Showing 72001 words to 75000 words out of 219361 words

Chapter 25 - AJIYA A DUHU COMPLETE HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

5199

yay wucewarsa ya barsu....

? ?? & && &

 Baby anya kinyi murna da dawowata kuwa? .
? ? RK dake kallon Maanal cikin wani yanayi ya faWa murya a raunane. Karo na farko ta Wan dubesa, sai kuma tai murmushi da bata cika yi ba. Shi kansa saida ya lumshe idanu saboda yanda murmushin nata ya wani ratsa masa zuciya. Idanunta ta Wan janye daga kallonsa ganin yanda yake wani ?an?ance nasa idanun.  Daga dawowa zaka fara rigimar taka ko . Ta faWa ?asa-?asa batare da tunanin zai jita ba.
? ?? Amma a mamakinta sai taji ya saki ?aramar dariya da faWin,  Oh ashe kallon rigimamme ake min ni Rafeeq .
? ? ?? Murmushi kawai ta sake yi batace komai ba. Shima sai ya tada motar suka fice a kamfanin. Sun Wan yi nisa da tafiyar yanata mata labarin inda yaje. Ita dai bata cewa komai shi kuma bai damu ba. Sai da suna gab da shiga anguwar su Shahidah tace masa,  Yaya jikin Aunty kuwa? Ka?i dai bani address Win naje na dubata .
? ? ? ??  Ayya! Amin afuwa gimbiya. Kin san tafiyar nan ce da babu shiri kawai ta kawo tsaikon. Amma idan babu damuwa gobe idan ALLAH ya kaimu dai ki shirya nazo muje bayan sallar magrib .
? ?? ?an jimm tai sai kuma ta ce,  Okay ALLAH ya kaimu, zan dai fara sanarma Didi yanda tace .
? ? ?  Ba damuwa hakan ma yayi . Ya ?are maganar dai-dai yana horn a ?ofar gate Win. Da sauri maigadi ya wangale ?ofar bayan ya le?o yaga shine. Sun saba sosai saboda RK akwai sau?in kai ga ?yauta, da wannan halayen nasa yake saurin saye zuciyar mutane da yawa. Mutum ne mai sau?in kai matu?a, da wahala ka zauna da shi bai shiga ranka a lokaci Waya ba. Sai da ya gama dai-daita parking idanun Maanal suka sauka akan motar Yazeed. Motar ta zubama idanu na tsayin sakanni, sai kuma ta buWe ta fito. Shima RK Win fitowar yayi hannunsa Wauke da ledar da bata san da ita ba, sai lunch box Winta daya haWa ya Wakko. Ganin inda take kallo shima sai ya kalla wajen, a take fara'ar fuskarsa ta canja, har zai mi?a mata kayan dan baida niyyar shiga ciki amma sai ya fasa. Cike da basarwa yace mata,  Muje .
?? Kallonsa tayi, sai ya Wauke kansa. Baki ta buWe kamar zatai magana amma sai ta fasa, dan ta tabbatar sai ya shiga Win tunda yaga Yazeed Win na ciki. Ita kam bata san yaya zatai da wannan mutanen ba ?an rigima. A tare suka shiga falon tana gaba yana biye, Yazeed kuwa na zaune tare da su Barrah kasancewar yau babu islamiyya alhamis ce. Tunda ta shigo shima idonsa kyam a kanta, sai dai yana ganin RK ya tsuke fuska. Jitai kamar ta fasa ihu, amma ta daure dai ta ?arasa, sannu da zuwa tai masa tare da gaishesa. Shima RK sai ya mi?a masa hannu a Wage. Shima Yazeed Win a Wagen ya bashi nashin suka gaisa sama-sama. Daga haka RK ya kai zaune yana janye ra'ayin su Haneeff. Shi kuma Yazeed sai ya maida hankali ga Maanal duk da dai yanzu babu fara'ar data shigo ta Wan gani a fuskarsa. Dama dai can shima Win kamar ita ne ba gwanin fara'a bane ba.
? ? ? ? Magana Yazeed Win ke mata ?asa-?asa tana bashi amsa cikin yanayinta na rashin son magana. Yanda RK ya maida hankalinsa akan shirmen su Barrah sai ka Wauka bai damu dasu ba, sai dai gaba Waya kunnesa da hankalinsa na akansu. A haka Shahidah tai sallama ta shigo falon. Wata irin ajiyar zuciya Maanal ta saki acan ?asan ma?oshi, kamar an saita sai ga Huznah itama ta shigo, sai dai ita tana cin karon da Yazeed tayi wani turus na Wan firgici, shima Win kallonta yake da mamaki. Cikin Wari-Wari ta gaida shi gefe kuma tana satar kallon RK da tunda yay mata kallo Waya ya Wauke idanunsa ya maida ga Maanal. Amsa mata Yazeed Win yay da faWin,  Ke daga ina haka? Yaushe kika zo Abuja? .
? ?? Daburcewa Huznah tayi, dan duk fitsararsu suna tsoron Yazeed kasancewar baya Waukar raini dukansu uban kowa yake ci a gidan. Cikin Wan sar?ewar murya ta buWe baki zata masa bayani Shahidah ta tari numfashinta.
? ??  Ayya yaya Yazeed zumunci tazo yi mana. Jiya ta iso zata mana hutu ne .
? ? Shahidahn ya kalla kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Da wannan Huznah ta samu ta gudu Waki cikin sassarfa. Maanal nason shigewa ta Wan watsa ruwa babu dama, sunzo sun sakata tsakkiya. Haka dole ta ha?ura har ALLAH yay balling ta akai kiran sallar magriba sannan suka mi?e dan zuwa massalaci. RK dai ya mata sallama alamar bazai dawo ba. Amma Yazeed baice komai ba, hakan ba nufin shi yana nan kenan.
? ?? Sanda ta shiga Waki baje-baje ta iske Huznah a gado tana waya. Sai ?yal?yala dariya takeyi. Komai Maanal batace da ita ba ta wuce bathroom. Daga cikine take Wan jiyo hirar Huznah Win.
? ? ? ??  Ai ki bari kawai guy Win nan ?arshe ne. Ga ?yau, ga aji, ga kuWi ga iya wanka. Kin san ALLAH yau jinai kamar na rungumesa.
?? Dariya ta ?yal?yale da shi alamar ana magana daga can, caraf ta cigaba da faWin,  Ai gara kam kuyi sauri ku kaini kada naja muku abin kunya a gari, wlhy har gida yasa aka kawoni a wata azababbiyar motarsa. Wa ai gobe ma komawa zanyi dan ya tabbatar da ?arfina na shigo ..
? ? ? ?? Kai kawai Maanal ta girgiza da taSe baki, sai ma ta Wauke hankalinta daga sauraren zantukan shirmen. Ita dama tasan ba banza ta kawo Huznah Abuja ba, ashe kuwa namiji ta biyo. Kai wannan abun kunya dame yay kama mtsoww!.

__________&

? ? ? ? Washe gari sai ga Yazeed wai yazo kaita office da kansa. Rasama abin cewa Maanal tayi, tadai cigaba da cusa breakfast Win da Shahidah ta tsareta yi saboda shan magani. A haka yazo ya samesu. Ta gama shan maganin tana tattara kayanta sai ga maigadi yazo yana sanar mata ga RK yazo, wai ya kira wayarta switch off. Gaba Waya sai Maanal ma ta kasa motsi, idanunta cike da ?walla ta kai dubanta ga Shahidah da abin yama fara bata dariya. Dan ita kam Yazeed da RK Win yanzu dariya al'amarin nasu ke bata. Kowanne baya iya Soye kishinsa akan Maanal. Ta wani gefen kuma tausayi suke bata su duka ukun ma. Inda Yazeed yake Shahidah ta juya, sai ta samu wayam alamar ya fita.
? ?  Tofa, shi kuma Ya Yazeed yaushe ya fita .
?? Da sauri Maanal ta juya inda Yazeed Win yake, itama ganin wajen empty sai ta Wan waro idanunta tare da maida kallonta ga Shahidah.  Didi ina kuma yaje? .
? ? ?  Wajen abokin takararsa mana. Ai wannan samari naki Maanal na kula kowanne da zafinsa yake. ALLAH dai yasa a rabu lafiya kawai. Kinga muje kawai ni na saukeki da kaina sai a raba rigimar. Ya kamata ma su duka ki hutar dasu zuwa kaiki da Wakkokin nan dan na fahimci abin yana neman Waukar wata hanya ne a tsakaninsu .

? ?? Koda suka fito sun samu rayukan Yazeed da RK Win duk a Sace, kallo Waya Maanal tai musu ta wuce ga motar Shahidah tai shigewarta. Sai ita Shahidahn ce ta ?arasa wajensu. Maanal bata san mi yayar tata ta sanar musu ba, koda ta dawo motar kuma batai mata bayani ba ta tayar suka fice.
? ? ? ? ? Haka ta kasance a office babu wani walwala a tare da ita. Dan fuskarta tafi kowacce rana kasancewa a tsuke. Yau ma anyi zama tsakaninta da Marketing and sales manager, sai Head of operation da quality control manager, bayan sun gama meeting akai kiranta da mata tambayoyi akan dai wannan zane nata da company zai fitar. Yau ma da yake bata bu?atar kowa yazo Waukarta da wuri ta tashi. Ta fito harabar companyn hankalinta akan agogon hannunta tana kallon lokaci suka kusa cin karo da assistant Win CEO. Ha?uri ya shiga bata itama ta bashi. Ta raSesa zata wuce idonta ya sauka akan AA Darma Win dake tsaye shi da wani dattijo suna magana. Yau dai sanye yake cikin farar shadda ?al datai masa shegen ?yau da sake fitowarsa a cikakken bahaushensa Wan arewaci dan harda hula. Da sauri ta kauda kanta tare da ?ara sauri a takunta duk da hakan bai hanata kasancewa a nutsenta ba.
? ? ? Sarai AA Darma ya ganta shima. Amma ya basar ya cigaba da maganarsa da Alhaji Wakili. Alhaji Wakili tamkar uba ne a wajensa, dan kuwa abokine ga mahaifinsu, sai kuma huWWar kasuwanci ta haWasu, dan yanzu haka ma akan wannan project da zasuyi wanda Maanal tai zanen agogon Alhaji Wakili Winne ya kawo mutanen....

?? Dai-dai Maanal ta fito gate Win da nufin samun abun hawa wata taxi ke ?o?arin shiga cikin Companyn. Sai dai securitys sun hana mai taxi Win shiga, sun tabbatar masa da dole wanda ke ciki sai dai ya fito ya ?arasa ciki da ?afarsa. Yanda aka buWe ?ofar motar a fusace ya Wan ja hankalin Maanal, a mamakinta sai taga Huznah ce ke fita a motar. Jitai ma gaba Waya ta ?ame a wajen ganin yanda Huznah Win ke musu masifa da tabbatar musu akanta zasu iya rasa aikinsu. Sukuwa dai securitys Win sunce bafa zasu bar mai taxi ya shiga ba dan dokar companyn ce hakan. Ko ma'aikatan wajen indai motar haya suka shigo ?a'ida anan suke sauka su ?arasa ciki da ?afarsu.
? ?? Ran Huznah ya kai ma?ura a Saci, kuma dole ta ha?uran ta sallami mai taxi Win ta ?arasa da ?afar zuwa ciki. Ga ma'aikatan sun fara fitowa sai kallonta ake ana ?us-?us, itako tana wani yau?i da taku Wai-Wai. Maanal dai tuni ta shige taxi Win da Huznah Win ta fita. Haka ta iso gida al'amarin nata mata kaikawo. Har jitai ta ?agara Didin ta ta shigo. Zuwa duba Auntyn RK yasata watsar da komai bayan tayi wanka ta shiga kitchen. Da taimakon Linda ta fara haWa cake da wasu ?an kalolin snacks da suka shirya zatayi dan dubiyar ita da Shahidah. Suna tsaka da aikin Shahidah ta shigo tare da yara data biya ta Wakko a makaranta yau da kanta. Dama haka take musu duk juma'a sai dai idan aiki ya mata yawane tabar driver ya Wakko su kamar yanda ya saba.
? ?? Joining Winsu tayi a kitchen Win, anan ne Maanal ke labarta mata batun Huznah. Itama mamaki sosai tayi Shahidahn, sai dai basu iya hasaso abinda ya kai Huznah Maawad company ba, har kuma suka kammala aikin bata dawo gidan ba. Dama ba kowa take sanarma zata fita ba, ko jiya Shahidah bata san da fitar tata ba hakama yau Win. Ganin har anyi la'asar RK bai kirata ba bai kuma zo gidan ba ta fara tunanin ko lafiya? Gashi ta riga ta Wauri niyyar zuwa dubiyar nan yau dai ta huta. Kuma jiya da dare ta sanar masa da anyi la'asar yazo ya kaita dan Didi tace bata yarda sai bayan magrib Win nan ba. Jitai kamar ta sharesa, sai kuma dai ta danne zuciyarta ta tura masa gajeren sa?o, daga haka ta koma falo ta zauna dan ta shirya tsaf hakama Barrah da Haneeff da zasu mata rakkiya tsaf suke.
? ? ? ? Sai kusan huWu da rabi RK ya iso gidan, yana sanye da shadda shima yanzu ruwan zuma harda hula. A ranta ta Wan taSe baki da faWin (idan anga kuna wankan shaddoji sai juma'a kawai) a fili kam tayi kicin-kicin da fuska daga gaisuwa bata sake kulashi ba, dan shima dai fuskar tashi yau babu walwala. Da alama tun fushin safen ne bai gama sakinsa ba........
'?



('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

?an NIGER 1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
=?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=؞?AJIYA A DUHU....=؞?_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



........A motar ma gaba Waya sai ya maida hankalinsa akan tu?i da surutun su Barrah ya shareta, itama dai hankalin nata naga duba wasu novels da Aneesa ta tura mata sunayen su. Tafiyar tasu ba wata mai nisa bace suka iso. Gidane daya amsa suna gida, dan ko'a cikin garin Abujar kasan mai shi yaci ya ?oshi. Sai da security Win ?ofar yazo har inda suke yaga waye sannan ya danna remote Win hannunsa gate Win fari tas ya zuge kansa. Godiya RK ya masa tare da shigewa cikin katafaren gidan daya yalwatu da shuke-shuke masu matu?ar ?ayatarwa da bama zuciya nutsuwa. Kafin yau Maanal na jinjina girma da tsaruwar gidan Daddy, hakama gidan Didinta Shahidah gidane mai ?yau da ?awa. Sai dai gidan nan ya matu?ar disashe mata waWan can da take tunanin babu kamarsu. Hatta da parking space a tsare yake anan.
? ? ?? Tunda suka fito su kansu yaran ke bin ko'ina da kallo baki a buWe, Haneeff dai daya kasa ha?uri matsowa yay kusa da Maanal cikin raWa ya ce,  Mie-mie! Uncle R house ya haWu kamar ba'a Nigeria ba .
? ? ? ? Kasa cema yaron komai tayi, sai hannunsa daya ri?o nata ta Wan matsa kaWan. Dai-dai nan RK dake tattaro kayan tsarabar da bai san ko minene ba ya juyo garesu. ?aramin murmushi ya mata ganin yanda take binsa da kallo, batare da yace komai ba ya nuna mata hanya alamar suje, tare da kama hannun Barrah. ?auke kanta tayi kamar bata fahimta ba, sai ya sake sakin murmushi yay gaba, dan wannan yana Waya daga cikin halayenta dake matu?ar birgesa. A gidan sassa ne har kusan shida. Kuma kowanne da tsarinsa, sannan tsakaninsa da Wan uwansa akwai ?ar tazara ta yanda baka isa sanin mi nacan keyi ba, ko shi yasan mi kakeyi a naka part Win.
? ?? Part na tsakkiya a hannun dama suka nufa, RK ya danna bell tare da Wan juyowa ya kalla Maanal.  Ni dai kar aje ana fushi dani a gaban Aunty na . Yay maganar yana kashe mata ido Waya. Harararsa ta Wan yi kawai, tare da Wauke kanta. Shi kuma sai ya sake sakin murmushi. Zaiyi magana aka buWe ?ofar. Matashiyar budurwa ce da bazata wuce sa'ar Maanal ba, cike da girmamawa ta Wan rissina tanama RK Win sannu da zuwa. Duk da jikinta fes yake cikin tsafta a kallo Waya zaka fahimci mai aiki ce, sai dai masu aikin ma irin wanda ke samun kular nan dan babu wani nakasu a tare da ita. Kayan hannun RK Win ta amsa, yayinda shi kuma cikin dakewa kamar bashi ba yake tambayarta  Aunty fa!? .
? ? ??  Tana upstairs....
?? Kansa kawai ya jinjina mata, batare da yace komai ba suka ?arasa shiga cikin falon da yasha black & golden color na kujeru da labulale, sai wani irin ?amshin turaren wuta ke tashi mai ratsa zuciya. Ga sanyin ac mai kashe jiki. Gaba Waya jikin Maanal sai ya ?ara sanyi. Bata sake tsinkewa da al'amarin ba sai da ya danna wani maSalli ?ofar glass Win dake kamar bango guda ta zuge kanta suka shigo wani falon, nan kam komai golden yellow & white ne, shima dai babu kowa sai ?amshi dake tashi, wayar da yake dannawa ya kai kunnesa, ba'a wani jima ba aka Waga.
? ? ?  Aunt mun iso . Ya faWa cike da girmamawa. Maanal dai data zama kamar wata gunkiya bata san amsar da aka bashi ba taga ya juyo ya kalleta da murmushi, sai kuma ya furta,  Okay gamu nan . Yana yanke wayar.?
? ??  Sorry muje tana sama .
Ya sake faWa idanunsa akan Maanal Win. Kanta kawai ta jinjina masa batare da tace komai ba. Sai dai tana mamakin ta ina kuma zasu bi zuwa saman dan bataga hanya ba sam anan. Amma a mamakinta sai ya nufi wata ?ofa da su, anan ne taga ?afar benen da shima aka ?awata matu?a, dan hatta a ?asansa ma wasu kujeru ne guda biyu aka tsara da gani wajen zaiyi daWin hutawa. Haka dai suka haura upstairs Win Maanal na sake jinjina jin daWin da masu hannu da shuni keyi a ?asar nan. Dole su manta da talaka, dole talaka yasha wahala dan bataga ta yanda za'a iya tunawa da rayuwarsa ba anan. A sama ma wani tsararren falon suka samu, wanda aka ?awata da ash color na kujeru dama labulalen, nan Win ma dai ?amshin turaren ne yay musu sallama da sanyin ac kaWan, sai kuma nutsatstsiyar muryar dattijuwar dake musu lale marhabun cike da ?asaita. Kasancewar RK ya rufe Maanal yasa bata ganin dattijuwar itama bata ganinta, sai dai muryar ta wani irin dakar mata ?irji.
? ? ?  Rafeeq ?aniyarka, dalla gyara ka wani rufe min ?anwar tawa bana ganinta .
? ?? Dariya RK yayi tare da matsawa gefe yana faWin,  Oh Aunt ni yau baki son ganina kenan? .
? ? ? ? Baki ta buWe zata bashi amsa amma sai ta gagara hakan, sakamakon saukar idanunta akan Maanal da ita nata idanun ke kallon ?asa, dan RK Win na matsawa daga rufetan da yay ta rissinar da idanunta saboda yanda bugun zuciyarta ke ?ara ?arfi. Ga wani irin yanayi mai wahalar fassara dake ratsata. Hakama zuciyarta ta mata nauyi matu?a a cikin ?irjinta.....
?? Gaisuwar Barrah da Haneeff ce ta katse dattijuwar daga kallon Maanal, ta saki ajiyar zuciya da sakin murmushi tana mi?ama yaran hannu da faWin,  ?anwata kinga ?araso mana, Bismillah zo gareni .
? ?? Sake motsawa zuciyar Maanal tayi a karo na babu adadi, dan Muryar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login