a safiyar alhamis babu zato kawai sai gashi ya dawo da kansa. Baki hanci idanu duk maigadi ya saki yana kallonsa, shiko cike da basarwa ya ja box Winsa yay ciki, dan taxi ce dama ta ajiyesa. Kai tsaye kuma sashen Oum ya nufa, su kansu masu aikin sashen Oum Win daya shigo duk sai da suka shiga shock. Suma bai kulasu ba balle amsa gaisuwarsu, sai tambaya daya jeho musu akan ina Oum. Baki na rawa suka bashi amsa da tana sama dama duk mutanen gidan bata da lafiya.
? ? ? Saman ya haura zuciyarsa na wani kalar bugawa, ko kallon Saheeba da Nibras dake a falo suna shirya abinci a dining baiyi ba nan ma, kai tsaye bedroom Win Oum ya nufa, shigar sautin muryarsa da yay sallama ya sakasu juyowa gaba Wayansu lokaci guda suna kallonsa. Yayinda shi kuma nashi idon ke akan Oum datai wata zabura har tana ture hannun Babban Yaya dake bata abinci, abincin daya Wibo a spoon ya zube musu a jiki ita da shi. Hawaye ne suka ciko idannunta dake kallonsa, ta nunashi a hankali lips Winta na rawa.  Ajwaad! Da gaske kai ne ka dawo? Ko mafarkin dana saba yi ne Fadeel? .
? ?? Kafin wani ya samu bata amsa AA da nasa idanun suka kaWe ya shiga takowa a hankali, gefenta ya zauna tare da kwantar da kansa a kafaWarta, cikin wata irin murya mai rauni sosai ya furta,  Oum ki gafarceni. I miss you, really really miss you . Sai kawai ya kife kan nasa a kafaWar tata, tana mai jin damshin hawayensa na sauka mata. Itama sai hawayenta suka shiga sakkowa a guje, tasan a duk duniya abinda zai saka Ajwaad Winta hawaye ba ?aramin abu bane ba. Gefe Mamy ta kauda kanta, zuciyarta na mata wani irin ?una, jitai sam bazata iya daurema zaman Wakin ba, sai kawai ta nufi hanyar fita. Da sauri Nibras da Saheeba da suka biyo bayan AA suka bata hanya ta fice.
? ? ? ? Abah kam ajiyar zuciya kawai yake faman saukewa da godema ALLAH. Dan shi kansa kwana biyun dannewa kawai yake yi, amma yana cikin matsananciyar damuwa akan batun AA Win da halin da Oum ke ciki. Yana dannewa ne kawai baya nunawa a zahiri. Su kansu su babban Yaya tausayin Autan nasu ne ya sake shigarsu, duk da suna jin haushin abinda ya aikata Win. Bayan AA ya Wago ya share hawayen Oum ya juya yana bama Abah da su Babban Yaya ha?uri suma. Babu wanda ya nuna masa komai dan a ganinsu babu amfanin hakan, tunda har ALLAH ya dawo musu da hankalinshi gidan batare da ankai wani mataki ba ai Alhamdullah. Dan danan sai ga Oum ta ware kamar ba ita ba, taci abincin sosai tasha magani. Shima kuma ta tsareshi yaci abinci dan duk ya faWa nata a ido.
? ? ? Sai da komai ya nitsa yaje sashensa har yay wanka sannan Abah ya zauna da su, AA ya sake bada ha?uri tare da neman gafarar su, musamman Mamy data nuna fushin ta a fili, harda tabbatar da cewar wai tana fushin ne saboda halin daya jefa Oum a ciki. Al'amarin Mamy na bama AA mamaki da tayar masa da hankali, shin wace irin zuciya ce da ita? Miyasa ta zaSi irin wannan rayuwa ga waWan da suka aminta da ita. Miyyasa shi ta yarda ta nuna masa ainahinta sauran ?an uwansa kuma ta?e musu lulluSin biri da mahaifinsu da Oum? Amma ba komai, yayi al?awarin cigaba da rufa mata asiri, da mata addu'a da nasiha ko hakan zai sa ta gane, dan har abada baya fatan ace Oum da Abah sun gane wacece Mamy, ya tabbatar zuciyar Oum zata iya bugawa.
? ? ? Nasiha sosai Abah yay musu daga ?arshe ya Wakko batun zuwansu Kano da batun kai kuWin auren Rafeeq gidan su Maanal. A mamakin kowa sai sukaga AA yayi murmushi mai sanyi, babu alamar damuwa a tare da shi ya ce,  ALLAH ya sanya alkairi .
? ? ? A firgice Oum data kasa daurewa ta ce,  Ajwaad! Maanal fa akace an kaima kuWin aure, kuma Rafeeq? .
?? Kansa ya jinjina batare da ya yarda ya kalla kowa ba ya ce,  Eh Oum naji, Rafeeq mutumin kirki ne ai, na tabbatar zai ri?e min ?anwata da mutuntawa, dan haka ina musu fatan alkairi .
? ? ? Babu wanda baiyi mutuwar zaune ba a falon. Baki sake Abah da Oum suka kalla juna, hakama Fawzan da Babban yaya kallon AA Win kawai suke. Mamy tai ?asa da kanta tana sakin wani Soyayyan murmushin cin nasara, koda suka haWa ido da AA sai ta lumshe masa ido. Kansa kawai ya maida ya Wu?ar...........
'?


09032345899

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=؞?AJIYA A DUHU....=؞?_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



______________



.......... Nifa wannan yanayin na Ajwaad ya fara bani tsoro babban Yaya. Anya babu abinda ke damun yaron nan? Ko wanda bai san ala?ar baya data shuWe tsakaninsa da Maanal ba ya kalli idanunsa yasan akwai soyayyar ta a ciki, amma batun aure ya?i ya amsa. Wannan abu na birkita min tunani .
? ? ?? Nannauyan huci Babban yaya ya furzar, idanunsa akan Fawzan ya ce,  Bakai kaWai ba, ni kaina a wannan gaSar zuciyata ta fara shiga nazari. Fawzan mu dukanmu mun san soyayyar Maanal

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login