Showing 66001 words to 69000 words out of 219361 words

Chapter 23 - AJIYA A DUHU COMPLETE HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

5146

wuta yake kamar bamai ?ananun yara ba. Gashi da gani tana fama da laulayin wani cikin ne ma. Cike da girmamawa ta gaida Ammie kafin ta fita sai gata da ruwa.
? ? Ammie ta ce,  Amarya ai da baki wahala ba ma. Ina yaran nawa ko duk an wuce makaranta? .
? ? ?  Duk sun wuce shiyyasa ai muka samu lafiya Aunty, sai Ameen kawai yana barci ne .
? ?  A'a ai shima ko ya kamata a sakashi makarantar tunda naji bakinsa akwai surutu .
? ? ?? cikin dariya Amarya ta ce,  Sosai kuwa Aunty .
? Bayan Ammie ta sha ruwan ta fito, amarya biye da ita har Wayan sashen. Nan kam mace Waya ce, itama ta amshi Ammie da girmamawa da mutuntawa, bayan sun gaisa ta fito ta shiga wajen sauran suma su biyu. Daga haka ta shiga wajen Nene. A falonta ta sameta zaune ta baje kaya tanata lissafi. Sai wata dake gefenta tana tayata. Da mamaki Ammie ta furta,  A'a Saratu yaushe a gari? Nene shine baki sanar min munada da ba?uwa ba? .
? ?? Murmushi wadda aka kira Saratun tayi, yayinda Nene ta Wan taSe baki da faWin,  Zuwan nata ne dama ya sani nemanki, tunda ita dai fitinar gidanta bata ?arewa .
? ?  Tofa wani abunne kuma ya faru Nene? .
? ?  Humm Asiya ke dai cire mayafi a kawo miki abinci, ga waina can nasa tun Wazun aka sayo miki gidan Hajiyayye ALLAH yasa ma bata huce ba. Saratu Wakko mata .
? ? Kasancewar Ammie na son wainar sosai ta zauna taci, sai da ta ?oshi sannan suka fara maganar Saratun. Sosai ran Ammie ya Saci, tace bako zata bar gidan ba har sai sauran ?an uwanta sun dawo ai zama akan al'amarin Saratun, wannan karon dole su Wauki mataki akan mijin nan nata mara mutunci, dan bazasu yarda da auren duka ba. Bayan sun gama tattauna wannan suka koma batun nasu gidan, ita kanta Nene ta jinjina batun zuwan Huznah Abuja. Amma sai ta kwantarma Ammie da hankali akan ta barta taje Win, amma sun kira Shahidah sun gaya mata komai, sun kuma mata gargaWin ta sanya ido sosai. Ammie dai bata bar gidan nene ba sai bayan magriba da sauran ?a?an Nene huWu ringis suka dawo kasuwa suka tattauna batun Saratun. Da zata tafi sai ta wuce da Saratu can gidanta akan zata huta kwana biyu.

_________&

? ? ?? Washe gari ?an Dubai suka wuce domin haWo kayan lefe dana shagalin biki harma da kayan Wakin amarya. Itama Huznah ta wuce Abuja, sai dai abinda ya sake tabbatar ma da Ammie akwai wata a ?asa ko sallama Huznah batai mata ba. Sai bayan ta tafine uwar ta shigo tana cema Ammien tayi hakuri wai driver ne ya azalzali Huznah Win shiyyasa bata shigo ba. Murmushi kawai Ammie tai ta ce,  Babu komai ai ALLAH ya tsare hanya ya kaisu lafiya . Daga haka bata sake tofa komai ba dole Hajiya Basariyya Win ta fito tana taSe baki, dan taso ne Ammie ta biye mata su Wan yi gulmar ?an tafiya Dubai. Itama Ammien kuma ta ganota shiyyasa ta mata haka...

? ?? Maanal bata san wainar da ake toyawa ba. Da safe dai sanda Shahidah zata sauketa ne a office take gaya mata zuwan Huznah Win. Dan yanzu itace ke kaita, wani lokacin ta dawo a taxi. Tun randa AA Darma yay mata wannan gargaWin ta so yima RK magana, sai kuma wani ikon ALLAH ma a daren ranar RK Win yay tafiyar gaggawa har yanzu bai dawo ba. Dan itama a waya ya kirata ya sanar mata. Busy kuma da yayi sosai yasa ba koyaushe suke waya ba sai ya samu lokaci. Amma ya tabbatar mata bazai wuce kwanaki biyar ba. Yau kuma kwanansa huWu kenan gobe idan ALLAH ya kaimu take saka ran dawowarsa. Yazeed dai ne da yake yana garin yanzu kullum da dare sai yazo gidan Shahidah Win, dan da farko yaso ya mata fushi akan batun aiki wai bata sanar masa ba sai Daddy ya gaya masa, ha?uri kawai ta bashi da nuna masa ai Daddy Win dan ya isa da su ne su duka shiyyasa. Ya dai ?yaleta kawai, amma a ransa ya gama ?udirar wannan aikin sai ta barsa duk da yanada planing Win anan Abuja Win zata zauna ita ko anyi bikin su.
? ? ? A gajiye ta fito daga office Winta zuwa office Win Designer Director Win dake kula da aikin nata, har yanzu dai suna akan project Win nan daya haye mata. Bayan tayi knocking aka bata izinin shiga. Ganin yana haWa kaya alamar zai tashi ne a sanyaye tace,  Director badai zaka tashi bane ba? .
? ? Kallonta yay fuskarsa da murmushi, dan yanzu kam ta fara sabawa da su. Yanda kuma take girmamasu da bawa kowa hakkinsa da kame kanta yasa su jin ?aunarta a rayukansu.
? ? ??  Lallai ba?ya kallon agogo, bakiji yanda company yay tsit ba kusan duk an wuce ai .
?? Agogon ta kalla kafin ta sake dubansa, dan tabbas magrib tama kusa.  Ayya ALLAH ban lura ba. Dan ALLAH ka samun hannu a document Win nan, so nake yanzu na mi?asa office Win CEO idan ALLAH ya taimakeni da safe sai ya duba shi da wuri kafin zaman meeting .
? ? ?  Wayyo ba?ya jin tausayina ALLAH, kinji bayana kuwa ga Madam nata kira na yau birthday Winta. Amma kawo nayi sauri .
? ? Godiya ta masa tare da matsawa ta ajiye masa file Win, tana daga tsaye ya shiga dubawa. ?agowa yay ya dubeta cike da tsokana ya ce,  Anya ba kwanan nan zan baki kujerar nan ba Manaal Giro? Ke Win ?uruwace fa. ?an murmushi kawai tai masa kanta a ?asa dan iyakarta da su kenan, shiyyasa duk da yanda take girmamasun wasu ke mata kallon mai girman kai da faWin rai. Wasu a cikinsu duk sun ?yasa, sai dai kamewarta na zame musu barazana, ga kuma RK da kowa ya tabbatar budurwarsa ce a companyn yanzu duk da kuwa yau ne take cika kwanta na takwas a Companyn. Bayan ya saka mata hannun ta karSa tana masa godiya. Sallama ta masa ta fice, haka ya bita da kallo zuciyarsa na zallo. Tun ranar farko da sukama Maanal interview yarinyar tai masifar shiga masa rai. Abinda ya faru tsakaninta da Boss yaso taka masa birki, amma daga baya sai yaga kuma komai bai sake faruwa ba, sai sabon soyayyarta a zuciyarsa ya dawo fil, sai dai kuma Maanal babu sakin fuska........
'?



('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

?an NIGER 1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=؞?AJIYA A DUHU....=؞?_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



.......Ita kam koda takai file office Win Boss ta ajema AS office Winsa ta koma ta cigaba da aiki, dan akwai abinda take son kammalawa kafin ta wuce gida. Kiran sallar magriba ya sata ?arasawa sauri-sauri sannan ta tashi tayo alwala ta haWa kayanta ta kashe komai ta fito dan su Yaqub tuni duk sun wuce sai ita kaWai. Shiru babu motsin kowa duk an wuce. Sai offices Wai-Waine ?an over work irinta koma wanda suka fita ke'a buWe. ?ananun ma'aikata ma ta wuce kusan mutane huWu basu wuce ba, koda ta?fito harabar companyn ma motoci biyar kawai ta gani sai mashin biyu alamar na wanda suka ragene. Idanunta suka sauka akan motar boss. Janyewa tai tana taSe baki, shi dama ai yafi kowa iya over work, dan kullum shine ?arshen barin office. Masallaci ta nufa domin gabatar da magriba. Bayan an idar koda ta fito bata koma ciki ba, hanyar gate ta nufa abinta a ?afa. Street Win shiru babu yawaitar mutane a ?afa sai motoci, sai dai ko'ina akwai haske kamar kana wata ?asa ba Nigeria ba. Taxi nada wahalar samu a wajen kasancewar duk manyan ma'aikatu ne ata wajen, sai gidajen cin abinci da suma ba laifi suke da yawa ta wajen da shopping malls guda biyu dake can farkon shigowa. Tsoron kar dare ya sake mata ya sata cigaba da tafiya a ?afa tana jin nadamar kaiwa haka bata tafi gida ba, har Shahidah cewa tai zata aiko a Wauketa idan ta gama tunda tace ita karta biyo Waukarta yau tana da aiki amma tace mata a'a zata hau taxi. Tayo tafiya babu laifi zuciyarta ta fara karaya, dan ?afafunta sun fara gajiya. Mamakine ya kamata ganin ?ammata tsaitsaye kamar masu jira azo Waukarsu, amma abinda zai baka mamaki suna da yawa duk da kowanne yana tsaye ne shi kaWai ko su biyu. Cigaba tai da tafiyarta dai tana Wan kallonsu sai taji ana horn, da sauri duk hankalin ?ammatan ya koma wajen motar, wasu ma duk sun nufi motar ne, sai dai kuma mai motar bai tsaya ba ya cigaba da bin bayan Maanal ne ana kuma horn Win dai. Da sauri ta Wan ja da baya sakamakon shan gabanta da akai da motar, cikin wani irin Sacin rai ta Wago dai-dai mai motar na sauke glass Winsa. Babban mutum ne da a shekaru ma zai iya haihuwar su Shahidah bama ita ba, yana daga baya kwance driver Winsa a gaba, cikin tsareta da ido ya sakar mata murmushi. ?auke kanta tai da sauri ta raSa ta wuce wani irin Sacin rai na mamayeta. Jin an ?ara biyo bayanta da mota ana mata horn again ta tsaya cak, cikin matu?ar fusata da harzu?a ta Wago dan ta gama shirya yima tsohon banzar nan zagin ?are dangi, amma sai kawai taga motar boss ba wancan bane. Kafin ta iya haWiye abinda ke bakinta AS ya fito daga gaba, kai tsaye inda take ya iso, furkarsa da murmushi ya furta,  Sister Maanal bismillah ki shiga . Yay maganar yana mi?a mata hannu da nufin amsar kayan hannunta. Kai ta girgiza masa tare da janye hannun nata tana faWin,  Karka damu na gode .
? ? ? ? ?  Idan shi bai dace ba, inaga ni kamar zan dace tunda dama ni na fara tayawa . A bazata taji muryar tsohon nan cikin kunnenta daga bayanta. Jitai gaba Waya kamar ta daburce, ga zuciyarta na wani kalar bugawa da sauri-sauri har numfashinta na neman fara yin sama-sama. Babu alamar wasa ko ragi a tare da ita ta juya ga tsohon nan, hannu ta Waga da nufin nunashi a hankali taji saukar wani tattausan hannu ya ri?e mata yatsu, batare da cewa komai ba yaja hannun nata. ?o?arin fisgewa ta fara sai dai bai bata damar hakan ba har ya iso da ita jikin mota. Sai lokacin ta iya zuba masa manyan idanunta da suka kaWa, shima kallon nata yake cikin ido. Kusan minti Waya suna kallon juna kafin ya zare kayan hannunta tare da motsa lips Winsa a hankali ya furta,  Get in .
? ? ? ? Rasama mi zata ce masa tayi, dan sam babu ko Wigon wargi a fuskarsa. Yayi masifar yin kicin-kicin da ita kamar zatai aman wuta. Bai kuma sake cemata komai ba ya zagaya Waya side Win ya shiga mazauninsa ya Wauke kai. Dattijon Alhajin nan dake tsaye ransa a matu?ar Sace ya sake takowa inda Maanal take. Ai yana buWe baki zaiyi magana kawai ta shige motar, shiko AS ya rufe mata murfin ruf tare da kallon Alhaji fuska da murmushi ya furta,  Bye bye grandpa . Shima ya zagaya ya shige motar driver yaja suka wuce.
? ? ? Da wani irin kallon Sacin rai dattijon yabi motar da kallo, sai kuma ya jinjina kansa tare da cije lips da ?arfi ya koma tashi motar. Da sauri driver Winsa ya buWe masa ya shiga ya maida ya rufe suma suka bar wajen....

? ? ? ? Sosai Maanal ta takure jikinta waje guda, yayinda idanunta ke'a lumshe bugun zuciyarta kuwa gaba Waya ya sauya daga normal bugu. Ambaton sunan ALLAH kawai takeyi tare da ?o?arin danne kukan dake son kufce mata.
? ? ? AA Darma dake a gefenta kam tunda ta shigo bai ko kalleta ba. Gaba Waya ya tattara hankalinsa ne ga document Win hannunsa da dama shi yake dubawa kafin suga Maanal Win, koda yake bama shine ya ganta ba, AS ne ya ganta cike da mamaki ya furta (kai wannan ai Sister Maanal ce Alhaji Bukar ya tsare a hanya halan bata sami abin hawa bane har yanzu). Driver na tambayar AS wacece ita Win AA Darman ya daka masa tsawa akan su dakata, shine dalilin tsayawar tasu.
? ? ? ? A yanzun ma driver ne cikin Wari-Wari ya furta,  Sir! Zamu fara saukeka ne kafin a kaita? .
? ?? Shiru bashi da alamar amsawa. Sai da ya mula dan kansa batare da ya bar abinda yake ba ya bashi amsa a ta?aice.  Fara ajiye ta .
? ??  Okay sir. Sister ina muka nufa? . Ya maida akalar tambayarsa akan Maanal. Shiru bata amsa ba sai da ya sake maimaita tambayar sannan ta dawo hayyacinta. Cikin ?o?arin danne komai da yanayin nan nata na kamewa ta furta,  Samu waje kawai zan sauka na ?arasa a taxi .
? ? ? Kallon AA Darma drivern yay ta mirror Win gaba da tunanin ko zaiyi magana. Amma sai yaga ko kallon inda wani cikinsu yake bai yiba ma. Dan haka sai ya kalla AS cikin marairaicewa. Murmushi AS yayi tare da juyowa saitin inda Maanal Win take,  Please Sister Maanal bafa zamu ajiyeki ko'ina ba sai gida .
? ? ? Rasama mi zatace tayi, sai kawai ta faWa masa sunan anguwar a ta?aice. Bai gaji ba ya sake tambayar street, nan ma kamar bazata kula shi ba sai kuma dai ta faWa. Daga haka bata sake magana ba ta maida idanunta ta rufe. Cikin ?an?anin lokaci suka iso abinka da lafiyayyar mota a saman lafiyayyar kwalta. Shigowarsu cikin street Win ya sa AS sake mata tambayar inda za'a sauketa. A ta?aice ta ce  Nan ma yayi . Shi dai driver tunda ta?i faWar no Win gidan da zataje ai sai kawai ya samu waje ya tsaya abinsa. Itako ta kama handle Win motar ta buWe da nufin fita. Sai kuma ta Wan juyi domin Waukar kayanta da AA Darma ya amsa a Wazun akai rashin Sa'a shima ya kawo hannu kan kayan da nufin Wauke file Win daya Wora kawai ta ri?e masa hannu. Da sauri ta jiyo jin ta kama abu, dai-dai shima yana kallon hannun nasa da yaji an cafke. A tare suka dubi hannun sai kuma suka kalli juna. Maanal ta saurin yarfar da hannun tamkar wadda ta kama wuta, yayinda shi kuma ya wani irin dun?ule hannun nasa waje guda tare da dimtse lips Winsa da hakori tamkar zai kai naushi. Sauka Maanal Win tayi tare da zare kayan nata ta ajiye masa file Win batare data sake gigin kallon ko inda yake ba taima AS godiya da driver tai gaba abinta ko waiwayen motar bata sake yi ba. Shima driver sai kawai ta tada motar suka wuce.
? ? ?? Tunda suka tafin AA Darma hannun nasa kawai ya zuba ma ido tamkar mai karanta wani abu a jikinsa ko cigaba da ganin hannun Maanal Win. Kamar ance ya kalla inda ta tashi idonsa ya sauka akan Wan abin hannunta da alama wajen yarfar da hannu da tai sanda ta kama nashi ya cire batare data kula ba. Hannu ya kai a hankali ya Wauka Wan hannun ya juya. Mai ?yau ne sosai kalar golden, an masa kwalliya da fararen stones, da gani ba wani mai tsada bane, amma yayi ?yau sosai. Yanda ya tsirama Wan hannun ido yana kalli da jujjuyashi haka su AS ke kallonsa zuciyarsu cike da gulma, suna ganin zai Wago suka kama kansu. Shi ko a cikin aljihun jacket Win suit Winsa na ciki ya cusa Wan hannun kawai ya gyara zamansa......

? ? ? Ni dai nace,  Hummm. Idan tayi wari dai maji>?*?
_____________&

? ? ? ?  Wai ni wannan yaron zaima gadara? Ni nan! Ni a garin Abuja .
?? Abokansa uku da suka zuba masa ido cikin mamaki Waya daga cikinsu ya ce,  Sen.. Bukar wai kai da waye haka? Ka shigo kamar wanda aka wancalo kuma kanata kai kawo da zantukan da bamu gane ba .
? ?? Tsaki mai ?arfi ya sake ja, sai kuma ya Wauka bottle na ruwa ya Salle murfin ya hau kwankwaWa. Tas ya shanye yay jifa da robar, kafin ya dubi abokan nasa Waya bayan Waya yana furzar da huci.  Wannan yaron Wan gidan Darma mana, lokaci yayi da zan koya masa darasin rayuwa. Saboda na fahimci tashen balagar iskanci ne ke Wibarsa da giyar ?an kuWaWen da yake gani ya tara kamar yaje dai-dai da kowa....
? ? ??  Halan AA!? Dan nasan shine tsageran cikin ?a?an Darma . ?aya daga cikin abokan nasa ya faWa shima cikin Sacin rai.
? ?  In ba shi Win ba sai wa? Wato wannan yaron shifa jinsa yake dai-dai da kowa yanzu a garin Abuja. Haka ranar Alhaji Badamasi yace min ya masa rashin mutunci. Wai yaje masa da business amma ya?i ?arSa harda gaya masa ba?ar magana. Tsageran cin yaron kullum sake ?aruwa yake yi .
? ? ? ?  Kufa daina Sata bakin ku, wannan yaron duk abinda yake Waurin ?ugu ya samu, ba daga kowa ba kuma sai Mr president, tunda ya Wauki mu?amin nan ya bashi yake jin kansa dai-dai da kowa. Sannan kaima kayi ganganci, da girmanka da mutuncinka a ?asar nan bama garin Abuja ba minene na sauka yima yarinya magana. Ko ?ar uban waye zaka aika a Wakko maka ita har gidane balle nasan bai wuce karuwan dake tsayawa a wajen bane ba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login